NOVELSUncategorized

MUTUM DA DUNIYARSA 65 – 66

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
             _(ya dace ya gyara kansa)_
                 *_Bilyn Abdull ce????????_*
                  *_[65➖66]_*   
…………Hajia hindu dai shirinta tai tsaf domin tafiya, Sai dai kuma ita kaɗai zata tafi bada yaraba, ƴan kuɗin da
ake tarama Abba na dubiya tasaka Kalifa yabi duhun dare ya lalubesu tas, shima saida ya ɗiba rabonsa sanan ya kawo mata sauran.
    Kafin ta kwanta kamar wasa ta gwada Number ƙaninta harisu kamar yanda ta saba, yaukam saiga waya ta shiga kamar almara, jikinta har rawa yake ta fara faɗin hello-hello tunkan a ɗaga. 
       Sai da takusa tsinkewa ne aka ɗaga wayar.
    Cikin mamaki tace, ”Wanene? Ina kuma mai wayar?”.
      Dariya yaron harisu yayi irinta basawa wadda harta tsorata Hindu, saida yayi mai isarsa sanan yace, “Wanan yakwana biyu a barzahu. Halan kece yayarsa da tai mana hanyar samun ƴan canji”.
    Zumbur hindu ta miƙe dan bata fahimci maganar tasa ta farkoba, tace, “Eh wlhy nice, tun washe gari nake nemanku a raba kuɗin amma wayar taƙi shiga, dan ALLAH ina harisun yake?”.
     Wani wawan tsaki yayi yace, “ke wai halan kanki baya kawo wuta ne, kajimin mumun mata, nace miki yana barzahu, bara na miki gwari-gwari danna kula ƙwaƙwalwar kifi gareki, dama Oga haris baizo amsar kuɗi danya raba dakeba, yazo amsane ya ware abinsa, shiyyasa ya saka miki Number busy yanda kokin kirashi bazaki samuba. Duk wahalar da mukasha wajen amso kuɗin nan muka wanke ƙafafunmu tundaga legas mukai masa rakkiya amma yay nufin cin amarmu, muko bazamu iya ɗaukaba, sati huɗu kenan muka caccake cikinsa da wuƙa muka aikashi gidan kowane shege da shegiya (lahira kenan), yanzu kema na ɗauki wayarkine danki daina wahalar nemansa ma, kisamu gobe kisa ai masa addu’ar uku data bakwai data arba’in, wainar da za’a bamu kirabama almajirai, muna miki gaisuwar ta’aziyyarsa fa, kuma karki damu sai da mukai masa salla kafin mu jefashi ruwa……”
    Ƙitt ya yanke wayar.
  Ihu kawai hajia hindu ta dage ta fasa, ta kware baki tana rusar kuka da kiran “Wayyo kuɗina, shikenan na mutu, Harisu ka talautani…”
    Wanan ihune yay sanadin tashin su Umma a barci, sukazo suka rufu akan hajia hindu ana tambayar miya faru?.
     Batareda tasan mi takeba tashiga sakin surutai akan yanda ta ƙulla makirci da haris aka amshe kuɗin Jiddah, harma da dukan da Abba yaci wanda gashinan ya zame masa sanadin doguwar jiyya.
     Wannan lamari yayi masifar girgiza su Umma da Abba dake cikin ɗaki kwance yana saurarensu, jiyay hawaye kawai suna gangaro masa, matar daya fifita fiye da kowace ta aiko masa ɓarayi? Wadda yay burin guduwa da ita suci kuɗin tare, dama abinda ta ƙulla masa kenan shiyyasa ta lallaɓashi subari sai da safe su wuce, tini wutar kan Abba ta ɗauke gaba ɗaya, yaji komai yamasa ɗif, bayajin sautin komai, baya ganin komai sai duhu, daga haka bai sake sanin inda kansa yakeba kuma.

************

      Washe gari Uncle yahya yasa aka kama hindu, dai bata cancanci cigaba da zama batareda ta fuskanci hukunciba.
    Abinda yabata matuƙar tsoro da mamaki shine ko damuwa su kalifa basuyiba, sai Munner ne kawai ke kuka da riƙeta.
      Abba kam saida aka kaishi asibiti, dan jininsa yayi ƙololuwar hawa sama.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


        Alhamdulillah ALLAH ya sauki Maimuna lafiya gabannin asubahi, sai dai tasha matuƙar wahala abin tausayi, ta haifi babynta Namiji mai kama da Sheikh Aliy masha ALLAH, bayan sun shiga sun dubata tana barci suka fito suka barta.
      Rige-rigen ɗaukar jariri akai tsakanin Aliyu da Jiddah, ALLAH yabama Jiddah damar karɓa, shiko ya haɗa da Jiddah n da jaririn duk ya rungume, Jiddah ta ɗago tana kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi ta furta,
     بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي الْمَوْهُوبِ لَكَ، وَشَكَرْتَ الْوَاهِبَ، وَبَلَغَ أَشُدَّهُ، وَرُزِقْتَ بِرَّهُ. 
      *_Barakal lahu laka fil mawhubi laka, wa shakartal wahiba, wa balagha ashuddahu, wa ruzikta birrahu_*.      
        _ALLAH Ya yi albarka ga abin da aka azurta ka da shi, kuma  Ya sa ka godewa wanda ya baka (shi), kuma Ya sa shi ya rayu har zuwa ga matukar karfinsa, kuma a azurta ka da biyayyarsa._
   
     Aliyu yakuma rungumeta yana amsawa da “Ameen ya rabbi Noorunnisa, nagode sosai, ALLAH ya kawomin kema ta tsatsonki”. 
    Murmushi kawai tayi tana sumbar goshin yaron, yanda takejin ƙaunar mahaifinsa haka shima takejin tasa ƙaunar.

★★★★★

         Tunda gari yay haske bayan Aliyu yadawo sallar Asubahi yafara sanarma Malam, daganan sai Aunty Ruƙayya da Aunty Siyama da gidansu Maimuna.
    Kafin kacemi labari ya gama zagaye dangi, zuwa tashin hantsi duk masu kusanci dasu sun iso asibitin, lokacin kuma Maimuna ta farka daga barcin datai na hutawa.
     Zuwa ƙarfe sha biyu aka sallamesu suka koma gida tareda babynsu abin sha’awa, fuskar Aliyu kawai zaka kalla ka tabbatar yana tareda tsantsar farin ciki. Addu’oi dai yaro ya shashi tuni har yamasa huɗuba da suna Muhammad. Maimuna kam yanda yaketa nuna mata tattali har kunya abun yake bata, duk mintuna kaɗan ya kirata yace ya jikinta da babynsa.

     Dukda Jiyyar Abba haka Umma ta fisge tazo tayi barka ita da maman sadiq, hakama su Aunty Nafisa tazo tayi, haka su aunty Hannatu duk sai da suka kira a waya sukaima Maimuna barka da shi kansa Aliyun.
    
*_Bayan sati ɗaya_*

         Ranar da yaro ya cika sati da haihuwa aka raɗa suna a masallaci, da yamma akayi walima.
     Su Jiddah ansha hidima, dan kuwa tayi lis da gajiya, tunda akayi haihuwarnan bata samun kanta, koda yaushe cikin hidima take, danma su Aunty Siyama na taimakonta da wasu ayyukan, da dare kuma Sheikh Aliy yay mata tausa har tayi barci yana jera mata sannu da saka albarka. 
     Washe garin sunan Maimuna ta koma gidan malam wankan jego badan Aliyu yasoba, ko Jiddah saida ta shiga damuwa, harda ƴar kwallanta kuwa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

        Bayan sati ɗaya da sunan yaron Maimuna aka shiga kotu da hajia hindu wanda tagama jigata da fita hayyacinta wajen kwalawa .
      Zan iya cewa wanan zaman kotu yazama silar tone-tone ne masu tada hankula, dankuwa hajia hindu bata ɓoye komaiba gameda yanda suka ƙulla karɓe ƙuɗin itada ƙaninta, sai dai tace ita batace su dokeshiba…….
    Kafin ta rufe baki wata murya a cikin kotun tace, “Ƙaryane, tunda kika iya shirya kasheni shima zaki iya sawa a kasheshi”.
      Gaba ɗaya jama’ar kotun juyowa sukayi domin son ganin mai maganar. 
     Zaune yake cikin ƙananun kaya, fuskarsa lulluɓe da hular rigar sanyi ƙatuwa dake a jikinsa. Babu mai ganin fuskarsa….
     Alƙali ya yanke shirun da faɗin kowaye mai maganar ya fito.
     Tunda ya taso kowa ya zuba masa ido, kansa a ƙasa babu mai ganin fuskarsa har yanzu, idanun hajia hindu kai kace faɗowa zasuyi ƙasa wajen son ganin wanene shiɗin?, sai zufa ke keto mata a kowanne sashe na jikinta.
      Bayan an nuna masa ya tsaya a akwatin kotun Alƙali yace ya buɗe fuskarsa.
     Wani murmushi yasaki kafin ya janye hular kansa fuskarsa ta dattijantaka alamun yanada shekaru ta bayyana. Ƙara hajia hindu ta ƙwalla tareda zubewa a sume, da sauri jami’ar tsaro taje ta yayyafa mata ruwa ta farfaɗo.
     Hajia hindu sai sambatu take tana faɗin “Wlhy karku aminta dashi fatalwane, na rantse da ALLAH ba mutum bane fatalwane.
      Banda murmushi babu abinda mutumin keyi, yayinda dukkan jama’ar kotun suka zuba musu ido sunason jin mike faruwa?.
     Tsawatarma hajia hindu Alƙali yayi, dan haka ta nutsu tana maƙyarƙyatar tsoro.
     Alƙali ya gyara zamansa yana faɗin, “bawan ALLAH kai ɗin wanene?”.
       “Da farko dai ya mai shari’a sunan SHAZALI, ni ɗan asalin garinan ne, anan natashi nai wayo har zuwa samartakata, bayanan ne nabar garin kano dalilin rabani da akai da ita Hindu aka aurar da ita ga wanina, takaicin hakanne ya sakani barin kano, amma sai sonta ya hanani sukuni a inda nake, hakanne yasani yin waiwaye adon tafiya, na dadawo kano rama abinda mahaifinta yaymin, dan iyayenta sunce bazan aureta bane saboda tantirine ni, gashi babu wanda yasan sana’ata, babanta ya haɗata aure da ɗan abokinsa badan tana sonshiba. Da wanan damar nayi amfani wajen jawo ra’ayin hindu muka cigaba da soyayarmu a ɓoye da auren nata, harma takaimu ga fara aikata zina. wataran mijinta yazo ya iskemu awanan halin, shine ya saketa, tareda ƙwace abinda suka haifa, amma sam yaƙi sanarma iyayenta abinda yasa ya saketa, saidai yace kawai zamanne ya ƙare. Wanan shine cikar burina daman, Hindu tacigaba da zaman zawarci a gidansu, yayinda nikuma na maidata tamkar wata matata, ana cikin haka wata hanyar samu tazo mini, banyi baƙin cikin jawo hindu jikinaba na biya mata makka. Tayi mamakin a ina na samu kuɗin, dan nidai tasan ko sana’a banida ita sai kame-kame. Amma koda ta tambayeni saina ɓata rai akan ta rainani, haƙuri ta bani taje ta sanarma iyayeta, Koda wanan magana taje kunnensu sai suka ƙaryata, musamman babanta, amma mamanta sai ta nuna murnarta har tana jifan baban hindu da kalmar yanama ɗiyarta baƙin cikin cigabanta. Wannan magana ta ɓata ransa yace ya zare hannunsa daga kan hindu da harisu ƙaninta dayazama ɗan iskan gaske. Bata wani damuba muka tafi saudia aikin hajji, saida mukaje can nake sanarmata ma’anar zuwanmu saudia, dan satar kuɗin jama’a ƴan aikin hajji zamu rinƙayi, da farko taƙi, amma dana kalamayeta da daɗin baki saita amince muka fara, kafin kacemi mun tara kuɗi masu yawa, duk abinda muka samu wani abokina mazaunin saudia yake amsa yana tura mana ta banki. Dalilin haɗuwarmu da Alhaji Zakari kuwa ɗakinmu ɗaya ni da shi, wataran sai naji Alhaji zakari yana waya da labarin miliyan hamsin dayaci a banki zai faɗaɗa kasuwancinsa, tunda naji wanan batu sai hankalina ya tashi, dan haka nasami hindu da batun na yarda su ƙulla soyayya da Alhaji Zakari dan muci kuɗin, da farko taƙi amincewa saboda tana sona sosai, saida nagama lallaɓata da daɗin baki akan ai muna tare bamu rabuba, kuma zamu cigaba da Mu’amularmu sanan ta amince. tashiga jikin Alhaji Zakari har suka ƙulla soyaya tun’a can, muna kuma dawowa aka ɗaura musu aure dashi, shirinmu shine bayan kamar wata ɗaya mu mallake kuɗin tasa ya saketa. Sai dai tun bayan aureta da Alhaji Zakari muna tare muna cigaba da mu’amularmu, cikin farko data samu nasan nawane tabbas, dankuwa inada hujjata, abin daɗi kuma saita haifi namiji kamar yanda Alhaji Zakari yake buri, wanan ne yakuma sakata ƙin yarda tarabu da Alhaji Zakari, nayi-nayi amma taƙi, sai dai tace mudai cigaba da tarayya, bazanyi takaici kojin kunyar faɗama duniya abinda basu saniba, abinda yasa zan faɗa kuwa danya zama izina ga ƴan baya masu aƙida irinta Alhaji Zakari yaro, dukda ƙyautar da ALLAH yay masa saiya bijire masa, ya manta ALLAH shike bada haihuwa ga wanda yaso, yakuma hana wanda yaso, sanan shike bayarwa daga jinsin dayaso, mutane da yawa zasuyi mamaki idan nace su Kalifa ba ƴaƴan Alhaji Zakari yaro baneba, indan kacire autansu dabansan sunansaba……..”
       Tuni kotu ta rikice da ƙananun magana, Abba kam yama daskare acikin WheelChair ɗin dayake ciki, hakama Uncle yahya dasu Umma da Jiddah.
    Alƙali ya buga gudumarsa alamar ayi shiru.
   Tsit kotun tayi aka maida hankali ga Shazali daya cigaba da faɗin,
     “Tabbas ƴaƴansa duk nawane, zama a iya gwada jinsu daduk dalilan da zasu tabbatar da hakan, bayan ta haifi ƴan biyu ne na matsa mata akan a kashe alhaji zakari mu kwashe kuɗin, amma sam sai tace bata yardaba, wai ba yanzuba, tabi ta tsarani da zance na yarda da ita. Sai dai danayi bincike saina gane wayo tamin, ni tama saka a kasheni saboda taci kuɗin ita kaɗai. Ban nuna mata na saniba har tayi ƙulla-ƙullarta a motata da nayi shirin yin tafiya a lokacin, daga baya muka canja komai na biya waɗanda tasaka su kasheni suka kaima babanta motar shi ya shiga ya mutu a lokacin. Daga baya bayan sunsha alhinin mutuwar babanta labari yazo mata nima na mutu, sai dai tana shirin samun dukiyar Alhaji Zakari itama ciki ya bayyana a jikinta, shine ta hakura saita haihu. To bayan haihuwar tatane kuma abubuwa sukaita faruwa ta gagara kashe auren ta gagara mallakar dukiyar tasa har wanan abun ya faru na ƙwatar kuɗaɗen Alhaji Zakari aka bama Alhaji Garba da ƴarsa, ta tura ƙaninta yaymusu fashi ya amshi kuɗin dan itama ta samu rabonta karta tashi a tutar babu, shine suka jibgi Alhaji Zakari saboda gardamar dayay musu, dama tace ko kasheshine ya kama ayi itadai kuɗin take buƙata, shikuma ƙaninta dama yajene da nufin amsar kuɗin ya hanata, nikuma na saka aka bishi aka amshe kuɗin shima aka kasheshi, dan nayi alƙawarin bazataci kuɗinba itama. Wanan bayanin danake muku duk ina samunsa ne ga direban gidansu, wanda ni yakema aiki tsawon shekaru ba tareda hindu ta saniba, na zaɓi zuwa na faɗi wanan sirrine domin Alhaji Zakari yasan ƴaƴan daya ƙwallafa rai a matsayin nasa to ɗayane nasa, ita kuma na nuna mata ramin mugunta ƙurarrene, ta gina kuma ta afka, sanan tasan ina nan a raye ban mutuba kamar yanda tayi fata”.
      Kotufa takuma ruɗewa da ihu, daga masu ALLAH ya ƙara sai masu faɗin maganin Abba kenan, sai masu tsinema hindu da shazali, Su Jiddah kam kuka suke sosai, dan ita kasama daurewa tayi tafito daga cikin kotun itada Umma.
     Da ƙyar Alƙali ya samu kotu ta nutsu, aka tambayi hindu abinda shazali ya faɗa gaskiya?.
    Batayi jayayyaba ta amsa da eh hakane tana sharar ƙwala.
      Alƙali ya yankema hajia Hindu hukuncin shekaru Ashirin a gidan yari, shikuma Shazali saboda kisa da yayi ɗaurin rai da rai.
    Ihu Hajia hindu take tana kururuwa, amma ba’a sauraretaba aka fiddata, shazali ya roki alfarmar abashi ƴaƴansa, dan sukaɗai ke gareshi a duniya sai mahaifiyarsa. Atake kotu tace ta bashi, mahaifiyarsa tazo ta amsa.
      Har aka wuce da hajia hindu da takoma tamkar mahaukaciya tanata sambatu su Uncle yahya basu iya motsawaba, saida kowa ya watse suka fahimci Abba a sume yake ma.
    Da gaggawa aka ɗaukeshi zuwa asibiti mafi kusa……..✍????


*_Abba kagani ba aima ALLAH wayo, kuma ba ai masa tilas_*.☹☹☹⛹‍♀




_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

????????karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*????????????????????????



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button