MUTUM DA DUNIYARSA 67 – 68

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[67➖68]_*
…………Kuka sosai su Jiddah keyi, tunda suke basu taɓa gamo da makamancin wannan rikitacciyar rayuwarba, bakuma su taɓa kawo faruwarta a
zahiriba sai yau, ashe abinda ke faruwa a films da hikayoyin marubuta yana faruwa a zahiri?.
Dafe kai Jiddah tayi saboda wani jiri dake neman kwasarta ƙasa, da sauri ta durƙushe a ƙasa tana toshe baki da hanci saboda wani warin magani daya doki hancinta.
Da hanzari Zarah da Walida sukai kanta suna tambayar lafiya? Hakama Uncle yahya, Umma nadaga tsaye tana kallonsu amma ta kasa koda motsa ƙafarta balle tazo garesu.
Da hannu tai musu nuni da Amai.
Zarah data fahimta tai saurin faɗin, “Yaya Jiddah Amai?”.
Kai ta ɗaga mata tana kuma danne bakinta dan gab yake da zubowa.
Kamata sukai da hanzari sukayo waje, bama su ƙarasa inda ya daceba tafarashi babi ƙaƙƙautawa, sauƙinma sunbar idanun mutane, sosai Jiddah ta galabaita, idonta sai lumshewa sukeyi, ga wani azababben ciwon ƙirji daya taso mata lokaci ɗaya, kafin kace mi tuni tagama fita hayyacinta, daganan bata sake sanin abinda ke faruwaba kuma.
★★★★★★
A hankali ta buɗe idanunta da sukai mata jingim saboda nauyi, ƙamshin turarensa ne yabata amsar shaidar yana kusa da ita, takuma ɗaga idonta da ƙyar takai dubanta gareshi, dishi-dishi take ganinsa.
Sheikh Aliyu da shima idonsa ke a kanta ya sauke ajiyar zuciya tareda kai bakinsa saman goshinta ya sumbata, hannunta dake cikin nashi ya matsa a hankali, kafin cikin sanyinsa ya ce, “Sannu Jiddatulkhair kinji, ALLAH yabaki lafiya”.
Bata iya cemasa komaiba, sai idanunta data maida ta lumshe hawaye na zirarowa ta gefen idonta.
“Ya isa kukan haka Hauwa’u, ki kwantar da hankalinki Abbanma ya farfaɗo, likitoci na Complain jininki ya hau, gashi kuma bake kaɗai baceba”.
Babu shiri takuma buɗe idonta tana kallonsa, kamarya ba ita kaɗai baceba? Kardai maganar dayaketa ambata mata kwanannan ace tazama gaskiya?. bayan tafiyar Maimuna wanka da kwana biyu saitaita fama da ciwon kai da jiki, ko tausar yay mata batajin ya daina, saiya fara cemata anya kuwa wanan ciwon nata bana ƙanin Muhammad ko ƙanwarsa bane? Ko kaɗan bata ɗauki batun da muhimmanci ba, dan itadai bayan ciwon kai babu abinda takeji sai ciwon jiki wanda take dangantawa da wanan hidimar haihuwar dasuka sha. Kwana biyu dayi mata wanan zance ya kasance da ita, tun a daren yaketa maimaita mata lallai tanada ciki, dan takuma canja masa gaba ɗaya. Ita maganarma kunya taita bata, taƙima yarda su haɗa ido balle ta yarda da maganarsa, yau kuma sai gashi yakuma maimaitawa, hakan kuma na nuni da cewar doctor ne ya faɗa musu………
Hawayen dayake share matane yasata dawowa hayyacinta, ta kama hannunsa ta riƙe tana kallonsa, “Abbu Muhammad ina Umma yanzun?”.
“Sun wuce gida, sabod Abba ya matsa akaishi gida”.
“Dan ALLAH mu bisu to, inason ganin halinda Abbana yake ciki ko zuciyata zata samu nutsuwa”.
“Kinga kiyi haƙuri, dare yayi yanzun kalli agogo ɗaya saura na dare, insha ALLAHU da safe zan kaiki idan kinji ƙwarin jikinki”.
“Ni wlhy na warke”.
“To naji ya isa haka bar kukan Umm Muhammad”.
Murmushi tayi badan ta shiryaba, a duk sanda ya danganta sunanta matsayin Uwa ga ɗansa tanajin wani sanyi a ransa, hakama Maimuna yanzu gaba ɗaya takoma kiranta Umm Muhammad, tana yaba karamcin waɗannan bayin ALLAH a ranta a kullu yaumin, tamusu kutse a zamansu amma sai suka jawo hannayenta suka riƙeta da zuciya ɗaya, itako mizatayi ta biyasu dashi?. Ajiyar zuciya ta sauke saboda abinda taji Aliyu na mata, ta riƙe hannunsa tana tura baki kaɗan.
Murmushi yayi ya janye hannunsa yana tashi zaune, itama ya taimaka mata ta tashi, da mamaki tabi ɗakin da kallo sanan ta kallesa. “Yaushe ma na dawo gida to?”.
“Ai tun bayan farkowarki a asibiti sai likita ya fahimci warin magani da Asibitin yakeyine baƙyaso, dan yunƙurin amai kika fara farkawa dashi, shine yakuma miki allura, a lokacin kuma Zarah ta kirani da wayarki a ɓoye, dan Uncle yahya ya hana a kirani a tadamin hankali”.
Jiddah tayi murmushi tanajin ƙaunar kawun nasu wanda takeji ƙaunarsa tamkar mahaifi.
Da taimakon Aliyu tayi wanka sanan ta rama sallolin dake kanta, da ƙyar yasamu tasha tea ɗin daya haɗa mata, tana gama sha ma ta amayar dashi.
Kallo ɗaya zakai masa ka hango tsantsar tausayinta a gareshi, ya gyara mata jikinta sannan ya kamota suka dawo ɗaki suka kwanta yana saka mata albarka da jera mata sannu.
*WASHE GARI*.
Da ƙyar Aliyu ya yarda ya kaita gwammaja kusan ƙarfe ɗaya na rana, dan kallo ɗaya zakai mata ka fahimci batajin daɗin jikinta, gashi takasa cin abinci, tace, “sai taje gida zataci awara”.
Kana doso hanyar shigowa cikin gidan zaka fara jiyo kukan Abba da sambatun da yakeyi, cikeda sassarfa Jiddah ta ida shigowa, dan Aliyu yana mota saiya jira tamasa iso, mamaki ya kama Jiddah ganin duk ƴan uwanta zagaye da Abba dake riƙe da hannun Umma dana Uncle yahya yana kuka. Yana ganinta ya saki hannayen su Umma ya miƙa mata alamar tazo gareshi, ganin lamarin take tamkar a mafarki, dan haka tai tsaye takasa koda motsi, aunty Zulai da suma suketa sharce hawaye tazo ta kama hannunta ta kaita gaban Abba.
Durƙushewa Jiddah tayi takuma fashewa da kuka mai ban tausayi tana faɗin, “Abbanmu kayi haƙuri, ka ɗauki hakan matsayin ƙaddar da bata goguwa a rayuwar ɗan adam, dama rayuwa tana tafiyane da jarabawa kullu yaumin…….”
Abba ya katseta shima cikin kukan, “Jiddah wannan ba ƙaddara bace kawai, akwai son zuciya irin nawa, na bitilcema ni’ima da rahamar da Ubangiji yay mini ta ƙyautarku, na wulaƙanta mata masu ƙyawawan zuciya akan abinda basuke badawaba, nakasa sauke nauyin da ALLAH ya ɗoramin na tarbiyarku da haƙƙokinku a matsayina na mahaifi, na yofantar da matata da ɗan uwana, na wofantar da karatunku inata bautama ƴaƴan wasu. Kaicona da dukkan masu irin halayyata a duniya, wlhy ƴaƴana inajin matuƙar kunyarku a rayuwata da tsanar kaina……..”
“Abba ka daina faɗar haka dan ALLAH, insha ALLAHU mu masu yafe makane, dan duk duniya bamuda kamarka, kuma bamu taɓa takaicin samunka a matsayin uba ba, sai dai abinda nakeson tuna maka Abba nau’in abinda ake samarwa a mahaifa na daga ɗiya mace ko Namiji ƙwan namijine ke badashi, sanan ALLAH ta’ala dai yace shine ya haliccemu baki ɗaya kuma ya sanyamu maza da mata domin musamu natsuwa da juna. Amma kuma seyace mafifici acikinmu shine wanda yafi tsoron ALLAH sannan kuma yace Maza sunada fifikon daraja akan mata saboda sadakin auren da suke biya dakuma ɗawainiyar ciyarda matan dasu mazan sukeyi, wannan kawai shine abunda yasa maza suka samu fifikon daraja akan mata. Amma kuma wannan baya nuna cewa su matan ƙasƙantattune kokuma basuda daraja. A’a akwaima matan da sunfi mazan daraja nesa ba kusaba kai akwai mace guda ɗaya wadda matsayintama yafi na mazanda suke rayuwa a duniya ayanzu dukkansu. Kukaranta ƙissar Maryam mamar Annabi Isa (AS) sadda aka haifeta se mamarta take cewa ai namiji ba kamar mace ba, tanuna bataji daɗiba dan ta haifi mace se nan take ALLAH yace shi yafita sanin abunda ta haifa, sekuwa gashi ya bayyana cewa wannan macen da ta haifa tafi duk mazajenda take tunani. Kaga kenan kasancewa mace ba aibu bane bakuma nakasu bane. Sannan Kaduba Nana Khadija uwar Muminai kuma kaduba Asiya matar Fir’auna kaduba irinsu Sayyidatuna Fatima ga irinsu Aisha dasu Ummu Shuraikh wadda saboda karfin walittakarta daga Aljanna kai tsaye aka miko mata ruwa tasha ta koshi, shin kanada wani namiji a yanzu wanda zakace yafi waɗancan matan daraja? Dan haka babu shakka maza da yawa masu wanan aƙidar suna kan kuskure, amma su sani kasancewa mace ba aibu bane bakuma gajiyawa bane, illa iyaka aduba tsoron ALLAH kawai da takawa, sannan idan kaduba sharhinda malamai sukaiwa hadisinnan na ANNABI (s.a.w) dayace ayiwa mata wasiyya da kyautatawa dakuma hadisin wanda ya raini mata biyu zuwa sama zasu kasance masa garkuwa tsakaninsa da shiga wuta, to waɗannan hadisan sun kore abunda mutanenmu suke faɗa, kuma su tabbatar da cewa mata sunada daraja, kuma suna daga cikin waliyyan ALLAH, sannan kuma ba kaskanci bane kasancewar mace, sannan kuma idan mace taji tsoron ALLAH to zata iya fin maza daraja. Malamai irinsu Zahabi idan kaduba Siyaru A’alamin Nubala yakawo tarjamar manyan malaman hadisi mata kuma shima daga cikin malamanshi akwai mata sunfi hamsin, sannan acikin Mizanul I’itidal yana cewa ba,a samu wata mace ba wadda tayiwa ANNABI (s.a.w) ƙarya, dan haka inkaga mace malamar hadisi to amintacciyace, ba’a tuhumarta da yiwa ANNABI ƙarya. Kai malamai dayawa sun ambaci falalar mata a wajaje daban daban saboda haka zamantowa mace babbar darajace matukar akwai imani da taƙawa, kuma acikin magabata akwai waɗanda har raba dare suke suna roƙon ALLAH akan yabasu ƴaƴa mata yabasu ikon musu tarbiyyah, wani kuma zuwa yake cikin danginshi yaroƙi su bashi ƴaƴansu mata domin ya rainesu, dan yasani cewa macece zaka raineta dandanan kasamu gidan aljanna, dan haka mata sunada falala sosai kuma duk mutuminda har yagama haihuwa be haifi maceba to yakamata ayi masa jaje. Amma koda ace mutum aduniya ƴa mace guda ɗaya tal ya haifa to wannan aimasa barka matuƙar ya iya jure tarbiyyarta. Mata babu shakka a musulinci sunada daraja sosai inhar sukaji tsoron ALLAH, sannan kuma duk wani malaminda kasani ya shahara a duniya to inka bincika zaka samu cewa mata sunyi ƙoƙari sosai a wajen tarbiyyarshi, hatta mamalan da suke karama juna sani daku anan idan da ace andaka ta iyayenmu mazane banda matan to da bamuzo kan wannan matsayinba. Kuje kuji tarihin Shafi’i mana ko Malik ko Abu Hanifa da Ahmad binu Hambal cikinsu wanene mace batai masa tasiba akan iliminsa? Imamul Bukhari albarkacin mace yazama abunda yazama a babin hadisi, hakaman Sibawaihi a fannin nahwu ya gagarane albarkan Mace. Ibnu Taimiya kuwa ai Taimiyar ma macece ba namijiba dan haka mata sunada tasiri sosai da amfani a rayuwa kuma duk wani wanda kaganshi a duniyarnan yana ƙafafa da tunƙaho to arziƙin macece, dan haka mata suma mutanene kuma banda sadaki da ciyarwa babu abunda maza suka daramu dashi. Amma kuma saurin kai mutum aljanna da saurin kaishi wuta to babu kamar mata, abu kaɗan zakaiwa mace ka samu aljanna kuma abu kaɗan zakayiwa mace katafi wuta. Kuma ana iya gane nagartan namijine tayadda akaga yana kulawa da matarsa da ƴaƴansa Abba”.
“Wlhy duk gaskiya kika faɗa Hauwa’u, nima son zuciyane ya lulluɓe ganina da jina, Yagana dolene na gode muku matuƙa keda yahya, ALLAH ne gatana kune gatana, kune kuka tsaya tsayin daki wajen ganin tarbiyyar ƴaƴana da haɗuwar kawunansu a waje ɗaya, ku kun kasance mutanen kirki ababen alfahari da kwaikwayo ga kowanne mutum, duk wanda ALLAH ya bama ƙyaƙyƙyawar zuciya irin taku yagama cin ribar duniya da lahira, dan girman ALLAH ku gafarceni akan kurakuraina kuda ƴaƴana, wlhy nayi nadama nayi nadama matuƙa……”
Daga Umma har Uncle yahya dasu Jiddah kuka suke suna faɗin sun yafe masa, suma ya yafe musu.
“Ba kuyimin laifin komaiba wlhy, koma kunyi mini na yafe muku tuni”.
Wannan rugun tsumi ya mantar da Jiddah Aliyu dake ƙofar gida, wanda shi tunima ya gaji da jiranta yashigo soron da nufin yin sallama, sai yaji kukan jiddah tanama Abba nasiha, hakane yasashi fahimtar akwai matsala kenan, saiya juya dan wannan ba huruminsa baneba ai.
Haka Jiddah ta yini a gida cikin ƴan uwanta batajin daɗi, awararma datasaka Walida ta sayo mata tanaci sai Amai, sosai tabasu tausayi sukaita jera mata sannu, data motsa Abba zaice “Sannu Jiddah kinji, ALLAH ya rabaku lafiya”.
A yau kam duk wanda ka kalla a ƴan gidan su jiddah zaka fahimci suna cikin tsantsar farin ciki, komai suna yinsa cike da walwala, gasu ga Abbansu a inuwa ɗaya suna hira da dariya, abinda bai taɓa faruwaba a tarihin gidan.
Sai dare Aliyu yazo yaga Abba ya ɗauki Jiddah suka tafi, saida ya kaita gidan malam ganin Muhammad da Maimuna sannan suka wuce gida.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Haka rayuwa taci gaba da tsabagen gudu da sauri, Jiddah nata rainon cikinta, ga soyayya da take samu ga mijinta mai tsayawa arai da ruhi, dolene ka gansu suyi matuƙar birgeka sosai. Watan Maimuna biyu a gida tadawo, yaronta yayi ɓul-ɓul dashi tamkar ta bani????.
Tunda suka dawo ɗawainiyar Muhammad ta koma ga Jiddah, idan ka gansa hannun Maimuna nono zaisha kokuma barcin dare, hakanne yabama Aliyu da Maimoon ɗinsa damar cin soyayyarsu da kewar juna da sukayi.
Abba ma dai jikinsa Alhmdllh, dan zamu iya cewa ya warke sarai, sai dai kuma baya koda iya miƙewa, ko yaushe yana cikin wheelchair zaune, itace ƙafafunsa a yanzu, idan kaje gidansu Jiddah saikaga dukya canja saboda kwanciyar hankali takuma samuwa, sai dai matsalolin yau da kullum da baza’a rasaba. Muneer yana wajen Umma, ta kama ta riƙe tamkar nata, yayinda duk gidan suka ɗauki son duniya suka ɗora masa. A wanan yanayinne kuma aka shiga hidimar bikin zarah da mijinta Nazeer.
Su Jiddah kirjin biki, ga shagali ga ciki daya fito sosai kowa na gani, sai dai tanata kumshe abinta a hijjab kar a gani, dangi abokan wasa kam suka tasata gaba da tsiya, itadai nata murmushi, saisu Aunty Nafisa ne ke rama mata.
Wannan karonma Uncle yahya shine yayma Zarah komai, dan Abba yace basuda uban daya wuce Uncle yahya, shi hotone a garesu, bai isa zuwa rana tsaka ba yace zai wata fiffika akansu.
Ansha biki aka kai amarsu Zarah gidanta tana tiƙar kuka, hakama su Jiddah na tayata a gefe.
Kwanaki biyu da gama bikin Jiddah Mutuwar hajia deluwa ya baje gari, koda Jiddah taji sai da taimata Addu’ar samun rahmar ubangiji, Walida tace, “Tab, sannu yaya Jiddah, wlhy kinada zuciya mai ƙyau, duk abinda tai miki amma kike mata wanan doguwar addu’ar haka?”.
Murmushi kawai Jiddah tayi bata iya cewa komaiba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Lokacin da cikin Jiddodon Uncle ya cika watanni goma cif ta haifo ɗiyarta mace santaleliya, murna a wajen ya Sheikh da Maimuna ba’a magana, hakama su Umma da sauran dangi, ranar suna yarinya taci suna Maryam, akasha walima da daddare.
Washe gari Jiddah tadawo gida wanka cikeda kewar ɗanta Muhammad da ya Sheikh ɗinta da ƴar uwarta Maimunatu.
Sosai Umma ta tsaya akan kula da jiddah, yanda Abba ke nunama Maryam soyayya har mamaki take basu, ko yaushe yana mamuƙe da ita, ko kukanta yaji yata faɗa kenan wai sakacin Umma da Jiddah ne, su dai su Umma sai dai kawai suyi dariya.
Ahaka Jiddah tagama wanka ta tattara ta koma ga ya Sheikh ɗinta, aka ɗora soyayya daga inda aka tsaya, yayinda dukkan kulawar Maryam takoma wajen Maimuna itama.
Haka rayuwa tacigaba da shurawa cikin amincin ubangiji da rahamarsa, wataran aji daɗi wataran ayi kuka.
*_BAYAN WASU SHEKARU_*
Rayuwa ta shura, gidan Sheikh Aliyu Abdul-ra’uff maina yazama na ƴaƴa da al’umma, yanzu kam shine magajin malam ɗin na gaske, dan ALLAH yayma malam rasuwa shekaru uku kenan da suka wuce, hakanne ya saka girman malma da hidimarsa ga al’umma duk ta dawo kan Aliyu.
A yanzu haka akwai ƴaƴa tara a gidansa, maimuna nada biyar. Muhammad, Ai’sha, Hauwa’u, Umar, Aliyu.
Jiddah nada huɗu, Maryam, Maimunatu, Abubakar, Usman.
Rayuwa mai cike da tarin farin cikice ke gudana a gidan ya Sheikh, ga girmama juna da sanin haƙƙin zaman tare, duk sun zama manyan mata, dan daga Maimuna har Jiddah sunyi ƙiba tamkar ba suba, sun zama iyaye alamun girma duk ya bayyana a garesu. A yanzu haka suke riƙe da islamiyyar mata ta ƙofar gidansu, yayinda suma basu zauna hakaba, suna neman ilimi a wajen mijinsu ga kasuwancinsu na hijjabai da sukeyi da jallabiyoyi daga ƙasar saudia, wanda Aliyu ne yay musu wanan hanyar.
Rayuwar gidan na tafiya dai-dai gwargwadon iko, ba wasu tarin kuɗine dasuba, babukuma talauci na an shiga uku an lalace.
************
Ɓan gaten su Umma ma masha ALLAH, tuni Walida ma tayi aure, yanzu haka dagasu sai Munner daya zama saurayi, yanata karatunsa ɓangaren shari’a, tsufa sosai ya kama Abba da Umma, musaman ma Abba da abin ya haɗa da lalurar rashin tafiya, dan har yanzu a Wheelchair yake yawo. Shida ƴaƴansa kam sai sambarka, dan sune ke riƙe da gidan yanzu, cinsu shansu suturarsu shida Umma da karatun Munner du ƴaƴansa matane keyi, bai nemi komai ya rasaba dai-dai gwargwadon iko.
Shiyyasa lokuta da dama yakan zauna yayta kuka idan ya tuna taɓargazar da yayi na butulcema ALLAH, duk sanda wani acikin ƴaƴansa yazo gidan sai ya maimaita neman gafararsa, hakama Uncle yahya.
Shidai saidai yace masa dan ALLAH abar tuna abinda ya wuce, komai ya wuce ai yanzu.
Shima Uncle yahya yazama dattijo sosai, furfura dukta taso masa, yaransa sun girma sunata ɗawainiya dashi harma da Abba, sanan sunata zuminci dasu Jiddah abin gwanin sha’awa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sheikh Aliyu maina kishin giɗe a falonsa yana kallon wani program a Sunnah tv, yayinda Maimuna da Jiddah ke gefensa suna tayasa hira da kallon program ɗin suma, daka gansu zaka fahimci tsantsar soyaya da kwanciyar hankalin dake tattare dasu, zukatansu fayau suke babu nukufurcin kishi mara ma’ana, hakama adalin mijinsu kulawarsa tana akan kowaccensu. A gabansa juk ne na kunin aya da yake dorawa.????????
yarone da bazai wuce shekara 8 ba, ya shigo da kuka hannunsa riƙe da litatafai, yana sanye da Uniform ruwan ganye masu haske.
Harya shigo ya koma da baya danya tuna baiyi sallama ba, daga Sheikh Aliy harsu Jiddah babu wanda yamasa magana, saida yakoma yayo sallama suka amsa aka bashi izinin shiga sanan ya shigo, har yanzu kukan yakeyi.
Kai tsaye wajen Maimuna ya nufa ya faɗa jikinta yana faɗin “Ummina kinga Yaya Umar yasaka yaya Muhammad ya dakeni”.
Maimunatu tace, “Duka fa auta? A lallai yau babu maicin abinci a gidanan tunda aka dakarmin Auta, kai har Abbu bazamu yima maganaba shida Ammi”.
Baki Jiddah ta taɓe tana miƙewa da faɗin “Sai kukam kuƙi ci Ummi, kema kinsan tsokanar Usman da hana bakin mutane zama shiru, aini yayama baimin dai-daiba dabai barka a ƙofar gida ka kwanaba ya kullo mana gidanmu”. Ta ƙare maganar da hararar Usman dake lafe jikin Maimuna.
Murmushi Aliyu yayi shidai, rayuwar matansa na birgeshi, baka isa banbance ƴayan gidan na wanenenba idan har ba’a faɗi makaba……
Sallamar Muhammad daya zama ɗan saurayi dan kusan shekararsa 22 yanzu ta katsesu, daka gansa kaga cikakken Ustazu, ga tsananin kamanninsa da Aliyu sun fito ɓaro-ɓaro. Jiddah ce ta amsa masa sallamar tareda bashi izinin shigowa, tunda ya shigo Maimuna ke dalla masa harara.
Murmushi yayi yana sunkuy da kai, cikin muryarsa mai sanyi da batada maraba data mahaifinsa yace, “Afuwa Ummi, wlhy autanki ne bayaji, ki dinga bashi ruwan al’awa kozai dai-daita, muna karatu amma sai tsokanar ƴaƴan jama’a yake…..”
Jiddah ta katseshi da fiɗin, “I shurunka yarona, itama ai tasan halin abunta, ni sonaima kabarsa can ƙofar gida ya kwana ai”.
“Wai Ammi ashe yau Ummi zata hanani tuwo kenan a gidanan, gara dai mu lallaɓa ko Abbu?”.
Aliyu datun ɗazun yake musu dariya ƙasa-ƙasa yace, “Da gaskiyarka babban yaya, mu lallaɓa dai Ammi, kar Ummi ta turamu bayan ƙofa akan wannan autan nata sarkin shagwaɓa”.
Maimuna tace, “dakun taimaki kanku kam”.
Dariya duk suka ɗanyi, Usman ya sakko daga cinyarta yakoma wajen Aliyu ya zauna jikinsa, “Abbu!”.
Aliyu yace, “Na’am autan Ummi ta samune?”.
“A’a Abbu bata samuba, zance maka dai nama haƙura na daina kukan, shima yaya Umar ɗin na yafe masa”.
Rungumeshi Aliyu yayi tareda sumbayar goshinsa, “Yauwa autan Ummi mai halin manya, ai haka akeso, yanzu kaima kaje ka bama yaya Muhammad hakuri, kace bazaka sake rashinji a ajiba”.
“To Abbu”.
Gaban Muhammad Usman yaje ya durkusa, “Yayanmu kayi haƙuri kaji, kaga ALLAH yana tare da masu hakuri, indai nine zan dinga jin magana insha ALLAH, na daina tsokanar kowa a aji”.
Muhammad ya ajiye littatafan hannunsa ya ɗauki Usman ya ɗaga sama yana nufar kofar fita da faɗin “yawwa Autanmu, ALLAH ya maka albarka kaji”.
“Amin yayanmu” usaman ya faɗa shima suna gab da fita……
Da sauri Aliyu ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunan Muhammad, hakanne yasaka Muhammad amsawa ya juyo, “Na’am Abbu”.
“Inasu Maryam suke? Banace kadaina shigowa gidaba sai kaga sun shigo?”.
“Afuwan Abbu, na biyo Usman ne dama amm……”
Sallamar sauran yaran ta hanashi ƙarasawa.
Maryam da Ai’sha kusan kansu ɗaya, sun zama ƴan mata masha ALLAH, sai Hauwa’u (Noor) da Maimoon (Amatallah) suma kansu ɗaya, sai sauran yaran maza Umar, Abubakar, Aliyu, yaran gwanin sha’awa, atare suka durkusa suna gaida iyayensu, dan tasowarsu kenan daga makarantar dare dake a ƙofar gidansu.✍????????
*_ALHAMDULLAHI ALAH KULLI HALIN, GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TALIKAI, WANDA SHINE YABANI DAMA DA LOKACIN RUBUTA WANAN ƊAN LITTAFI NAWA, ABINDA NA FAƊA DAI-DAI ALLAH YA BANI LADANSA DAKU BAKI ƊAYA, WANDA NAYI KUSKURE ALLAH KA YAFE MANA DAKU BAKI ƊAYA DA KUKA KASANCE DANI_*
_Babu abinda zance da masoya sai godiya, nagode ƙwarai da gaske da Comments naku, da addu’oinku a gareni da mahaifina????????????, wanan kaɗai da kukamin kun biyani ƙwarai da gaske, dan mai ƙaunarkane zai maka addu’a harma ya tuna da mahaifanka a ciki, ALLAH ya haɗamu a aljannarsa baki ɗaya, ina kuma godiya irin trillions ɗinnan musamman
*_MUTUM DA DUNIYARSA GROUPS_*
*_MASARAUTAR BILYN ABDULL_*
*_TASKAR LITTATAFAN HAUSA_*
*_KUNDIN HASKE_*
*_HUGUMA CONVERSATION ROOM_*
*_ZAUREN BIEBEE ISA_*
*_BENEFICAL WRITERS ASSO…_*
*_ZAUREN HASKE WRITERS_*
*_ZAUREN KHADIJA CANDY_*
*_HOME OF NOVELS_*
*_ZAUREN SADEEYER NOVELS_*
*_ALFAHARI NOVELS ONLY_*
*_NI DA AMARYATA FANS_*
*_MANSHAT NOBELS_*
*_ZAFAFA PAID GROUPS_*
*_SAIFUL-ISLAM FANS_*
*_WUTSIYAR RAƘUMI FANS_*
*_KAI MIN HALACCI FANS_*
Kunada yawa matuƙa, ina godiya ga sauran waɗandama ban lissafoba, harma waɗanda ban saniba kuda admins naku gaba ɗata????????????❤❤❤❤????????????????????????????????????????????????????????????????????
*_Daga ƙarshe muna muku albishir da zuwan zafafa biyar insha ALLAHU a ranar 7 ga watan janaury nan da muka shiga, muna fatan waɗanda basu sayaba zasu garzayo kusa suma ayi dasu, dan har yanzu hajarmu abuɗe take a gareku, shima wannan babban halaccine da zaku nuna mana wanda bazamu taɓa mantawa dashiba, zukatanmu sukuma yarda kuɗin masoyane na gaske????????????????_*.
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
????????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????