Uncategorized

SAMEEHA T

_????SÂMÊÊHÂ????_*

            (T)

Ɗan a dai daita sahu Mona ta tare musu a bakin titin sukayi ciniki akan (250),ta juyo ga umma ta ce”Umma ki fara shiga ya amin ce zai kai mu akan Dari biyu da Hamsin(250). “Kai ɗari biyu da hamsin maimuna,Ina laifin mu bashi ɗari biyu nan da kwanar gandujen zai chaje mu har ɗari biyu da hamsin gaskiya malam ka rage mana mu baka biyun tun da a titi zamu sauka ba ciki zaka shiga damu ba kaji,Umma ta ɗan duƙa kanta cikin a dai daita sahun tana duban matashin yaron,mai adai daitar ya dubi Umma shima ya ce”

Hajiya mai ne ya haura akan yanda muke siyan sa Ku bada biyu da hamsin din a hakan ma sauƙi nayi muku Ku bayar da hakan mu tafi Allah yasa mata albarka.

To ai shikenan wannan rayuwa sai dai Allah ya Iya mana mai makon ace  mai yai ƙassa sai dai kaji yayi samma Allah ya kyauta,ɗan a dai daita sahu ya amsa da”

“Amin hajiya.

“Bissimillahir’rahmanir rahim,Umma ta taka qafarta cikin a dai dai ta sahun ta juya ta zauna tana mai juyowa wajan da mona ke tsaye,”Subhanallahi,umma ta furta ta miƙe da sauri tayi kan Mona da ta tafi luuuu zata fadi ƙassa Umm ta kai hannu zata taro Mona Ina har Mona taje kassa sai sallati kake ji mutane nayi wasu suka nufo wajan da gudu har ɗan Adai dai ta sahun shima sai da ya fito da sauri yana sallati,kuka Umma ta fashe dashi tana tofawa mona Addu’ar da duk ta faɗo mata baki haɗe da kiran sunanta mona ta sandare idanuwanta suka kakkafe samma sai wani irin jijjiga take jama’a na ta cece kuce akan ta har wasu daga ciki suka bada shawarar ko a yayyafawa mona ruwa ko summa tayi umma ta amsa da sauri aka samo ruwan wanda ya bada shawarar ya tsiyayawa umma a hannu ta shiga shafawa mona a fuskarta tana kiran sunan ta shiru mona tayi sai ma ƙara mimiƙewar da take tana fusga kamar zata tashi samma umma na riƙe da ita gam,wani ya furta”

       “Baiwar Allah anya yarinyar nan ba farfaɗiya take ba.


A’a bata da wani ciwo daya danganci haka dan Allah ku taimake ni wallahi lafiya lau muka fito da ita inna lillahi wa inna ilaihirraju’un ku taimaka min kamar yanda Allah ya taimake ku,gaba ɗaya umma ta fita a hayyacin ta sai tattauna yanda za’ayi jama’a suke gashi kamar ƙara angizo mutane wajan ake manya da yara har da mata ana haka wani dattijon mutum ya ƙaraso wajan a hankali sanye da fararan tufafi da wata ƴar gajerar sandarsa da hula akansa da ƙyar yake nufo wajan jama’ar da suka cika a wajan suka fara buɗa masa hanya yana dogarawa har ya ƙaraso inda mona ke kwance Umma na tofa mata Addu’a tana kuka,sai da yagama ƙarewa mona kallo kafin nan ya dubi cincirin don jama’ar wajan ya ce””



“Dan Allah ku ɗan buɗa mana iska akuma bani ruwan rijiya insha Allah yarinyar nan yanzu zata miƙe amma bani da tabbas dan Allah ne kaɗai mai yi ba wani ba.


Surutu ne ya karaɗe wajan tsohun ya sake cewa akaro na biyu.


“”Ɗa’a tana daga cikin girmama wanda ya ɗara maka koda da yinni ɗaya ne,idan bazaka iya shiru ba ina roƙon ƙu da Allah da Annabi kuyi tafiyarku inda yafi muku amfani ko ka kama Sallati ga Annabi Ɗan Gatan Allah kunga kun sami lada a maimakon furta abinda zai iya kai ku ga halaka.


Rufe bakin dattijon tayi dai dai da wata yarinya ƙarama tazo gabanshi ta duƙa ta ce”


“Baba gashi na ibo maka na rijiyar gidan mu.


“”Ubangiji ya albarka ci rayuwarki yarinya ya sa ki gama da duniya lafiya.


Dattijon yasa hannayensa biyu dake karkarwa ya amshi ruwan rijiyar yana mai yiwa yarinyar murmushi tashi yarinyar tayi ta koma gefe guda ta tsuguna shi kuma tsohon ya da duƙa kansa kan moɗar ruwan yana karanta Addu’o’in da babu wani mahaluki dayake ji sai shi kansa umma na goge hawaye wasu na antayowa kamar fanfo har dattijon ya idar da Addu’o’insa ya ɗago ya dubi umma da itama take duban sa ya ce.


“Sannu Hafsatu.


Mamaki fal bayyane a fuskar Umma tayi ƙarfin halin amsawa da.


“Yawwa baba.


Murmushi tsohon ya kuma yi ya ce.


“Karɓi da bissimillah ki shafewa maimuna fuskarta har izuwa tafin sahun ta insha Allah da yardar Ubangiji zata miƙe.


Cike da tsoro da fargaba Umma tasa hannu biyu ta amshi tofin daga hannun dattijon ta fara bissimillah kafin nan ta ɗora da shafawa mona tofin a fuskarta da sauran gaɓɓan da dattijon ya ambata cikin hukuncin Ubangiji saukar tofin jikin mona ta farka da sallati a bakin ta ta miƙe zaune a hankali data yi ido biyu da Umma sai kuka kuma Umman ma ta fashe da kuka duk jama’ar wajan sai da jikin su yayi sanyi.





………..






A matuqar ƙufule da tashin hankali Sarkin hatsabibai ya dubi inda sameeha ke ɗaure ya dawo da dubansa ga inda momy ke tsaye ya ce”


“”Na Kwana uku akan cikin jaririyar nan ina aiki bai yuba shin wacece ita? me take da shi wanda yake lulluɓe taurarin ta?me ta taka yake nisanta ta daga laluban mu,sam babu wata hanya da zan iya bi na lahanta ta ta a yanzu in dai na matsa akan haka to zamu iya fiskantar samun matsala dani dake har ƙarshen rayuwar mu abaya mukan turo da ɗan aike zuwa ga gangar jikinta da ƙwaƙwalwar kanta amma a zahirin yanzu babu wannan damar daya kusanto inda take zai fara kamawa da wuta har ya samu tserewa kina ina har hakan ta faru nasarar ki tana ga mutum biyu ta ukun ta rushe ta lalace sai ki ƙara lalube cikin duhun daji…… kamar ƙiftawar ido da buɗewa momy ta nemi sarkin hatsabibai ta rasa duk matsa layar da danneta da kiraye kirayen sunan sa da momy ke yi bai sa sarkin hatsabibai dawo wa ba haushin hakan yasa momy direwa Sameeha kasko a gabanta bayan ta kunna garwashin wuta ya kama momy ta cika barkono damƙam akan garwashin haɗe da fitowa daga ɗakin da sauri ta banko ƙofar tana tare me yaji……….



    



*Kuyi haƙuri da wannan fan’s saboda ku kaɗai na ƙuƙe na dage sai da nayo muku dan farin cikin ku????*






_*By*_

_*Maman Dr*_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button