NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 11 to 20

    *MONDAY*        Ɗahira ce tsaye gaban mirror ta buɗe locker ta ɗau ɗan siririn glass ɗin ta tasanya a idanuwan ta sannan ta juya ta ɗau jakan ta ta fice, Direct ɗakin Maman ta ta nufa, tana shiga ita kuma tana fitowa daga Toilet

Kallon ta tayi tace, “Ke har yanzu ashe baki tafi ba?”

Ɗahira tace, “Eh Mama ban gama shiryawa bane yanzu zan tafi”.

Aunty Amarya tace, “to ki kula sosai abinda ya kai ki shi za kiyi, Allah ya tsare”.

Murmushi Ɗahira tayi tace, “Ameen Mama na tafi bye”.

Ta juya ta fice, a parlour ta tarar da Umma tana zaune

“Umma sai mun dawo”.

Umma kallon ta tayi sannan tace, “to adawo lafiya”.

Amsa mata kawai tayi ta fice cikin sauri, parcking space ta nufa ta buɗe motan ta da ta kasance ash colour ta shige tabar gidan

Mintuna 15 ya ɗauke ta kafin takai Babban Hospital ɗin wato *AL’AMEEN FAMILY HOSPITAL* tana shiga tayi parcking motan sannan ta ɗau jakan ta tare da rigan aikin ta tafito, rufe motan tayi kafin ta juya ta doshi cikin Asibitin cikin tafiyan ta na yanga, Lifter ta hau yakai ta hawa na uku kasancewar anan ne Office ɗin ta yake, ko wani Doctors akwai sunan sa agaban office ɗin sa, itama haka an saka Dr. Ɗahira Al’ameen Al’ameen, sai da ta kalli sunan nata tasaki kyakykyawar murmushin ta kafin ta buɗe tashiga ciki, ahankali ta taka har ta’isa kan kujera ta zauna tana ajiye jakan ta tare da rigan aikin ta, files ɗin da ta gani azube akan table ta soma buɗe wa tana dubawa, sai kuma ta miƙe tsaye da nufin fita taji anyi nocking

“Yes come in”. Tafaɗa tana kallon ƙofan

Baffa ne ya shigo hannun sa riƙe da wasu files, murmushi suka sakarwa juna kafin ya’iso ciki ya zauna, itama ɗin komawa tayi ta zauna tana cewa

“yayana Barka da safiya”.

“Yauwa my sweet sister, hope dai kina enjoyed aikin?”

Murmushi tasaki cike da farin ciki tace, “Yes sai dai ban fara ba zuwana kenan”.

Shima murmushin yasaki cike da ƙaunarta a ran sa yace, “Ok ga wasu files ɗin; su ne waɗanda zaki duba anjima da ƙarfe 10:00am, waɗannan kuma na gaban ki na petiens ɗin ki ne Big Dady ya kawo miki, idan kin shirya sai muje in nuna miki Rooms ɗin da suke”.

Ɗahira kallon sa tayi har alokacin da murmushi a face ɗin ta tace, “Tom muje”.

Miƙewa yayi itama ta miƙe tana ɗaukan farar rigan aikin ta tasaka, sosai rigan yayi mata matuƙar kyau fiye da tunanin me karatu, eyeglasess ɗin ta tagyara tana me bin bayan sa

bayan sun fito atare suka jera suna tafiya suna hira sai zuba murmushi duk kan su suke yi.

              ⚫⚫⚫

   .   Buɗe ƙofan tayi ta shigo bayan da Shakira ta bata umarnin shigowa, ahankali ta ƙariso ciki tana karairaya cike da son burgewa ta samu waje ta zauna tana kallon Shakira da itama ta zuba mata idanu tana kallon ta, murmushi ne kwance a face ɗin ta tace

“Suna na Dr. Ayush Abdulkarim, Ni ce office ɗina ke kusa da naki kuma nima ɗin ina cikin wanda Hospital ɗin nan suka ɗauke ni aiki ranan Waliman ku, am.. shine nace bari na shigo mu gaisa”.

Sai alokacin Shakira tasaki fuskarta tace, “ok Ni kuma Dr. Shakira Abubakar Al’ameen”.

Murmushi Ayush tayi tace, “idan babu damuwa zan so mu zama Friends coz tun alokacin Walima naga kin burge ni”.

“Why not”. Shakira tafaɗa tana ɗage kafaɗa

“Thank you, bari inje zan sake dawowa idan na gama aiki”.

Murmushi Shakira tayi mata tace, “ok babu damuwa”.

Tashi Ayush tayi ta fice tana me rufo mata ƙofar, murmushi ta saki tana cije leɓe afili ta furta

“Da sannu Burina zai cika, da sannu mafarki na zai zama gaske, tabbas sai na cika burin zuciyata”.

Juyawa tayi ta shige office ɗin ta dake kusa da na Shakira.

                 ⚫⚫⚫

       Ɗahira bayan ta gama duba petiens ɗin ta ne ta juyo ta nufi office ɗin ta, ta zo karya kwana kenan su kayi karo da wata matashiyar budurwa har files ɗin hannunta suka zube, cikin sauri atare suka ce

“Sorry”.

Sai kuma su kayi murmushi sannan Ɗahira tariga ta cewa

“Kiyi haƙuri fa”.

Budurwan me suna Safna tace, “no babu komi”.

Sannan ta duƙa ta soma kwaso ma Ɗahira files ɗin, itama duƙawa tayi ta taya ta har suka gama kafin ta’amsa na hannun ta ta wuce

Bayan ta Safna tabi da kallo har ta ƙule sannan ta saki ajiyan zuciya tana murmusawa a ranta tace, “Tana da sauƙin kai ba kamar wancan bugaggiyar da mu kayi karo da ita ba”.

Juyawa tayi taci gaba da tafiyan ta har ta’iso wajen lifter ta buɗe zata shiga, ji tayi an bangaje ta an shige, tana ɗago kai taga Yusra, a ran ta tana mamakin halinta, yanzu suka gama karo da ita ta balbale ta da tsiya but gashi yanzu ta buge ta bata ce mata tayi haƙuri ba. ɗauke kai kawai Safna tayi ta shige ciki tare da danna Number liftern ta rufe.

         Yusra ta soma sauka kasancewar office ɗin ta a hawa na biyu yake sannan ita kuma Safna ta sake latsa number yakai ta ƙasa, wasu files taje ta’amso a reception sannan ta sake hawa ya maida ita block 4 inda anan ne office ɗin ta yake, tana ɗaya daga cikin waɗanda aka ɗauka sabbi.

              ⚫⚫⚫

           Ƙarfe 01:00pm. Ta gama duba marasa lafiyan ta, miƙewa tayi ta shiga Toilet ɗin cikin office ɗinta ta ɗauro alwala ta fito, sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da Sallah sannan ta miƙe ta ɗau duk abinda take buƙata ta zuba cikin jaka ta fito ta rufe office ɗin, lifter ta hau ya kaita upstairs na 5 inda anan ne office ɗin mahaifin ta yake, Direct office ɗin ta nufa tayi nocking aka bata iznin shiga, tura ƙofan tayi ta shige da sallama a laɓɓanta

Abbu ganin ƴar shi da yafi ƙauna cikin ƴaƴan shi a office ɗin sa yayi matuƙar saka shi farin ciki, cike da fara’a ya’amsa mata yana cewa, “Mama na”.

Ɗahira da itama take faman doka murmushin ta ƙariso ta zauna tana cewa, “Abbu Barka da aiki”.

“Yauwa Mama na ya naki aikin?”

“Alhmadulillah Abbu”.

Abbu yace, “masha Allah haka ake so, har kin tashi kenan?”

“Eh Abbu, nazo ganin ka ne sai mu wuce tare”.

Murmushi yayi yace, “Mamana kenan ai ban tashi ba, ina ga yanzu sai zuwa 04:00pm.”.

Gyara zaman ta tayi tace, “to Abbu bari in jira ka sai mu tafi tare”.

“A’a tashi kije gida ki huta Mamana ba na son ki zauna nan, kin ma ci abinci?”

“A’a Abbu”.

Coolarn dake kan desk ɗinsa ya turo mata yace, “ɗauka ki ci”.

Duk da ba ta jin yunwa bata yi masa musu ba ta ɗauka ta soma ci, kaɗan taci ta tsame hannun ta ta shiga Toilet ɗinsa ta wanko hannu ta dawo

Lokacin ne Abbu ya ɗago kai daga rubutun da yake yi yace, “Kin ƙoshi kenan?”.

Gyaɗa masa kai tayi sai kuma tace, “Abbu ko ma ban ƙoshi ba idan na koma gidan zan sake ci ai”.

“To shikenan Allah ya miki albarka ki kula kinji”.

“To Abbu byee”.

Ta ɗaga masa hannu sannan ta fice tana murmusa wa, tana fita haraban asibitin ta shige motan ta taja tayi gida, bayan tayi parcking ta fito ta nufi Part ɗin su, sai da ta soma shiga ɗakin Mamanta ta sanar mata dawowar ta sannan ta nufi ɗakin su, wanka ta soma yi ta shirya cikin wata koriyar atamfa ɗinkin Buba ta ɗaura ɗankwalin shi, eyeglasses ɗin ta tasanya ta fito ta nufi kichen, abinci ta ɗiba ɗan kaɗan ta fito parlour ta zauna tana ci, lokacin ne itama Fadila ta dawo

Ɗahira amsa mata sallaman ta kawai tayi taci gaba da cin abincin ta idanuwan ta na kan t.v, bayan ta gama ta tashi tamayar da plate ɗin kana ta wuce ɗakin Mamanta, tana tura ƙofan da sallama Aunty Amarya ta ɗago kanta daga karatun Hisnul Muslim da take yi, ta kalle ta tana amsa mata sallaman

1 2 3 4 5 6Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button