NAFEESAT 1-END

NAFEESAT Page 1 to 10

Ad

_____

EPISODE One*        Doctor ” Al’ameen Abubakar Khabeer Cindo ”and his wife ”Prof. Nafeesa (Baby) Isma’il Audu, ” as you know in the story of *NAFEESAT* They live in Kaduna, and they still live in the city, owned by their five children.

        *1_ DOCTOR NOOR (LAWAL AL’AMEEN ~YARON UMMEE NAFEESA~)* Wanda a yanzu ake kiran sa Big Dady, matar sa ɗaya *Hajiya Asiya (Hajiya) ƴa ga Muhsina,* yaran su uku, Doctor Usman, sai Doctor Zainab ~yanzu haka tayi aure,~ sai kuma Yusra.

*2_ HAJIYA RABI’ATU AL’AMEEN (IKRAM) ~WANDA A YANZU TANA AURE A GARIN KATSINA~* tana zaune da iyalan ta acan.

*3_ DOCTOR ABUBAKAR AL’AMEEN ~WANDA YANZU AKE KIRAN SA DA ABBA~* matar sa ɗaya Doctor Fatima (Hajja Fatu) ~ƴa ga Abokin Doc. Al’ameen wato Haidar da ƙanwar sa Ihsan,~ yaran su Biyu, Doctor Al’ameen (Baffa), sai ƙanwar sa Shakira.

*4_ DOCTOR AL’AMEEN AL’AMEEN (ABBU)* Matan sa biyu, ~Bilkisu (Umma) ƴa ga Baseera,~ yaran ta uku Doctor Zulaiha ~tayi aure,~ sai Fadila da autan su Fadil. Sai matar sa ta biyu *A’ISHA (AUNTY AMARYA)* yarinyan ta ɗaya ”’NAFEESAT”’ suna kiran ta da Ɗahira.

*5_ HAJIYA LAILA AL’AMEEN* yanzu haka tana aure a Kano, ta auri babban Yaron *WALID.* Suna zaune da iyalan su can.

       Waɗannan familyn yanzu haka suna zaune ne a gida ɗaya kowa da part ɗin shi, sai dai akwai Babban parlour’n da ya haɗa su, yanzu haka Doc. Al’ameen Wanda a yanzu suke kiran sa da *KAKA* ya kai shekaru 89years. Tuni ya ajiye aikin sa sakamakon yana fama da ciwon ƙafa wanda a halin yanzu yana zaune ne a wheel chair, matar sa Prof. Nafeesa (Baby) Shekaru uku kenan da Allah ya amshi abin sa.

Za kuyi mamaki idan nace muku duk ka familyn Doc. Al’ameen gaba ɗayan su *DOCTORS* ne, wannan shine burin sa kuma Allah ya cika masa.

        Babban asibitin da ya gina ya ƙara haɓɓaka shi wanda a halin yanzu Five Block ne, kuma sosai asibitin me suna *(AL’AMEEN FAMILY HOSPITAL)* tayi fice a ƙasar Nigeria, gaba ɗaya familyn suna aiki ne a Hospital ɗin.

Yanzu haka a halin yanzu an shirya yin babban Walima don taya Doc. Ɗahira(Nafeesa) Al’ameen Al’ameen, Doc. Shakira Abubakar Al’ameen, Doc. Yusra Noor Al’ameen, da Doc. Fadila Al’ameen Al’ameen. Murnan kammala karatun su na likitanci, wanda za su soma aiki ne a ranan da a kayi musu waliman tare da sabbin ma’aikata da za’a ɗiba a ranan.

Ad

*KU BIYO NI DON JIN LABARIN WAƊANNAN FAMILYN*

         Zaune suke su Huɗu a Babban katafaren parlour’n gidan da ya’amsa sunan sa a haɗuwa da ƙayatarwa, da shigowan ka parlour’n Babban Hoton Prof. Nafeesa (Baby) zaka soma cin karo dashi, wanda tayi sa ne lokacin da ta zama Professor, tana sanye da baƙar abaya me tsananin kyawu da burgewa, wanda duk da kasancewar ta baƙa ba ƙaramin kyau yayi mata ba, sai tayane kanta da Milk Colour ɗin Veil, kyakykyawar fuskarta yalwace take da murmushin da ya ƙara fito da tsantsan kyawun ta tare da Dimpul ɗin ta, a tsaye take ta riƙe ƙugu da hannu biyu tare da ɗan ɗage kanta, da alamun sanda akayi hoton bata san ma za’a yi sa ba. kusa da hoton kuma wani tanƙamemen hoton ne da a cikin sa Al’ameen ne tare da ita Babyn, suna zaune manne da juna sun saka ankon shadda me ruwan powder, gefe da gefen su kuma Noor ne tare da Ikram jingine da jikin su, duk kan su dariya suke yi time ɗin da aka ɗauki hoton, sai gefe kuma sauran hotunan ƴan gidan ne kowa da iyalan sa, sannan sai aka ɗau guda ɗaya wanda su kayi gaba ɗaya familyn, shi wannan ba’a daɗe da yin sa ba, don gab da rasuwan Prof. Baby akayi sa, gaba ɗaya idan ka kalle su sosai suke kamanceceniya da juna, sai dai banbancin launi da ya raba su. 

Doc. Al’ameen wato KAKA tare da yaran sa maza su uku zaune cikin parlour’n suna tattauna yanda za su gudanar da Waliman yaran su kamar yanda suka saba a duk sanda yaran gidan suka gama karatun su na likitanci.

“Kai takwara yaushe matarka zasu dawo ne? Kasan jibi ne walima, ya kamata su dawo don itama Matata (yana nufin Ɗahira kenan) ta sami damar shiryawa yanda Ya kamata”. Kaka dake zaune saman wheel chair yake wannan maganan

ABBU yace, “insha Allahu Dady zasu dawo zan sake tuntuɓan su inji, sabida mahaifin A’isha (matar sa Aunty Amarya) jikin ta yayi tsanani ne shiyasaka suka jin kirta”.

Kaka yace, “to shikenan Allah ya dawo da su lafiya”.

Gaba ɗaya suka amsa da “ameeen”.

Sannan ya kalli Big Dady yace, “Kai kuma da yaushe ne Usman yace “zai dawo?”

Big Dady yace, “Allah ya taimaki Dadyna! na yi masa magana amma yace “in ba ka haƙuri ba zai samu daman zuwa ba sabida aiki sun yi masa yawa”.

Cikin nuna alamun fushi Kaka yace, “wai yaushe Usman yabzama me taurin kai ne? Ko don yana tunanin na ba shi dama ya zauna acan yayi aiki shine yake son ɓata min rai? To, ka gaggauta kiran sa ka faɗa masa umarni nake ba sa; dole ne ya zo wannan taron Waliman da za’a yi, ko me yake yi ya’ajiye sa ya halarci taron nan”.

Gaba ɗayan su su kace “Allah ya huci zuciyar ka Baba”.

“Insha Allahu zan sanar masa Dady kuma zai zo”. Cewar Big Dady kenan

Gyaɗa kansa Kaka yayi kana yace, “za ku iya tafiya na sallame ku, Allah yayi muku Albarka”.

Gaba ɗayan su suka amsa da “ameen” kana suka tashi suka fice.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button