NAFEESAT Page 11 to 20

Kafin yayi magana Ɗahira tayi saurin cewa, “Yaya ka je zan zo har Office ɗin ka”.
Gyaɗa mata kai kawai yayi jin wayan sa na ringing, zaro wayan yayi cikin aljihu yana yin gaba abin sa bayan ya ɗaga mata hannu alamun ya tafi
“Hmm Ni dai ina mamakin wannan shaƙuwa na ku, anya.. anya..”?
Ƙwalalo idanun ta Ɗahira tayi tana kallon ta tace, “kai Aunty babu daman Yaya ya nuna wa ƙanwar sa kula wa sai da wani abun? Ni fa na ce miki abinci muka je ci”.
“To ai nima ba fitar da kuka yi bane nake magana, mu je kawai”. Aunty Zainab ɗin taƙarike maganar ta tana yin gaba
Ɗahira tabi bayan ta suna sauya hiran su
Office ɗin Aunty Zainab ɗin suka shiga, bayan sun zauna ta ɗauko mata wasu files ta miƙa mata
“Ga shi don Allah Ɗahira, ki kai wa Dr. Said don ba na son ya sake damu na”.
Amsar files ɗin Ɗahira tayi tana kallon ta tace, “Aunty who is Dr. Said?”
“Aff baki san shi ba ashe, yana nan office ɗin sa na kallon nan wajen ta hannun dama”.
“Ok sai na sake zuwa kenan Aunty?” Tafaɗa tana miƙewa tsaye
Murmushi Aunty Zainab tayi tace, “Tom My Sister, ki gaishe dasu Kakus me ran ƙarfe”.
Dariya tayi tace, “insha Allah zai ji”.
Daga haka ta fice bayan sun sake sallama.
Tana fita kamar yanda Aunty Zainab tace mata hakan tayi ta nufi hannun daman ta, tana zuwa ta soma dudduba sunayen Offices ɗin, nan kuwa taci karo da sunan sa a saman nashi Office ɗin, Nocking ta soma yi
Dr. Said dake zaune yana ma wata budurwa bayani yayi saurin ɗago kansa cike da fargaba, kallon Budurwan yayi yace, “Yi maza ki kwashe magungunan nan ki saka a jaka”.
Babu musu kuwa ta kwashe ta zuba a jakan ta
Shi kuma ya gyara zaman sa yana rufe Files ɗin dake gaban sa tare da kifa wa sannan ya ba da umarnin shigowa
Turo ƙofan Ɗahira tayi da sallama ta shigo
Idanun sa ƙyar a kan ta ya’amsa mata sallaman yana kallon ta, duk da be santa ba amma ya ga tana masa kama da Familyn Dr. Al’ameen
Ita kuwa ƙariso wa wajen Table ɗin sa tayi ta miƙa masa files ɗin tace, “ga shi Aunty Zainab ta ce in kawo maka”.
Sai a lokacin ya ɗan saki fuskar sa yana bin ta da wani irin kallo, cike da murmushi a face ɗin sa ya miƙa hannu ya’amsa yace, “Ok thanks”.
Juya wa kawai tayi ta fice ba tare da ta kalli ko budurwan dake zaune ba
Har ta fice yana kallon ta cike da tsananin burge sa da tayi, sosai Ɗahira ta ɗauke masa hankali da kyawun ta da cikan halittan ta, musamman ma da take siririyan mace, domin yana ƙaunar irin su. sai faman doka murmushi yake yi ya kasa ɗauke kai daga ƙofan da ta fice
Sai da budurwan nan ta buga table kafin ya dawo hayyacin sa
Ɗan shafa kan sa yayi yana kallon ta kafin yace, “kin tabbatar cikin nan be wuce 5 Months ba?”
Kallon sa tayi a yatsine kafin tace, “Dr. Na rigada na faɗa maka wata 4 ne”.
“Ok bari in zo”.
Miƙe wa yayi ya nufi wani dogon sip ya buɗe, ya soma bincika kayan aikin da zai yi mata amfani wajen cire mata cikin.
Wannan shi ne halayyan Dr. Said, yana cire wa ƴan mata ciki ba tare da sanin kowa a cikin a sibitin ba, domin doka ne idan har aka kama ka kana irin wannan cin amanar za’a kore ka, asibitin kwata-kwata basu yarda da aikata wannan zunubin ba.
⚫⚫⚫
Ɗahira sai da ta koma Office ɗin ta tayi sallah kafin taje ta ƙara duba patients ɗin ta, tana dawowa ta haɗa komi nata da abinda zata buƙata ta fito ta rufe office ɗin
Office ɗin Baffa dake hawa na biyu ta nufa, dai-dai zata shige cikin office ɗin Yusra ta fito nata office ɗin dake kallon na Baffa, kallon juna kawai su kayi suka ɗauke kai, Yusra har da wani sake tamke fuska ta wuce abin ta tana jan tsaki
Ɗahira juya kanta tayi tana kallon ta cike da mamakin ta, har yanzu ta rasa meyasaka Yusra take nuna mata tsana
Bata gama tunanin ta ba Baffa ya buɗe ƙofan yana kallon ta
Murmushi ta ƙirƙiro tana kallon sa tace, “Yayana na gama”.
“Ok Muje Nima tafiya zan yi na gama na yau kuma”.
Share this
[ad_2]