MAKAUNIYAR KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAKAUNIYAR KADDARA 55

 *Page 55*

………….Motarsa ya buɗe ya shiga badan son tafiya ba sai dan son samun sararin yin tunani. Dan abinda ƙwaƙwalwarsa ke neman ayyana masa game da 

zantukansu sosai yake figitar da ziciyarsa. Lallai yana buƙatar haɗuwar Aunty Zakiyya da Zinneerah akan wasu dalilan da yake auna labarin data bama Granny 

da nasu zantukan, sannan yana son sanin mi zasu tura Farah yi Morocco?, dan idan bai mantaba tunkan tahowarsa Nigeria a wancan karon Mammah ta sanar masa 

Farah zataje Morocco tayi rainon cikinta kamar na farko har sai ta haihu. A lokacin bai amsa mataba yace ta bari ya dawo daga Nigeria zasuyi maganar, shine 

kuma komawar tasa ya koma da Hajiya Iya. Kenan tafiyar tata nada alaƙa da wani abu dake ɓoye kenan?.

          Ya jima yana tarawa da kwashewa, daga ƙarshe ya yanke shawarar komawa cikin gidan bayan ya kira Khalipha yace idan yaje gidan ya jirasa karya 

tafi. duk da Khalipha nada nashi uzirin shima sai ya amsa masa da to saboda girmamawa. Dan komai girman uzirin nasa zai iya ajiyewa domin amsa kiran Yayan 

nasu.

      Sai da ya gyara yanayinsa sannan ya tada motar ya ƙarasa gaban gate ɗin da ita. Yayi horn kusan sau huɗu sannan aka buɗe masa. aunty Zakiyya ce da 

kanta dan gidan babu maigadi tazo ta buɗe masa, hasalima mijinta ya sayesane kawai saboda harkokin siyasarsa idan ta kawosa kano yakan sauka.

     Yana gama fakin tana ƙarasowa inda yake, yanda tai wani kicin-kicin da fuska sai ya ƙara ɗaure tasa shima. A ɗage yace mata, “Barka da safiya” yay gaba 

abinsa batare daya jira amsarta ba. Bayansa ta raka da harara zuciyarta na ƙara mata zafi akan rainin wayonsa. Dama can ita bawani shiri take dashi ba 

sosai. Ta girmesa sosai amma sam baya bata irin girma ɗin nan yanda take buƙata, wani lokacinma idan yana mata faɗa akan abu sai ka ɗauka shine babba, dan 

akwai lokacin da mijinta ya taɓa sanar masa wata rigimarsu, daya bincika yaga itace bata da gaskiya ya dinga mata masifa harda cewa zai iya mata dukan tsiya 

har sai fatar jikinta ta fashe.

    Suna gab da shiga falon tace, “Kai yanzu Abdul-Mutallab ka ƙyautama kanka kenan?”.

     Batare daya juyo ya kalletaba a daƙile yace, “Da nai mi?”.

     Cikin hasala tace, “Aure!. Mi kake buƙata ga mace wanda matarka bata da shi? Wane irin rayuwane wannan mutum yayta tara mata a gidansa kamar wani 

binsuru…..”

      Cak ya tsaya tare da waiwayowa gareta tamkar mai ciwon wuya, ya zuba hannayensa duka cikin aljihu yana jifanta da wani irin shegen kallo da har cikin 

ranta sai da razani ya kamata, “Masu mata huɗu da ƙwarƙwara su kuma wane matsayi kika basu?”. 

       “What!?”

Ta faɗa a razane tana kallonsa dan tasan da ubanta yake. Gira ɗaya ya ɗage mata yana ƙara kicin-kicin da fuska. Cikin hayayyaƙo masa itama tace, “Mikake 

nufi Abdul-Mutallab?”.

      “Na baki gundarin baƙin ai, sai ki masa fassarar data dace”. Ya bata amsa da juyawa ya cigaba da tafiya abinsa kamar bashi ya aikata tsiyarba.

     Wani irin ƙululun baƙin ciki ya saka idanun Aunty Zakiyya cikowa da ƙwalla, cikin ƙunar rai ta fara zazzaga masa masifa. Ko waiwayenta bai sakeyiba 

harya shigo falon gidan da sallama.

     A kusan tare Mammah da Mahma da Farah suka ɗago suna kallonsu, musamman Zakiyya dake masifa iya iyawarta.

      “Ku lafiya kuwa?”.

Mahma ta faɗa tana tsare Abdul-Mutallab da idanu. Zama yay kusa da ita cike da basarwar da ya iya yace, “Mikika gani Mahma?”.

      Sosai ta sake zuba masa idanu dan tasan halin Abdul-Mutallab ɗin ya iya manni ya kuma fika tsare gida, sai kuma ta maida ga Zakiyya dake masifa iya 

iyawa har hawaye na sauka mata a fuska. Kafin ta sake cewa dasu wani abu Mammah tace, “Wai miya faru Zakiyya kike wannan zantukan?”.

      Hawayenta ta share da nuna AK dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, yayinda Farah ta kafesa da ido zuciyarta na 

harbawa da sauri-sauri akan yanayinsa. “Mammah waini Abdul-Mutallab zai jefa ubana da kalmar suna bunsuru!”.

     A kusan tare Mammah da Mahma sukace, “Bunsuru kuma?”.

    “Ai gashi nan ku tambayesa mana”. Ta sake faɗa tana fashewa da kuka.

       Ganin ko motsi baiyiba yasa Mahma kallonsa da ƙyau tace, “Abdul-Mutallab!”.

     Idanunsa ya buɗe a hankali ya kalleta batare daya motsa ba. “Miya kaika wannan zance haka babu daɗin ji? Zakiyya ba yayarka bace?”.

        Murmushi ya saki mai ƙayatarwa a karon farko da ɗan yamutsa fuska, kansa tsaye yace, “Mahma ni ƙarya takemin, ita da bakinta ta kirashi hakan”.

    Ba mahma ba har Farah sai da ta maida kallonta ga Aunty Zakiyyan da tace, “Kaji munafiki, dagafa na masa magana akan ƙara aurensa nace miyasa zaita tara 

mata kamar wani bunsuru shine yace wai masu mata huɗu da ƙwarƙwara fa? Kenan yana nufin Abbanmu ko?”.

        “To ke miya kaiki faɗa masa haka Zakiyya da girmanki? Aure ba ALLAH ya halasta ayisa ba? Taya za’a danganta wanda yay koyi da MANZON ALLAH (S.A.W) 

da wannan mummunar kalmar domin ALLAH idan ba neman tada zaune tsaye ba? Dan ALLAH ku ringa sassautama kanku, rayuwarma duka nawa take ALLAH natuba. Kai 

kuma Abdul-Mutallab baka ƙyautaba daka bata wannan amsar, saika fahimtar da ita kuskurenta ko kai mata shiru”.

      “Am sorry Mahma” ya fa ɗa batare da nuna nadamar abinda yay ma aunty Zakiyya ba. Mammah kuwa kasa cewa uffan tayi. Zakiyya ma ƙin cema Mahma komai 

tayi, dan kai tsaye ta fassara abinda Mahma tayi da son kai. Duk da Mahma ta fahimceta batabi dakantaba ta fara musu nasiha su duka. Sai da ta gama AK ya 

samu damar gaishesu.

    Rai ɓace Mammah tace, “Sai yanzu muke ganinka a gidan? Bayan kasan matarka na cikin halin rashin lafiya, Abdul-Mutallab! Abdul-Mutallab! kana shigarmin 

hanci fa da yawa”.

      Murmushi yayi yana gyara zamansa. Cike da girmamawar da yake bata yace, “To yi haƙuri karki fyatoni Mammah, ba gani nazoba yanzu kuma nama ganta 

ragal”.

    Harara Mammah ta zuba masa kawai dan takaici, zata ƙara magana Mahma tai saurin katseta da faɗin, “Tunda ya nema afuwa basai a sarara masaba a kama wata 

tashar kuma”.

     Dole Mammah ta haɗiye maganar tana marairaice fuska. “Ke kam Addah bakison ace yayi abu saiki fara karesa,  to naji yanzu sai ya nema mana ticket ɗin 

tafiya Morocco”.

       “Morocco kuma Mammah? Mizakuyi acan a irin wannan lokacin daba komai akeyi ba?”.

      “Eh to lallai ubanmu, sai ana wani abu zamuje tushen uwarmu kenan? To Farah zamu kai ta ƙarasa rainon cikinta acan har sai ta haihu.”

       “Kaji kuma wani abu, to banda abinki Mammah sai kace mai cikin fari? sannan wancan karonma bacan tajeba har ya zama sanadin fitar cikin? Ni wannan 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button