NOVELSUncategorized

NAJEEB 13

ZAKU IYA DANAN DOMIN AMFANA DA JUNA

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


Dakata Granny ta katse Mum “da kike fad’in basu dace ba, wa kika samo mishi wacce kike tunanin sun dace dashi din? “ko wannan Mai Jan kunnen kike so ya aura?. 

Mum tace ba haka nake nufi ba, abunda nake nufi shine “Najeeb yana irin wannan Abunne saboda bai samu ilimin addini Sosai ba, ya kamata inza a bashi mata a zabo mishi wacce take da ilimin addini, wanda zata daurashi bisa hanya. 

Granny tace toh ce muku aikai wannan batai karatun addini ba, koya? 

Mum tace a’ah, ina dai zargin haka, “tashi Granny tayi ta nufi d’akin dasu Hanne suke inda ta gansu tsaye suna ma hanne fiffita, “D’ayan na fad’in Wlh Hanne kin more tunda zai aureki, zaki fara tu’ka Mota, ki dinga juya mamanshi da y’an uwansa, saifa yanda kika ce, “dayar ta cafe da fad’in uhm Aida ni akace ya aura danayi mulki Aradu, nifa sai nasa yama duka dangin mu gini inda ni ya aura Wlh Hanne kin more zaki aura kyakyawa gaki kin taba aure harda yaro.  Hanne tace uhm nikam ban son komai Inda zai taimakeni in samu Abun yi, da ban aureshi ba, domin yanda yake abu Wlh tsoro yake ban “Granny gyaran murya tayi wanda yasa dukansu sukai shuru tare da fatan Allah yasa bataji abunda suke fad’a ba “Granny tace toh ku kunna Abun sanyi mana da wannan fiffitan da kuke mata. 

Granny ta kalli Hanne tace zo in ganki 

Tashi hanne tayi tabi bayan Granny, inda suka fita har falo, “Granny tace ma mum ga Hanne nan, banda tabbacin tayi karatun addini, tunda nabar yola, sai dai abunda na sani suna karatun allo, Kinga kenan tana da ilimin addini Indai tayi na allon, saiki tambayeta. 

Mum shuru tayi tana nazari, can tace mama “Aida kin barta kawai, “Granny tace a’a ki Mata tambayar, “Mum kallon Hanne tayi ta Fara Mata tambaya, Hanne na bata amsa, “duk tambayar da Mum tama Hanne ta bata amsa, “Mum taji dad’in hakan dama ita burinta kenan, tunda tana da ilimin addini yanzu zatai supporting d’anta ya aureta, “sannan zata taimaka wajan gyara Hanne, domin ta Lura akwai kauyanci a kanta. 

Granny tace toh Kinji ?ko zaki k’ara Mata wani tambayar ne? “Mum tace a’a na gama.

Granny tace Hanne koma ciki. 

Bayan tafiyan Hanne , Mum ta kalli Granny tace yarinyar tayi, tunda tana da ilimin addini. 

Granny tace toh Alhmdlh, gobe sai aje a d’aura auren, mu dawo da ita .

Mum tace mama ina ganin kaman yayi sauri, da an bari anyi komai kaman yanda al’ada yake .

Granny tace a’ah kawai a d’aura aure, tunda bazawara ce, babu wani abu, tunda ba budurwa bace. 

Mum tace toh shikenan zanyi magana da Najeeb, ya kamata muje tare dashi, yaga family din matarshi 

Granny tace miye kuma mil? 

Mum tace y’an uwan matanshi, ya kamata ya sansu. 

Granny tace oho, eh gaskiya hakane kam, ya kamata ya sansu. 

Ibtisam ce ta fito, falon ita da Zarah, “Granny tace har an tashi daka baccin? “Zarah tace eh granny wannan raguwar tasa mun tashi da sassafe munje asibiti 

Ibtisam tace oh nice raguwa koh? Lallai ai dama Abu Inba akan ka yake ba, baka ji. 

Mum tace Kinga rabu da ita, ai kina da dauriya ma, kuje kuyi breakfast, “yauwa Dad d’inku yace kuje ku duba suna a cafe, yace vc da kanshi ya kirashi yace an saki suna, saiku duba kuga course din da aka baku. 

Zarah tace nidai Allah yasa basu canza min course ba wlh, dan low d’ina nake son karanta “ibtisam tace su low manya, “Zarah tace Kinga wata rana in case ya had’ani nazo wajan kabir. 

Hararanta ibtisam tayi, ganin yanda take maganan Kabir gaban Mum, “mum tace Waye Kabir din? 

Granny tace wanda zai aureta, shima naji shuru bai turo ba, “Anya dagaske yake kuwa? “ban son k’arya irin nasu Na samarin zamani, ni dama keda miskili na had’a, tunda naga kabirun kaman bai shirya ba. 

Zarah ta cabe da fad’in Wlh kuwa Granny dama had’asu kikayi, itada bros Najeeb, “sunyi bala’in dacewa da juna 

Mum tayi dariya tace Hanne dinfa? Sai ayi yaya da ita? 

Zarah ta kwashe da dariya tare da fad’in wace Hanne? Badai y’an matan da Granny ta Kawo ba? 

Mum tace eh su, gobe insha Allah, zamu yola a d’aura aure. 

Ibtisam da fuskanta ke d’aure tunda taji ana fad’in dama ita da Najeeb aka had’a, jin ance za’a had’a Najeeb da Hanne ta saki wata dariya wanda bata san zai fito ba. 

Granny tace lafiyan ki kuwa? 

Da sauri ibtisam tace lafiya, granny kice mu Fara shirin zuwa yola gobe? “muje muga dangi 

Granny tace eh “tare da fad’in kira mun abbanki, “ibtisam tace toh tare da tashi taje ta d’auko karamar wayarta, ta doka ma abbanta kira tare daba Granny wayar. 

Bayan ya d’auka suka gaisa, granny tace gobe za’a d’aura ma Najeebu aure acan yola. 

Yace mama ban sani ba. 

Granny ta Fara fad’in eh Muma jiya muka yanke maganan auren, dan haka saika kwana da shiri mu had’e acan. Tana fad’in haka ta kashe wayan 

Zarah tace gaskiya granny bros bai dace da Hanne kuke ce mata kowa? Taya Bros zai aureta dan Allah wanda ya taso a Turai “Wlh ba ajinshi bane, wannan ko driver bazai aureta ba, balle NAJEEB gaskiya a…..  “granny ta Katseta tare da fad’in kinci gidanku, Kema na kusa dawowa kanki, zan nemo miki ki wani a yola, duk da kun gama tsufa a gida 

Ibtisam dariya ta saki ita da Mum “Granny tace gwara ku Fara shiri, ina ma miskilin yake? 

Mum tace kaman yana cikin d’akinshi ai 

Wayar ibtisam ce, ta Fara K’ara d’auka tayi tare da barin falon, ganin kabir ne ke kiranta. 

Koda ta d’auka cewa yayi yana hanyar zuwa ya ganta, dan zai wuce Kano 

Tace OK sai kazo, tare da kashe wayan, ta Fara k’okarin saka wasu kayan, tare dasa hijab akai, Tana Abu a hankali saboda ciwon hannunta, falo ta fito inda taga Zarah da Granny ne kadai mum tabar falon. 

Zarah tace kabirun yazo ne? Ibtisam tace miye wani kabiru? Banso ,Zarah ta kwashe da dariya “Granny tace toh ba sunanshi bane kabirun!? Ibtisam tace Hmmm sai kuyi tayi Ai….. Wayarta ce tayi k’ara ta d’auka tare da fita…  “Granny tace duk ku gama, shima na bashi lokaci ne inbai turo ba wlh zan korashi ban son kashe kasuwa. 

Zarah dariya ta saki tace kaman ya kashe kasuwa Granny? 

Granny tace eh mana “Inba kashe kasuwa ba, miye haka? Shibai turo ba, kullum yana zuwa, duk Wanda yazo zaice tana dashi, Kinga ai ya kashe mata kasuwa, ni bana son irinsu Wlh. Gwara yaba masu yi dagaske waje .

Zarah tace Granny dagaske shima yake, yana sonta kabir din Sosai,.  Suna cikin fira saiga Najeeb ya fito daka shi sai riga da wani wando 3quater jeans. 

“Granny tace miye haka? Ka fito rabi da rabi tsirara. 

Najeeb ko kallonta baiyi ba Ya fita bayan yaja tsaki 

Granny tace kama uwarka, dan banza, farin banza da hofi. 

Zarah tashi tayi tana dariya tare da fita tabi Najeeb, kiranshi tayi yace what? 

Tace Bros I need to discuss  something very important to you 

Yace not now, ina sauri, let talk letter, tare dayin gaba abunshi 

Mota ya shiga inda yayi horn, yaji shuru ba’a bud’e gate dinba, tsaki yaja tare da fita yaga Ina security din, Kabir ya gani da ibtisam a tsaye a kofar gidan, “ganin ya fito daka gidan kabir ya mi’ka mishi hannu, Najeeb kam k’in bashi hannu yayi tare da wucewa ya koma ciki danshi a duniya baya son kabir, kodan saurayin ibtisam ne oho, amma yana jin tsanar Kabir har cikin ranshi, kwata kwata guy din baiyi mishi ba ko kad’an,  fasa fitan yayi inda ya koma cikin gidan ranshi a jagule…..  Toh muje zuwa gadai Granny dasu mum suna shirin zuwa auren Najeeb gobe, koya zata kaya oho muje dai zuwa…… 

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button