NAJEEB 15

Zaran ce ta shigo ta samu ibtisam kwance, tace Wlh ibti na gaji, “yanzu sai mu Fara shirin zuwa registration dasu Kama d’aki, ni nafi son d’akin wajan makaranta.
Ibtisam tace Kai Aiko ni nafi son hostel, saboda Kinga cikin makaranta yake, babu wani fargaba, akan d’akin waje.
Zarah tace kin San fah hostel mutane da yawa ake had’awa a ciki, wani d’akin sai kiga mutum shida, har bakwai fah.
Ibtisam dariya ta kwashe dashi tare da fad’in kai,wlh a’a, akwai Mai mutane biyu uku ma, nidai gskiya nafi son hostel yafi mana, Kinga mu mata nefa, ance akwai kwartayen maza.
Dariya Zarah itama ta kwashe dashi tace Kai Wlh sharri ne, a Boarding school ne akace akwai kwartaye masu shiga, amma banda high institutions, Indai Kinga kwarto yazo to ke kika Kawo shi.
Haba high institutions wani kwarto kuma, Kema da abun dariya.
Ibtisam tace uhm, nidai gaskiya mu samu d’aki a cikin skul din, “nifa a duniya Ina tsoran wani namiji yazo yamin fyade, “so nake nakai y’anci na gidan miji
Dariya Zarah tayi, tace kice kikai ma Kabir dai, tare da d’aga mata gira Tana dariya
Ibtisam tace eh naji d’in, “ni Wlh bazan iya zama a wajan skul ba.
Zarah tace ok sai mu nema cikin skul din, duk da ance yana wahala, “amma zamma Dad magana saiya ma Vc magana, “Nasan for sure zamu samu insha Allah
Ibtisam tace ya maganan zuwa yola? “ni an wanke min kayana da kika bada a wanke kuwa?
Zarah tace eh, “an wake nasa miki cikin wardrobe, “sannan maganan zuwa yola k’ila wa k’ala ne.
Ibtisam tace kaman ya k’ila wa k’ala?
Zarah tace koma dai miye mu jira mu gani, amma ke kina ganin Najeeb ya dace da Hanne?
Ibtisam tace eh miye a ciki? Aida cewa kikayi Hanne ta dace dashi? Nifa ina tausayawa Hanne Wlh, “domin Nasan zai dinga cutar da ita dan baida hali ko kad’an wlh.
Zarah tace uhm, “ni Wlh naso a had’aki dashi dan Kunfi dacewa Sosai.
Tsaki ibtisam tayi tare da fad’in Wlh Zarah ki fita idona, tun Kafin in miki abunda ranki zai Baci, “da in auri wannan gwara na mutu wlh, Allah ya kyauta, “gwara Kibar wannan maganan tun Kafin kisa wancan tsohuwar taji, ta d’auka ko dagaske akwai wani abu a tsakanin mu.
Dariya Zarah ta saki tare da fad’in Aida nafi kowa murna wlh, inda Granny zata had’a wannan auran, in hakan ta faru sai inga karshen kiyayya
Tsaki ibtisam taja tare da fad’in kanki akeji, “yayanki na Hanne ne, gobe Uwar haka muna yola insha Allah.
Uhm kawai zarah tace, ba tare da tace komai ba.
Najeeb bacci yake Sosai, shida Gina, hankali kwance, suna manne da juna,” sai wajan 6 Najeeb ya tashi tare dayin mi’ka, kai tsaye toilet ya nufa Bayan ya ture Gina daka jikinshi.
Wanka yayi sannan ya fito, yana goge kanshi da towel, Gina kam bacci take har yanzu bata tashi ba, “Najeeb kayanshi yasa tare da d’aukan wayanshi ya danna, 12 misscall ya gani, sauran number ne sai kuma kiran Mum, dialing number din mum yayi tare da sakawa a kunne
Mum d’auka tayi tare da fad’in my only son, “kana ina?
Yace Mum na d’an fita ne, maiya faru?
Tace OK, ina son ganinka yanzu.
Yace OK Ina nan tafe yanzu bada dad’ewa ba.
Tace OK am waiting for you. Tare da kashe wayan
Maganan Najeeb ne ya tashi Gina, “kallonta yayi bayan ya tashi tana k’okarin janyoshi jikinta yayi gaba “tare da fad’in ki shirya gobe zamu koma tare.
Tace OK, tare da fad’in “please Nagit ka dawo mu kwana tare.
Bai kulata ba ya fita abunshi
Kai tsaye Najeeb gida ya nufa inda ya faka motarshi, ya fito ya shiga.
Direct d’akin Mum ya nufa dan baiga kowa a falo ba, “koda ya k’arasa nocking ya Mata, “tace Waye ne?
Yace mum am d one.
Tace come in son.
Bud’e kofar tayi ya shiga tare da fad’in Mum “lafiya kike nemana, naga misscall d’inki da yawa.
Mum tace lafiya son ,zoka zauna muyi magana.
Zama yayi akan kujeran d’akin, mum kuma nakan gado.
Tace yaushe zaka koma son?
Yace gobe zan koma
Tace but Ina son ka d’aga tafiyan inda hali.
Yace why Mum? “in naji dalilin yayi min sai in d’aga tafiyan
Mum tace son akan maganan aurenka ne…
Ya katse Mum tare da fad’in what? Mum Mai kika ce? Aurena dawa? Yanda yayi maganan kaman bai San komai ba.
Tace kaida Hanne.
Kallon Mum yayi tare da fad’in “yanzu Kema Mum kin Fara biyema Dad koh? Nace bazan aureta ba, wlh Ina cewa an d’aura auren zan saketa saki uku, so is better kar Ayi wannan auren
Mum shuru tayi , can tace Najeeb ina son kayi hakuri ka amshi wannan auren K…..
Yace Mum plz, ban son abunda zaisa in fad’a miki wata magana, ” bai kamata ki biyema Dad ba, shi d’an Nigeria ne, And ke kuma ba y’ar k’asar nan bace, so kar ki manta ko a k’asar dana taso ba’a ma mutum dole, Mum in mutum zaiyi aure a barshi ya auri wacce yake so
Mum tace kana magana akan constitution, but mu muna magana akan addini ne, karka manta mune iyayenka, “mune muka haifeka, in kana son farin cikin mu ya kamata kayi accepting wannan auren S….
Yace Mum am begging you, “kibar wannan maganan, “and ki fad’ama mijinki I will not accept d marriage ,”and ina son ki fad’a mishi bazan auri wacce yake so in Aura ba, karya Fara wannan mistake din, in baso yake yayi regretting ba, am his son but Idan ya aura min wacce bana so, “I will forget that he is my Dad.
Mum tace Najeeb kana da hankali kuwa? “Anya baka shan wani abu kuwa? Kaita magana kaman mara hankali, “lallai Abun naka ya girmama but anyway ba laifinka bane tashi kaban waje
Tashi yayi yana fad’in Mum am telling you ki fad’ama mijinki, bazan auri illiterate ba, ina bukatar mace Mai ilimin boko, wacce ta Waye, wacce zan iya zuwa da ita ko ina ba irin wannan monkey d’inba, kai Dad ya Gama dani Wlh, “maiya d’aukeni ne da yake son had’ani da wancan y’ar kauyen for god sake tsaki yaja ya fara tafiya.
Har yakai bakin kofa Mum tace, da Farko Banyi supporting aurenka Da yarinyar ba, saboda ina son ka auri mace Mai ilimin addini, “domin naga baka san komai ba, babu komai a kanka sai duniya, ” but yanzu Ina supporting aurenku 100% , duk da Nasan Idan akayi auren ita za’a cuta, domin ta auri wanda bai San addini ba.
Amma ina son ka sani Indai Kaga wannan auren baiyu ba, toh yarinyar ta rasu ne, ko kuma wani babban Abu ya faru
Najeeb dariya yayi tare da girgiza kai yace Mum, ina baki shawara ki daina fad’in wannan maganan, ‘Wlh mum kuna aura min ita zan saketa, kuma Idan kukai haka zan barku bazan k’ara dawowa gareku ba, tunda bakwa sona,
Mum kallonshi take, Kun San d’a da uwa, “tace Najeeb cikin sanyin murya, tare da nufanshi ta d’aura hannunta akan kafadanshi Tana magana kaman Haka “kayi hakuri ka aureta in yaso daka baya saika auri wacce kake so, kaida kake da daman auren Mata hud’u, daka biyu mafa akace ku Fara, uku hud’u….
Yace Mum yes I know but in zanyi auren sai a had’ani damai yaro, bazawara y’ar kauye wacce batai boko ba, “Mum ko kin manta a k’asar dana taso, bama wannan ba ko wanda ya taso mutum Mai ilimi Mai shiga waje daban daban yana bukatar mace Mai ilimi,”babu wanda zai yarda ya auri wannan matar Mai kama da monkey a matsayin mata
Mum shuru tayi, maganan yaron Nata duk da akwai rashin kunya babu da’a a ciki, amma ya fad’i gaskiya, “bai kamata a aura mishi wacce batai boko dinba, duk da tayi na addini, toh amma yata iya, tunda mijin Nata ya ku’ke ya kuma dage akai, kota bashi shawara baji zaiyi ba, kuma tasan indai aka d’aura auren kaman yanda Najeeb yace Wlh zai aikata sakinta zaiyi, tunda taga baya shakkan kowa balle yaji maganan mutane.
Najeeb yace Mum nidai gobe zan wuce, in kuna bukatar dole sai kun ban mata sai kuban dai dai ni, balle bana bukatar a zaba min matar dazan aura, ni dakai na zan zaba, “basai Kun zaba min ba, “inada idon da zan Zaba matar dazan aura dakai na, so Please kuban sometime zan Kawo wacce nakeso, in aura, yana fad’in haka yayi waje yana fad’in gobe zan wuce
Mum shuru tayi, ita yanzu abun yafi karfinta, “Toh maiya kamata tayi yanzu? ” Hmmm Gaskiya Najeeb yana bukatar mace Mai ilimin addini dana boko, duka”maganan dan nata hakane, “amma zataja bakinta tayi shuru, yanzu in tayi magana sai a Mata wani Fassaran, sai mijin Nata yaga kaman ita ke zuga shi, inta nuna itama abar maganan auren.
Karfe 9 dai dai duka iyalan gidan suna zaune akan dinning suna cin abinci, amma banda Granny dake zaune akan kujeran falon, sai Najeeb da baya wajan shima
Najeeb fitowa yayi daka d’akinsa, kai tsaye dinning ya nufa, gaida Dad d’inshi yayi tare da zama, Granny tace yaro dai kwanan nan zaka koya fulatanci inka aura Hanne..
Najeeb hararan Granny yayi domin yasan dashi take dan yaga idonta na kanshi
Tace ai ban San ka iya harara ba sai naga idon a k’asa miskili kawai, mummuna.
Zarah ta kwashe da dariya tare da fad’in kai Granny, kuma fah dake yake Kama
Tace wa?
Badai dani ba, wannan mummunan yaron mai miskilanci, ni ban son namiji kyakyawa da yawa wlh, in kyau yama mutum yawa sai kiga yayi muni.
Dariya Zarah ta saki, Sosai
Ita kam ibtisam ko magana batai ba, dan haushin Najeeb take Sosai, domin har yanzu hannunta bai daina Mata zafi ba, “ita gaba d’aya bata son taji ko maganan shi anayi ma.
Najeeb kam wayarshi ce ta Fara K’ara, d’auka yayi yaga Gina ce, yace I will call you back tare da kashe wayan.
Ibtisam kam tsaki tayi mara sauti, karaf a idon Najeeb, wani irin kallon tsana yayi mata, kwata kwata baya son yarinyar nan, bata da kunya da wani mummunar fuskanta.
Ibtisam ganin irin kallon da yayi mata yasa itama ta galla mishi harara tare da tashi tabar wajan ma, “Najeeb ji yayi kaman ya janyota ya mareta but Koba yanzu ba I will teach her a lesson, saina cire mata hannunta da taji ciwo idiot.
Dad yace maganan tafiyanka gobe Ina son ka d’aga, saboda tare zamu yola dakai.
Yace Dad mai zanyi a yola kuma?
Dad yace maganan daurin aurenka
Murmushi yayi tare da ciro wata takarda yace wannan takardan na rubuta saki uku, so idan kun d’aura auren saiku duba ku gani, “Dad Wlh bazan aureta ba in kuma kuka aura min ita Wlh nan take zanyi abunda za’ayi da’an sani, yana fad’in haka yabar wajan Fuuuuu
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Granny tace ikon Allah miye haka kaman iska, Mai yake fad’a ne?
Dad shuru yayi cikin bacin rai, lallai Najeeb yana son yayi Fito na fito dashi, ya kamata ya koya mai hankali
Mum bata ce komai ba, sai Zarah data tashi ta nufi Granny tana fad’a mata abunda Najeeb yace, tare da fad’in Wlh Granny tunda baya so inaga Ayi hakuri kawai kar Ayi abunda za’a zo ana dana sani.
Granny shuru tayi tana nazari.
Hanne ce ta fito ita da d’anta a hannu, Tace Sannunku?
Granny tace Hanne lafiya kuwa?
Tace nidai gaskiya bana son wannan auren, dan Allah ku maidani gida, wlh bana son wannan auren, ni nasan yafi karfina, kawai ku maidani gida
Granny tace ikon Allah, mai kike fad’a Hanne?
Tace eh ni bana son auren
Granny tace ikon Allah, keda nake tausayawa saboda d’anki shine kike fad’in haka?
Hanne tace Idan saboda d’ana ne, kawai a taimaka min yafi, bana bukatar inyi auren da ba’a sona, ni nasan yafi karfina nesa ba kusa
Granny ta tashi ta nufeta cikin sigar rarrashi Tana fad’in haka Hannatu kodai yayi miki wani abu ne? Karki damu Ina nan babu abunda zai faru ki kwantar da hankalinki Kinji Hanne na?…… Toh Bari muji yanda zata kaya
Plz need ur prayers Wlh banda lafiya