NAJEEB 18

Wajan karfe 10 da wani abu saiga kiran kabir ya shigo cikin wayar ibtisam, da sauri ta d’auki wayan ganin kiran kabir ne yasata sakin murmushi tare da fad’in kaman yasan Ina son magana dashi, “tashi tayi da sauri tabar d’akin dan suyi magana.
D’aukan wayan tayi tare da sakawa a kunne tana fad’in hello.
Kabir yace Barka da Safiya, ina fatan kin tashi cikin koshin lafiya tare da kwanciyan hankali.
Tace uhm lafiya kalau, kaifa?..
Yace Nima haka Alhmdlh,
I just call to hear your voice my ibti, I really miss your face and dat your smile
Murmushi tayi tare da fad’in yaushe na dawo? Harka Fara missing dina?
Yace Sosai kuwa, “nifa Inba gani Nayi ance yau an mallakamin ke a matsayin mata ba, toh bazan daina fargaba ba ko tsoro, wlh ibti a kullum Ina kwana da tashi tare da fargaba, da kuma tsoro cikin raina, kar ace wani ya kwace min ke “inko hakan ta faru ban San wani irin hali zan shiga ba,”Ina miki son da baki bazai iya fad’a ba, tunda nake ban taba son wata mace ba saike, “plz ibti karki yaudareni koki Bari wani ya canza miki ra’ayi akaina I really love you so much my ibti
Sonda nake miki shine yasa zanyi hakuri in jiraki ki gama karatu, badan komai ba sai dai hakan shine zaisa kiyi farin ciki, kuma hakan shine zai nuna miki cewa Ina sonki dagaske bada wasa ba.
Tace uhm nagode Sosai, sannan insha Allah bazan taba yaudaranka ba, duk rintsi duk wuya bazan taba juya maka baya ba, sai dai ban sani ba kasan kana naka Allah Na nashi,kuma na Allah shine dai dai.
Kabir yace wannan haka yake, tabbas kana naka Allah Na nashi
Ibtisam tace Abba yana son ganinka.
Yace ni? Ina fatan dai lafiya koh? Ba laifi nayi ba.
Ibtisam tace lafiya tare da fad’in Abba yaga wayan daka bani ranshi ya baci Sosai, ya kuma nuna cewa Ina son aure, wanda yace bazani karatun ba sai Nayi aure ku…. Sai kuma ta fashe mishi da kuka
Cikin tashin hankali ya fara rarrashinta tare da bata hakuri akan tabar kukan suyi magana.
Dakyar ta tsagaita dayin kukan tana shessheka
Yace my ibti plz tell me Mai yake faruwa?
Bata kulashi ba, sai sauke ajiyar zuciya da takeyi alaman har yanzu tana kukan
Yace my ibti cikin damuwa plz fad’amin inji komai ke faruwa plz plz
Tace Abba yace yana son ganinka, yace bana son karatu aure nake so, labarin abunda ya faru ta bashi
Kabir yace kiyi hakuri ibti Zanzo inga Abba sannan zan tabbatar dagaske nake son auranki, “Nasan bakya son kiyi aure yanzu sai kin kammala karatu ina sonki zanyi duk abunda kika ce “sai dai ina son ki sani ko ince zan ro’ki alfarma akan dan Allah Karki bari wani ya canza miki ra’ayi a kaina plz “ibti sonda nake miki yayi yawa idan na rasaki ban tunanin zan iya jura, “plz ki ri’ke min alkawari
Magana ta Fara cikin dashewan murya irin na wacce tayi kuka tace bazan taba yaudaranka ba, “domin Nima Ina Sonka.
Kabir jin tace Tana sonshi abunda bai tabaji ta fad’a mishi ba, “ido ya lumshe cikin jin dad’i.
Taci gaba da fad’in Nasan bakowa bane zai iya hakuri da abunda nace ba, nasai na Gama karatu inyi aure ba, na tabbata kana sona Sosai tunda har zaka iyamin wannan uzurin kum….. Sai kuma tayi shuru
Kabir yace inaji kuma me??
Tace ina jin tsoro Kar Abba yace bai yarda ba.
Murmushi yayi tare da fad’in karki damu, “amma ibti Indai kina sona dagaske inaga komai Abba ya yanke zakiyi na’am dashi, koda kuwa yace wannan satin zamuyi aure “bai kamata inga damuwa a tare dake ba, “karki manta Ina sonki kuma na fad’a miki tun Farko aure baya hana karatu.
Tace hakane aure baya hana karatu, “amma ni bana son in had’a Abu biyu aure da karatu nafi son in kammala karatun sai inyi auren
Ajiyan zuciya ya sauke tare da fad’in babu damuwa, ina sonki zanyi hakuri da duk abunda kika ce,”Zanzo jibi insha Allah inga Abba
Tace Allah ya kaimu
Ya amsa da Ameen tare dayi mata sallama, akan sai sunyi magana anjima
NAJEEB ne zaune akan gadon dake bedroom d’inshi, daka shi sai boxer babu riga a jikinsa, hannunshi ri’ke da kwalban alcohol yana sha, “turo kofar d’akin akayi wata yarinya ce ta shigo kallo d’aya mutum zai Mata ya gane balarabiya ce domin irin dressing din dake jikinta, jallabiya ne brown a jikinta sai k’aramin gyalen jallabiya din.
Nufan Najeeb tayi ta rungumeshi tana fad’in inata kira bakai picking ba.
Dan janyota yayi, Ido ya kura mata lokaci d’aya kuma ya sakar mata murmushin da yake k’ara mishi kyau, tare daja mata hanci “da sauri ta lumshe ido, “ganin haka Najeeb ya hura mata iska a fuska
Da sauri ta bud’e ido tare da sakar mishi murmushi tana fad’in I miss you Najeeb rabona dakai tun a Dubai wajan wata 10 fa kenan. “yanzu an kusa shekara
A hankali yace miye Abun mita ko korafi? Bayan kina tare dani yanzu?
Tace ina fad’a maka ne saboda na dade ban ganka ba, kuma Nayi kewarka Sosai da Sosai
Janyota yayi jikinshi tare da matseta Sosai, lokaci d’aya ya fara taba nononta da suke a mi’ke kuma a cike manya manya,”matsa mata su yake tare da murzawa babu abunda take sai lumshe ido tana sauke nishi sama sama, tare da kashe ido tana k’ara matse shi jikinta
Shiko Najeeb Sosai yake taba mata nonon domin yana matukar sonshi fiye da komai, musamman ya samu irin wanda yake so, manya gasu a tsaye, shi bako yaushe yake son yin sex ba, Indai zai samu nono ya taba yana wasa dashi, toh burinshi ya cika, wani zubin yakan biyema matan da yake hulda dasu ne dan yasan ya taso musu da sha’awa sai kawai ya biya musu bukata.
Dan sakinta yayi domin yaji k’aran wayarta dake ajiye akan gadon d’akin, kallon wayar yayi yaga an rubuta my love
Wani irin tureta yayi tare da tashi tsaye cikin bacin rai yace tashi kibar min gida
Tace Najeeb maiya faru?
Yace nace kibar min gida, and karki k’ara nuna kin sanni a rayuwarki, I hate cheaters.
Shuru tayi tana kallonshi cikin mamaki lokaci d’aya ta tuna da kodan Sunan da yaga ana kiranta da shine yasa yake ce mata cheater? Yes tabbas saboda shine “wani irin murmushi ta saki tare da fad’in Najeeb karka manta “am not your wife or your girlfriend am hare just to have fun me and you, “so miye Abun damuwa a ciki? Kodai kana sona ne? Tare da nufanshi Tana k’okarin tabashi.
Wani irin tsawa ya daka mata Wanda yasa gaba d’aya ta rud’e tare dayin baya da sauri danta tsorata Sosai dashi
Yace bana auranki, kuma bana sonki, so just leave from here tun Kafin in fitar dake dakai na
Cikin tsoro da yana yin daya sauya lokaci d’aya tace Najeeb “plz am so sorry plz, I don’t mean to hurt you, wlh Najeeb ina Sonka da yawa nasan ba lallai bane dama kaika soni ba, sannan wannan kiran daka ga anyi min is my Mum let call her kaji.
Danna wayar tayi tare dayin dialing number din sai gashi mace ta d’auka
Kallon Najeeb tayi alaman kaji koh? Bana miji bane.
Najeeb sauke ajiyan zuciya yayi, domin a duniya ya tsana yaudara baya son yaga abunda yake Nema yana tare da wata, shi koda baya son Abun Indai nashi ne Toh baya son wani ya taba sai dai inya Bari
Bayan ta gama wayan ta nufeshi tana fad’in am sorry Najeeb, ina Sonka Sosai
Dan janyeta yayi jikinshi tare da bar mata bedroom din alaman har yanzu yana fushi da ita
Ido ta bishi dashi tana murmushi,lallai Ina son Najeeb, inda zai aureni da nafi kowa Sa’a, ji yanda ya nuna kishi a kaina, ido ta lumshe cikin jin dad’i.
Kabir yazo garin Kano, kuma a yau yace zaiga Abba domin suyi magana
Abba da kanshi yakai Zarah kaduna, domin an fara lecture, amma ita ibtisam ya hanata zuwa, taci kuka harta gode Allah
Yace aure take so kuma shi zatayi, “har mum saida ta kirashi amma yace tayi hakuri, domin ibtisam ta bashi mamaki, bai taba sanin tana kula wani ba saida ummi ta nuna mishi wayar daya bata ,”duk da Mama ta sani shima ya kamata ace ya Sani, “in saurayi zai dinga yima yarinya hidima haka ba tare da yaga iyayenta ba, ko ince ya turo magabatanshi ba, ya dinga bata Abu Tana ansa ai dole iyaye suji tsoro, “kuma a haka Tana gabanmu Idan taje jami’a saiya kuma?
Mum dai taita bashi hakuri akan yabarta ta wuce skul domin lecture yana wuceta
Abba yace sai yaga yaron da take tare dashi, daka nan sai ya yanke hukunci akan abunda ya dace
Granny kam Murna takeyi sai faman zuga Abba take akan Ayi ma ibtisam aure yafi,.
Saboda takaici ibtisam ko kula Granny batayi.
Yau da daddare wajan karfe 8:30 saiga kabir shida wani Kanin mahaifinshi Sun hallara a gidansu ibtisam
An saukesu a falon ba’ki, inda Abba da wani Abokin shi suka tarbesu, domin ganin irin shigarsu Kabir din ya nuna ma Abba y’an gidan mutunci ne “wani abunda ya k’ara burge Abba da kabir din gaba d’aya ya’ki zama akan kujera a k’asa ya zauna, Abba yace tashi kahau kujera mana
KABIR yace a’ah Abba nan ya isa
Kawun Kabir addu’a ya fara sannan ya fara fad’in nine k’anin mahaifin Kabir, kwanaki ya Sanar dani Akwai yarinyar daya gani yana so, kuma yana son muje muga iyayenta.
Toh a lokacin nace mishi zanyi tafiya Amma inna dawo zanje insha Allah, bayan na dawo ban zauna ba, sai shekaran jiya nace ya kamata dai inzo, sai ga kiranshi akan ance in turo
Abokin Abba yace Allah sarki, dama abunda yasa muka bu’kaci ya turo saboda mu tabbatar dagaske yake ko wasa, domin mudai yarinya ta isa aure kuma auren za muyi mata
Kawun Kabir yace madallah, Abu yayi dai dai kenan ,domin muma abunda muke fama kenan, domin mutuncin mutum saida iyali
Abokin Abba yace hakane, kam gaskiya
Nan dai sukai magana, inda Abba Shima yayi magana akan aure Zaima y’arsa.
Inda kawun Kabir yayi magana akan su a shirye suke
Abba yace Toh Alhmdlh, nan dai suka k’ara gabatar da junansu.
Kabir yace Abba Ina neman alfarma.
Abba yace name?
Yace Abba Ina neman alfarma abar ibtisam ta tafi makaranta
Abba yayi shuru can yace kabiru zata makaranta amma a d’akinta domin nidai ba’a gabana ba
Jin haka yasa kabir yin shuru domin yasan tunda yace haka, bai kamata ya k’ara cewa komai ba, domin ba Abokin musunshi bane, ko kuma yana fad’a shima yana fad’a ba, “amma yaso abar ibtisam ta tafi makaranta
Nan dai suka tattauna inda sukai sallama akan zasu dawo bada dad’ewa ba
Koda kabir suka tafi, yana zuwa Gida ya kira ibtisam d’inshi
Bayan ta d’auka yace ibti yanzu na dawo gida daka wajan Abba.
Tace Sannunku da dawowa
Ya amsa da yauwa, sannan yayi shuru na wani lokaci, “Kafin ya fara magana ibti Abba ya’ki yarda akan maganan makarantar ki, yace sai dai kiyi a d’akin ki.
Itbisam hawaye ta farayi domin tasan tunda Abba yace haka, ko zata mutu bazai canza magana ba, shikenan yanzu zatai aure tare da karatu abunda batai taba tunani ba, gashi zai faru da ita yanzu.
Kabir yace ibti kiyi hakuri, sannan Ina son ki sani koda anyi auran ba gari d’aya zamu zauna ba, saboda karatun ki karki damu insha Allah auran bazai kawo miki matsala ba a cikin karatun naki ba
Ibtisam tasan bata da wani mafita yanzu Illa ta amince da auran kaman yanda Abbanta yace, yama zaman mata dole tunda ko taso ko bata soba, dole auren Abba zai Mata tunda ya furta bata da wani option
Kabir ya katse mata tunani da fad’in ibti just trust me, komai zai tafi normal, bazaki samu wata matsala a karatun kiba I promise insha Allah
Tace Allah yasa hakan shine alkhairi cikin muryan kuka
Kabir ya amsa da Ameen cikin jin dad’i, dan yasan tunda tace haka ta amince kenan” dan haka dole cikin satin nan ya turo a Gama magana, domin yana son inya turo a barta ta Fara skul Kafin Ayi auren duk da ba wani lokaci Mai tsawo yake son akai bikin ba, abunda zai kawo tsaiko danma bai k’arasa ginin da yakeyi ba, amma yanzu dole yaba Abun muhimmanci Ayi a gama ginin domin yasa ibtisam a ciki
Yace ibti yanzu sai in turo ayi komai saboda in nemi izinin ki koma makaranta koh?
Tace eh da sauri
Kabir murmushi yayi domin ya Lura da yanda take mutuwar son tayi karatu Sosai.
Kabir ya turo an kawo kud’in gaisuwa dana sadaki, duk da Abba baiso amsan kud’in sadakin ba saboda yace shi yafi son a bada ranan daurin aure, “da yake harda Dad cikin masu amsan kud’in shine ya amsa dubu d’ari na sadaki, inda aka tsaida wata biyar na auran ibti da kabir
Inda iyayen Kabir suka nemi alfarma a barta ta tafi makaranta.
Dad yace babu damuwa, ai tunda an amshi sadaki, shaidu Kawai muke jira yanzu.
Abba dai baice komai ba, Bayan iyayen Kabir Sun tafi Dad yace dama ba tafi skul ba?
Abba yace eh
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Dad yace akan wani dalili? Kuma Zarah bata fad’amin ba
Nan Abba ya bashi Labarin abunda ya faru.
Dad yace Allah ya kyauta, yanzu dai saita tafi gobe, “koda yake dakai na zan kaita goben sai in wuce Nima
Tashi Dad yayi yana fad’in Bari inyi musu sallama Kafin in tafi inje in huta….