NOVELSUncategorized

NAJEEB 25

Zarah tsayawa tayi tana kallonta cikin mamaki, “lokaci d’aya tace ikon Allah, kai Indai ana son ganin fushin ibtisam toh a had’ata da Najeeb, ace sun dace, dariya Zarah ta saki lokaci d’aya sannan tayi gaba itama 


Koda ta k’arasa ganin ibtisam tayi dasu Aisha a cikin d’akin, “inda Aisha take tambayan ibtisam ina wannan handsome cousin din naki? 

Ibtisam tace Idan Zarah tazo ki tambayeta yayanta ne…. 

Shigowan Zarah ne yasa Aisha fad’in yauwa Zarah naji dad’in ganinki, “wlh tun jiya na k’osa ku dawo sai naga baku dawo ba, yanzu ibtisam ke fad’amin kunje kaduna ne 

Zarah tace eh bata wlh

Aisha tace Zarah naga brother d’inki Kai Wlh ya had’u Sosai, plz ki had’ani dashi mana 

Zarah murmushi tayi cikin ranta tace aikam Indai Najeeb ne yafi karfinki domin keda kika watsar da kanki kizo kice kina sonshi, Allah ya kyauta, “amma a fili sai tace uhm karki bada mata mana 

Aisha tace Wlh Indai akan dan uwanki ne wlh zan bada mata kam, “Dan Allah Zarah ki had’amu dashi, “wlh sonshi kawai naji Inayi 

Zarah tace toh fah

Aisha tace ki taimaka min da number d’inshi 

Zarah tace aishi baida number d’aya, domin baya zama waje d’aya 

Aisha tace miye aikinsa? 

Zarah tace pilot ne 

Aisha tace wow, Toh plz ki bani number d’inshi na Nigeria 

Zarah fad’a mata tayi, domin tasan indai Najeeb ne gata gashi 

Ibtisam kam sai taji tausayin Aisha ya kamata, ita ta rasa wanda take so sai wannan mara imanin, mara tausayi Wanda bai san darajan dan Adam ba, lalle Tana da aiki, inda tasan Waye shi dako kallo bai isheta ba, miye ma Abun so a tare dashi? Tsaki ta saki mara sauti 

Karfe hudu dai dai ibtisam ta tafi lecture wanda Dr jibril ne ya shigo musu, bayan ya gama lecture ya bu’kaci ibtisam ta sameshi a office 

Koda ibtisam taje office d’inshi tayi nocking, “bada izinin shigowa yayi 

Kai tsaye ibtisam ta bud’e kofar sannan ta shiga, “gaida Dr jibril tayi 

Idonshi na kanta ya amsa tare da nuna mata kujera ta zauna.. 

Ibtisam zama tayi

Dr jibril baice mata komai ba sai rubutu da yayi tayi, a kalla yayi minti Goma yana rubutu sannan ya d’ago ya kalleta tare da kiran sunanta da Amina.. 

Amsawa tayi da na’am sir 

Yace Amina Mai yasa kike son bata rayuwarki? Koma ince kin bata, keda y’ar uwarki 

Kallon mamaki take mishi alaman bata gane abunda yake nufi ba 

Yaci gaba da fad’in, “koda kika ga ina biye miki, ina son hulda dake badan komai bane sai yanda naga irin nutsuwarki, da kunyarki, Ashe ba haka kike ba a cikin zuciyarki ….

Amina a yanda na fahimta, koma ince gidanku kaman dakyar aka barki kika zo skul, na tabbata gidanku gidan tarbiya ne, koda ka irin firan da naji kinayi kwanaki keda granny d’inki, “is lyk ba’a son kizo skul but an barki kinzo shine kike son cin amanar iyayenki kika Fara bin kawayen banza Kece har tafiya kaduna 

Da sauri ibtisam tace sir bani d’aya naje ba, wlh nida Mum ne da Zarah 

Kallonta yayi cikin mamaki yace a wajan garage din Kawo na ganku kuna fitowa zaku shiga mota 

Ibtisam Labarin abunda Ya faru ta bashi, lokaci d’aya hawaye ya siraro mata, wanda bana komai bane sai na zarginta da yayi da Farko, Koba komai a zargi mutum abunda ciwo Sosai 

Dr jibril ido ya kura mata, yana kallonta yanda take hawaye, “lokaci d’aya ya sauke ajiyan zuciya tare da fad’in miye na kuka ibtisam??  Yau ce rana ta farko daya kirata da ibtisam 

Kasa magana tayi balle ta bashi amsa 

Dr jibril yace ibtisam abunda yasa na kiraki har nake fad’a miki haka, because ina miki kallon sister na, so am so sorry Kinga inda bakiyi min bayani ba zanyi ta miki wani irin kallo 

Ibtisam ta share hawayenta tare da fad’in hakane, ngd daka fad’amin 

Nan Dr jibril yaita bata shawara akan ta k’ara kame kanta akan kawayen banza, “daka karshe ya bata umarnin ta tafi, “koda ta tashi da ido ya bita har saida ta bace ma ganinsa 

Ibtisam da Dr jibril yanzu sun saba Sosai, har takanje office d’inshi tayi mishi tambaya wani zubin, “inda su Aisha suke fad’in soyayya suke ita da Dr jibril din 

Duk yanda ibtisam tayi musu bayani akan ba soyayya suke ita da Dr jibril d’inba sunki yarda Dan haka kawai ta barsu a haka dinne,.

Su ibtisam Sun Fara exam gaba d’aya koda yaushe bata samun kanta saina karatu kullum suna cikin karatu ba dare ba rana 

Kabir ya kawo mata Katin biki danta rabama friends d’inta, “amma ibtisam ta’ki bama kowa, inda Zarah tace abama su Aisha Katin 

Ibtisam tace a’ah bata so ta gayyaci su Aisha, domin wlh Idan Abba ya gansu zaice da y’an duniya nake kawance 

Zarah taci dariya tare da fad’in Allah ya kyauta, “in mun dawo skul zasu San kinyi aure ai, zaki sha ciwon baki, suce baki fad’a musu ba 

Ibtisam tace karki damu Nasan yanda zanyi musu kawai Kedai kiyi shuru dan Allah karki fad’a musu 

Zarah tace shikenan, Nina k’osa ma muyi hutu wlh muje mu fara shiri dashi yanzu saura sati uku 

Ibtisam tace uhm nikam ko kad’an ban k’osa ba wlh

Zarah tace uhm wai irin gulman nan na amare 

Ibtisam tace Wlh dagaske nake 

Zarah tace “kabir fah zaki aura masoyinki, Wanda kike so, kuma kike k’auna, wanda kuke burin mallakan junanku “ko yanzu dai an rage sonshi ne? 

Ibtisam tayi murmushi tare da fad’in ko kad’an, wlh Zarah ina matukar son kabir, tsantsar so nake mishi, bazan iya kwatanta miki irin sonda nake ma kabir ba, but zan iya cewa sonshi yana tafiya tare da jinin jikina ne, domin daka ranan da sonshi ya fita ina tunanin nabar duniya kenan, domin jinin dake gudana a jikina ya tsaya cak…. 

Zarah tace ikon Allah, haka kike son kabir din? Ah lallai Kabir yayi Sa’a Sosai 

Ibtisam murmushi tayi tare da fad’in, ko kuma kice Nayi Sa’a ba, domin na samu namiji kamili, bai tabamin maganan banza ba, wanda da yawa mazan yanzu in suka had’u da yarinya maganan banza ke kawo su 

Zarah tace hakane kam, sai dai muyi fatan Allah ya had’amu da maza na gari 

Ibtisam tace Allahumma Ameen.

Kullum Aisha bata da hira yanzu saina Najeeb tare da k’ara fad’a musu yanda take sonshi, da kuma irin haduwarshi, gashi kullum ta kira baya d’auka 

Shi kam Najeeb a duniya ya tsani yaga aita kiranshi da yawa, sai yaji kawai baya bukatar d’aukan wayar, domin kuwa a cewarshi Indai aka kira mutum sau d’aya sau biyu bai d’auka ba, saika barshi yana uzuri, inya gani zai kira, “amma bawai kaita kira ba, yana ganin kira da wata number wanda bai sani ba, baya d’auka ne kawai saboda baya son yawan kira, sannan yasan koma Waye mistake din number yayi domin Najeeb waya Sani a Nigeria balle ya kirashi, duk Wanda ya sani yana da number d’insu, saina ibtisam dana Granny da baida shi. 

Najeeb wannan karan shi d’aya yazo, ba tare da y’an matanshi ba, dan haka sai yaji kwata kwata baiji dad’in k’asar ba, dan haka ya yanke zai koma jibi kawai.

Ranan dasu ibtisam sukai hutu harna wata d’aya da sati d’aya, haka suka dinga sallama da kowa, yayinda wasu ke murna zasu gida, sukam irinsu Aisha haushi sukeji, domin Sun san idan suka koma Gida babu runs, dole a kame Kai sai an dawo skul 

Ibtisam office din Dr jibril taje amma bata sameshi ba, dan haka ta tura mishi message da fad’in “sir I come to your office but you are not around, “nazo Nayi sallama, but mun wuce sai an dawo skul, Tana fad’in haka ta tura mai sa’kon sannan ta wuce tare da saka wayan cikin jaka 

Ibtisam da Zarah motar Haya suka shiga, inda suka tafi Kano, domin dai Zarah tace Tana tare da ibtisam tunda biki ya matso.

Koda su ibtisam suka isa Gida, basu suka kaiba saida yamma, gaba d’aya a gajiye suka k’arasa gida, domin motar da suka shiga batai wani gudu Sosai ba 

Granny ganin su ibtisam da zarah yasa ta saki gud’a tare da fad’in kunga Amarya wajan kabiru 

Ibtisam da gudu ta nufi Granny din tayi hugging dinta tana fad’in wayyo Granny I miss you so much wlh 

Granny tace karki karyani miye kuma nis ziyu

Dariya ibtisam da Zarah suka saki, sannan ibtisam tace Granny ina nufin Nayi kewarki da yawa 

Granny tace au yanzu na gane 

Nan sukai ciki inda suka zauna a falo sunata fira harda ummi.

Koda ibtisam suka shiga d’aki ta ciro wayarta cikin jakarta Wanda tunda ta saka wayoyinta cikin jaka bata K’arabi ta kansu ba, sai yanzu, ganin misscall  d’in Dr jibril tayi har guda biyu, sannan message d’in da shima yayi mata kaman haka… 

Plz just give me 5minnute muna meeting, I need to see you before you leave.

Koda ta gama karantawa ido ta lumshe alaman kash mai yasa nasa wayar cikin jaka? Gashi banji kiranshi ba and banda message d’inshi ba, kiranshi tayi amma taji baya shiga har sau biyu tana kira amma not reachable dole ta hakura ta barshi

Tun daka ranan da ibtisam ta dawo aka fara Mata gyaran jiki, su dilka

Gefen maganin Mata kuma Granny tace baza’a bata wani abu Sosai ba, tunda budurwa ce, kar a wahalar Mata da jika, gwara inta tare da sati biyu sai ta Fara shan maganin Mata, granny Tana gyara ibtisam Sosai, kaman yau ibtisam da Zarah na zaune saiga Granny da wani magani tazo tana fad’in firan Mai akeyi ne haka? 

Zarah tace firan duniya mukeyi da kuma yanda biki zai kasance 

Granny tace ai ranan saina taka rawa, “lokaci d’aya kuma ta saki gud’a 

Ibtisam dariya ma Granny ta bata, tare da fad’in ai dole ki taka rawa tunda burinki ya cika za’ayi min aure, kinyi nasara 

Granny tace Wlh kuwa, kaman kin sani, yarinya ai bazaki gane ba, sai an d’aura kin shiga daka ciki, zaki gane banbancin aure da kuma rashin aure, “wlh ibtisam babu abunda yakai dad’i yau a duniya kaman ace mutum na d’akin mijinshi, cikar mutum saida iyali, “yau ki duba koda namiji ne In baida iyali duk dukiyarshi sai kiga ana mishi wani kallo, in ba’ayi wasa ba sai kiga ana zargin mutum, wanda ba komai yaja mishi ba sai rashin iyali da bai dashi 

Zarah tace Wlh hakane Granny ai cikar mutunci shine gidan miji, sannan in mutum Nada aure ana mutunta shi Sosai, fiye da wanda bai dashi 

Granny tace yauwa y’ar albarka, “Kema Bari a Gama na takwarata sannan in dawo kanki keda wancan dan banzan miskilin, ni naji ance yazo yana nan koya koma? 

Zarah tace kaman yana nan fah, dan munyi waya dashi d’azu amma yace cikin week dinnan zai koma 

Granny tace saboda tsiya bazai tsaya Ayi auran ibtisam ba, Kafin ya koma? 

Zarah tace Granny ai saiki kirashi kice karya koma ya jira 

Granny d’auko yar karamar wayarta tayi tana fad’in kiramun mamanki tare da mi’ka ma Zarah wayar 

Zarah saka number d’in Mum tayi tare da dialing number din sannan ta mi’ka ma Granny 

Ringing uku Mum ta d’auki wayar tare da sallama, tana gaida Granny 

Granny amsawa tayi, tare da fad’in “Ina miskili? 

Mum tace yana d’akinsa…  Yauwa gashi ya fito ma in bashi wayar ne? 

Granny tace a’a koya amsa wayar Mai zaice? Koni Mai zance Mai tunda ba yaran juna muke jiba

Mum dariya tayi tare da fad’in hakane Mama, Yadai kamata ki koya wannan yaran na Najeeb 

Granny tace wa? Allah ya kyauta barni da nawa Yaran, kina jina?

Mum tace eh inaji Mama 

Granny tace ki fad’ama miskili ya tsaya Ayi bikin ibtisam Kafin ya tafi, “naji Zarah tace Zai koma…. Kallon Zarah tayi tace yaushe ma kika ce zai koma? Fassara min d’azu naji turanci kikayi 

Zarah dariya ta saki sannan tace cikin satin nan, “Granny tace yauwa kina jina 

Mum da itama Dariyar takeyi tace eh inaji 

Granny tace cikin satin nan zai koma, kice ya tsaya Ayi bikin dashi, dan naga shi baya son zumunci sai rashin mutunci ya iya 

Mum tace zan fad’a mishi yanzu sannan sukai sallama da Granny 

Mum kallon Najeeb tayi dake zaune yana danna waya, tace Najeeb yanzu mukai waya da Mama 

Kallon Mum alaman wace Mama kuma? 

Mum kaman tasan abunda yake nufi tace da Granny mukai waya, tace in fad’a maka ka jira Ayi bikin ibtisam dakai 

Tsaki Najeeb ya saki tare da fad’in that old woman sai kuma ya kuma sakin wani tsakin tare da fad’in bazan tsaya ba akan Mai zaisa in tsaya? Mum ki fad’a mata nace bazan tsaya ba, ina ruwana da wani biki? Miye nawa a ciki da zan tsaya? Plz Mum ni inada abunyi 

Mum tace Najeeb bikin y’ar uwarka nefa za’ayi, kake fad’in haka 

Yace Mum banda business da bikin, saboda biki sai inki tafiya wajan aiki? 

Mum tace zaka iya d’aukan excuse ai Najeeb, inaga hakan zaiyi 

NAJEEB yace no Mum gobe zan koma, bazan zauna ba, sannan aure kuma Allah ya bada zaman lafiya, I have nothing to do with d weeding infact yarinyar da bata da kunya why will I have to attend her wedding 

Mum tace toh fah, kai kowa kace baida kunya?lallai kam amma k’aryar mutum yace ibtisam bata da kunya yarinya mai ladabi 

Najeeb tabe baki yayi 

Mum taci gaba da fad’in aure ne dai kace bazaka tsaya ba, amma kar ka k’ara fad’in cewa ibtisam bata da kunya domin kuwa tana dashi Sosai ga girmama na gaba 

Najeeb yanda Mum take Yaban ibtisam sai Abun ya bashi mamaki da dariya kuma, cikin ranshi yace Mum bata san wacece wannan yarinyar bace, green snake kenan 

Hhhhh kunji NAJEEB wai ibtisam ce green sneak 

Granny Bayan ta gama wayar ta mi’ka ma ibtisam maganin dake hannunta, tace gashi Kinga nama manta na tsaya fira gashi ki dinga tsarki dashi 

ibtisam tace Granny miye wannan kuma? 

Granny tace maganin sanyi ne, kin San yanzu idan Mace Nada sanyi saiya rage mata ni’ima, kiga miji yana Abu da mata baya jin dad’i 

Ibtisam kam kunyar maganan Granny taji 

Granny ta lura da hakan tace yama kuke kiran abunda da turanci? 

Zarah tace infection 

Granny tace yauwa shi, ai mugun ciwo ne, kusan yawanci mata na d’auke dashi, wasu sun sani wasu basu sani ba, sai dai muce Allah ya kiyaye, “Dan haka ke ibtisam saiki Fara maganinshi 

NOTE: yana dakyau in yarinya zatai aure tayi treating infection, kije hspt a dubaki aga ko kina dashi, ko baki dashi, inko kina dashi ki nemi magani Kafin aure, domin infection yana rage ma mace ni’ima Sosai, bawai aita dura ma yarinya maganin Mata ba, a’ah ku nema Mata maganin sanyi, domin duk maganin da zaku bata babu abunda zai Mata Indai tana da infection, domin yakan saka ni’imar mace ta daskare, gashi kunyi ta dura mata maganin Mata, wanda zai tursasa ni’imar fita, gashi tana da infection ya’ki fitowa sai yaita sama yarinya ciwon ciki da sauransu, “so plz maganin Mata bashi bane, Nop kuyi maganin infection shine babban matsalan, da yawa Mata na complain akan matsalan wata tace tayi na asibiti baiyi ba wata tace tayi na gida shima baiyi ba, y’ar uwa saifa kin dage, domin infection ba lokaci d’aya yake tafiya ba, shigarshi baida wuya amma fitanshi akwai wuya, musamman masu abokiyar zama, inke kina magani keda miji, ita abokiyar zamanki batayi Kinga infection bazai barki ba, sai dai ya ragu, so mata ku daina wani rubibin siyan kayan mata, just ki tsaya ki nemi lafiya daka wannan cutar ta infection 

Najeeb kam kaman yanda Ya fad’a Washe gari yabar k’asar domin shidai bazai iya zama ba, gashi babu giya babu y’an mata, dole yasa ya koma inda yafi wayau 

An fara hidiman bikin ibtisam da Kabir, ibtisam tayi wani mugun cikowa, tare da wani haske Tana shinning, lallai anyi mata gyara ko Ince ana kanyi, ibtisam gaba d’aya ta saki jikinta Sosai ana hidiman da ita, dan tasan Kabir bata da matsala dashi akan karatun ta.

Yau za’a kawo kayan akwati  dan haka ibtisam da Zarah suka bar gidan gaba d’aya, suka shiga kasuwa, Dan suyi siyayya 

Zarah da ibtisam suna wani shagon siyan Gyale domin Zarah zata siya, saiga kiran Dr jibril ya shigo wayan ibtisam mamaki tayi domin tunda ta kirashi baije ba tun sanda sukai hutu bata K’ara kira ba, dan haka ta d’auka tare da sawa a kunnenta 

Tace ina wuni sir? 

Dr jibril ya amsa da lafiya Amina, ya gida hope ana karatu a gida? 

Ibtisam tayi dariya tare da fad’in eh munayi sometimes

Yace sometimes kuma? 

Tace eh sir kasan ba kaman a skul ba,  nan mutum yana gida, koka Fara wani abun zai taso dole ka bari kaje kayi, ga kuma Aiki, Kaga duk a skul babu wannan 

Yace you are right, I just call to say hi 

Ibtisam tace nagode sir, tare dayi mishi sallama 

Zarah ta kalli ibtisam Bayan ta kashe wayan, tace Dr jibril neko? 

Ibtisam tace eh 

Zarah tace yasan ko zaki aure kuwa 

Ibtisam tace a’a nifa babu wanda ya Sani a skul 

Zarah tace inaga yana dakyau ki fad’ama Dr jibril zaki aure 

Ibtisam tace akan wani dalili zan fad’a masa? 

Zarah tace saboda wlh mutumin nan koda bai fad’a ba, sonki yakeyi 

Tsaki ibtisam taja tare da fad’in kema kin Fara biyema su Aisha koh?.. 

Zarah tace ba haka bane, na dad’e Ina nazari akai, amma ina Mai baki shawara ki fad’a Mai zaki aure domin…. Toh wai miye na boye boyen zaki aure ne ma

Ibtisam tace Kinga malama biyashi kud’inshi mu tafi inada abunyi 

Zarah tace uhm Allah ya kyauta tare da biyan kud’in gyalen suka fita

Shop rite, suka je daka kasuwa, inda suka fara siyayyan kayan za’ki, duk dan su bata lokaci kar suje gida da wuri, tunda 4 akace za’a kawo akwatin.

Y’an Kawo lefe Sun kawo akwati goma sha biyu, aka kawo set biyu kenan, gaskiya kabir yayi k’okari domin ya zuba kaya na Kece raini, anba ma y’an Kawo akwati abunda aka tanada na ciye ciye tare da kud’i wanda ake badawa na tukwici 

Au ibtisam sai wajan 6 suka dawo gida a gajiye, suna shiga toilet ibtisam ta fad’a domin tayi wanka, dan KABIR yace zaizo anjima 

ita kam zarah kayan akwati ta tsaya gani tana fad’in ibtisam anyi goshi gaskiya kayan sunyi kyau, domin kaya ne masu tsadan gaske KABIR yasa ma ibti d’inshi 

Koda ibtisam ta fito daka wanka, bata koje inda kayan lefen suke ba, domin kunya takeji, Toh akan wani dalili ma zata tunda Nata ne, kuma tare dasu za’a kaita 

Wajan karfe 8 da wani abu saiga kabir yazo wajan ibtisam, kiranta yayi a waya tare da fad’in ina waje 

Fita tayi Kai tsaye hijab ne a jikinta domin wando tasa da top saita d’aura hijab, “Kai tsaye cikin motarshi ta shiga inda ta ganshi shi d’aya tace yazo su shiga falon ba’kin dake gidansu.

Kabir yace a’ah nazo ne kawai na ganki, in wuce Nayi missing d’inki Sosai 

Murmushi ibtisam tayi tare da fad’in yaushe ma ka shigo Kano baka fad’amin ba sai d’azu naji ka kira zaka zo. 

Kabir yace Wlh Ina zaune kawai naji Ina son ganinki 

Ibtisam murmushi tayi tare da satan kallonshi taga shima ita yake kallo 

Da sauri ta juya tare dayin k’asa da kanta 

Kabir kam dariya yayi danya ganta sanda take kallonshi domin idonshi na kanta, “a hankali yace ibtisam bazaki iya kallon mijinki ba na wani lokaci? 

Uhm kawai tace tare dasa hannunta a fuska ta rufe tana murmushi 

Jin hannun Kabir tayi akan hannunta ya ri’ke yana k’okarin cire mata hannunta akan fuskanta 

Gabanta taji ya fara dukan uku uku, domin tunda take dashi Bai taba Taba mata jiki ba sai yau, harya cire mata hannun nata daka fuskanta kanta a k’asa ta kasa koda d’aga kanne domin ta rasa mai takeji a halin da take yanzu 

Hannunshi yasa ya d’ago Mata da fuskanta tare da juyo da fuskan Nata tana kallon nashi, ido suka had’a, da sauri ta lumshe idonta domin bazata iya kallon idonshi ba dan ko yanzu data kalla saida taji wani irin mugun faduwan gaba 

Shiko kabir idonshi na kanta, wani irin sonta ne ke fusganshi ji yake kaman yayi hugging d’inta, “lokaci d’aya ya saki murmushi tare da kiran sunanta da ibti plz open your eyes I need to see it 

Ibtisam bata bud’e idon ba,haka bata motsa ba, domin gaba d’aya jikinta a mace yake tunda kabir ya tabata, mamaki take cikin ranta tare da fargaba, ko ince sabon al’amari daka Kabir din data gani yasa ta kasa wani kwakwaran motsi. 

Kabir kam har yanzu idonshi nakan fuskan ibtisam yana kallonta, wanda idonta yake a lumshe, lokaci d’aya yasa bakinshi cikin nata ya fara kissing d’inta 

Ibtisam da sauri ta bud’e idonta tare da k’okarin tureshi amma ta kasa, a kalla yayi wajan 2mnt yana tsotsan bakinta, tun tana tureshi harta Fara hawaye….. 

Lokaci d’aya ya saketa.

Ibtisam ganin ya saketa yasa ta Fara k’okarin bud’e kofar amma ya danna luck, wanda kofar ta kasa buduwa 

Kuka ta saki Sosai tare da fad’in ka bud’emin kofa in fita 

Kabir janyota yayi jikinshi 

K’okarin tureshi ta farayi amma ya ri’keta dakyau wanda yasa ta kasa kwatan kanta, dole yasa ta tsaya tare da k’ara kwantar da kanta akan jikinsa tana kuka 

A hankali yace am so sorry my ibti, na kasa controlling kaina, plz forgive me, sonki yasa nayi hakan amma ba halina bane ibtisam 

Bata ce mishi komai ba, sai dai kukan da takeyi yad’an lafa, ba kaman daba 

Nan yaci gaba da rarrashinta, cikin ranshi kuwa k’ara godema Allah yayi domin ya tabbata ibtisam koda baya nan zata ri’ke mishi kanta, duk da yana fama da so da kuma burin kasancewa da ita, yayi hakan ne danya gwadata kuma Alhmdlh taci jarabawan 

Domin inda ta yarda batai k’okarin hanashi ba, zaiji tsoran auranta domin zaiga bazata iya ri’ke mishi kanta ba, toh yanzu Alhmdlh gashi harda kuka takeyi danya Mata kiss Wanda shi d’aya yayi mata bata maida mishi martani ba, sai k’okarin cire bakinta daka nashi da tai tayi 

A hankali ibtisam ta janye jikinta daka nashi tare da saka hannunta Tana share hawayenta 

Mi’ka mata tissue yayi 

K’in amsa tayi tare da fad’in plz ka bud’emin kofar Ina son shiga gida 

Kabir yace ibtisam wai wannan fushin da kikeyi na miye? Karki manta nine Zan aureki nan da kwana biyar za’a d’aura auranmu, toh miye dan nayi kissing d’inki is nothing b…. 

Ibtisam ta Katseshi tare da fad’in may be Kai a wajanka ba wani abu bane, kabir ina son…. Murmushin da kabir yayi shine yasa tayi shuru ba tare data fad’i abunda tayi niya ba

Kabir murmushi yayi domin jin ta kira sunanshi Kai tsaye abunda bata tabayi ba kenan, 

Kabir yace ina son ki sani ibtisam ni kabir nine mijinki insha Allah, Ina son ki fahimci wani abu, wlh ibtisam ina sonki dagaske ban taba tunanin koda da minti d’aya bane ni in cutar dake ba, so ina son ki sani sonki a jinina yake, nayi miki kiss just to know who you are, in zakiyi min adalci how many month na sanki, but ban taba attempting na in taba koda hannunki ba.

Ibtisam shuru tayi tana jinshi lallai abunda kabir ya fad’a hakane, bai taba tabah mata jiki ba sai yau, ido ta lumshe cikin jin kunya wannan ne rana ta farko dana miji yayi kissing d’inta, gaba d’aya jikinta wani iri yake mata, damma anyi bada son ranta ba hhhhh

Kabir yace my ibti plz forgive me 

ibtisam cikin murya wacce tayi kuka, tace ina son hakan Karta kuma faruwa, plz karka manta Idan mace dana miji suka kebe na ukunsu shaidan ne, ina jin tsoran karmu aikata abunda zai haramta auranmu, ko kuma muyi abunda za muyi dana sani, ban taba fad’a maka wannan Abun ba but yau zan fad’a maka, “bazan iya juran in rasaka ba, ni nasan Sonka a jini na yake, ban San ya kakeji a tare dani ba, but ni Ina jinka duka ilahirin jiki na, nasan abunda nake fad’a mata bako wace mace zata iya fad’ama namiji gaba da gaba ba, ina fad’a maka hakan ne domin kasan irin sonda nake maka, sannan kuma karka k’ara aikata abunda kamin yau, domin bazan iya juran rasaka a rayuwa ta ba,”ban taba son wani namiji ba sai kai, ban San so ba sai a kanka, Dan Allah Ina son karmu aikata abunda za muyi dana sani, wlh Ina jin tsoran abunda zai rabamu sai kuma ta saki kuka mai sauti 

Gaba d’aya KABIR rudewa yayi tare da rungumo ta jikinshi yana fad’in ibtisam ni nasan abunda nayi miki Allah shine shaida na bada wani mugun abu nayi miki ba, sannan ina son ki sani bazamu aikata abunda za muyi dana sani ba, “ibti Kece mace ta farko Nima dana Fara so, duk da y’an mata da dama sunce suna sona, amma Kece naji Ina So, kuma nake burin aure, ban taba tunanin inyi wani abun da zai zama Abun kunya gareni ni dake ba, yau Ina cikin farin ciki my ibti ta fad’amin irin sonda take min am so happy 

Da sauri ta janye jikinta daka nashi, wani irin kunya taji ta kamata lokaci d’aya, tare da fad’in maina aikata, hannu tasa ta rufe fuskanta cikin jin kunya 

Kabir kam dariya yayi tare da canza firar tasu dan yaga yanda taji kunya akan abunda yace, dan haka saiya canza firan da fad’in ibtisam kinga kayan lefenki kuwa?.. 

Kaita girgiza alaman a’a 

Yace Mai yasa ko kayan ne basuyi miki ba? 

Tace a’a haka kawai

Kallonta yayi tare da kura mata ido, yace ibti are you happy with this marriage kuwa? 

Da sauri ta kalleshi ido cikin ido domin ita yake kallo, tace am happy with it mana, “maika gani?? 

Kabir yace naga kince baki ga kayan lefenki ba, naso in miki yafi haka, in miki guda 24, but banda enough kud’i gidanki ya cinye kud’in 

Ibtisam tace ko d’aya wlh, abunda kayi yayi fatana shine Allah yasa ma auren albarka, sannan abunda yasa ban gani ba saboda ina jin kunya, bazan iya zuwa ince zan kalla ba, gasu ummi a gidan,”kaji wannan shine dalili na, nak’in kallon kayan 

Kabir yayi murmushi tare da fad’in yayi kyau, hakan yayi my shy ibti 

Dariya tayi 

Yace Bari inzo in gudu yunwa nakeji Sosai

Ibtisam tace ko in kawo maka abinci 

Kabir yace a’a, Bari inje kawai 

Ibtisam tace plz muje kaci, kaga in…. 

Yace ya kikai shuru 

Tace ba komai, muje kaci a nan. 

Yace no my ibti 

Ibtisam tace Bari in kawo maka snack Toh, bud’e kofar tayi amma taji a rufe kallonshi tayi alaman ya d’aga mata 

Murmushi yayi tare da d’aga mata sannan ta fita 

Tayi wajan 5mnt sai gata da cooler guda uku a cikin basket dasu wasu Abu a plate guda biyu ansa full paper an rufe, bayan motar ta bud’e tare da ajiye Mai sannan ta rufe kofar 

Bud’e gaban motar tayi wanda ta tsaya a tsaye ba tare data shiga ba, tace gashi saida safe koh 

Kabir murmushi yayi tare da fad’in wannan ne snack din koh? 

Dariya tayi tare da fad’in Toh naga kaki yarda in kawo ma, kuma Nasan in ba’ayi wasa ba, sai dai kasha tea 

Dariya yayi yace tunda shine abincin gauraye koh 

Ido ta lumshe tana murmushi 

Sallama yayi mata tare da fad’in sai munyi waya yayi gaba 

Cikin gida ibtisam ta shiga, kai tsaye d’akinsu ta shiga inda ta iske Granny da Zarah suna fira 

Granny tace Sai yanzu kabirun ya tafi? 

Ibtisam eh kawai tace tare da kwanciya tayi ruf da ciki Tana tunani, wanda ba tunanin komai take ba saina abunda ya faru tsakaninta da kabir, ido ta lumshe wani irin son kabir Mai tsafta takeji yana k’ara shigarta, lallai ina son kabir, sonshi ya kamani da yawa.

Allah na gode maka daka bani shi a matsayin miji, Allah ka bamu zaman lafiya, tare da hakuri da junanmu da kuma son juna….. 

Zarah ce ta katse mata tunani da fad’in ibtisam Yadai naga kinyi shuru?.. 

Granny tace uhm ai tayi shuru tunda ansha kalaman soyayya 

Dariya ibtisam tayi tare da tashi ta zauna tana kallon Granny tace Wlh Granny kina da abun dariya 

Granny tace ahaf ai Nasan komai, domin wannan shurun bana banza ba 

Ibtisam sai taji ta tsargu tana tunanin kodai Granny taga sanda kabir ya mata kiss ne?

Wanda hakan yasa ta kame bakinta tayi shuru ba tare data k’ara cewa komai ba 

Granny tace uhm bari dai inje in watsa ruwa inyi bacci 

Ibtisam kam gaba d’aya ranan sai juyi take tana tunanin abunda ya faru tsakaninta da kabir

Haka shima ta gefen KABIR din, wani irin sonta yakeji yana k’ara fusganshi, lallai yana son ibtisam da yawa, wanda ya tabbata sonta a jininshi yake.

Hidima ake Sosai na bikin ibtisam anje anyi mata danki a dangareren gidanta ginin gidan sama, sama akwai d’aki uku, k’asa kuma akwai d’aki biyu, ansa Mata gado a d’aki uku, sannan anyi mata jeran falo, gaskiya Abba yayi k’okari Sosai domin ya kashe dukiya Sosai akan wannan hidiman bikin, sannan ya fitar da y’arshi kunya, dan yayi mata kayan d’aki masu kyau masu tsada kuma, sai dai ayi musu fatan samun zaman lafiya da zuri’a dayyiba 

Biki Wan shagali, yau za’ayi bridal shower inda aka kayata a hall, Mata ne zallah kawai a wajan inda Amarya tayi dressing cikin wata arniyar gown, Wanda yayi mata mugun kyau, ibtisam ba’a Mata wani makeup Sosai ba, Zarah ce tama shafa mata powder domin sunce kwalliya sai ranan dinner, Anci ansha anyi rawa kowa ya watse 

Ranan da za’ayi dinner Mum tazo Kano Wanda ranan bikin saura kwana uku

Masu makeup aka kawo inda suka tsara ma Amarya kwalliya na Kece raini, gaba d’aya ban gane ibtisam ba, domin tayi wani irin mugun kyau, lallai ibtisam kyakyawa ce, shi kanshi kabir daya ganta ranan saida yayi mamaki, domin ita ba ma’abociyar yin kwalliya bace, lallai yayi Sa’a daya samu ibtisam a matsayin mata, wajan zaman amarya da ango su biyu inda sukai bala’in kyau, gaba d’aya iyayen amarya da ango sun hallari dinner din, inda Zarah ta bada kad’an daka tarihin Amarya, Tahir kuma ya bada na ango, ranan anyi B’ari da kud’i wajan lik’i, kabir sai kafu kafu yake da ibti d’inshi

Anci ansha sannan aka fara tafiya, ango da kanshi ya dawo da Amaryanshi gida, koda suka faka motar a kofar gidansu ibtisam, kallonta yayi tare da fad’in Amarya bakya laifi, koda kin kashe dan masu gida 

Ibtisam tayi dariya tare da fad’in kai dako an d’aureni, in kashe d’an masu gida Kut 

Shima dariyan yayi tare da fad’in babu Mai d’aureni karki manta kefa amaryan barrister Kabir ce, Kinga kuwa babu Mai d’aure min ke 

Dariya tayi Sosai ba tare da tace komai ba 

Yace Kinga yanda kikai kyau kuwa? Kai dama haka kike dakyau ban sani ba? Gaskiya am lucky 

Ibtisam tace uhm.

Kabir ido ya k’ura Mata yana kallonta.

Ibtisam da kanta ke k’asa jin yayi shuru yasa jikinta ya bata kaman yana kallonta ne, A hankali ta d’ago kanta Aiko caraf idonta ya sauka a nashi, da sauri ta kauda kanta gefe tare da fad’in ina jin bacci Zan shiga gida 

Kabir murmushi yayi tare da kamo hannunta ya ri’ke yace kin gaji da ganina ne?? 

Kaita girgiza alaman a’a tana kuma k’okarin kwace hannunta daka nashi 

Ganin tana son ta janye hannunta daka nashi yasa ya k’ara ri’ke hannun Nata dakyau, tare da fad’in tunda dai bakya son ganina let me go 

Tace a’a kawai na gaji ne Sosai 

Kabir yace OK saida safe 

Da sauri tace Allah ya kaimu, domin ita burinta ya sakar mata hannu daka ri’kon da yayi mata 

Shiko kabir bai sakar mata hannun ba, sannan bai bud’e motar ba,dan yayi luck d’inshi 

A hankali tace let go of my hand, I need to go and sleep plz 

Sakar mata hannun yayi tare da fad’in take care 

Tace I will sannan yayi unlock din motar ta fita 

Cikin gida ta shiga wanda yake makil da mutane, kai tsaye d’akinsu ta nufa wanda babu wani ba’kon daya sauka a d’akinsu 

Zarah tace ina kuka je keda angon naki? 

Ibtisam tace muna waje tun d’azu 

Zarah tace nasha ko AI kun biya wata duniyar ne 

Uhm kawai ibtisam tace tare da kwanciya akan gadon d’akin Tana fad’in Kai na gaji Wlh, Bari in huta kad’an, in tashi inje in wanke wannan makeup din 

Zarah tace aiki ja, wlh kinyi kyau Sosai, sun iya makeup 

Ibtisam tace Sosai kuwa. 

Zarah tace nifa ina son saki a status Amma saboda karsu Aisha su gani na kasa saki 

Ibtisam tace in banda abunki kiyi Hiding nasu su daina kallon miki status mana 

Zarah ta saki dariya tare da fad’in hakane fah, kai Bari inyi yanzu in saka 

Washe gari Thursday kuma ranan za’ayi kamu, A ranan Ahmad brother d’in ibtisam yazo, shida Dad, ita dama Mum a hotel ta sauka, domin tace bata iya kwana cikin mutane 

Ibtisam tayi murnan ganin Ahmad Sosai 

Anyi ma ibtisam makeup inda aka tafi wajan kamu, shima kamun an k’ayata shi Sosai, inda ango da abokanan ango suka zo suka musu lik’i tare da d’aukan amarya da ango hoto, suka dan zauna na wani lokaci wanda bai wuce minti 30 ba, sannan suka wuce. 

Hall din da akai kamu din yayi matukar tsaruwa, da had’uwa, komai dai gwanin burgewa da sha’awa, abun ba’a cewa komai 

Anci ansha Anata son Barka Kafin kowa ya watse daka wajan 

Koda suka koma Gida, ibtisam wanka tayi tare dayin sallah sannan ta kwanta danta huta, domin gaba d’aya tunda aka fara wannan hidiman bikin bata samun hutu

Tana kwance tana tuna ranan da Kabir yayi kissing d’inta, ido ta lumshe tare da furta Anya zai barni kuwa har in kammala karatu na kuwa?  Uhm naga yanda yake ta zakewa uhm….. K’aran wayarta ne ya  Katse Mata tunani 

D’auka tayi taga kabir dinne, sawa tayi a kunne tare da fad’in hello 

Kabir yace my ibti kinyi bacci ne?

,
Tace a’a, nadai kwanta Ina shirin inyi 

Yace OK, yau fah kinyi kyau Sosai gaskiya 

Tace uhm nagode 

Yace gobe zani Abuja, gaba d’aya na manta muna da zama a court wlh, gashi gobe Friday 

Ibtisam tace toh fah, yanzu inka tafi goben sai yaushe kenan? 

Kabir yace goben zan dawo, zan tafi da sassafe, coz 10 zamu zauna, shap na manta wlh gaba d’aya 

Ibtisam tace Allah ya kaimu, Allah ya kaika lafiya ya dawo mun dakai lafiya 

Ya amsa da Ameen my ibti 

Sun taba fira Sosai inda yayi mata sallama

Washe gari tun 6 kabir ya kama hanyar zuwa Abuja 

Masu iya magana dai sukace rana bata k’arya sai dai Uwar d’iya taji kunya, A yau juma’atu babban rana a garin Kano Bayan an idar da sallah juma’a aka fara maganan daurin auren ibtisam da Kabir Wanda Dad ne wakilin ibtisam 

Ana faman son a d’aura aure sai ga wani ya shigo cikin masallacin da sauri yana fad’in ku dakata, inada magana 

Nan kowa hankalinsa yayi kanshi.. 

Mutumin ya kalli Abba, tare da fad’in karka yarda ka aura ma kabir y’arka, domin yana da cutar nan Mai karya garkuwan d’an Adam, wato HIV aid 

Gaba d’aya aka saki salati, d’aya daka cikin dangin kabir ya tashi cikin zafin rai, tare da fad’in amma kam bawan Allah wannan wani irin kazafi ne? 

Mutumin idonshi nakan Abba yace, bawan Allah gaskiya na fad’a, amma idan zaku cuci yarinyar shikenan, ni Nayi gaba, in kuna tantama ku gwada 

Abba kam shuru yayi yana nazari, gaba d’aya kanshi ya kulle 

Dad ne yayi karfin halin yin magana tare da kallon iyayen Kabir, yace inaga Ayi gwajin HIV, Kafin Ayi bikin 

Nan k’anin mahaifin Kabir yace wannan ai cin fuska ne, kenan Sun yarda da abunda wannan Makaryacin yace? 

Dad yace ko d’aya, amma domin a kauda tantama ko zargi inaga Ayi gwajin 

Nan k’anin mahaifin Kabir yace tunda suna zargin kabir su ri’ke y’arsu, basa son auren 

Wani aminin mahaifin Kabir yace gaskiya ne, dama su Dad sun tarasu ne dan suci musu zarafi 

Dad abun dariya ma ya bashi, shidai baiga Abun fad’a ba, kojin zafi, kenan dagaske yana da HIV, din tunda suka d’auka da zafi 

Dad yace kuyi hakuri, dukanmu ba yara bane, ina son ku sani mu iyayen yarinya bazamu Jefa rayuwarta cikin hatsari ba S…. 

Nan abokin baban kabir yace babu damuwa mun gode, amma ina son ku sani yanda aka tara mutane a nan, toh sai anyi wannan aure, ni naba ma kabir auran y’ata, ku kuma saiku aurar da y’arku mu gani 

Dad murmushi yayi tare da fad’in shikenan, itama yanzu za’a aura Nata auran a gabanku, tunda baku da adalci… 

Nan Dad ya ciro kud’i ya mi’ka ma Abba d’aya sannan yaba iyayen Kabir masu, ya kalli Abba yace ina nema ma Najeeb auren ibtisam 

Nan Abba ya girgiza kai tare da fad’in ni zan bada sadaki domin d’ana ne NAJEEB, 

Nan take Abba ya ciro dubu d’ari aka d’aura auren Najeeb da ibtisam 
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Suma aka d’aura auren kabir da Hafsat 

Toh kabir dai yana hanyar dawowa kaduna, koya zaiji wannan Abun inya dawo?

Sannan ga ibtisam da aka d’aura mata aure da babban enemy d’inta, itama koya zata ji wannan Abun? 

Toh Uwar Gayya NAJEEB, Zaima yarda da wannan auren kuwa? Musamman yanda baya shakkan kowa, yaga an d’aura mai ibtisam yarinyar da yake fad’in bata da kunya, sannan bata da komai…..  Yanzu aka fara muje zuwa……

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button