NAJEEB 26

Bayan an d’aura auren ibtisam da Najeeb, nan take aka d’aura na hafsat da kabir suma. Inda dubban mutane suka shaida wannan auren
Bayan mutane sun Fara fita, daka family din ibtisam saina KABIR cikin masallacin
Abokin mahaifin Kabir yace kayan da kuka saka a gidan nawa kuka kashe?
Abba shuru yayi ba tare da yace komai ba, domin ya Lura kaman y’an uwan kabir sun d’auki abunda zafi, wanda shi baiyi zaton haka daka garesu ba, ko kad’an, dan yasan y’an gidan mutunci ne
K’anin mahaifin Kabir yace ku Fada nawa kuka kashe, dan Inaga tunda Abun ya zama haka gwara a baku kud’in kayan tunda ankai an kuma jera
Dad yace hakane, sai dai ina son ku sani, mun bar ma kabir kayan da duk mukasa a cikin gidan, koba komai ya nuna mana k’auna domin na tabbata inda ya…..
Mahaifin hafsat ya dakatar da Dad tare da fad’in kayi hakuri amma maganan gaskiya bazamu amshi wannan kyautar ba, domin y’atace zata zauna a gidan, kuma a matsayina na mahaifinta inada burin yi mata komai in zatayi aure Dan haka ku fad’i abunda kuka kashe
Dad ya kalli Abba tare da fad’in ya fad’a abunda ya kashe tunda yace haka
Nan Abba ya fad’a, tare da fad’in wasu ya manta
Mahaifin hafsat check ya rubuta tare daba wani yace yaje banki yanzu da sauri inya Kawo kud’in saiya kaima mahaifin ibtisam gida
Abba da Dad tashi sukayi suka tafi, harda Allah Abba baiyi zaton haka daka family din KABIR ba, koda yake ya gode Allah da hakan ta faru Koba komai y’arshi ta tsira daka wannan mugun cutar Mai Karya garkuwan jikin d’an Adam, toh Ina ma mutumin da yazo ya fad’a? Koma wanene Allah ya biyashi, “lallai aure Kafin gwaji yanada matukar amfani Sosai ya kamata a dinga yin gwaji Kafin Ayi aure domin gudun dana sani nan gaba
Nan su Dad da Abba suka shiga mota Bayan sun gama gaisawa da mutane Wanda suka zo ko ince suka tsaya aka d’aura aure Bayan an idar da sallah
Kai tsaye gida suka nufa inda taron mata ne makil a ciki, amma haka Abba ya shiga bayan yakai Dad falon ba’ki ya zauna wanda babu kowa a ciki.
Gidan cike yake da mutane y’an biki, Zarah dake zaune a falo tana ganin Abba tasan an d’aura aure dan haka da sauri ta shiga inda ibtisam take tana waya da kabir kwace wayar Zarah tayi a hannun ibtisam tare da fad’in kai wannan angon ai sai kayi hakuri tunda an d’aura aure ka barta taji da mutane Wanda suka zo dan tayaku murna, waya tun d’azu
Kabir yayi dariya tare da fad’in ayi mana hakuri, Nima tun dazu aketa kirana amma na’ki kashe wayar inata ganin calls Nasan duk y’an tayamu murna ne
Zarah tace toh gaskiya ka d’auka kabar ibtisam taji da mutane, anjima fah za’a kawo maka ita
Kabir dariya yayi cikin jin dad’i tare da fad’in insha Allah, Nima na shigo Kano yanzu plz ki kulan min da my wife
Zarah tace an gama barrister Kabir tare da kashe wayan
Kallon ibtisam tayi dake zaune tana dariya, Zarah tace congratulations burinku ya cika yanzu Naga Abba ya shigo Nasan har an d’aura auren
Ibtisam tace uhm
Dukan wasa zarah takai Mata tare da fad’in ya kika ji?
Ibtisam tace Zarah gabana yana fad’i, wlh yanzu naji gabana ya fara fad’i,kodan an d’aura auren ne yasa nake jin haka??
Zarah tayi dariya tare da fad’in ina tunanin hakane amma ki dinga furta Kalman Innalillahi’wa inna ilaihirajiun.
Ibtisam tashi tayi daka k’asa tahau gadon d’akin ta kwanta tare da fad’in Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, tana ta nanata wa, lokaci d’aya kuma ta lumshe ido
Tayi wajan 5mnt sannan ta bud’e idon tare da kallon Zarah wacce ita din ita take kallo
Ibtisam tace Zarah har yanzu gabana yana fad’i plz bani wayana in kira kabir
Zarah tace ki kira kabir kuma? Ba yanzu kuka Gama waya ba? Kai Wlh ban taba ganin amarya da ango masu zumudi ba irinku,saurin Mai kukeyi ne? Anjima fah kad’an za’a kaiki
Ibtisam tace uhm wlh ko d’aya kawai gabana ne ke fad’i, sai yasa nake son ji ko KABIR ya isa Gida, kin San yana hanya ne
Zarah tace kwantar da hankalinki dazu dana amshi wayar yace Min ya shigo Kano, may be yanzu yana gida ma
Ibtisam tace nidai plz bani waya ta, inyi magana dashi
Mi’ka mata zarah tayi ganin yanda ta damu, kiran Layin KABIR tayi taji call waiting alaman yana waya, dan haka ta kashe dan tasan inya gama zai kirata
Aiko ko 1 mnt ba’ayi ba sai gashi ya kirata, d’auka tayi da sauri tare da fad’in ka isa Gida?
Kabir yace ibtisam maike faruwa ne wai?
Tace Dame?..
Yace waya nakeyi yanzu haka Ina kan Layin gidanmu ne, ance an samu matsala wajan auren kuma sunki fad’amin wai saina k’araso
Ibtisam tace matsala kuma? Kai Anya kuwa
Yace zan kiraki Ltr Bari in shiga inji
Tace OK tare da kashe wayar ta tashi tsaye…. Dai dai lokacin Ummi ta shigo d’akin Tana fad’in ibtisam abbanki yana kira
Tace ummi yana ina
Ummi tace yana falonshi na ba’ki
Ibtisam gyalenta ta d’auka tare da yafawa tabi bayan Ummi suka shiga har falon ba’kin, inda taga su mum da Dad da Abba da Granny
Granny tace ku fad’amin maiya faru mana, tun dazu sai jira muke gata tazo AI
Ibtisam zama tayi a k’asa tare da gaida Dad wanda ya amsa
Lokaci d’aya Dad ya fara magana kaman haka, an samu matsala wajan daurin auren ibtisam da Kabir
Dam ibtisam taji gabanta ya yanke ya fad’i
Dad ya zayyano musu abunda ya faru har d’aura auren najeeb da ibtisam da akayi da kuma auren da akayi ma kabir din
Ibtisam tashi tayi tana hawaye tare da fad’in Wlh sharri akayi masa, wlh k’arya akayi masa, ni na yarda koda yana da HIV Wlh zan aureshi a haka, dan Allah Abba kar a fasa wannan auren na ro’keka Abba cikin kuka mai ban tausayi….
Abba yace rufemin baki mara hankali, baki ji abunda akace ba, an d’aura miki aure keda Najeeb b….
Wani irin ihu ta saki Wanda ita sai yanzu taji hakan, domin sanda Dad na bayani tunda taji ance an fasa aurenta da Kabir saboda yana da HIV gaba d’aya taji kunnenta ya toshe bata ji
Tace Wlh Abba bana son wannan auren, kabir….. Lokaci d’aya jiri ya d’auketa tayi k’asa luuuuuuu..
Da sauri mum ta ri’keta tare da kiran sunanta ibtisam ibtisam, amma ina ko gezau batayi ba
Granny ce ta kawo ruwa aka yayyafa Mata ta Farfado aiko tana farfadowa tare da fad’in Wlh kabir nake so Dan Allah karku rabamu sai kuma ta saki kuka mai ban tausayi Tana fad’in na shiga uku
Abba ranshi ya baci da abunda ibtisam din take fad’i dan haka cikin bacin rai yace in batayi shuru ba saiya karyata
Dad yace a’a akan wani dalili, taya zaice mata haka, Aiko dan abunda ya sameta dole tayi shock, in baka lallabata ba ai baka Mata fad’a ba, abun saiya mata yawa
Abba kallon Ummi yayi tare da fad’in ku tashi ku shiga ciki da ita.
Tashi sukayi harda Granny akai ciki, ibtisam na ri’ke jikin Mum Kai tsaye d’akin su ibtisam din suka shiga, inda suka iske Zarah
Zarah ganin ibtisam na kuka yasa ta d’auka ko anyi mata irin nasihan da akema amare ne yasa take kuka
Mum tace ibtisam kiyi hakuri, ki d’auki hakan a matsayin kaddara, Allah yasa kabir bashi bane mijinki K….
Cikin kuka tace mum Dan Allah ki taimaka kisa a bama kabir ni, na yarda zan zauna dashi koda yana da cutar, wlh Mum zan zauna dashi hakan, kuma Wlh nasan kabir baida Shi,sharri ne wlh sharri ne….
Ummi takai Mata duka tare da fad’in yi mana shuru mara hankali kawai, tunda ke baki San inda yake miki ciwo bako? Wlh…..
Mum tace haba ya zaki bigeta? Miye haka kuma? Damai zataji?..
Ummi tace baki ji abunda take fad’a ba? In banda iskanci tanaji ance yanada cuta amma tana fad’in ita zata zauna dashi haka, tunda bata da hankali bata san maike mata ciwo ba.
Zarah kam gaba d’aya ta shiga rud’ani, kenan ibtisam da Kabir ba’a d’aura aurensu ba? Gaba d’aya sai tausayin Itbtisam din ya kamata
Mum tace ai ba’a haka, bakya ganin irin halin data shigane? Komai a hankali za’a bishi
Ummi tace ai zancan Abu a bishi a hankali wlh bai taso ba, dan bazamu bita a hankali ba dan ubanta, tunda an d’aura aure, yanzu ita matar aurece kar in k’ara ji ta kira sunan wani kabir a gidan nan sha sha sha kawai mara tunani
Granny ce ta shigo tazo ta zauna kusa da ibtisam wacce ke kuka kaman ranta zai fita, wai itace matar Najeeb? Wlh da sake, gwara susa ya saketa domin kabir Zan aura
Granny tace ibtisam kiyi hakuri Kinji? Ki d’auki hakan shine dai dai, kuma haka Allah ya tsara, inaso ki sani komai da yake faruwa a rayuwar Dan Adam rubutacce ne, Allah ya riga ya tsara sai hakan ya faru, mu kawai muna bine, “Allah yasa kabir bashi bane mijinki NAJEEB shine mijinki Ina son ki dauki hakan a matsayin kaddara…..
Cikin kuka tace Wlh Granny bazan d’auka ba, ni Kabir nake so, shi kuma zan aura bana son wannan auren, dan Allah ku taimaka ku rabani da wannan ba’kin auren, wlh da nasan zanga wannan ranan dana ro’ki mutuwa Kafin tazo min, wayyo Allah kabir…. Lokaci d’aya tayi shuru tare da Fara dube dube kaman zararra, d’auko wayarta tayi ta Fara dannawa tare da dialing number d’in kabir…..
Amma Abun mamaki sai taji switch off.
K’ara kira tayi shima switch off, kuka ta k’ara saki mai sauti tare da fad’in shikenan, shikenan yaji wannan mummunan labarin, k’asa tayi jiri ya d’ibeta.
Da sauri Mum ta rukota Tana kiran sunanta ibtisam, ruwa aka saka mata amma gaba d’aya ta kasa bud’e idonta sai dai tana numfashi sama sama dan haka Mum tace ma Zarah kamata muje toiket
Kamata Zarah da mum sukayi sukai toilet da ita inda Zarah ta fita Mum ta Fara tube Mata kaya, wanka Mum ta Mata wanda yasa ibtisam ta farka tare da bud’e idonta da sauri, ganin mum yasa ibtisam kallon jikinta da sauri tasa hannunta ta rufe kirjinta Wanda suke a tsaye kyam dasu gwanin sha’awa
Mum ganin haka yasa tayi murmushi tare da fad’in tashi ki d’aura towel
Bata musa ba, ta tashi da sauri duk da jikinta babu kwari ta d’auki towel ta d’aura, sannan suka fito
Gaba d’aya su Zarah na zaune a d’akin, kowa da abunda yake tunani, wato ibtisam NAJEEB ta aura ba KABIR ba, sai taji ibtisam din ta bata tausayi domin tasan irin sonda suke ma junansu ita da kabir din, “amma kabir bai kyauta ba daya boye yana da cutar HIV da yanzu ya saka ma ibtisam, data kwasa
Ta gefen Granny kam dad’i takeji, dan dama ita burinta taga NAJEEB yayi aure shida itbisam, sai gashi Allah ya cika mata burinta sunyi aure an had’asu, wanda ita bata taba tunanin hakan zai faru ba, a hankali tace ikon Allah ya wuce wasa
Ibtisam zama tayi akan gadon d’akin, yanzu ko kukan ma ta kasa saboda tashin hankali, ganin zaman bai mata ba yasa ta kwanta tare da lullube jikinta da blanket harda kanta ta rufe, ba komai bane cikin ranta sai tunanin wani hali KABIR ke ciki yanzu, zuciyarta da kirjinta ji take kaman zasu fito, wani irin zugi takeji, cikin ranta, gaba d’aya duniyar tayi mata ba’ki, lallai an gama da ita a rasa wanda za’a aura ma ita sai wannan mugun azzalumi Wanda bai san darajan d’an Adam ba, lallai su Abba basu mata adalci ba, da suka bata Najeeb, amma koma dai miye bazan taba yarda da wannan auren ba, haka kuma bazan taba d’aukanshi a matsayin miji ba har abada, domin kabir shi d’aya shine mijina
Sanda kabir ya shiga cikin gidan nasu, kai tsaye falon gidan ya shiga inda yaga iyayenshi zaune, ciki harda abokin mahaifinshi wato mahaifin hafsat kenan
Zama yayi tare da gaidasu cikin damuwa tare da kosawa yaji maike faruwa
Nan k’anin mahaifin ya kira sunanshi da kabir
Kabir yace na’am Abba
Kawun Kabir yace ashe k’aramin gida ka Kai mu bamu Sani ba? Mun d’auka babban gida ne wanda suka san mutunci Ashe basu sani ba, tunda har za’a iyayi maka k’azafi sannan su kama su yarda?
Kabir daya k’osa yaji maike faruwa yace Abba wani abu ya faru ne?
Kawun Kabir yace ya faru kam, domin anzo ance musu kanada cutar nan Mai karya garkuwan jikin d’an Adam, wato HIV aid, ana gab da…..
Salatin Da kabir ya saki yasa kawun nashi yin shuru, salati kabir yayi da fad’in Innalillahi’wa inna ilaihirajiun
Kawun Kabir yace, babu yanda bamuyi ba akan Karya ake maka, amma Sun d’age sai anyi gwaji Kafin a d’aura aure, dan haka mu kuma mukace su ri’ke y’arsu suka aura Mata aure da wani, Muma muka aura maka Hafsat, gidan nan ba gidan mutunci bane tunda har zasu iya yarda da abunda wani yace akan ka ……
Tashi kabir yayi cikin tashi hankali yana fad’in no ibtisam tawa ce, ban yarda ba fita yayi fuuuuuu Kai tsaye motarshi ya shiga ya fita da gudu, bai tsaya ko inaba sai hspt inda ya buk’aci a mishi HIV test, domin shidai inma yana da cutar Toh bai sani ba, “bayan an gwadashi aka bashi result da sauri ya duba yaga negative, ido ya lumshe tare da furta Alhmdlh Kai tsaye gidansu ibtisam ya nufa inda yaga mutane makil, yaro ya tura akan yayi mishi sallama damai gidan in yana nan, Aiko akaci Sa’a Abba da Dad suna nan a falon ba’ki kuma nan ne Farko Kafin a shiga cikin gidan
Abba fitowa yayi ganin kabir yasa yace ya shigo ciki, “binshi yayi ya shiga cikin falon ba’ki, kabir zama yayi tare da gaida Abba da Dad
Duka suka amsa tare da fad’in lafiya
Kabir mi’ka ma Abba takardan da aka Mai gwajin HIV yayi tare da fad’in Abba dan Allah gashi ka duba wlh sharri ne bani da wani cuta, dan Allah Kar ku hanani ibtisam
Abba duba takardan yayi yana mamaki tare da fad’in ikon Allah,lokaci d’aya ya mi’ka ma Dad shima ya amsa Yana dubawa, Dad yace Toh amma Mai yasa wannan mutumin yayi maka wannan k’azafin??
Kabir yace Wlh nima ban sani ba, gashi duka y’an uwana babu wanda ya sanshi.
Abba yace ikon Allah, toh amma kabir ai sai dai ayi hakuri amma wannan bawan Allah ya cuceka ko Waye, amma bakai ya cuta ba, kansa ya cuta, sannan ina son ka d’auki hakan a matsayin itace kaddaran ka, Allah yasa ibtisam ba matarka bace, yanzu ibtisam matar wani ce
Kabir bai San lokacin da hawaye ya fara zubar mishi ba, gaba d’aya ya kasa furta komai, “babu komai a ranshi sai Mai yasa wannan mutumin yayi mishi haka? Ko Waye ya cutar dashi wlh, ya gama dashi,yasa bai samu abunda yake buri ba Innalillahi’wa inna ilaihirajiun.
Abba yace KABIR kayi hakuri, haka Allah ya tsara, ko sanda aka fad’i abun saida nace Ayi test dan a tabbatar amma iyayenka Sun kasa fahimta Sun d’auka da zafi, wlh KABIR Allah shine shaida kai muka so bama ibtisam amma family din’ka sun mana fassara, wanda suke ganin munki yarda dakai ne, amma kayi hakuri haka Allah yaso, ibtisam ba matarka bace
Kabir hawaye yake Sosai yana ro’kan Abba da Dad akan su taimaka su bashi ibtisam
Dad gaba d’aya tausayin kabir ya kamashi,
Abba yace Kabir ka tashi kaje gida zan nemeka
Kabir jin haka yasa ya d’auka ko za’a bashi ibtisam dinne, yasa shi fad’in Abba zuwa yaushe?
Abba yace kaje zan kiraka
Dad yace kai Yaron nan yana son mamana, ina tunanin NAJEEB ya rabu da ita, tunda bawai tana sonshi bane, kuma ban tunanin shi najeeb din shima yana sonta
Abba yace haba haba, sai kace Abun wasa? Taya za’ace NAJEEB ya saketa? Ai wannan bai taso ba
Dad yace suna son junansu Sosai, Kaga halinda yaron Ya shiga abun yaban tausayi, itama kanta ibtisam din ta shiga wani hali, inaga gaskiya ban tunanin zasu iya juran rashin junansu
Abba yace dole kuwa su jura, domin kuwa dole suyi imani da kaddara, dole su amshi kaddaran data fad’o musu.
Tayu ma ana d’aura auren wani a cikinsu ya mutu tunda Allah yasa ba matarshi bace, ai wani baya auran matar wani, haka wata bata auren mijin wata
Dad yace hakane tare da fad’in kaje Kaga wani hali ibtisam din take
Tashi Abba yayi yana fad’in Bari inje in duba
Koda kabir yabar gabansu Abba Jiki a sanyaye ya tafi, tuk’i yake cikin damuwa, lokaci d’aya yaga duhu a idonshi wanda ya bugi wata trailer dake gabanshi, domin irin gudun da yakeyi gashi idonshi ya rufe, motarshi tayi sama tare da kundun bala tana juyi
Nan mutane sukayi kan motar tashi inda aka fara dubawa aga Waye a ciki, Aiko ganin mutum sukayi gaba d’aya ba’a gane fuskan ko Waye domin jini ne gaba d’aya ya bata fuskan, jikinshi gaba d’aya jini ne, babu wanda yayi yunkurin yace a kaishi asibiti aga ko yana da rai koya mutu
Saida yayi wajan 30mnt sannan saiga police da motar ambulance sunzo inda aka d’auko kabir wanda gaba d’aya ban tunanin yana da rai ko yana Raye, wanda dakyar aka ciroshi a motar dan wani k’arfe ya shigar mishi cikin cinyar kafarshi ya faso, ya bullu’ko
Nan akai asibiti dashi inda za’a duba yana Raye koya mutu…..
Ibtisam da Abba ya shigo d’akin dai dai lokacin da kabir yayi accident Wanda take kwance tun sanda tayi wanka, tashi tayi tare da sakin ihu Tana kiran Sunan kabir
Dukansu ido suka zuba mata suna kallonta cikin mamaki
K’okarin tashi ta farayi tana kuka tana fad’in na shiga uku, dan Allah ku kaini inga kabir Dan Allah ku kaini in ganshi na shiga uku wayyo KABIR..
Tsawa Abba ya daka mata tare da fad’in zan saba miki Idan na kumaji kin kira sunan kabir….
Cikin kuka take fad’in Abba kayi hakuri Wlh Abba Ina jin tsoro jikina yana bani wani abu ya sameshi Abba Ina tsoran Kar in rasa KABIR Dan Allah Abba ku barni inje in gansa koda sau d’aya ne….
Gaba d’aya kallonta suke, suna mamaki yanda take abu, sai kace wacce ta zare ko akayi ma asiri
Ibtisam ganin suna mata wani kallo yasa ta rarumi wayarta ta doka ma number d’inshi kira amma still switch off
Cikin tashin hankali tace Abba da…..
Abba yace Yimin shuru ibtisam bana son wata magana, ashe haka kike? Lallai gaskiyan mamane na tabbata wannan jami’a din da kikaje shine yasa idonki ya bud’e haka….
Ibtisam ri’ke kirjinta tayi wanda yake mata zafi Sosai, lokaci d’aya ta zauna wanda ganin haka yasa Abba yin shuru ba tare daya k’arasa abunda yayi niyan fad’a ba
Zama tayi tana cije lebe tare da shafa kirjinta tana lumshe ido
Granny cikin tashin hankali ta Fara fad’in na shiga uku ni Aminatu, ibtisam tashi tashi maike damunki maiya samu kirjin naki??
Ibtisam a hankali tace Granny ina son ganin kabir wlh jikina yana bani wani abu ya sameshi, plz Granny I need to see him help me plz allow me to see him, Tana maganan tana lumshe ido alaman kirjinta yana mata zafi gashi yana buga mata Sosai tare da faduwan gaba
Zarah Gaba d’aya tausayin ibtisam yasa itama ta Fara kuka
Shi kam Abba tsaki yayi tare da fad’in Indai dan kiga kabir ne, kike wannan abun sai dai ki mutu, domin ke yanzu matar aurece kabir ba muharraminki bane, mutuniyar banza yana fad’in haka ya fita fuuuu cikin fushi
Ibtisam kam gaba d’aya idonta ya rufe bata ganin komai, bakinta kabir yake furtawa Wanda jikinta ya gama bata wani mummunan Abu ya samu kabir din……
Ruwa zarah ta kawo mum ta Fara shafa ma ibtisam din, amma ko gezau batayi ba
Duka suka d’auka tayi bacci ne..
Ummi kam ita ta rasa mai takeji a halin yanzu gaba d’aya halinda ibtisam ta shiga yasa jikinta ya mata wani iri, ita ba mara lafiya ba, sannan bazata ita Mai lafiya bace dan gaba d’aya bata gane komai itama
A asibiti kuwa ansa ma kabir oxygen, domin baya ko motsi balle nishi sai dai Anga jijiyar hannunshi yana bugawa.
Gaba d’aya jikinshi duk jini ne, an gano I’d card d’inshi inda aka gano ko Waye, nan take aka kira y’an uwanshi domin ansan barrister Kabir dan ba k’aramin lowyer bane
Cikin tashin hankali family d’inshi suka zo asibitin, amma ganin halinda yake ciki yasa hankalinsu ya k’ara tashi, wanda suke tunanin abubuwa da dama tare da fargaba karsu rasa shi
Koda Abba ya koma wajan Dad fad’a mishi halinda ibtisam take ciki yayi inda ya buk’aci Dad daya kira NAJEEB yazo ya d’auki ibtisam din su tafi
Dad yace kai Anya za’ayi hakan kuwa? Inaga mu Bari ta dawo normal dan gaskiya dole ta shiga damuwa, Sosai ace za’ayi auren mutun zai yaji an canza anyi da wani abun bamai sau’ki bane
Abba yace hakane, amma abunda nake son ka gane shine, shifa kaddara ya riga ya faru, kuma bamu isa mu canza ba, dole hakuri zamuyi kawai,sannan Idan NAJEEB ya tafi da ita inaga hakan shine zaisa ta manta komai a nawa ganin
Dad yace hakane, amma inaga mu Bari nida Mum d’inshi zamu je London mu Kai mishi ita, inaga hakan zaifi
Abba yace duk yanda ka tsara hakan yayi, babu damuwa
Dad yace jibi zamu mu kaita, sai dai maganan karatun tafa??
Abba yace ka manta da wannan karatun taje tayi bautar uban giji kawai, ta nemi lahiran ta, tabar maganan neman duniya..
Dad yace a’a hakan bazai faru ba, dole taci gaba tunda ta Fara, inaga idan muka kaita koda 2week tayi saita dawo Kafin nan sun koma skul, jibi zamu tafi zansa Ayi mata visa
Haka kam akayi dad yasa anyi ma ibtisam visa, domin tafiya London
Ibtisam kam gaba d’aya tunda ta Farfad’o daka suman da tayi wanda da Farko suka zaci bacci take, gaba d’aya bata magana sai hawaye cikin damuwa, ita d’aya tasan mai takeji, duk Wanda yayi mata magana bata bashi amsa sai dai tabi mutum da ido, wai itace yau matar NAJEEB, gaba d’aya ta tsani duniya tare da abunda ke cikinta,inda tasan wannan ranan zaizo data ro’ki mutuwa, wai NAJEEB din data tsana a duniya wanda baida imani shine aka d’aura mata, kuma taga gaba d’aya family d’inta kaman sunji dad’in hakan wanda wannan shine silan da yasa ta share kowa
Harta abinci bata ci, sai da ummi ta mareta da safe saboda yanda ta’ki amsan abinci taci, ganin Ummi tayi zafi Sosai yasa Mum yima ummi fad’a akan ba’a haka, ita ta amshi abincin ta Fara bama ibtisam a baki
Ummi gaba d’aya taji ibtisam ta Fara bata haushi, wanda take ganin akan Mai yasa bazata amshi kaddara ba? Duk da tasan Abun da ciwo Sosai
Kaman yanda Dad ya fad’a haka aka shirya tafiya, ita dai ibtisam komai sukace mata yi takeyi, amma bata furta koda kalma d’aya, gaba d’aya ta koma kaman wata kurma, tsorata d’aya ita Kar ace wani abu ya samu kabir domin ita har yanzu jikinta yana bata babu lafiya
Haka suka tafi London ibtisam bin kowa take da ido, ita gaba d’aya bata tunanin komai da kowa sai Kabir
Mum gaba d’aya tausayin Itbtisam take ganin irin halinda take ciki wanda gaba d’aya ta canza tayi rama sai kace wacce tayi ciwo, sai dai ta k’ara haske sai fuskanta tayi kyau Sosai, dama ga gyaran jiki anyi mata
Bayan su Mum sun sauka a airport wanda dama sun Sanar da NAJEEB akan zuwansu sai dai basu fad’a mishi dalili ba, jin iyayenshi zasu zo yasa duk wata kwalban alcohol dake gidan ya fitar dasu tare da boye wasu cikin bedroom d’inshi tunda yasan ba lallai bane su shiga
Shida kanshi Najeeb yaje airport d’aukosu ganin ibtisam a tare dasu yasa Abun ya bashi mamaki, kallo d’aya yayi ma ibtisam ya kauda kai amma yasan ta tare kaman bata da lafiya, sai kuma ya fara tunanin ba anyi aurenta yau four days kenan ba? Kodai bata da lafiya ne, tabe baki yayi lokaci d’aya tare da fad’in I don’t care
Rungume iyayenshi yayi tare da fad’in welcome Dad, welcome Mum
Mum dake ri’ke da ibtisam tace my only son ina motar muje plz
Yace yana waje
Fita sukayi inda suka shiga cikin motar Dad shine a gaba, mum da ibtisam a baya NAJEEB na tuk’i, gidan suka wuce
Bayan sun karasa Mum ta kalli NAJEEB tace ina masu aikin suke?..
Yace mum duk na sallamesu sai mutum d’aya na Bari wacce take Shara da goge gidan, itama nace bana son tana Kwana a nan
Mum tace akan wani dalili NAJEEB
Yace mum ban son takura dat why
Mum tace Allah ya kyauta
Kallon ibtisam tayi data kafe kanta a k’asa alaman tana tunani, kiran sunanta tayi da ibtisam
D’ago dakai tayi ta zuba ma Mum ido alaman tana jinta
Mum tace kina bukatar ki huta koh?
Ibtisam bata ce komai ba sai ido data xuba ma mum
Ganin haka najeeb daya kura mata ido yasa shi fad’in mum ta samu tabin hankali NE???
Mum Hararanshi tayi
Ita kam ibtisam jin haka hawaye ya fara zubo mata, Aiko tana fara hawayen sai kuma kuka lokaci d’aya ta Fara furta Kalman Innalillahi’wa inna ilaihirajiun
Mum taji dad’i da taji ibtisam din tayi magana, sai hakan yayi mata dad’i Sosai
NAJEEB kam wani irin tsaki yaja, tare dajin haushin kukan da ibtisam keyi, tashi yayi yabar falon danshi kwata kwata baya son yarinyar, cikin ranshi yace ina jin tausayin mijinta, shima idiot ya rasa wacce zai aura sai ita
Rarrashin ibtisam tai tayi inda daka karshe ta kaita wani d’aki dake kusa dana NAJEEB tace ta huta Kafin a Kawo abinci
Bayan mum ta fito daka d’akin, d’akin NAJEEB ta shiga Bayan tayi nocking yace ta shigo
Mum kallon d’akin tayi tace Kai NAJEEB ka canza komai na d’akin nan
Yace Mum bana son tarkace da yawa a bedroom that why na cire
Mum tace Allah ya kyauta, kazo falo muyi magana.
Yace akan me Mum? Yauwa Wai maiya samu wannan yarinyar ba tayi aure ba, maiya Kawo ta nan? Nifa am scare dan naga kaman hauka takeyi Karta hanamu bacci
Mum tace Mai yasa kake haka ne
Yace Mum ni ban son ganin yarinyar nan I hate her bata da kunya
Mum tace fita muje ban son shirme
Tashi yayi yabi Mum suka fita falo inda suka tarar da Dad zaune yana kallo
Mum tace gashi nan sai kayi mishi bayani
Dad yace yauwa NAJEEB zauna muyi magana
Zama NAJEEB yayi yana fad’in akan me Dad
Dad yace akan maganan aurenka
Yace what aurena? Dawa kuma? Dad plz ban son wannan maganan just change the topic
Dad yace NAJEEB wannan maganan ta zama dole, domin kuwa aure an riga an d’aura
Tashi yayi tsaye tare da fad’in what?…. Lokaci d’aya kuma yayi murmushi tare da fad’in Dad you are joking right?..
Dad yace ko d’aya, NAJEEB kasan ibtisam zata auri KABIR….
NAJEEB ya Katse Dad tare da cewa wannan bashi bane damuwa ta Dad, nidai Ina fatan maganan aurena bada gaske kake ba
Dad yace na taba maka wasa ne NAJEEB?
NAJEEB zama yayi tare da d’aura k’afa kan d’aya yana juyawa
Dad ya fara magana tare da bashi Labarin abunda ya faru har d’aura mai ibtisam da akayi…..
Idon najeeb ne ya kad’a yayi jaaa saboda bacin rai, tashi yayi cikin zafin rai yana fad’in Dad wa yace kuyi min haka without my permission?
Dad akan wani dalili zaku yanke decision akan biggest thing in my life without my permission how dare……
Mum ta daka Mai tsawa tare da fad’in will you keep quiet?
Kana da hankali kuwa najeeb? Mahaifinka kake fad’ama haka? Kasan abunda kakeyi kuwa!? Kai har ka isa kace sai munyi shawara dakai Kafin mu yanke hukunci? Baka isaba sannan kayi kad’an
Najeeb yace plz Mum ki daina sa baki am respecting you
Kallon Dad yayi yace Dad I won’t accept this marriage
Dad yace ko kaso ko kar kaso wannan ba damuwa ta bace, amma Abu d’aya nake son ka sani idan ka cutar da ita zan manta nine mahaifinka Wlh koda sau d’aya tace kayi Mata wani abu I will make sure to punish you.
Najeeb fita yayi daka gidan cikin fushi lallai Dad ya raina shi, eh ya raina shi mana akan wani dalili zai aura mishi wannan karamar yarinyar kuma mara kunya, wace bata da komai, kai tsaye wani club yaje duk da yanzu yamma ne giya ya bu’kaci a bashi yasha inda ya amshi kwalban giyan ya farasha
Najeeb giya yake sha Sosai a kalla yasha kwalba wajan biyar, wanda bai taba shayuwa irin haka ba tunda yake, gaba d’aya ya bugu a nan ya fad’i Bayan ya gama surutai barkatai
Najeeb bacci yayi a nan ganin haka suka daukeshi sukai ciki dashi, dama akwai d’aki ga Wanda suka sha giya suka bugu sai a kaisu nan in bacci ya d’aukesu
Dad Bayan fitan NAJEEB zama yayi cikin bacin rai, lallai najeeb yayi nisa, har zamu dinga fad’a yana fad’a? Lallai duniya ta lalace d’an daka haifa ya dinga fad’a maka haka
Mum ganin irin halin da mijinta ya shiga yasa ta Fara bashi baki tare da fad’in kayi hakuri da halin najeeb, gaba d’aya baya kyautawa, na rasa irin wannan halin nashi
Dad yace karki damu, I will teach him a lesson very soon, zanyi maganin rashin tarbiyanshi
Mum tace Allah ya kyauta
Ibtisam dake d’aki duk taji abunda ya faru, tunda abun ya faru sai yau tayi murmushi tare da fad’in lallai tasan NAJEEB zai iya sakinta tunda baya son auren, wani irin dad’i taji domin tasan zata koma ma kabir d’inta….
KANO NIGERIA
Kabir yau kwananshi biyar a asibiti amma babu wani ci gaba, domin har yanzu jiya I yau ne, abun gwanin tausayi kallo d’aya zaka mishi kaga ya canza yayi wani fayau dashi, lallai in baka mutu ba, ba’a gama maka halitta ba, kabir gaba d’aya ya sauya kaman bashi ba
Family d’inshi suna cikin tashin hankali, Hafsat itama tana asibitin duk ta shiga cikin duniyar tunani tare da damuwa, wanda ita tun tuni take son kabir amma bata taba fad’a ba sai gashi Allah ya bata shi, gashi kuma tana k’okarin rasa shi
Ganin irin halin da yake ciki babu wani ci gaba yasa suka yanke shawaran su kaishi waje kawai domin hakan shine suke ganin zaifi
Koda suka ma Dr magana bai musa ba, domin yasan can Sun fisu kwarewa inda ya rubuta musu takarda na neman yarda a fitar dashi domin a duba lafiyanshi a America
Washe garin ranan aka tafi da kabir cikin masu tafiyan harda hafsat da wani k’anin Kabir din sai mahaifiyarshi suka wuce inda zasu sauka a hotel in sunje domin can ba kaman nan bane inda za’ace za’a kwana da mara lafiya, su ba’a kwana da mutum
Koda suka isa America an amshi Kabir inda suka fara sabon gwaje gwaje akanshi domin su gano miye matsalar duk da sun duba takardan asibitin da suka fara dubashi a Nigeria amma basu wani gamsu dashi ba, dan haka yasa suka fara sabon nasu binciken
Najeeb bashi ya tashi ba sai washe gari wajan karfe 1 da wani abu, mi’ka yayi tare dajin ya manta duk wata damuwa dake tare dashi, kai tsaye tashi yayi ya fara kallon d’akin da yake ciki, da sauri ya tashi tare da tunanin maiya Kawo shi nan?
Lokaci d’aya ya lumshe ido domin ya tuna da abunda ya faru, ido ya bud’e da sauri tare da fad’in kai impossible I won’t accept that girl as my wife, tashi yayi ba tare da yayi sallah ba tun na jiya ya fita kai tsaye gidan ya koma, koda ya shiga baiga kowa a falo ba, dan haka Kai tsaye ya nufi part d’inshi inda ya shiga toilet yayi wanka, koda ya fito wanda yasa 3quater irin crazy jeans dinnan, sannan yasa riga mara hannu itama crazy shirt, gaba d’aya jikinshi kamshin turare yake tashi
Falon ya kuma fita inda ya iske Mum na fitowa daka kitchen, kallonta yayi tare da fad’in mum Ina Dad?
Banza dashi tayi ba tare da tace mishi komai ba, domin taji haushin abunda ya aikata jiya Sosai
Yace Mum am asking you Ina Dad yake?
Muryan Dad yaji yana fad’in kazo ka k’ara fad’amin magana ne?
Murmushi NAJEEB yayi tare da fad’in a’a but Ina son baka shawara ne
Dad zama yayi akan kujeran falon ba tare daya kuma cema NAJEEB komai ba
Najeeb yace Dad am I your real son?
Dad da sauri ya d’ago ya kalli NAJEEB tare da fad’in what kind of stupid questions is this?
Najeeb yace Dad Ina tantama akan niba d’anka bane, inda ni d’anka ne am sure baza min aure ba, ba tare Daka fad’amin ba, koda a waya ba, sai dai kawai ka zarce hukunci ba tare da sani naba
Dad I hate dat girl, wlh Dad gwara matan da Granny ta Kawo min akan ita, Mai zanyi da ita, wlh an cuceni
Dad yace NAJEEB itama kanta ibtisam din bawai tana son wannan auren bane, karka d’auka ko itama tana sone, ina tunanin ita ta fika tsanan wannan auren, domin na tabbata inda saki a hannunta yake da tuni ta sakeka, ni kaina da nake Mahaifinka nafi Sonta da kabir, akan Kai, domin ibtisam bata dace dakai ba dashi Kabir din ta dace, domin yana mata so Mai tsafta
Mum tace even me Wlh Ina son ibtisam da Kabir, domin Sun dace…..
Tsaki NAJEEB yaja tare da fad’in oh really? Saiku d’auketa kukai Mai ita
Mum tace you can say whatever, but ibtisam bata dace da mara kunya irinka ba
Najeeb tsaki yayi tare da tashi yabar musu falon gaba d’aya yayi gaba Abunsa
D’akinshi ya Shige inda ya rufe kofar ya d’auko kwalban alcohol d’inshi ya fara sha, lokaci d’aya yaji ranshi ya fara sanyi tare da manta abunda ya faru
Ita kam ibtisam dama take nema domin tayi magana da NAJEEB domin duk abunda suke fad’a tana ji, ta tabbata zai iya sakinta
Kwanan su Mum biyar suka fara shirin tafiya gida, ana gobe zasu tafi Mum ta shiga kasuwa da ibtisam wacce ta Fara sakewa yanzu domin tasan dole ma najeeb ya saketa ta auri KABIR d’inta tunda baya Sonta, kaman yanda itama bata sonshi.
Kayan sawa mum tasai ma ibtisam Sosai, kuma duk English wear sai jallabiya guda biyu da kuma kayan bacci, inda Mum tace zata had’a mata akwatin ta, Kafin ta dawo Nigeria insha Allah
Koda su Mum zasu tafi suka tara NAJEEB da ibtisam, inda Dad yayi ma najeeb warning akan idan yama ibtisam wani abu saiya hukunta shi
Itama ibtisam din dad yayi mata nasiha akan tabi mijinta sau da k’afa, tare da fad’a mata Mai nene aure da hakkokin mace akan miji, shima NAJEEB aka fada Mai hakkin mace akanshi
Najeeb tunda Dad yake magana baice komai ba, yanda yayi kaman yaji maganansu yanda yayi shuru
Ita kam ibtisam bama jinsu take ba, domin ita magana Indai bana kabir bane Toh bata ma saurara
Daka karshe Mum ta fad’ama najeeb kwanakin da ibtisam zatayi, saboda karatun ta
Ibtisam da NAJEEB duka suka tafi rakiya domin kai su Mum airport, saida jirgin su Mum ya d’aga sanna ibtisam ta tashi ta koma mota, wanda ta bud’e ta shiga gidan baya domin koda za suzo Dad ne a gaba
Najeeb bai zoba haka taita zama cikin motar, a kalla tayi wajan minti talatin tana jiranshi amma bai fito ba, gashi gaba d’aya ta gaji da zaman
Kwantar da kanta tayi akan kujeran motar, jin an bud’e motar yasa ta d’ago dakai, ganin najeeb yasa ta kuma kwantar da kanta
Muryanshi taji yana fad’in, uban wa kike so ya zama driver d’inki?
U better come front ko ki fita a motar kisan inda dare yayi miki idiot
Ibtisam da take a gajiye sannan bata da lokacin magana dashi yasa dole ta tashi ta bud’e kofar tare da fita ta koma gidan gaba
Tun Kafin ta rufe kofar yaja motar da gudu wanda hakan yasa tayi saurin rufe kofar, sanda yazo yin wata kwana saida ta buge kai domin yanda ya juya motar
Kai tsaye gidan suka koma inda yana faka motar ya bud’e ya shiga cikin gidan yana tsaki tare da fad’in Wlh an cuceshi yanzu an kawo mai abunda zai dinga takura mishi, tsaki yaja tare da fad’in I hate that girl ban San tunani ba amma tasa na Fara, haka ban San damuwa ba amma tasa na Fara I hate her with all my heart
Zama yayi a kujeran falon
Shigowan ibtisam falon yasa ya wurga Mata wani dan iskan kallo Mai cike da tsana
Ibtisam kam dashi da banza duk ta bada ajiyansu domin ita bata san ma yanayi ba
Shiko fad’i yake cikin ranshi yanzu da wannan karamar yarinyar aka had’ashi, gata mara kunya, ko uban Mai zan Mata oho K…..
Muryan ibtisam dinne ya Katseshi daga tunanin da yakeyi
Inda tace mishi ina son magana dakai
Kallonta yayi sannan ya kauda kai
Tace dan Allah Ina son ka taimaka ka sakeni
Wani irin kallo ya watsa mata sannan ya saki murmushi tare da fad’in kina tunanin ni NAJEEB ina sonki ne? Inma haka kike tunani you are wrong
Ibtisam tace Nasan baka sona, haka nima bana Sonka, shine dalilin da yasa nace ka sakeni.
Najeeb wani irin murmushin mugunta ya saki tare da kallonta a wulakance yace do you know what?
Bata bashi amsa ba, shima bai damu da hakan ba
Yace mistake din da akayi shine da aka d’aura miki ni a matsayin miji, you will leave hare as my servant, komai nawa ke zaki dinga yi daka yau, baki da wani hutu, domin ni banga abunda zakiyi min ba, Inba bauta ba
Ibtisam hawaye ne ya fara zuba a idonta tare da fad’in Dan Allah NAJEEB ka tausaya min ka sakeni in auri wanda nake so kuma yake Sona p…..
Yace keep quiet stupid, kina tunanin zan sakeki? You are wrong, duk wani abu da aka danganta shi dani har aka kirashi nawa ne, toh is only mine alone
Let me tell you something Ina son kisan wannan Abun inma kina tunanin ni NAJEEB zan sakeki kinyi kuskure, nasan am not your type har Abada niba ajinki bane, nafi karfinki, but tunda Sun cuceni Sun aura min ke duniya tasan you are my wife dole in zauna dake but not as my wife but as my servant
Sannan abunda yasa bazan sakeki ba, karki d’auka ko am in love with you…. Murmushi ya saki tare da fad’in god forbid never
Idan na sakeki in an tashi kwatance za’ace tsohuwar matar NAJEEB, wannan ne kadai yasa zaki zauna dani har ki koma ga Allah domin bazan bar haka ta faru ba, I won’t allow anyone to call you with my ex wife that is d reason da yasa bazan sakeki ba…….