NAJEEB 43

Ganin granny bata ko motsi yasa ta nufi d’akin ummi dake bacci da gudu tana fad’in ummi Ummi kizo mukai Granny asibti na shiga uku Granny ta fad’i k’asa
Ummi dake bacci sai taji kaman tana mafarki da sauri ta tashi amma sai taji ba mafarki bane domin dai dai lokacin ibtisam ta shigo d’akin Tana fad’in ummi Granny ta fad’i muna cikin magana Dan Allah mu kaita asibti ki kira abba
Da sauri Ummi ta tashi tare dasa hijab tana fad’in maiya faru da ita?? Kai tsaye waje suka nufa inda suka tarar har yanzu tana nan kwance a k’asa tana nishi sama sama
Nan Ummi tace maza su kamata su kaita asibiti, hakan ko sukayi ibtisam ta fita ta kira Mai adai daita sahu inda suka Kama Granny ita da Ummi sukai motar da ita, direct asibiti suka nufa da ita inda aka amsheta akai emergency da ita domin a duba lafiyarta
Ibtisam kuka take Sosai, domin a duniya Tana son Granny, ko kad’an bata son taga wani abu ya sameta
Ummi sai a sannan ta kira abba Inda ta fad’a mishi halin da ake ciki, ko minti 30 baiyi ba ya garzayo asibitin Kai tsaye inda ya Tarar dasu suna zaune ibtisam nata faman kuka
Abba yace maiya sameta?? Nan ibtisam ta Fara fad’a mishi Abba muna fira na tashi inje inyi shanya tasa ihu tare da faduwa
Abba yace Toh ya isa mana kibar wannan kukan Mai Dr yace ??
Ummi tace baice komai ba, har yanzu Dr bai fito ba
Nan Abba ya zauna suna jiran fitowan Dr din
Wayar abba ce tayi K’ara d’auka yayi yaga Dad ne Bayan sun gaisa Dad yake cema Abba d’anka ya dawo yau
Abba yace a Barka da fatan ya dawo lafiya
Dad yace lafiya
Abba yace gamu a asibiti Mama bata da lafiya
Nan Dad yace Subhanallah maiya sameta??
Abba yace gamu nan dai har yanzu Dr bai fito ba
Nan Dad yace bari yanzu mu kamo hanya
Abba yace kai yamma yayi fah
Dad yace ya zamuyi dole mu tawo
Nan Bayan sun kashe wayan Dad ya kalli Mum yace mama bata da lafiya yanzu zan kama hanyar Kano
Mum tace maike damunta?
Dad yace wlh ban sani ba, Tadai fad’i ne kuma ance Dr bai fito ba
Mum tace amma daka bari gobe saimu tafi gaba d’aya koh??
Yace a’a yau zani ku saiku tawo gobe
Nan Zarah tace zata bishi
Yace Toh kiyi sauri muje kin San ban son jira
Zarah tashi tayi da gudu taje ta zuba kayanta a akwati tare da abun bukata sannan ta fito suka Kama hanya ita da Dad, mum dai tace ita da najeeb gobe zasu tawo
Bayan fitan su Dad saiga najeeb nan ya fito ya tashi Daga bacci.
Mum tace harka tashi
Yace eh mum Ina Dad ya fita ne??
Tace ya tafi Kano yanzu
Yace yanzu da yamma haka? Lafiya kuwa??
Mum tace granny ce aka kwantar a asibiti, shine ya tafi shida Zarah Nima gobe zamu tafi
Yace Subhanallah maike damunta?? Kai ni bamma taba ji ance tana ciwo ba sai yau
Mum tace Wlh bata ciki ciwo ba, gashi wanda bai ciwo inya tashi yi bai iyaba
Najeeb yace Allah ya Sawake, nima da Ina nan Aida nabi Dad munje tare
Mum tace gobe saimu tafi da safe ai, kaci abinci ko saina zuba maka ne??
Dariya yayi tare da fad’in tunda y’ar autarki bata nan yau nine autan sai a zuba min din kawai
Mum tayi dariya tare da zuba mai, nan suka zauna suna ta fira Inda NAJEEB yace Mum yanzu nasan ina rayuwa wanda da gaba d’aya ba rayuwa nake ba
Mum tace kaman ya??..
Yace Nasan addini na, Mum da gaba d’aya Ina amsa sunan ni musulmi ne amma ban San miye addini ba, amma a yanzu Alhmdlh Nasan abubuwa da dama kuma ina kan koya
Mum cikin mamaki tace najeeb a Ina ka koya??..
Murmushi yayi tare da bata labarin abubuwan daya faru Bayan tafiyar shi
Mum wani hawaye ne ya zubo mata tare da tashi ta rungumeshi ta baya tana kuka tare da fad’in Alhmdlh Alhmdlh Alhmdlh yau nafi kowa murna yau Ina cike da farin ciki d’ana ya fara neman ilimin addini, najeeb Wlh baka ga yanda naji dad’i ba, abunda yake ranmu kenan akan muyi maka magana sai gashi kaida kanka ka Fara koya Wlh ji nake yau kamun anyi min kyauta Mafi girma a duniya
Najeeb yayi murmushi tare da fad’in Mum nima yanzu baki ji yanda nake jin dad’i ba, nasan miye rayuwa nasan yanda zan tafiyar da rayuwa domin samun tsira wanda da duk ban sani ba yanzu kam Alhmdlh
Mum tace najeeb Allah yayi maka albarka
Tashi yayi tare da kamo hannun Mum Ya ri’ke tare da fad’in mum plz ina son duk wani abu dana miki na rashin tarbiya ki yafe min, Dan Allah domin na gane da ba’a akan dai dai nake ba
Mum ta rungumo shi tare da fad’in na yafe maka duniya da lahira, Wlh najeeb komai kayi min ban taba ri’keka ba cos ni uwa ce sannan nasan duk wannan abunda kakeyi ina maka uzuri duba da irin kasar daka taso a cikinta
Wani irin hawaye ne ya zubo a fuskanshi wanda yayi sauri ya goge, lallai uwa uwace, shida kanshi yana jin kunyar abubuwan daya musu baya amma gashi yanzu tace bata rik’eshi ba, Allah sarki rayuwa duk Wanda bai mutunta iyayenshi ba yayi Asara, kun dai ga irin abubuwan da najeeb yayi amma Mum tace bata ri’ke shi ba, waye Zaima wannan inba Uwar data haifeka ba
Jin kiran sallah magrib yasa najeeb nufa masallaci
Su dad sun k’arasa Kano wajan karfe 9 da wani abu, kai tsaye asibitin suka nufa wanda koda Dr ya fito baiyi musu wani bayani akan abunda yake damunta ba, yadai ce jikin da sauk’i sannan suna kan gwaje gwaje akan abunda ke damunta, sannan har yanzu bata farka ba
Hankalin kowa ya tashi da wannan ciwon na Granny, ibtisam gaba d’aya sai kuka take, inda Zarah take ta rarrashinta, wajan k’arfe Goma Ummi tace ya kamata su tafi gida ita zata kwana da Granny….
Nan ibtisam tace ina, ita zata kwana da ita, saida ummi tayi dagaske Kafin ibtisam ta yarda harta suka wuce suda Zarah da abba inda Dad ya tafi hotel shima Bayan ya sai musu su madara ruwan roba da duk wani abu da zasu bukata sannan yaba Ummi kud’i yace ko za’a bukata
Koda su ibtisam suka je gida sai kuka take tana fad’in Wlh Ina jin tsoran wani abu ya samu granny ina matukar Sonta da yawa, Wlh baki ji yanda nake jiba na shiga uku Granny na
Zarah tace haba ibtisam babu abunda zai sameta addu’a za muyi mata, ki daina fad’in haka insha Allah komai zai wuce sannan granny zata warke Kinji
Ibtisam shuru tayi tana sauraran zarah
Zarah tace ki tashi kije kiyi wanka, kinga duk Fuskanki ya tashi idonki ya kumbura kaman wacce tayi shekaru gidan yari
Ibtisam tace hmm zarah Wlh hankalina a tashe yake ban son wani abu ya samu granny Wlh ko kad’an
Nan zarah tace babu abunda zai sameta maza tashi kije kiyi wanka Kinji
Ibtisam tashi tayi ta fad’a toilet tayi wanka, koda ta fito zarah bata d’akin can saiga zarah tazo da tea a hannunta da kazan da abba ya siya musu
Ta ajiye ma ibtisam tace gashi Nima Bari inje in had’a nawa tea din
Tashi tayi ta nufi kitchen inda itama ta had’o tea d’inta ta dawo ta Fara sha ibtisam kam kasa sha tayi
Zarah tace wai miye haka ibtisam kisha mana, ibtisam tace Wlh zarah bana son sha
Zarah tace Indai baki shaba Nima Wlh bazan shaba…..
Ibtisam tace ke nifa bana jin yunwa gwara kici
Zarah tsaki tayi tare da fad’in kinga saida safe
.ganin dagaske take yasa ibtisam fad’in zo kici Nima zanci
Jin haka yasa Zarah ta zauna tare da d’aukan cup din tea din ta farasha tare da kazan
Bayan sun kammala, itama Zarah wanka tayi tazo ta kwanta
Washe gari tunda sukai sallah asuba suka shiga kitchen inda suka d’aura abinci domin sukai asibti, Bayan sun kammala sukai breakfast suka nufi asibitin Wanda suka tarar har yanzu Granny bata farka ba ga oxygen ansa Mata.