NAJEEB 43

Ibtisam hawaye ta farayi domin tausayi, taji Granny ta bata, tare da furta ciwon lokaci d’aya jiba jiya Uwar haka lafiyanta kalau amma kalla yanzu ko numfashi saida aka sa mata oxygen, kai ikon Allah, fita tayi waje tana kuka domin tausayin halin da Granny d’inta ke ciki
Zarah ce ta biyota inda ta zauna kusa da ita Tana fad’in ibtisam hakuri zakiyi kibar wannan kukan, inba haka ba kanki ne zaiyi ta miki ciwo….
Zuwan Dad ne yasa Zarah fad’in Ina kwana dad? Da fatan an tashi lafiya
Dad yace lafiya yamai jiki??
Tace da sauki
Itama ibtisam gaida Dad tayi inda yace har yanzu kina wannan kukan mamana
Ibtisam hannu tasa tare da share hawayen idonta
Murmushi Dad yayi sannan yace yauwa gwara kibar wannan kukan
Dad ya kalli Zarah yace Mum d’inki bata k’araso ba??
Zarah tace eh
Dad yace a’ah tace min fah tun d’azu sun shigo Kano bari in kirata d’auko wayarshi yayi yana k’okarin kira Zarah tace ga sunan
Nan Dad ya nufesu inda sukai gaba shida mum bayan ibtisam ta gaidata, d’ago kanta tayi sukai ido biyu da najeeb wani irin faduwan gaba taji wanda bata taba jiba sai yau, najeeb kam kallo d’aya yayi mata ya kauda kai tare da kallon Zarah yace yamai jiki hope da sau’ki??
Zarah tace toh har yanzu bata farka ba dai…..
Mum ce tazo tana fad’in ibtisam kuna ina kuzo Granny na kiranku NAJEEB kaima tawo
Da gudu ibtisam ta nufi d’akin inda taga Granny tana kallon sama hawaye na zuba a idonta, jin muryan ibtisam yasa Granny kallonta ibtisam nufan Granny tayi tana kuka tare da kamo hannunta
Granny cikin murya tana hardewa tace ina na je bu
Mum tace najeeb jeka mana
Najeeb kusa da gadon yaje inda Granny ta Kamo hannunshi Tana mishi murmushi, shima murmushin ya sakar mata, had’a hannunshi tayi dana ibtisam ta Fara magana najeeb Ina son ku kasance kaida ibtisam a haka har karshen rayuw….. Kallon mum tayi tace fad’a mishi abunda nake fad’a nan Mum ta Fara fad’a mishi abunda Granny take fad’a….. Granny tace naso inga yaranku amma Allah bai nufa ba…..
Ibtisam cikin kuka tace Granny ki daina fad’in haka dan Allah na ro’keki
Granny tace ibtisam ni nasan bazan tashi ba, wannan ciwon bazai barni ba, dan Allah najeeb ku koma ku zauna kaida ibtisam hakan zaisa koda na mutu in mutu cikin salama, wlh Ina takaicin rashin jituwan ku,, ina so kumin alkawari zaku zauna a tare har abada……
Da sauri najeeb yace I promise Granny kin gani tare da K’ara matse hannun ibtisam duk mum na fassara Mata
Granny wani irin murmushi tayi lokaci d’aya ta saki hannunsu Tana salati wanda dai dai lokacin oxygen din da aka saka mata yake k’okarin d’aukewa…….
Plz I don’t tin gobe zanyi posting coz gobe gaba d’aya Ina busy sai yasa na muku yau but inna samu time may be inyi koda babu yawa