NOVELSUncategorized

NAJEEB 5


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());

Ibtisam tace na Fara mana, sai dai Granny ta sani gaba da maganan aure, kai wannan tsohuwar akwai jaraba 

Zarah tace Niko Tana sani dariya wlh, dama ta mana wata biyu a nan 

Ibtisam tace Aiko ko sati tayi a nan sai kince ta isheki, ko sanda take zuwa kina skul in kin dawo kin gaji, yanzu da kike zaman Gida ai wlh saita isheki, dariya zarah tasa inda suka fara tsara yanda za suyi a skul, wayan zarah dake wajan wardrobe d’inta ne ya fara K’ara, tashi tayi da sauri ta d’auka, ganin Mai kiran yasa tayi saurin d’auka tare da fad’in bros 

Yace yakike?  Cikin harshen turanci 

Tace am fine my bros, sai dai nayi missing dinka 

Murmushi yayi tare da fad’in gobe Zanzo Nigeria, make sure kisa a gyaramin part d’ina 

Tace an gama bros, Granny tazo ma 

Tsaki yaja tare da fad’in har yanzu bata mutu ba? 

Zarah tace what?  Sai kuma ta fashe da dariya tare da fad’in Bari Dad ya jika, kana ma mum d’inshi fatan mutuwa.

Kashe wayan yayi ba tare daya kuma ce mata komai ba.

Kallon ibtisam tayi tare da fad’in bros gobe zai zo,, rabonshi da gida wajan wata hud’u kenan 

Tabe baki ibtisam tayi tare da fad’in wannan ba damuwa ta bace. 

Zarah dariya tayi tare da fad’in oh na manta Ashe enemy d’inki ne, sai kuma ta saki dariya tare da fad’in nima a waya yake sake min, inya dawo sai yayi ta d’aurewa kaman dodo, na rasa irin halinshi Wlh, zanso inga matarshi inya ya zai dinga mata. 

Itbtisam tace lallai Aiko duk wacce ta auri wannan ta shiga uku, sunanta sorry, lokaci d’aya kuma ta tuna da abunda ya kawo Granny, cikin ranta tace Allah ya tabbatar inga yanda zaiyi. 

Zarah tace dama Ayi auran zumunci ke dashi, tunda naga halinku d’aya K…. 

Da sauri tace aniyarki ta biki, da in auri wannan yayan naki gwara in mutu Banyi aure ba, wannan wani banzan tunani nema kikayi haka, tsaki ta saki cikin bacin rai. 

Zarah tace Allah ya huci zuciyarki, wasa nake miki,  ai nasan in aka had’aku wata rana k’ona gidan zakuyi 

Itbtisam dake huci tace wannan Aiba wasa bane, in mala’iku suka amsa fah? Haba dan Allah, wlh gwara in mutu yau da ace na auri NAJEEB, dan Allah karki k’aramin wannan Wasan plz, wlh kinsa raina yayi mugun baci Sosai 

Zarah tace ikon Allah, haka tsanan NAJEEB yayi girma cikin zuciyarki? Adai dinga hakuri d’an uwanki ne dai 

Tsaki Itbtisam taja tare da tashi tana fad’in naga baki da wata firan arziki saina wannan yayan naki Kinga Bari inje wajan Granny n…. 

Da sauri zarah ta janyota Tana fad’in na daina miki firanshi, amma kudaina wannan abun babu kyau Wlh, duk da Nasan laifin bros NAJEEB ne, yana da shegen miskilanci da raini wlh, kodan ya girma mutane ne oho, wlh koni hakuri nake dashi, ga Dad komai yace saiya biye mishi tsaki taja 

Itbtisam tace Kema kenan, balle ni ki….  Karan wayarta ne yasa bata k’arasa abunda tayi niya ba, d’auka tayi taga kabir ne wanda a jiya tayi saving number d’inshi, sawa tayi a kunne tare da fad’in hello 

Ta gefenshi yace ibti Barka da yamma, sorry ban kiraki ba, aiki yamin yawa, yanzu nace gaskiya sai naji muryanki, ya kano? 

Tace uhm lafiya kalau, nima bana Kano Ina Abuja 

Da sauri yace yaushe kika zo Abuja? 

Tace d’azu nazo nida Granny gidan uncle d’ina 

Kabir yace shine baki fad’amin jiya ba, muzo tare 

Tace naga hakan bai kamata ba, bai dace in bika ba har zuwa wani gari, hakan ba dai dai bane 

Murmushi yayi tare da fad’in hakane, my ibti, tare da fad’in na gode ma Allah daya had’ani dake, ina Mai farin ciki, Allah ya tabbatar yasa ki zama mallaki na 

Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.

Yace anjima zan kiraki, ina fatan zaki bani dama inzo in ganki a nan? 

Tace babu damuwa tare da fad’in sai anjima, ta kashe wayan. 

Zarah dake zaune kusa da ita, tace ke dawa haka? Daka ji saurayinki ne yanda kike wani kashe murya 

Ibtisam takai Mata duka tare da fad’in ta ina na kashe murya?kina da sharri Wlh 

Zarah tace fad’amim Waye inji tare da d’aga mata gira 

Nan ibtisam ta bata Labarin inda suka had’u 

Zarah saida tayi dariya Sosai tare da fad’in Wlh Granny tana da matsala, Tab gaskiya ki daina fita da ita.

Uhm kawai ibtisam tace 

zarah tace Amma inda nice ke Wlh zan yarda in aureshi, tunda muda zamu karatu kaduna, shi kuma yana Abuja, Kinga zaki samu daman karatu, yanzu fah maza tsada suke sai kiga mata da yawa babu mijin aure, wlh ibtisam inka samu dama Kar kayi wasa dashi, kyace ya jiraki shekara hud’u ai yayi yawa wlh, kina da tabbacin zai iya jiranki har shekara hud’u, haba ibtisam Wlh nima da badan Dad ba da yake son inyi karatu ba Aida aure zanyi Wlh, nifa aure nake so, Amma Dad ya’ki fahimta inaga saina fito na fad’a musu 

Dukanta da wasa ibtisam tayi tare da fad’in amma dai da kin cika mara kunya number d’aya, Tabdi Niko Wlh karatu ne a gaba na, Kinga mazan yanzu basu da tabbas, wlh gwara koda zanyi auran saina gama karatu in samu aiki sannan inyi, dan ban son ina bin namiji Ina bani yana min wulakanci, gwara in tsaya da kafafuna, Suma yanzu mazan basu cika auran zauna gari banza ba, dan basa son wahala 

Zarah tace uhm, ni Wlh aure nake so, ke nifa wannan karatun kaman dole ne, amma Wlh Ina bala’in son inyi aure, Kinga in Nayi sai inyi karatun a d’aki na, hankali kwance, amma hakan bazai yihu ba, Allah yaban iyaye duka y’an boko, ko wanne zai ka’ida, ba mum ba, ba Dad ba, yanzu koda wasa ban isa ince Ina son aure ba, wai dana shiga uku, ko bros NAJEEB baiyi ba shida yake aiki sai ni, Hmmm ta sauke ajiyan zuciya 

Ibtisam tace zarah kin San muhimmancin ilimin mace kuwa? Inda za’a tambayeni tsakanin mace dana miji waya kamata a fi bama ilimi? Zance mace ya kamata, kin San mai yasa? Mace itace tushen gida Mace itace take zama a gida ita da yara ta basu tarbiya tare da duk wata kulawa, in mace bata da ilimi taya za tayi hakan? Da yawa yaran da zaki gani suna rashin ji Toh uwarsu bata da ilimi, sannan yana dakyau mata a dinga basu ilimi domin ko ina a dinga damawa damu, ki kalla aikin soja akwai mata Kinga wannan abun alfahari ne, ki duba fannin Siyasa akwai mata wanda da ana ma mace y’ar Siyasa kallon y’ar iska, amma yanzu an fara fahimta, inda babu Mata a Siyasa da baza’a dinga bamu hakkin mu ba, bazan musan miye Siyasa ba, sannan mune dai mukaci jefa ruwan kuri’a, sannan yana dakyau mata su dinga karatu kodan su zama likitoci, yanzu Idan mace tazo haiyuwa namiji zai amshi haiyuwar tayu ba musulmi bane, Kinga inda mata suna karatu Sosai da an huta, komai mu ana tauye mu, daka munyi aure shikenan, in namiji yace ba zamuyi ba shikenan ta zauna, bayan ilimi shine ginshikin rayuwa, wlh zarah in Kinga yanda in naga mace take burgeni in naga tana karatu ko aiki sai Kinji mamaki, zan iya bama mace tallafin komai nake dashi dan tayi karatu domin Nasan al’umma zasu amfana da ita, yana dakyau komai a dinga saka mata, ana bamu y’ancin mu, Idan kika duba yanzu zamani ya canza duniya ta canza, ilimi both na addini dana zamani is like kaman ya zama dole mace tayi, indai Tana son ganin ci gaba da taimakon Al’umma.

Zarah tace bank’i taki ba,  shima auren yana da muhimmanci, sannan aure baya hana karatu, nidai Ina baki shawara a matsayina na y’ar uwarki, indai kabir dagaske yake kice Ya fito Wlh, Kinga kyaci gaba da karatun a d’akin ki, amma baki da wani hujja kice saboda karatu k’iki yin aure, Abba Nasan shi zai miki aure amma nikam Dad Nasan Wlh koda wasa saina gama wannan karatun zaimin aure, har shekara hud’u ta k’arasa maganan cikin tausayin kanta.

Muryan Granny sukaji Tana fad’in kuna inane haka? 

Zarah tace Granny gamu a nan, Granny shigowa tayi ta saki baki Tana fad’in yanzu wannan kaman mota, motar nan taya akayi ta shigo wannan d’akin, naga dai kofar karama ce, ni ban taba ganin irin wannan motar ba Wlh, mota harda katifa, ya ake tukata? 

Dariya suka saki su duka sannan zarah tace Granny gado nefa 

Sakan baki tayi tana mamaki tare da fad’in yanzu bakya tsoran wannan abun, salan kina bacci ya fara tu’ka kanshi? Ina gadonki Nada? 

Zarah tace Kai granny wannan fah ba mota bane, gado ne mai shape din mota, gadona Nada anbama Mai aiki takai gidanta da aka canza min wannan. 

Sakan baki tayi tana mamaki tare da fad’in naji kince gado ne mai chape din mota, miye chape? 

Dariya suka saki, itbisam tace haba Granny Tana nufin gado ne mai fasalin mota, yanzu kin gane? 

Tace Hmmm wanna ai iskanci ne, in banda asaran dukiya, ace gado za’a saka a d’aki Mai fasalin mota da haka a siya motar mana a ajiye, yanzu wannan gadon nawa aka siya? 

Zarah tace million biyu da rabi 

Salati Granny ta saki tare da fad’in audullahi yana tunanin mutuwa kuwa? Yanzu gadon da zaki kwanta ki tashi shine har million biyu da rabi, oh ni Aminatu, wannan asaran dukiya haka Kai audullahi zai gamu dani, dama aure yayi miki keda wancan dan banzan, koda yake Bari in Gama da munafukin yayanki da wannan ta nuna ibtisam, sannan in dawo kanki, bari audullahi ya fito naji ance ya dawo yana hutawa 

Zarah cikin jin dad’in maganan Granny tace Granny gobe ma zai zo gida NAJEEB din 

Granny tace yauwa Alhmdlh Nima zani yola, dan Wlh wannan karan da Mata zai koma dan banza, sai na mishi iya shege, tunda bashi da niyan aure, inma aljana ce ta aureshi zata rabu dashi in na saka aka d’aura mai aure, zan zabo mata guda uku cikin dangi in tawo dasu ya zaba d’aya, inma duka yake so ya auresu dan banza kawai……. Muje zuwa muga had’uwan  Granny da miskili, sannan muga ya zata kaya in aka zabo ma NAJEEB mata har uku kaman yanda Granny tace hhhhhh. 

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button