NOVELSUncategorized

NAJEEB 50, END

Ibtisam fuska d’aure ta zauna ba tare da tace komai, ba domin duk yanda taso ta waske ta kasa

Kiran Aisha da akayi a waya yasa bata lura da halin da ibtisam din ta shiga da, hauwa ce ta kira Aisha inda take tambaya ko Aisha ta iso, Bayan sun gama wayar, Aisha ta kalli hauwa tare da fad’in wasa fa nake miki ibtisam ai tunda kin auri najeeb dole in hakura ya zanyi


Ibtisam jin haka yasa ta Dan saki, domin ta d’anji dama dama

Ibtisam Sun Fara lecture inda bini bini najeeb ya kirata, wanda shima ya tafi saudiya

Zarah da dr jibril soyayya suke sosai, wanda tun Zarah bata saki harta saki dashi, domin gaba d’aya ta yarda da duka dabi’arsa, kuma ta yaba

Inda Dr jibril ya bukaci ya tura gidansu Zarah tayi na’am da batun Bayan tayi shawara da ibtisam dan ita tana mugun son yin aure Sosai

Ibtisam ta fito daga lecture duk ta gaji gaba d’aya kwana biyun nan tana yawan jin kasala tare dajin bacci Sosai, bata da wani aiki sai bacci kaman wata kasa, wani zubin haka najeeb zaiyi ta kira amma tana bacci, har saiya kira Zarah ta tashe ta in tana kusa….. Kai tsaye d’akinsu ta nufa inda ta bud’e kofa tana shiga sai gado inda ta kwanta abunta.

Gaba d’aya ibtisam bata saka Gyale yanzu sai hijab kaman yanda najeeb ya bukata, domin a duniya yanzu bata son saba mishi….

Wayanta ne keta k’ara Wanda ta manta bata saka ta a silent ba, dan tsaki tayi sannan ta d’auka ganin Sunan najeeb ne wanda tasa my only, yasa ta saki murmushi tare da dannawa tasa a kunne

Najeeb yace yau bakiyi bacci ba kenan??

Ibtisam tace ina kwance ma

Yace ta kunna data d’inta yana son suyi video call ya ganta

Tace toh tare da tashi tasa ma kofar d’akin key inda ta kunna data Tana kunnawa saiga kiransa nan ta whatsapp video call ya shigo dannawa tayi tare da d’auka

Daga shi sai jallabiya yana kwance akan wani makeken gado

Najeeb yana ganin fuskanta ya saki murmushi tare da fad’in I miss you so much

Itama murmushin ta saki tare da fad’in nima haka, I really miss you

Murmushi kawai yayi, sannan yace in kinyi missing d’ina just come to saudiya and see me

Dariya ta saki tare da K’ara kwanciya itama

Najeeb yace zaki zo

Tace a’a muna karatu

Yace karatun ya fini??

Tace haba, kafi min komai, ka daina hada kanka da kowa plz my baby

Yanda tayi maganan cikin shagwaba yasa shi yin murmushi tare da fad’in daga nan zan wuce America but b4 that Zanzo in ganki, dan tsaki yayi tare da fad’in no need ma inzo tunda baki missing d’ina ba

Yana magana tana lumshe ido alaman bacci takeji sosai…

Najeeb yace ibtisam wannan baccin naki yayi yawa Mai yake damunki??  Kodai bakya bacci da daddare ne??

Ina ai tuni ta fad’i ta Fara bacci, hhhhh

Najeeb kai ya girgiza alaman mamaki tare da fad’in mai yake damunta, jin tayi shuru Kuma ya daina ganinta sai saman gado yake gani yasa ya kashe wayar

Dr jibril ya tura iyayenshi wajan Dad inda aka amince an basu Zarah, kuma akai Sa’a Dad yasan mahaifin Dr jibril an amince inda aka yanke biki aka saka wata uku kaman yanda iyayen Dr jibril suka bukata hakan ko akayi aka tsaida magana

Soyayya da shakuwa Mai karfi ya k’ara shiga tsakanin Dr jibril da Zarah

Dr jibril ba’a dad’e da turawa gidan su Zarah ba, ya ajiye lecturing inda ya koma kula da business din mahaifinsa, domin mahaifinshi yace yana bukatar hutu

Ibtisam da Zarah Anata shirya yanda za’a tsara biki

Aisha da hauwa kam su yanzu Abu yaci uban na da, domin sai suyi kwana uku biyar basa nan, ita kam kubra ta nutsu tayi aure bata ma musu magana sosai, duk da a d’akinsu take kwana, domin basu da magana kullum saina ta dawo suci gaba da abunda sukeyi, wannan dalilin yasa ta daina kulasu, sai dai Gaisuwan musulunci

Ibtisam ta fitar da anko din zarah inda kubra itama ta siya, su Aisha suma Sun siya domin lokacin bikin suna hutu

Najeeb kullum suna waya da ibtisam, wacce bini bini ana faman Bacci, sai dai yanzu abun ya rage ba kaman da ba, sai dai abunda ke damunta yanzu yawan Kwadayi

Yau ibtisam ta fito daga lecture inda salis yake bayanta yake yana fad’in Tana dai karatun exam ko??  Domin ya kusa

Murmushi tayi tare da fad’in Sosai kuwa

Ganin mutum tayi a gabanta a tsaye

Ido ta zaro tare da bud’e baki alaman mamaki

Shi kam idonshi na kanta, ganin haka yasa ya janyota ta fad’o jikinsa tare da fad’in come and hug your husband

Najeeb duk da akwai mutane abunda yayi ko a jikinsa

Ibtisam kam kunya taji

Salis dake bayanta ya saki murmushi tare da fad’in oh shine mijinki??

Mi’ka ma najeeb hannu yayi wanda shima ya mi’ka Mai fuska babu yabo babu fallasa suka gaisa inda salis ke cema najeeb ashe shine mijinta, gaskiya kun dace sosai

Najeeb thanks yace Mai tare dajan hannun ibtisam sukai mota inda yace driver yaja suje

Tunda suka shiga mota tana manne dashi har hotel inda ya Kama dak’i Kai tsaye d’akin suka nufa, suna shiga ya kalleta tare da tamke fuska ya dan saketa daga ri’kon da yayi mata

Itama kallonshi tayi, lokaci d’aya tace najeeb mai yasa zaka ri’keni haka a gaban mutane??

Wani irin iska ya furzar sannan yace just to show them that am your husband, sai yasa Nayi haka, kuma yanzu sun sani

Wannan guy din shine na ganki dashi tun farkon zuwa na skul d’inku sanda na d’aukeki, and yau ma gaku tare, ibtisam I hate him, bana son kina kallon kowa….

Hannunta tasa akan kugunshi tare da rungumoshi ta janyoshi tana fad’in oh my god, ina dakai kasan babu wanda zan kalla, hannunta d’aya tasa a kirjinshi tana shafawa tare da fad’in kai nake kallon bana ganin kowa……. Idonta na kanshi sannan tace Mai yasa kazo baka fad’amin ba

Idonshi na kanta shima yace Idan Zanzo ganin my baby saina nema izini??..

Murmushi tayi tare da fad’in no koda yaushe kaso hakan zaka iya zuwa

Matseta shima yayi a jikinsa Sosai, yana fad’in baby kinyi haske Sosai, kodai akwai ajiya nane a jikin ki

Dariya tayi Sosai tare da fad’in am a Dr banda komai

Dariya shima yayi tare da fad’in oh I see, u r a Dr amma baki gane maike damunki?

Murmushi tayi tare da fad’in am ok komai nawa lafiya

Dariya yayi tare da kaita gadon d’akin suka zauna

Kallonshi tayi tace gaskiya lokaci na gudu

Najeeb yace sosai Nima gashi na kusa komawa aiki baifi sati Biyu ba in koma

Ibtisam tace muma mun kusa Fara exam, ga bikin zarah yana zuwa

Najeeb yace Allah ya taimaka sai kiyi karatu dakyau

Kallonshi tayi tana fad’in Toh ka mayar dani plz in samu inyi karatu

Wani irin kallo ya watsa mata tare da fad’in Ina??  Muna nan harna sati d’aya, gwara ma ki cire wannan maganan, domin hakki na nazo amsa

Dariya tayi tare da fad’in 1 week?? Yaushe Nayi karatu, kaima fah kasan ba Bari na zakayi inyi karatu ba

Najeeb yace zan dinga baki 30mnt na karatu, sauran lokacin kuma nawa ne

Ibtisam dariya tayi najeeb ya rungumota tare da fad’in wai baki missing din mijinki ba???

Tace Nayi alot

Ido ya lumshe yana murmushi lokaci d’aya yace ok show me that you miss me…..

Ibtisam da najeeb saida sukai 1week a hotel Kafin Ya barta ta koma skul, inda suka Fara exam shi kuma daga kaduna ya wuce America akan saida bikin Zarah zai dawo

Ibtisam gaba d’aya bata da time saina karatu, ga yawan Kwadayi da takeyi Sosai, gashi ita bata cika wani cin abinci ba, sai dai tace wancan inta samu ta tsakuri kad’an taci, ta k’ara haske Sosai

Ranan da sukai hutu kai tsaye Kano suka wuce ita da Zarah inda za suyi sati d’aya a nan, saisu wuce Abuja

Ummi kallo d’aya tama ibtisam ta gano dawan garin, sannan taji dad’in ganin yanda ibtisam ta koma ta k’ara girma kyau, kana ganinta kasan tana cikin kwanciyan hankali

Ibtisam koda ta shiga d’akinta na gidan kuka tasa sosai, tare da fad’in yau gashi rana ta farko nazo bakya nan Granny, kuka take Sosai tare dayi mata addu’a lokaci kad’an kanta ya fara Mata ciwo, karan wayarta yasa ta d’auka ganin najeeb ne, da sauri ta daina kukan amma tana magana yace kukan Mai kikeyi??  Maiya faru??  Maiya sameki??  Duka lokaci d’aya ya jefo mata wannan tambayar

Ibtisam tace ina tuna granny ne kawai

Najeeb yace addu’a zaki dinga mata koda yaushe

Tace kullum Nayi sallah farillah guda biyar saina mata addu’a, koda nafila Nayi shima saina mata addu’a

Najeeb yace yauwa haka akeso

Nan suka taba fira kad’an sannan sukai sallama

Ibtisam tunda tazo Kano take zazzabi.

Yau dai Ummi tace suje asibiti ita da Zarah taga Dr

Haka ibtisam suka tafi Bayan ta kira najeeb ta fad’a mai zata hspt kaman Malaria na damunta .

Cikin damuwa yace Allah ya k’ara sauk’i, komai ake ciki ta kirashi ta fad’a mai, koda suka je hspt bini bini ya kira, harta shiga wajan Dr inda aka dubata tare dayi mata test da scanning inda aka gano Tana d’auke da cikin wata biyu da sati uku….

Ibtisam wani irin murna taji, domin tasan abunda najeeb keso kenan

Koda ya kira suna asibitin zarah ce ta fusge wayar tare da fad’in bros zaka bani goran albishir

Yace what happen

Tace ibtisam Nada cikin 7week

Najeeb wani irin murna yaji tare da fad’in zan baki babban kyauta in Zanzo..

Nan ta mi’ka ma ibtisam wayar inda najeeb yace my love am so happy, lallai najeeb yaji dad’in wannan labarin sosai

Sun fito zasu tafi saiga kabir ya ru’ko matarshi Wanda cikinta ya fito Sosai haiyuwa yau ko gobe

Ido Biyu sukai da ibtisam, kasa d’auke idonshi yayi daga Nata, inda ita kuma ta kawar da Nata idon tare da mamakin irin abunda yayi kenan shi harda yima matarshi ciki, hhhhhh kunji ibtisam sai kace keba cikin gareki ba

Kabir tsayawa yayi inda zarah ta gaidashi ya kalli ibtisam tare da fad’in ya hakurin Granny Allah yaji kanta, naje nayi ma abba gaisuwa

Ibtisam tace Ameen, KABIR ya kalli hafsat yace ga ibtisam, ibtisam ga matata

Ibtisam murmushi tayi tare da fad’in eyya sannu Ina wuni

Hafsat fuska babu yabo babu fallasa ta amsa da lafiya yau dai naga ibtisam…..

Ibtisam zatai magana najeeb ya kira wanda tasa mishi ringing d’inshi daban tare da hotanshi, nan wayar ta Fara K’ara I miss you like crazy, tell me when you coming back home….

D’auka tayi tana fad’in sai anjima my hubby ya kira tayi gaba abunta

Kabir ya d’anji wani abu, amma lokaci d’aya ya basar tare da fad’in haka Allah ya nufa

Ita kam hafsat kallo d’aya tama ibtisam tasan tana da ciki, wannan ne yasa ta cire ba’kin kishin data d’aura ma ibtisam din

Zarah itama Bayan ibtisam tabi suka tafi, Bayan ibtisam ta gama waya Zarah tace yau naga matar kabir, gaskiya kin fita kyau nesa ba kusa ba

Ibtisam tace uhm tunda nice taki ba AI dole kice haka

Zarah tace Wlh dagaske nake, Kin ganta kuwa??  Kawai fari zata nuna miki

Ibtisam tace ni mubar maganan bata su nake ba, domin ba wannan bane a gaba na, indai yana son matarshi ai shikenan

Dariya zarah ta saki Tana fad’in Toh fah

Haka har suka k’arasa gida

Inda zarah ta fad’ama ummi abunda ke damun ibtisam duk da dama ita ta sani

Washe garin ranan saiga driver Wanda NAJEEB ya turo yazo ya d’aukesu ya kaisu abuja, saida Ya buga ma driver din warning akan ya tawo da matarshi a hankali

Suna hanya bini bini ya kira yaji suna ina da haka har suka k’arasa Abuja, inda tun kafin su Iso labari ya iske mum akan yana ibtisam nada ciki

Mum tayi farin ciki Sosai

An fara gyara amarya Sosai gyaran jiki da sauransu

Ibtisam kam tunda tasan tana da ciki gaba d’aya kaman wani abu saita Fara amai Sosai wanda da batayi, komai taci sai amai, indai taci Abu sai anyi Sa’a sai dai wannan ciwon babu ciwon kai…..

Najeeb saida biki ya rage kwana biyar yazo, yana zuwa ya dauk’e matarshi yayi gaba da ita….. Zarah bata so hakan ba domin tace ibtisam ce Mai mata komai

Gaba d’aya ibtisam wannan cikin yazo mata da wani salo, wanda ya canza mata ba kaman wancan ba….

Fitowa tayi daga toilet tayi wanka jikinta babu komai sai towel iya Giwa d’aure a jikinta

Najeeb ne ya shigo cikin d’akin daga shi sai boxer da singlet a jikinsa, rungumeta yayi da sauri ta Fara tureshi tare da toshe hanci…..

Dan sakinta yayi yana kallonta cikin mamaki, tare da bud’e ido alaman maiya faru

Ibtisam da gudu tayi toilet tana amai

Bayan ta gama ta fito najeeb na nan tsaye yana mamaki yanda yaga ta toshe hanci.

Kallonshi tayi tare da fad’in baby wani turare kasa haka Mara dad’i

Baki najeeb ya saki lokaci d’aya yayi murmushi tare da girgiza kai, yace ibtisam yau perfume d’ina ne baida dad’i??

Ibtisam tace a’a just Wanda kasa yau ne bana so

Yace ibtisam perfume d’ina ne da nake sawa ban canza wani ba

Ibtisam tace plz Nidai bana so plz

Najeeb yace OK let me go and change

Kai tsaye yayi d’akinsa ya fad’a toilet tare dayin wani wanka, ko turare bai sa ba, sannan ya kuma nufa d’akinta, inda ya ganta tasa wata riga y’ar kanti dai dai wajan giwarta

Gadon ya nufa tare da zama kusa da ita, ya janyota jikinshi, shima dai hanci ta toshe tana k’okarin tashi

Najeeb ganin haka yasa ya barta

Tashi tayi tare dayin nesa dashi, tace plz najeeb Wlh bana son wannan kamshin

Najeeb shuru yayi yama rasa abun cewa hhhhhh

Ganin haka yasa tai k’okarin fita daga d’akin

Najeeb yace come back bari in fita, wannan cikin baya sona kusa da Mum d’inshi…

Ibtisam tace najeeb…..

Yace don’t worry na barku tunda ba’asan Dad kusa

Murmushi tayi tare da nufansa domin ya bata tausayi dan tasan yayi kewarta Sosai

Toshe hanci ta kuma yi Bayan tayi hugging d’inshi, wannan cikin dai na gudun miji ne

Dan janyota yayi tayi saurin cire Hannunta a hanci

A hankali yace baby I miss you but baby yana pushing d’ina

Ibtisam ido ta lumshe tare da fad’in idan yana pushing din’ka mum will not allow

Hancinta yaja da take ta matsewa

Lokaci d’aya yace mai za’a bani??

Tace abunda kake so

Yace you I need you

Tace am yours.

Murmushi yayi tare da saka bakinshi cikin Nata, gaba d’aya ibtisam ji takeyi kamshin turaren shi yana damunta

Haka har sukai gado, najeeb ya lura da ita dan haka baiyi wani wasa ba, domin yana saka bakinshi akan nipple d’inta ta saki k’ara tare da tureshi domin zafi yake mata, dan tunda tasan tana da wannan cikin ko brezia tasa saiya dinga mata zafi Sosai

Najeeb ganin haka ya cire bakinshi inda yasa banana d’inshi cikin hq d’inta, wani irin nishi take na wahala gaba d’aya bata jin dad’in abun

Najeeb lura da hakan yasa yayi realising da wuri tare da barinta

Tana ta sauke nishi dakyar

Najeeb rungumo ta yayi tare da fad’in wannan baby din baya son Dad koh??  Baya son Dad kusa dashi

Ibtisam tace no kawai bana son kamshin turaren ne, sannan sex dinnan zafi, ga nipple d’ina shima zafi, najeeb muje hspt ko za’a bani magani

Najeeb yace OK muyi wanka muje, domin gaskiya za’a cuceni

Yanda yayi maganan saiya bata dariya Sosai

Wanka sukayi tare amma still tana jinshi yana mata kamshin turaren koda zasu fita Bai saka komai ba, body spray yasa sannan sukai hspt, inda suka ga Dr ibtisam tayi mishi bayani yanda takeji

Bayan ta gama mishi bayani

Najeeb yace Dr plz ka bamu Magani muji yanda za’ayi

Dr yayi murmushi tare da fad’in hakuri za kuyi babu wani magani da zai daina wannan Abun haka yanayin cikin yazo, kasan ko wani ciki yana zuwa da yana yinshi, ita wannan haka yazo dashi, Akwai wata da ita inta samu ciki take son yin sex, wata kuma bata so

Hakuri za’ayi a dingayi haka

Najeeb yace yanzu har zuwa yaushe zai daina??

Dr yace ya danganta wata harsai ta haiyu fah, wata kuma Allah zai iya d’auke Mata kuma

Najeeb dai haka suka dawo jiki a sanyaye inda ibtisam tace ya maidata gidan bikin kawai domin bata ga amfanin zaman ba

Nan najeeb yace dagangan takeyi dama, danta koma can

Ibtisam taci dariya ranan Sosai gashi najeeb ya tamke fuska alaman shida gaske fah yake

Ibtisam tace haba my baby kasan bana haka  kaida kanka ka gane ciki ne yasa haka even warin gidan nan bana so kawai hakuri nake

Najeeb yace tashi muje in kaiki, ni mai hakuri ne ai Hhhhh Tab su hakuri manya

Ibtisam had’a kayanta tayi suka fita

Zarah taji dad’in ganin ibtisam ta dawo

Ciki Dai ya kwafsa ma najeebu

Hidiman biki ake Sosai su Aisha da hauwa da kubra sunzo

An had’a kamu wanda ya had’u Sosai

Ana gobe daurin aure akai dinner inda aka tsara amarya tayi mugun kyau

Ibtisam kam komai bata shafa ba domin bata jin zata iya wannan cikin dai yana wahalar da ita Sosai bata son komai

Najeeb yana manne da ita duk da bata son kamshin turarenshi duk da ya canza turaren amma still bata so

Aisha tazo Sun gaisa da najeeb wanda yake ta wani shan kamshi, domin kallo d’aya yayi musu yaga basu mishi ba Yaran

Kubra kam komai nata cikin mutunci domin gaba d’aya ta canza kaman ba ita ba

Hauwa ta kalli Aisha tace gaskiya ashe najeeb din ya had’u

Aisha tace bana fad’a miki ba, ai ibtisam tayi Sa’a kalla yanda yake ji da ita, muma Allah ya bamu masu son mu

Hauwa tayi dariya tare da fad’in Ameen

Sannan tace amma wannan ba k’aramin miskili bane, Kinga wani irin kallo da yake mana

Aisha tace uhm na gani

Anyi taro an watse Washe gari aka d’aura aure inda aka Kai amarya gidanta dake abuja inda yasai gida a nan Wanda aka tsara mata komai, dr jibril dai an aura Zarah, yau burin Zarah Ya cika, ranan tasha kuka sanda za’a kaita domin tunawa da tayi da Granny itama ibtisam tasha kuka Sosai, lallai inda granny na nan da babu wanda zai kaita murna yau

Allah dai yaji k’anta

Washe garin bikin su Hauwa suka Kama hanya bayan Mum ta musu sha tara na arziki an basu kayan biki Kala Kala harda kudi Mum ta basu sannan suka wuce

Itama ibtisam ranan NAJEEB yace shifa hakurin shi ya k’are ko zata toshe hanci suje a bashi hakkinshi

Ibtisam dai bata so ba haka ta bishi suka tafi, yanzu in Suna sex babu wasa Dan bata son wannan Abun yanzu, hhhhhh Kai Mata nashan wuya…..

Najeeb dai wannan karan bai samu abunda yake so ba, hakuri dai yai tayi haka daga karshe yama daina komai da ita, domin yaga dagaske bata so har hutunsu ya k’are suka koma skul shima ya koma America

Ibtisam kullum suna waya da najeeb Sosai karatu suke wanda sun kusa kammalawa

Wani hutu da sukayi tayi ma najeeb zuwan bazata inda taje baya nan yana office

Koda ya dawo Kai tsaye bedroom d’inshi yaje yana shiga ya bud’e ido ganin ibtisam da cikinta wanda ya fito sosai, domin yanzu yana wata 7 da sati wani abu, Yadai kusa shiga wata 8

Lokaci d’aya kuma ya nufeta tare dayin hugging d’inta, yana fad’in Kece dagaske??

Dariya tayi tare da fad’in nice

Dan sakinta yayi lokaci d’aya tare da kallon cikinta yana fad’in baby har yanzu baka son Dad??

Kanshi yasa a wajan cikinta tare dasa kunnenshi, lokaci d’aya yace see my baby yace I yarda yanzu….

Ibtisam dariya ta saki Sosai tare da shafa mishi kanshi, itama tana mamaki da yanzu bata jin kamshin da yakeyi yanzu

Gaba d’aya koda yake dama ciki yana saka haka, musamman in yana k’arami, babu abunda bai sawa, amma idan ya dad’e yakan canzawa

Tashi najeeb yayi tare da fad’in am so happy da wannan suprise din

Ibtisam dariya tayi tare da fad’in Mum and baby sunyi missing dad

Najeeb matseta yayi a jikinsa tare da fad’in Dad yafi missing d’inku, muje Kimin wanka

Ibtisam dariya tayi tare da fad’in no je kayi, zanje in duba maka abunda zaka ci before ka fito

Najeeb yace no karki damu zansa a kawo, ban son kina aiki

Ibtisam tace ai dole in dinga aiki, saboda in dunga motsa jiki

Najeeb yace Toh muje kiyi aikin mijinki

Janta yayi sukai toilet inda a cikin toilet daga mishi wanka zance ya canza, domin najeeb yayi kewa dama nan ya fara shafata har yanzu nonon yana zafi Sosai in an taba

Ganin haka ya barta tare da fara aiki, inda yake fucking d’inta a tsaye, ganin cikin na takura mishi ya kamota sukai waje inda suka nufi gado, wannan karan dai babu style tunda ciki ya kwafsa ma najeeb, butterfly akayi, ya d’aga kafarta d’aya ya fara fucking d’inta ta haka akai sex din har aka Gama  tana nishi dakyar domin cikin yayi tsini……  And Mata da yawa basa son sex in ciki ya fara girma, kuma a lokacin za kuga maza nada nacin son yin sex din

Ibtisam soyayya suke ita da najeeb Sosai, tana k’okarin daurewa wajan taga da biya mishi bukata

Satinta d’aya a kasar kullum sai Sun fita yawo Sosai

Yau sun dawo daga wani super market a gajiye, inda ibtisam kai tsaye tayi cikin dak’i domin tayi wanka ta samu ta huta

Tana cikin toilet NAJEEB ya bud’e ya shigo tare da rungumota shima ruwan ya fara jikashi sosai

Ibtisam dariya ta farayi Sosai Lokaci d’aya ya d’agota yana kallon fuskanta alaman Mai takema dariya haka?

Ido ta lumshe tana dan sakin murmushi lokaci d’aya ya girgiza Kai tare da shafa mata cikinta, lokaci d’aya kuma ya saka bakinshi cikin Nata inda ya fara kissing d’inta Sosai yana tsotsan mata baki

Ganin tana son d’auke wuta yasa ya barta tare da fita ya tube kayan jikinsa daya ji’ke

Ita kam murmushi tayi dan tasan ya barta ne dan yasan bata bukatar komai yanzu sai bacci

Satin ibtisam Biyu ta koma, kuma a lokacin ta shiga cikin watan haiyuwarta

Gidan Mum ta sauka koda ta dawo dama a nan take, domin in sunyi hutu gidan mum take sauka Indai najeeb baya nan

Wata ranan juma’a da safe ibtisam ta tashi da na’kuda Sosai, inda akai hspt da ita, wani abun mamaki cikin bai cika wata tara ba akace haiyuwa ne, dama yana haka, wasu wata 8 suna haiyuwa amma ita ibtisam ya wuce 8mnt tama kusa shiga 9mnt din

Mum bata kira najeeb ba, domin tasan inta fada mishi yanzu zai dame su, haka ta kwabi Zarah akan karta fad’a mishi sai ibtisam din ta haiyu, itama Zarah tana da k’aramin cikinta

Cikin ikon Allah da na’kuda da haiyuwar bata wuce awa biyu ba inda ta sintibo y’arta mace santaleliyar kyakyawa

Koda su Mum suka shiga suka ga yarinyar kamanta d’aya da najeeb harta farinshi  yarinyar kyakyaway

Nan take zarah ta doka Mai kira tana fad’in congratulations an samu baby girl

Najeeb na zaune ya tashi da sauri tare da fad’in yaushe ta haiyu babu wanda ya kirani??

Zarah tace yanzu ta haiyu nan take yace a bama ibtisam wayar suyi magana

Inda aka mi’ka mata, ita kuma zarah sai faman d’aukan hotan baby takeyi, domin ta tura ma najeeb yaga Mai Kama dashi

Najeeb yace baby sannu, ya jikin naki…  Yana maganan ne cikin tausayawa

Ibtisam tace lfya kalau Alhmdlh

Shigowan Dr ne yasa tace Tana zuwa…

Nan Dr ya fara tambayanta babu wani damuwa koh??

Ibtisam tace eh, da yake asibitin Indai ka haiyu saika kwanta dole

Zarah ta tura ma najeeb hotuna

Inda ta kirashi bai d’auka ba, dan haka ta barshi.

Labarin haiyuwar ibtisam ya baza ko ina

Itama ibtisam da taji shuru bai kira ba, ta kirashi taji a kashe

Mum da taga alaman ibtisam kaman babu wata matsala tace Dr ya Bari su koma Gida, da Farko yake a’a da an barta daga baya kuma saiya yarda domin yaga babu wani matsala inda suka koma gidan Mum

Su Zarah na zaune wajan magrib Dr jibril yazo inda yaga baby yama ibtisam murna sannan suka wuce

Ibtisam na zaune tana kallon yarinyar sai hawaye ba kowa ta tuna ba sai granny wacce taci burin ganin y’ay’ansu, Allah sarki Allah baya barin wani dan wani, ido ta lumshe tana hawaye Sosai yarinyar Nata kuka amma bata sani ba, ta tsunduma cikin tunani, da yanzu Granny ce zata mata wankan jego dan bazata yarda wani ya mata ba….

Ji tayi an tabo ta tayi firgit tare da bud’e ido wanda ya sauka akan fuskan najeeb

Da sauri ta k’ara bud’e idonta

Lokaci d’aya kuma ta kalli yarinyar dake hannunshi wacce ya ri’ke yana jijjigata

Mi’ka mata yarinyar yayi tare da fad’in ki bata nono, kina ji tana kuka amma kin barta

Ibtisam amsan yarinyar tayi tare da k’okarin saka mata nonon a baki cikin jin kunya

Najeeb ganin haka yayi murmushi tare da fad’in kunya na akeji yau??

Ibtisam ta kalleshi tare da fad’in shine ka kashe waya a…..

Yace Toh ba gani nazo ba, sai a fad’amin abunda ake  son fad’a inji

Baki ta turo

Matsawa yayi kusa da ita tare da k’ura ma yarinyar ido cikin so da k’auna, sannan ya kalli ibtisam yace thanks

Itama kallonshi tayi tare da fad’in thanks for what??

Tashi yayi ya rungumota ta baya tare da fad’in thanks for everything

Tare da fad’in an samu Granny k’arama, sannan namesake d’inki

Kinga ni kuma Na samu my love my baby kuma

Ibtisam hawaye ya fara zuba

Najeeb yace Oh oh sai yasa da naga kina kuka bance damme ba, saboda ban son kukan, and now gashi kin fara

Ibtisam tace kawai Ina tuna granny ne, lallai ina matukar godiya da kasa ma wannan yarinyar sunan Granny

Najeeb yace addu’a za muyi tayi Mata, lallai Granny ta hango alkairi a wannan auren namu, kallon ibtisam yayi tare da fad’in na tabbata saboda rasuwan granny kika yarda dani

Murmushi ta saki lokaci d’aya, inda najeeb ya fara tuna mata irin rigiman da sukayi baya, ibtisam dariya tai tayi,….

Inda tace bazan taba manta ranan daka karya ni ba,….

Yace ni?? Tare da zaro ido..

Tace eh ta bashi labari

Najeeb kamota yayi tare da fad’in am so sorry ban taba sani ba, kai rayuwa kenan….

Najeeb gaba d’aya ko ina ibtisam take yana manne da ita baya Bari tayi nesa dashi, inda yayi musu siyayya na ban mamaki, ita da baby d’inta

Ummi da Farko ta’ki zuwa, saida najeeb yaje shida kanshi ya tawo da ita, domin yaga yanda Matar tashi ta damu

Ganin ummi yasa ibtisam taji dad’i

Ranan suna an kashe naira inda akama yarinya da suna Amina, duka iyayensu sunji dad’in wannan Sunan, suna kiran baby da Afnan…..

Harda su Aisha sunzo da kubra da hauwa

Ummi kwana sati d’aya tayi ta tafi itama








*BAYAN SHEKARA UKU*

wata matashiya na gani cikin wata jallabiya inda na ganta a kofar airport ita da yara guda biyu tana ri’ke da hannunsu, kai tsaye taxi suka shiga inda suka tsaya a wani kofar katon gida suka fito da akwatunan su masu aikin Gidan suka kwashe Mata kayan sukai mata ciki dashi, yaran nan biyu mace dana miji suna manne da ita…. 

Kai tsaye cikin gidan ta shiga wanda ta tsaya turus ganin abun mamaki fuskan da bazata taba mantawa dashi ba a rayuwarta Najwa itace a cikin falon tana shan giya sai yanzu na gane ashe ibtisam ce, domin ta k’ara girma da cika tare da gogewa

Ibtisam kallon Najwa takeyi wacce take ta faman fadin najeeb nayi maka black magic amma baiyi ba, ance in nazo inda kake zaka so ni, nazo shine…..

Saita fad’i k’asa luuuuuuu ibtisam kallon najeeb tayi dake tsaye yana kallonta

Wani irin hawaye Mai zafi ya fara fitan mata, lokaci d’aya tayi waje da gudu bata bi kota kan yaranta ba

Najeeb ganin haka yasa ya rufa mata baya amma ko Kafin Ya k’arasa ta shiga taxi tana kuka anyi gaba da ita

Dole ya dawo gidan saboda yaran da kuma Najwa dake kwance gidan yasa a fitar da ita

Yaran kuka ya tarar sunayi saboda iyayensu Sun fita Sun barsu

D’aukansu yayi tare da rungumesu

Najeeb wani irin Abu yakeji cikin ranshi Mai yasa ibtisam zata tafi ba tare data mishi uzuri ba

D’aukan yaran yayi wanda suka bar gidan domin ya nufi airport dan yasan zata iya nufa can, koda yaje haka yaita dubawa bata nan, gashi ya kira layinta baya zuwa dan yasan tunda yanzu ta dawo k’asar daga Nigeria bata saka layinta na America ba

Najeeb gaba d’aya kanshi ji yayi yana juya mai, lallai yana mutuwar son ibtisam gaba d’aya ya yarda itace rayuwarshi domin bazai iya rayuwa babu ita ba, yanzu abunda yafi damunshi wani hali zata saka kanta, amma inda ta tsaya ta saurareshi data tabbatar baida laifi domin tunda yasan hukuncin mai shan giya da mazinaci ya daina ya tuba duk ya Bari dama rashin sani ne da kuma duhu, wanda har yanzu yana neman ilimi Sosai

Ibtisam kam gaba d’aya tama rasa wajan zuwa, na farko yaranta wanda ta bari a can, na biyu najeeb data Bari da Najwa, duk da taso ta cireshi cikin ranta domin tana tunanin mai yasa yabar Najwa din ta shigo…

Lokaci d’aya kuma ta Fara tunanin keda kika tafi in sukayi wani abu fah??  Da sauri ta girgiza kai tare da fad’in no najeeb bazaici amana ta ba, tunawa da tayi kwalban giya ne hannun Najwa tace ma Mai taxi din ya Mai data inda ya d’auko ta

Kai tsaye gidan suka nufa tare da tsoran kar NAJEEB yasha giya

Suna isa ta shiga gidan da sauri a falo ta ganshi yaran har sunyi Bacci..

Da sauri ya tashi ya nufeta tare da rungumeta yana fad’in ibtisam kin San I can’t live without you, shine kike k’okarin tafiya ki barni, Bayan kin San you are my life…

Yace ibtisam da nayi zina saboda banda ilimin addini, nasha giya saboda banda ilimin addini, wlh tunda Nasan babu kyau na daina tare da tuba, ban taba cin amanarki ba……

Nan ya fara bata Labarin yanda akayi har Najwa tazo

Yace zuwa tayi tare dayin nocking na bud’e tayi hugging dina, ni mamaki ma nai tayi yanda ta gane gidan nan, domin wancan ta sani

Da sauri na tureta ganin haka yasa tace itace fah, ko Banyi farin ciki da zuwanta bane

Nace tabar gidan nan kafin in fitar da ita, tana k’okarin tabani na dakatar da ita, shine ta Fara kuka tana bani hakuri shima dai nace ta fita

Bud’e jakarta tayi ta d’auko kwalban giya ta Fara sha, shine take fad’in taje anyi asiri ance zan nemeta shuru, shine taje wajan wani yace in tazo za……

Ibtisam toshe ma najeeb baki tayi tare da fad’in ka daina fad’amin na yarda dakai, I trust you

Najeeb K’ara matseta yayi a jikinshi tare da fad’in I love you so much my Dr

Dariya tayi inda sukai ciki

Ibtisam ta kammala karatun ta inda ta zama cikakkiyar Dr, yaranta Biyu Amina afnan, sai Najeeb wanda suke kira da Anan inda iyayensu suke fad’in Granny da mijinta Sun dawo 

Najeeb ya hana ibtisam aiki, domin ta dawo wajanshi da zama a America, amma ya gina mata hspt a Nigeria

Ita kam zarah yaranta uku, Umar faruk, Amina suma Sun saka sunan Granny, sai mai Sunan Mum

Zarah ta zama cikakkiyar barrister
Inda take aiki a federal high court dake abuja

Aisha ta samu wani tsoho Mai mata biyu ta aura, inda take zaman hakuri domin da Farko k’arya yayi mata ya nuna mata shi wani babba ne, ashe ba wani mai arziki bane, sai mak’o tunda ta shigo amma a waje yana mata, kuma tana tunanin raba auren mahaifinta yace inta fito bai yafe mata ba, amma still bata jiba, ganin haka mutumin yasa aka kafe mishi ita…..  Hmm rayuwa garin Kwadayi an fad’a halaka,ga Aisha ana zaune gidan Mai mata ana girki a murhu, ke sai Mai kud’i gashi kin aura dan k’arya, a kullum ana son bawa Ya dinga neman zabi na alkairi, bawai kai kace sai wane kaza ba

Hauwa ita kuma sunje wani part aka watsa mata acid, domin ta Fara soyayya da mijin wata y’ar maiduguri inda tasa aka mata bincike akan hauwa, Aiko ta turo aka watsa mata acid amma an Kama yaran inda suka fad’i gaskiya aka Kama matar, mijin ganin haka ya saki matar tare da barin hauwa din, kwata kwata bata fi wata uku ba da faruwan haka Allah ya d’auki rayuwarta.. Innalillahi’wa inna ilaihirajiun. A kullum ana so bawa ya aikata alkhairi domin baka san yanda karshenka zai kasance ba….  Sai dai shi Allah mai gafara ne ga bayinsa Allah yasa mu dace


Najeeb da ibtisam da yaranta Sun tafi Dubai wajan Ahmad inda yake karatu a can sukai sati d’aya sannan suka dawo America

Najeeb tunda yasa aka fitar da Najwa bata K’ara zuwa ba, domin tasan yafi karfinta yanzu

Ibtisam na kitchen saiga najeeb yazo ya rungumota ta baya yana fad’in baby nabar aiki zamu koma Nigeria domin yarana suyi karatun addini Sosai…..

Ibtisam tace amma AI suna zuwa islamiya a nan

Najeeb yace nafi son can, ban son su taso a wannan k’asar irin yanda nayi, domin mutum saiya dinga d’aukan irin halinsu abun dai sai wanda Allah ya kare

Ibtisam ban son a kuma Mai maita abunda ya faru baya domin yanzu na gane ilimin addini shine ginshikin rayuwa bana boko ba, ki duba koda mutum baiyi boko ba in yana da ilimin addini zaki ganshi a Waye, amma in akwai bokon babu na addini sai kiga mutum yana Abu kaman gabo shi yana ganin ya Waye sai yayi ta shirme

Ibtisam tace hakane kam

Najeeb yace gani ga wane ya isa wane tsoran Allah,…..

Muje mu fara shiri sannan a bani hakki na… 

Dariya tayi tare da fad’in girkin fah??

Yace a kashe I need you tare dakai hannunshi ya kashe gas din ya d’auketa cak sukai bedroom d’inshi inda take dariya…….. Toh najeeb yace d’aukan rahoton ya isa haka……

*ALHAMDULLILHAH…..*

Anan na Kawo karshen Labarin najeeb Ina fatan kuyi amfani da sa’kon dake cikin wannan labarin sai mun had’u cikin littafi na Mai suna…… *IN BAKI DA GASHIN WACCE(SLAY QUEEN)*

IN BAKI DA GASHIN WACCE….. Labari ne akan yanda duniya ta lalace, yanda Mata da maza matan aure mazan aure suke buga bariki……  Labari ne daya kunshi abubuwa da dama irin musamman yanda ake bariki saboda abun duniya…… Karki Bari a baki labari……


Wanda ta karanta wannan labarin bata biya ba, keda Allah kuma wlh Ina binki bashi, is better kizo ki Biyani, masu raina Abun kuna ganin kaman ba komai bane karki manta Allah ba azzalumin kowa bane….  Duk da banga laifinku ba, wanda suka siya da suke baku Bayan sunyi alkawari kuda Allah…….

NAJEEB YAKARE
MUNA FATAN ZAKU BAMU TUKYUICIN

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


Related Articles

Leave a Reply

Back to top button