NAJEEB 6

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Tsaki ibtisam tayi tare da fad’in dan Allah ki kyaleni inhuta.
Ibtisam dariya tayi tare da fad’in, Allah ya kyauta, itama zama tayi akan gadon d’akin Tana buga game a wayarta.
Kaman yanda Kabir yace wajan 7:30 sai gashi ya kira ibti yace mata yana waje,.
Kallon Zarah tayi tace kabir yazo, yana waje taya zan fita?
Zarah tace muje in rakaki sai in jiraki a bukka inkun Gama saimu shigo tare, ko kuma kice ya shigo mana.
Ido ibtisam ta zare tare da fad’in Rufamin asiri, so kike uncle ya ganni yace ban son karatu, Kome? Salan kisa yace aure nake so, nidai muje saiki jirani a bukka din in fita in sameshi, hakan zaifi
Zarah tace toh muje.
Har waje Zarah ta rakata suka gaisa da Kabir, har suna yar wasa da dariya kaman Sun san juna, komawa tayi ibtisam ta shiga gaban motar kabir.
Kallonta yayi Wanda ta canza kaya Kafin ta fito, wata doguwar rigan atamfa ne, saita yane kanta da wani karamin Gyale, ba karamin kyau tayi ba, duk da fuskanta babu make up, dama ita ba ma’abociyar yin kwalliya bace, yace ibti Anya zan iya jira shekara hud’u kuwa? Karfa wani yamin kwace
Murmushi tayi tare da fad’in ai kaman yanzu ne, shekara hud’un tayi, sannan kamin kyakyawan zato
Yace hakane, kaman yanzu ne, so ya Abuja din? Ashe kina da y’an uwa a nan?
Tace lafiya kalau Alhmdlh, eh uncle d’ina ne
Yace toh nidai na fad’ama ibti koni wanene amma ita ta’ki fad’amin
Murmushi tayi tare da fad’in mai kake son sani a tare dani?
Yace komai, inason sanin komai akan matata dazan aura insha Allah
Murmushi tayi cikin jin kunya, sannan ta Fara fad’a mishi ko ita wacece, tace toh kaji komai yanzu
Yace eh naji komai, ina Ahmad din bros dinmu?
Tace sai Friday yake dawowa gida, boarding school yake, duk da skul din akwai day, yace yafi son boarding din, so duk Friday yake dawowa, saiya koma Sunday, in anyi hutu kuma sai yazo Kano
Kabir yace Allah ya taimaka, ta amsa da Ameen.
Kiran sallah isha’i da akeyi yasa Kabir fad’in Bari in shiga masallaci, da yake akwai masallaci a jikin gidan wanda Dad yasa ayi, itama tace ok bari in shiga gida nima inyi sallah.
Fita tayi tana k’okarin yin nocking aka bud’e gate din, ido biyu sukayi dashi, gabanta taji ya fad’i, shiko kawar da kanshi yayi tare da wucewa masallaci, bayan yaja kofar ta datse kuma yasan ciki zata shiga, tsaki taja tare da fad’in dan rainin wayau, nocking tayi aka bud’e Mata kofar sannan ta shiga, a bukka ta samu zarah Tana sallah, itama alwala tayi a famfo din dake gefe ta cikin ciyayi, bayan zarah ta idar ta amshi hijab din Zarah tayi sallah, Bayan ta idar Zarah tace ya tafi ne?
Ibtisam tace a’ah yana masallaci, yan….. K’aran wayanta yasa bata k’arasa maganan da take son yi ba ta d’auka ganin kabir ne, sawa a kunne tayi ban San mai yace mata ba, naji tace ganinan
Tace ma zarah bari inje in ganshi yace In fito yanzu zai wuce ma
Koda ta fita a tsaye ta ganshi a jikin motarshi, hannunshi ri’ke da Leda, murmushi ya sakar mata tare da fad’in ibti Mai yasa koda yaushe inna kalleki sai inga kin k’ara kyau ne, miye sirrin
Murmushi tayi tare da fad’in babu wani sirri, kawai idonka ne yake ganin maka haka
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Yace Kai Anya kuwa? Ni Inda idonane da nafi kowa murna, dan ban son kowa yaga min kyanki saini d’aya, mi’ka mata ledan hannunshi yayi tare da fad’in zan gudu ana son ganina, sai munyi waya.
Tace gskya wannan kyautar da kayi hakuri ka barshi, inaga kaman yayi yawa.
Yace karki manta shaidan shike maida hannun kyauta baya, kuma in banyi ma matar da zan aura abuba wa zamma? Very soon Indai na turo komai ni zan dinga miki dan bazan bari Abba yaci gaba ba.
Uhm kawai tace tare da fad’in ngd, yace ko kefa, sai munyi magana, koda yake muje in rakaki, har kofar gidan suka jera dai dai lokacin NAJEEB yazo shiga gida, ganin yanda suke ma juna dariya abun ya bashi haushi yaja tsaki tare da shigewa gida tunda an bud’e kofar, itama shiga tayi tana fad’in sai anjima.
NAJEEB kam haushi Kabir ya bashi, ya rasa wanda zaiso sai wannan karamar yarinyar mara kunya da bata gaida mutane, hhhhh kunji najeeb fah, wai bata gaida mutane, ya tsaya yana mata dariya, y’ar 15yr ko 12 zance ma, tsaki ya kuma ja, tare da fad’in wasu mazan basu da tunani mutum ya tsaya yana soyayya yana bata ma kanshi lokaci dama Kananan yara ba babban mace ba, yaushe har tayi girman data iya magana da maza, lokaci d’aya ya d’aga kafada tare da fad’in miye nawa a ciki ma
Ibtisam bukka ta nufa inda taga zarah na zaune tana game a wayarta, Zarah ganin leda a hannun ibtisam yasa ta amsa tare da fad’in Bari muga maiya Kawo, tare da bud’e ledan, chocolate ne sai kwalin waya Samsung, Zarah tace inye kin fito gari za’a fara chatting
Ibtisam tace uhm, ai baki Sani ba Abba ne baya son in ri’ke babban waya, yanzu wannan ma ban San yanda zanyi dashi ba Wlh, ko in maida Mai kawai
Zarah tace Kai yanzu saiki maida Mai? Lallai dako kin cika mara wayau, ki boye kawai, balle yanzu nasan dole Abba zai yarda ki ri’ke babban waya, saboda makaranta su browsing da sauransu.
Tashi sukayi suka shiga ciki, inda suka tarar da NAJEEB a falo da Mum yana kallon ball, mum tace daka ina kuma haka?
Zarah tace Mum mun fita siyo abune, ibtisam tace sannu da hutawa Mum, tare da shigewa ciki, NAJEEB kam ko kallo basu isheshi ba, idonshi nakan tv, itama zarah ciki ta shige inda tace ma ibtisam tasa wayar a caji, suje suci abinci, ibtisam tace plz ki kawo mana nan, ki zuba mana, ban son fita na gaji, Zarah tace ok bari in Kawo mana.
Yau kwanan Granny uku da tafiya yola, kuma a yau tace zata dawo, tunda ta tafi sukan yi waya jefi jefi, domin inda Granny take babu network Sosai.
Ibtisam tunda ta had’u da NAJEEB sau d’aya basu k’ara had’uwa ba, ta fito sanye da hijab ya tsaya mata dai dai Giwa, ana ganin dogon wandon da tasa, NAJEEB na kwance akan kujeran falon yana danna waya daka duka alamu yana chatting ne, jin motsin mutum yasa yace a bashi ruwa ba tare daya d’ago ba, banza dashi tayi tare dayin gaba abunta, jin ba’a kulashi ba yasa ya d’ago ya ganta dai dai lokacin tana fita, ranshi yaji ya baci tare da fad’in I will teach her a lesson
Ibtisam samun Kabir tayi a waje, inda ta shiga cikin motarshi, sun dad’e suna fira yayin da NAJEEB yake ta kallonsu ta CCTV, ganin ta fito a motar yasa ya dawo falon ya zauna, koda ibtisam ta bud’e kofar falon a tsaye ta ganshi a gabanta, d’aga hannu yayi ya tsinka Mata Mari tare da fad’in karki k’ara a rayuwa, ke wacece da ina magana zaki wuce ba tare da kinyi abunda nace ba?
Hannunta dake kan fuskanta ta saitin wajan daya mareta, alaman taji zafin Marin, ta cire tana k’okarin marinshi shima.. Da sauri ya ri’ke hannun tare da murde mata shi ya juyo da ita ta baya, duka suka kalli gaba, yace baki da hankali koh? Ni zaki mara?
Wani irin nishi takeyi na wuya, tare da kokarin ta samu ta kwaci kanta dan murde mata hannun da yayi tana jin zafi Sosai, amma ta kasa Kwacen kanta domin karfin ba d’aya ba.
Yace how dare you, ni sa’anki ne? Ni zaki mara? Jin nishin da takeyi na wahala harda kwalla daya Fara zuban Mata duk da ta baya take yasan tana hawaye dan yaji alama yanda take nishi tare da shessheka ,yace inaso ki bani hakuri tare da alkawarin bazaki k’ara raina wani ba in ur lyf Kafin in sakeki
Ibtisam duk da tana jin zafin murde hannun da yayi mata, bata tunanin zata bashi hakuri domin bata ga abunda tayi mishi ba, dahar zai mareta, sannan yace ta bashi hakuri kuma, jin tayi shuru yasa ya k’ara murde hannun da karfi lokaci d’aya hannun yayi y’ar k’ara ‘Kas ta saki wani irin k’ara Mai sauti…….