NAJEEB 7

PAGE 7
Ganin haka yasa ya turata ta buge da jikin bango, tare da fita yabar falon.
Mum ta fito da sauri tana fad’in ibtisam fad’i kikayi Subhanallah, tare da nufanta tana k’okarin d’agota, hannun daya murde mata mum ta kamo da sauri ibtisam ta saki k’ara domin wani irin azaba taji da Mum ta ri’ke mata hannun ganin haka yasa mum tace badai kin buge a hannun ba?..
Ibtisam hawaye ke zuba a idonta Sosai, ga hannunta dake mata zafi, ga bacin rai lokaci d’aya taji kanta na Mata ciwo, tare da tsanan zaman gidan, ji tayi gaba d’aya Tana son komawa Kano gidan Abbanta, mum jikinta ta kama da d’agota, tare da fad’in sannu maiya samu hannun?
A hankali tace babu komai, na fad’i ne, Tana fad’in haka ta wuce ciki inda ta samu Zarah na kwance tana bacci, itama kwanciyan tayi hannunta yana zugi, gaba d’aya ji tayi kaman k’ashin hannunta ya fita dan taji ba yanda ta saba jin hannun ba, wani irin tsanan NAJEEB taji ta kar’ayi ninkin banin kin wanda take Mai, lallai a duniya bata da makiyi yanzu kaman shi, inda za’a tambayeta wata tsana a duniya? Toh lallai NAJEEB zata ce, kwanciya tayi tana hawaye da haka bacci barawo ya saceta
Sai wajan 6 ibtisam ta farka gaba d’aya ta kasa d’aga hannun da Najeeb ya murde mata, ga wani irin rad’adi da zafi da yake mata sosai, Lokaci d’aya tasa kuka saboda azaba.
Zarah ce ta shigo ta sameta tana kuka, cikin tashin hankali tace lafiya kuwa ibtisam kike kuka?
Ibtisam tace zarah hannu na ciwo yake min Sosai, na kasa d’agashi, zafi yake min
Da sauri Zarah ta nufeta tana fad’in tashi muje hspt maiya samu hannun? Kinji ciwo ne?
Kaita girgiza mata alaman a’ah, tare da tashi tace muje Aban magani zafi yake min Sosai tana shesshekar kuka, fita sukayi inda suka ga Mum a falo.
Ganin ibtisam na kuka Mum ta Fara tambaya lafiya kuwa?
Zarah tace Mum ta buge a Hannu ne.
Mum cikin tashin hankali tace badai faduwan da tayi d’azu bane? Maza kuzo muje asibiti, sannu ibtisam, fita sukayi inda suka shiga mota driver yaja ibtisam na hawaye, har asibiti suka nufa, inda suka nufi reception, receptionist suka fito da file dinsu tunda family card ne, nan suka shiga wajan Dr, inda ya fara fad’in mrs Abdullahi, Sannunku.
Dr kallon ibtisam dake hawaye yayi, yace lafiya kike hawaye? Maiya faru?
Mum tace hannun ke Mata ciwo, ta fad’i ne, nan Dr ya tashi ya ri’ke hannun wani irin k’ara ta saki, ya dad’e yana dan juya hannun sannan yace gocewan ‘kashi ne, Bari in kira Dr din kashi yanzu zai zo.
Ba’ayi ko 30mnt ba Dr din yazo bayan anyi gwaje gwaje inda aka fara gyara mata hannun, zo kuga kuka wajan ibtisam zarah kam gaba d’aya tausayin Itbtisam ya kamata harda kwalla, ita kam mum jikinta duk yayi sanyi cike da tausayin ibtisam din, sai take ji kaman a jikinta
Bayan Dr ya gama ya fara ce mata sorry dear, an gama.
Ibtisam kam tasha wuya idonta har yayi ja, dan azaba, an d’aure Mata hannun, wanda ana gamawa ta kwanta akan gadon wajan, babu komai cikin ranta sai tsanar NAJEEB wanda shine silan Jefata cikin wannan halin, ita ta rasa mai tamai ya tsaneta, tun Farko ta gaidashi yayi banza da ita, daka karshe ya zageta, toh miye laifinta danta kama kanta? Sannan miye na shiga sabganta har yace ta kawo mai ruwa bayan baya kulata, baya ganin darajanta, akan wani dalili zai aiketa? Lokaci d’aya ta sauke wani ajiyar zuciya tare da fad’in komai yayi min, danya ganni a gidansu ne, inda a gidanmu ne yaushe zai ganni, Bari Granny ta dawo gobe dole Zan koma Kano I….. Zarah da mum ne suka Katse Mata tunani da fad’in sannu ibtisam.
Ta kasa koda magana sai d’aga musu Kai da tayi.
Dr yace ibtisam dan yaji su mum sun kirata da Sunan, yace yanzu ya daina zafi, tunda Anyi miki alluran cire zafi, za’a baki magani, saiki kiyaye kar kiyi abunda hannun zai kuma gocewa Kinji?
Kaita d’aga mishi alaman toh
Mum ta kalli Dr tace zamu iya tafiya? Koya?..
Dr yace eh zaku iya tafiya, but tayi a hankali, zuwa jibi ku dawo sai muga hannun, kallon fuskan ibtisam yayi tare dayin murmushi yace ibtisam sai ayi tacin nama da yawa, a rage tsalle tsalle.
Ibtisam haushi Dr ya bata, waima a rage tsalle tsalle tunda ya maidata karamar yarinya ai dole yace haka.
Tashi sukayi suka fita inda zarah ta bud’ema ibtisam Mota ta shiga, sannan ta rufe, ita ta shiga gaba, mum baya, Bayan sun shiga driver yaja motar suka wuce
Koda suka isa Gida, Sun tarar da Granny da Mata har guda hud’u, ibtisam da hannu ke ciwo sakan baki tayi tana mamaki, domin kana ganin yaran Kaga y’an kauye futuk, d’aya harda yaro sai dai ibtisam tana tunanin Maman d’aya ce a cikin y’an matan, sai d’aya harda irin kalangun nan na Fulani, sauran biyun su basu da aibu sai dai sunyi yara da yawa, wanda zata ce basu wuce shekara Goma sha d’aya d’aya ba K…. Granny ce ta katse mata tunani tare da fad’in maiya sameki a hannu kuma?
Ibtisam jin haka yasa ta saki kuka, ta nufi Granny tana fad’in Granny faduwa nayi, mu tafi gida gobe
Granny tace garin yaya kika fad’i? Sannu Kinji Kai maiya samu hannun toh? Badai karaya bane?
Ibtisam cikin kuka tace gocewan k’ashi ne Granny
Su mum ko kallon matan da Granny ta Kawo ya hanata magana, tunani take badai suta kawo ma NAJEEB, ba ko waccen su tasha atamfa anyi d’inkin riga da zani, an cabe fuska da kwalli da janbaki, dinkunan yayi musu yawa, ita mai Yaron ma hannun rigan sai Zame mata yakeyi danya Mata yawa Sosai, ga falon gaba d’aya ya d’auki karni duk Kalan kamshin da yakeyi amma zuwan wannan ba’kin na granny yasa kamshin falon ya canza
Granny tace sannu takwarata maza jeki huta Kinji
Ibtisam tace toh Granny amma gobe zamu tafi koh?
Mum tace kina nan, har sai kin warke, sai sannan ibtisam tama tuna Ashe dasu mum take, sai taji kunya tare da fad’in kiyi hakuri mum wasa nake mata, ai nasan jibi zani ganin Dr
Mum tayi murmushi tare da fad’in hakane, kije ki huta Kinji, sannan ta kalli Granny tace sannu da dawowa mama, kunsha hanya.
Granny tace yauwa, hanya bakya, jikina duk yayi tsami, na gaji Sosai, ina wannan Yaron yake ne yazo ga mata nan ya zaba wacce tayi mishi
Zarah bata san sanda ta fashe da dariya ba, tare da fad’in Bari in dubashi, part d’inshi ta nufa amma bata ganshi ba, dan haka ta dawo ta shaida ma Granny da cewa baya nan, mum kam mamaki ne ya isheta, yanzu wa Innan ne NAJEEB zai aura? Lallai kam
Granny ta kalli mum tare da fad’in a basu masauki su huta, Kafin ya dawo.
Mum ta kalli zarah tare da fad’in kaisu gefen ba’ki, sannan kisa a basu abinci, Zarah tace toh tare da kallonsu tace muje, tashi sukayi suka bita inda takai su gefen ba’ki, sannan ta dawo Taba d’aya daka cikin masu aikin gidan umarni takai musu abinci suci.
Granny mi’ke k’afa tayi akan kujera, Tana zayyano ma mum bayani kaman haka, nasan cikinsu bazai rasa wacce zai zaba ba, ni Inda so samu nema ya auri Mai yaron, mijinta ya rasu ya barta da yaro dan shekara d’aya, gata marainiya, Abun dai gwanin tausayi, kin ganta duk ta tside saboda wuya, in miskili ya aureta Nasan zai ri’ke yaron tunda yana da hali, in kuma duka yake so shikenan saiya aure su, kallon zarah tayi da take ta dariya danta kasa boye dariyan ta.
Tace ku yanzu ba abun kunya bane, gid’a gid’a daku kuna gida babu aure, haba ai wannan abun yayi yawa wlh, yanzu dai Bari a d’aura ma miskili aure, ita takwara ta samu miji, ina fatan Kema kina da saurayi, in baki dashi sai in nemo miki
Zarah dariya ta saki har tanayin k’asa dan dariya, tace Granny Wlh na yafe zan zaba da kaina, dan inna baki zabi sa’an kakana zaki kawo min
Granny ta tamke fuska tare da fad’in, naga dai duk zaban da zakiyi bazai Kai wanda zan miki ba, jiba kyawawan matan dana zabo ma miskili, ku yanzu babu abunda kuka iya sai zaban maza masu shiga irin ta wa incan mutanan, bakwa zabo masu saka manyan kaya, Kema Fulani nake son ki aura yanda zaki dinga jin yaranki, ita ibtisam tana ji, tunda uwarta Fulani ce, Keko uwarki baji take ba Hhhhh Kai granny wannan maganan da takeyi duk a gaban mum takeyi
Zarah tace nikam ban son in iya wannan yaran, Kinga Bari inje in duba ibtisam inga ya take ciki, Granny itama tashi tayi tana fad’in muje Nima inga takwaran tawa, kai wannan Abu baiyi kyauba, Shigowan NAJEEB yasa Granny tsawaya.
Kallonta NAJEEB yayi tare da fad’in sannu Granny cikin gurbatarciyar hausan shi, dabai kware ba.
Granny tsaki taja tana fad’in shikenan abunda aka iya, sannu daka shi babu wani, ja’iri, ai yanzu na Kawo karshen Abun Wlh.
Najeeb kam ko kallonta bai kar’ayi yi, dan bajinta yake ba, sai dai yana d’an jin wasu kalma kad’an cikin magananta, wanda hakan ya nuna mishi cewa dashi take, dan haka k’okarin barin falon yayi tace Najeebu…. Tsayawa yayi ya tsana Tana kiranshi da wannan Sunan wai najibu, kaman wani d’an kauye, tsaki yaja tare da fad’in what Granny?
Tace kama uwarka tsaki gata a tsaye, mara kunya, kallon zarah tayi tace miye yake nufi da zat Hhhhh wai what shine zat, na daiji yace grandi, zat grandi Mai hakan ke nufi? Ko zagina yayi? Yanzu Inci uwashi
Zarah tace a’a cewa yayi miye Granny
Granny tace oho yanzu naji Batu, matsawa Granny tayi kusa dashi, wanda ya ri’ke kugu da hannunsa biyu alaman yana son ta fad’i abunda zata fad’a ya wuce, dan baya son takura irin Nata ko kad’an
Granny tace miye ka wani kama kugu? Ko dukana za kayi d’an banza, Toh Bari kaji tana mishi magana tana nuna mishi abunda take fad’a da hannu, tace aure za kayi wlh, ta rungume hannunta tare da nunashi tace Kai sannan ta k’ara rungume hannunta tace aure zakayi, na Kawo maka Mata guda hud’u ta nuna Mai da yatsa alaman, kallonta ya tsayayi sannan yace I think this old woman need to see a doctor, am sure she has mental problem.
Mum tace kana dakai kuwa, cikin harshen turanci
Granny kuka tasa Wai suna zaginta, tare da kamo zarah tana fad’in zoki fad’amin Mai sukace? Fad’amin inji.
Zarah tace Granny ba zaginka sukayi, ba, cewa yayi bai gane mai kike nufi ba, zai wuce, shine mum tace bashi da hankali taya kina mishi magana zaice zai wuce baki Gama ba.
Granny tace oho na gane, tare da cema Zarah jeki kiramin matan da nazo dasu.
Kallon Mum tayi tare da fad’in ki fad’ama wannan miskilin ya zauna, in sun fito ya zaba d’aya
Mum ta kalli NAJEEB tace ka zauna son, Granny zata maka magana.
Tsaki yayi tare da zama, yana fad’in wannan matar ta isheni Wlh.
Zarah ce ta fito da matan sun k’ara shafa ma fuskansu, kwalli da janbaki duk sunyi d’ige d’ige.
Najeeb dake zaune ta setin wajan, da sauri ya tashi yana fad’in wa innan wasu irin kazaman masu aiki kuka Kawo mum? Haba mum taya zaki kawo irin wannan yaran, plz ki sallamesu, Niko Abu suka taba bazan iyaci ba, kallon zarah yayi tare da fad’in plz tell them subar falon nan, sai wari sukeyi
Suko da bajin abunda yake fad’a sukeyi ba, duka sun saki baki suna kallonshi, domin fad’i suke Ashe bature ne, irin mamanshi, sai fari suke mishi da ido
Zarah tace bros wannan matan fah ba y’an aiki bane, Granny ta Kawo ne ka zabi d’aya ka aura.
Yace what? Wani irin kallo ya watsa ma Granny tare da fad’in you better tell them to leave, tun Kafin in illatasu tare da sakin tsaki yabar gidan ma gaba d’aya cikin bacin rai, Granny kam fadi take Ina zaka, ke Zarah kira mun dan banza.
Zarah tace Granny shifa yace ki fad’a musu su wuce tun Kafin ya illatasu
Granny tace au haka yace, zanyi maganinshi Wlh Bari audullahi yazo, wlh duka za’a d’aura mishi su zanyi maganin rashin kunya miskili mara mutunci. Kuyi manage plz na gaji sai gobe ko jibi kuma
MARYAM OBAM