NAJEEB 8

Granny barin falon tayi,bayan tace ma y’an matan su koma, ta nufi d’akin zarah inda ta iske ibtisam kwance tana baccin wahala, cikin tausayin ibtisam tace sannu Allah sarki dole kiyi bacci, gocewan k’ashi akwai azaba, targad’e mutum yayi yasha azaba, balle ace k’ashi ya goce
Zarah ta shigo d’akin Tana fad’in Granny bacci take amma kina damunta da surutu.
Granny tace Hmmm, wlh tausayi taban, gocewan k’ashi akwai azaba, Allah sarki takwara, Allah ya baki lafiya, k’aran wayan ibtisam yasa Granny tace wayar Waye haka? Duba ki gani karya tasheta k’aran, zarah d’auka tayi taga kabir, tace Granny kabir ne.
Granny tace Kabiru dan arziki d’auka kiban, dannawa Zarah tayi tare da mi’ka ma Granny, Granny tasa a kunne dai dai lokacin Kabir yana fad’in my ibti, da sauri Granny ta cire wayar a kunne tana son fad’in abunda yace mi ibt, lokaci d’aya kuma ta maida wayar a kunnenta tare da fad’in Kai Kabiru grandi ce.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Gaidata yayi tare da fad’in ya Abuja?
Granny tace habuja lafiya, kasan takwaran tawa ta samu gocewan k’ashi koh? Yanzu haka bacci takeyi
Yace Subhanallah, wlh ban sani ba, yaushe hakan ya faru? Dazu nazo na ganta fah?
Granny tace Kabiru a Ina ka ganta ita da take habuja, yace Granny Nima ai nazo Abuja din
Granny tace ah lallai soyayya, toh sai kazo ka dubata inta farka, yanzu dai tana bacci, yace insha Allah Zanzo inganta tare da kashe wayan, yana tunani, wani abokinshi dake kusa Mai suna Tahir yace kabir lafiya kuwa?
Yace Wlh ibti nace ta samu gocewan k’ashi, kuma dazu mun had’u, kai Wlh banji dad’i ba, ko kad’an ban son in ganta cikin damuwa, ina sonta da yawa
Tahir yayi murmushi tare da fad’in ina matsayin amininka, komai naka kana fad’amin amma shine baka fad’amin wannan ba, Allah ya bata lafiya
Kabir ya amsa da Ameen, tare da fad’in sorry Tahir naso sai Abu ya kankama Kafin in fad’a maka, domin kasan dagaske nake
Tahir yace Toh wannan wace yarinya ce haka da Abokina ya mutu a kanta? Gaskiya ko wacece tayi sa’a, toh amma irin halin da kake son mace dashi ita tana dashi?
Kabir yace Sosai kuwa, wannan shine dalilin da yasa na K’ara Sonta, sai dai abunda yake damuna, tana da burin tayi karatu, toh ni banda matsala, infact ma Ina son iyalina suyi karatu Mai zurfi, but matsalan shine ita ta’ki yarda muyi aure wai saita kammala karatu nan da shekara hud’u, ni kuma gashi an matsa min akan ya kamata in ajiye iyali, gashi wacce nake so tace sai nan da shekara hud’u, so ni Abun ma duk ya jagula min lissafi, gashi nace mata na amince data gama karatun, kuma gaskiya ban tunanin family d’ina zasu yarda Wlh.
Tahir dariya yayi sannan yace mutumi na an fad’a love, Niko in zaka dubiya tare zamu inje inga wannan yarinyar data tafi da Abokina, Toh amma Indai har Tana Sonka zata yarda kuyi auran, ai wannan ba hujja bace mace tace saita kammala karatu Kafin tayi aure, hakan bai kamata ba, aure ai baya hana karatu, sannan tace ka jirata shekara hud’u ai yayi yawa, sai kayi ta zama haka? Ni gashi inada yaro d’aya gana cikin na biyu amma kai har yanzu kuma Nima iyalin nawa na karatu, ya kamata ka mata bayani Sosai in Tana Sonka zata yarda.
Kabir yace sai dai in wakiltaka, dariya Tahir ya saki tare da fad’in ikon Allah, wato Kai bazaka iyaba, inko hakane zaka rasata Wlh, ko ince zata shigo Ata biyu, dan Nasan Wlh baza’a Bari ka K’ara shekara biyu babu iyali ba, balle har shekara hud’u haba is too much mutumina, kabir yace kai Abokina nifa bani da ra’ayin ajiye mace fiye da d’aya, ibti ta isheni kawai, nidai na wakilta ka, kayi Mata bayani kawai yanda zata fahimta.
Tahir dariya yayi sannan yace babu damuwa, yaushe zaka dubiya, sai muje danta sanni, inta warke daka baya mayi mata maganan, koya kace?..
Kabir yace hakan yayi, sai mu shiga zuwa anjima Bayan sallah isha’i. Tahir yace Toh Allah ya kaimu
Koda NAJEEB ya fita, wani store yaje yasai giyanshi, tare da tafiya dashi, yaje ya kama d’aki a hotel, domin ya sha abunsa, tunda yake bai taba shan giya a Nigeria ba sai yau, saboda duk abunshi yana taka tsan tsan, dan baya so ya batama iyayenshi rai, koya zubar musu da Kima, uhm Najeeb kenan, baka tunanin Allah, Allah yasa mu dace,.
Koda ya shiga bud’e kwalban yayi ya fara sha, domin granny tayi matukar bata mishi rai, wai kaman shi, Najeeb za’a ce ya zaba cikin wannan kazaman matan, ido ya lumshe yaci gaba da Kwan kwadar alcohol d’inshi, lokaci d’aya ya fara surutu ni NAJEEB ni that old woman zata ma haka, ta rasa wanda zata kawo min sai wa innan dako takalmi na bazan iya basu su goge min ba, zanyi maganin wannan tsohuwar Wlh, tunda nace mata ina son aure ai dole ta Kawo min wa innan tarkacen, koda nace ina son auren ni banda ido ne K… Shuru yayi lokaci d’aya kuma ya saki tsaki tare da fad’in Wlh ta raina ni that old woman, ci gaba yayi dashan alcohol d’inshi har saida ya shanye duka kwalban sannan yayi jiba dashi gaba d’aya wani bacin ran da yakeji saiya nemeshi ya rasa, baya iya tuna komai, toh taya Zaima tuna tunda a buge yake, k’okarin tashi yayi lokaci d’aya ya fad’i akan gadon bacci ya D’aukeshi
Zarah kallon Granny tayi wacce take ta cema ibtisam sannu, tace Granny Wai yanzu wa Innan matan Najeeb zai aura? Ibtisam dake zaune hannu na Mata azaba domin alluran da aka mata na cire zafi ya gama aiki, ta d’anja tsaki mara sauti domin jin an kira sunan Najeeb din.
Granny tace kwarai kuwa, duka zansa a aura Mai su, tunda shi Dan banza ne, inko kikaga bai auresu duka ba toh a ciki ya zaba d’aya ne, ni Wlh mai Yaron nake so ya aura, yaron tausayi yake ban, duk ya fige, Kinga ya murmure Idan miskili ya auri uwarsa, zasu tafi inane ma yake aiki k’asar masu jajayen fatan nan?
Zarah ta kwashe da dariya tare da fad’in America.
Granny tace yauwa Ameka.
Ba zarah ba harda ibtisam da hannu ke Mata zugi sai da tayi dariya
Zarah tace Kai granny America ba Ameka ba, kawai kice Turai in baki iya fad’a ba
Tsaki Granny taja tare da fad’in kince Ameka, maina fad’a ba dai dai ba Ameka
Zarah dariya harda sauka k’asa tace Wlh Granny bazaki kasheni da dariya ba, kallon ibtisam tayi tare da fad’in za kiyi wanka ne In taimaka miki?
Kaita d’aga alaman eh, toilet zarah ta nufa ta Tara Mata Ruwan zafi a bath sannan ta fito ta tayata ta tashi, har toilet takai ibtisam sannan ta fito ta barta dan tayi wankan, tunda tace zata iya
Wayar ibtisam ce tayi k’ara, Zarah ta d’auka ta Fara tsokanan Kabir tare da fad’in sai kira kake tayi, toh yanzu ta tashi amma tana wani uzuri kad’an, dariya kabir yayi tare da fad’in ya hannun nata? Zarah tace da sauki, yace Alhmdlh ina kofar gida nazo in ganta.
Zarah tace ok bari inzo in shigo dakai, tare da kashe wayan, ta kalli Granny tace kabir ne yazo, Granny tace maza jeki shigo dashi.
Zarah fita tayi inda taba security umarni dasu bud’e gate, bayan an bud’e kabir ya shigo, nan suka gaisa harda Tahir, falon ba’ki takaisu Kabir ya bata ledojin kayan fruit din daya siyo da yawa, ansa tayi tare da fad’in bari in kirata, koda zarah ta shiga saida ta bada umarnin akai musu Abun tabawa sannan ta nufi d’akinta, inda taga ibtisam tana cire hijab alaman ta idar da sallah, tace Aida kin maida Kabir yana jira
Granny tace maza kije Kinji, zarah rakata, zarah ta amsa da toh, tare da taimaka ma ibtisam tasa hijab din, sannan suka fita falon ba’kin, inda an ajiyema su kabir abun taba baki, amma basu ci komai ba
Kabir yana ganin Sun shigo ya tashi tsaye cikin tausayin ibtisam d’inshi, ya fara fad’in sannu ibti, ya hannun?
Murmushi tayi tare da fad’in Alhmdlh, zarah cikin wasa tace tunda ka ganta sai a zauna
Dariya yayi tare da zama, yana fad’in baki da dama, wai yaushe abun ya faru? Zarah tace dazu Wlh, yace Kai Allah ya kyauta. Shiko Tahir tunda ibtisam ta shigo ita da zarah, idonshi ke kan ibtisam din, lallai Allah yayi halitta, dole Kabir ya nace, gata ita ba faran mace ba chocolate colour, kala Mai tsada kenan, amma kallo d’aya zaka mata kaga madaran kyau lallai inda b…. Kabir ya katse mishi tunani da fad’in Tahir ga Ibtisam fah
Murmushi Tahir yayi tare da fad’in, Malama ibtisam ya hannun? Allah ya k’ara lafiya yasa kaffara ne
A hankali tace Ameen nagode, cikin muryanta Wanda ya dashe dan tasha kuka
Kabir yace ibti wannan shine Tahir, aminina, ko ince dan uwana, danya wuce amini a wajena.
Ibtisam murmushi tayi tare da kallon Tahir Wanda idonshi na kanta tace sannu da zuwa.
Nan dai sukayi fira harda zarah, inda ibtisam duk ta gaji da irin kallon da Tahir yake mata, bini bini daka ta d’aga idonta sai su had’a ido, sai ta kauda kai, gashi tana ta setin shi, kaman Kabir yasan ta gaji da zaman ya tashi tare da fad’in za muyi magana Allah ya k’ara sauk’i, ya kalli zarah yace plz ki dinga kulan min da ita Sosai Kinji?
Zarah tace insha Allah, amma fah sai an Biyani, gaskiya
Dariya kabir yayi yace ki fad’i farashi Mai tsada in biyaki, domin my ibti komai nata Mai tsada ne, duka dariya suka sa, sannan sukai musu sallama suka wuce ba tare da sunci abunda aka kawo musu ba.
Zarah da ibtisam cikin gida suka shiga inda suka ga Dad da mum da Granny zaune akan dinning, Granny na fad’in na kawo mishi Mata har guda hud’u amma dan banzan yaron nan baka ga Rashin mutuncin da yayi min ba, toh yanzu na yanke koya auresu duka koya zabi d’aya, inko ya’ki zaba toh Wlh cikin satin nan za’a aura mishi dukansu, tunda su auransu ba irin na y’an bariki bane, babu tsada
Dad yace kiyi hakuri mama, zai zaba, ina Najeeb dinma?
Granny tace tunda yamin rashin mutunci ya fita, bai dawo ba har yanzu
Su zarah da ibtisam sannu da dawowa sukai ma Dad, inda ya kalli ibtisam yace ya hannun naki?
Tace da sauk’i Alhmdlh
Dad yace sannu mamana Allah ya k’ara sauki. Ta amsa da Ameen , mum tace kuzo kuci abinci, zama sukai akan dinning din inda zarah ta Fara zuba ma ibtisam.
Dad yana ta kiran wayan Najeeb bai d’aga ba, yace Wai ina ya shiga haka ne, sai kira nake ya’ki d’agawa
Granny tace taya zai d’aga, bayan ya gama zuba min rashin mutunci, wlh inaga aljanace ta aureshi, yaro kwata kwata baya son aure, inaga Wlh a d’aura Mai duka hud’un zaifi
Dad yace Indai sun Mai AI babu matsala saiya auresu duka.
Granny tace Aiko basuyi Mai ba, saiya auresu tunda shi ya kasa kawo wacce yake so, yanzu ni na zabo mishi, a ciki harda wani Wanda mijinta ya rasu ya barta da d’a d’aya, ni Wlh tausayi take bani, Niko bai zabeta ba inaso inna isa kasa ya aureta saboda Yaron Nata, ta k’arasa maganan cikin tausayi
Dad yace Mai yaro kuma? Toh fah sai kuma yayi shuru yana nanata maganan cikin ranshi, lokaci d’aya ya cire tunanin tare da fad’in Bari Najeeb din yazo saiya zaba, inya d’auketa Mai yaron Kinga shikenan, in kuma bai had’a da itaba sai mu bashi ita mu
Ibtisam kam cikin ranta dad’i takeji, dan d’azu taga matan da Granny ta Kawo, kuma tasan sune, wani irin murmushi takeyi na mugunta, taso sanda aka nuna ma Najeeb matan ace tana nan taga yanda zaiyi, amma ba komai zanyi ta zuga Granny Wlh, a aura Mai y’an kauye mugu kawai, saiya kashe kanshi karshen miskilanci da mugunta…
gskya zan daina typing kullum saboda rashin sharhi, nifa bana bukatar godiya a’a sharhi nakeso inga kuna min, ta yanda zan gane kuna fahimtan sa’ko na ko a’ah, wlh saboda rashin sharhi gaba d’aya bana jin dad’in typing din, daka na Fara sai inji na gaji, amma in kuna sharhi Zan gane kuna fahimta
Pls masu samun sticker a whatsapp in Nayi posting ku daina, wlh da kisa min sticker gwara ki karanta baki cemin komai ba yafi min dad’i, indai kin San zaki dinga samun sticker ki ri’ke sticker d’inki bana so
facebook kuma ina bukatan sharhi ba thanks ba, wasu ko thanks dinma basa iya karasawa sai dai susa maka T, haba for god sake taya writers za suji dad’in muku posting kullum kaman yanda kuke bu’kata, gskya in bakwa sharhi zan daina posting kullum sai naga dama zanyi, tunda comment din da baifi 30 second ba inya dad’e minti d’aya ya gagara taya nida nake zama wajan awa biyu uku Ina typing sannan inji dad’in muku posting kullum, kunga hakan bazai yihu ba, duk da Nasan akwai masuyi Sosai so Ina magana akan masu samun thanks ko T, plz ku gyara
MARYAM OBAM