Ibtisam hawaye kawai takeyi, Ita ba komai bane yake damunta sai dai kar ace tana dauke da ciki, cikin kuma na NAJEEB, wani irin kuka mai sauti ta Saki Wanda bata san tanayi ba Najeeb wani irin kallon tsana ya mata tare da juyar da kanshi gefe, yana fatan kar Allah yasa abunda yake zargi ya tabbata Kallon driver yayi cikin zafin rai tare da fad'in I said you should drive fast, kana tafiya a hankali Driver k'ara ma motar gudu yayi na fitan hankali, gashi yana gudu amma shi ogan nashi baya ganin saurinshi Wanda shi driver din a tunanin shi ibtisam ce bata jin dad'i, shi yasa yake son suje asibitin da sauri musamman daya jita tana kuka Koda suka k'arasa wani asibiti private hospital ne wanda Kai tsaye Najeeb na fita ya fito tare da jan hannunta sukai ciki, kai tsaye reception suka nufa inda suka bud'e Kati a receptionist, Kai tsaye aka sadasu da Dr Koda suka shiga najeeb yace ma dr din yana son Ayi mata test.... ibtisam tayi sauri ta Katseshi tare da fad'in Dr plz kamun da sauri ina bukatar sanin Mai yake damuna cikin kuka take maganan Dr yace maike damunki? Najeeb yace Dr pregnancy test zaka mata right now, infact ma kawai ka mata scanning Dr yace OK tare da fad'in ibtisam ta tashi bayan ya kira nurse yace ta rakata wajan scan Bayan yayi rubutu a wata paper ya bata Najeeb na nan zaune ibtisam suka fita, jim kad'an sai gasu sun dawo, tashi NAJEEB yayi yana fad'in mai result ya nuna??? Nurse tace sai kun jira, bada dad'ewa za'a baku ba Dr Ya cabe da fad'in wannan ne first samun cikin madam right? Najeeb shuru yayi itama ibtisam shuru kawai tayi tare da fargaban Kar Allah yasa ciki gareta, domin idan shine lallai ta cutu, shikenan NAJEEB yayi Nasara akanta, shikenan karatu na, burina ya tafi kenan a Banza Bud'e kofar akayi aka shigo inda nurse dince cikin Fara'a ta mi'ka ma Dr result din.. Amsa Dr yayi inda ya fara dubawa, lokaci d'aya yace congratulations matarka Nada cikin sati tara..... Zumbur NAJEEB ya tashi tare da fad'in what 9week how many months kenan?? Dr yace wata biyu da sati d'aya, an Tana bukatar hutu, infact ma kar kayi sex da ita na sati b..... Najeeb yace ya isa plz dr Ibtisam kam sumar zaune tayi tana nanata Kalman cikin zuciyarta, congratulations matarka tana da cikin sati 9..... Lokaci d'aya ta saki ihu tare da fashewa da kuka tana fad'in Dr plz a zubar min da wannan cikin plz Wlh ban shirya haiyuwa ba yanzu.... Najeeb wani irin kallon tsana ya mata wanda idonshi ya kad'e yayi ja, gaba d'aya baya gane komai, wani irin abune ya tokare mishi a kirji Jan hannunta yayi ya figeta suka fita, direct Mota ya shigar da ita inda ya kalli driver yace muje hotel Koda suka k'arasa hotel din bama driver din key din d'akin yayi tare da fad'in Jeka kwaso komai nawa dake d'akin kazo mu wuce kano ibtisam da sauri ta kalleshi tare da fad'in ka barni in tafi wlh zubar da cikin nan zanyi domin Wlh bazan bari in ha...... Wani irin gigitaccen Mari ya sakar mata wanda saida yasa taga stars tare da fad'in you better keep quiet, wannan cikin da kika kwaso dole sai kin haifeshi, wlh koda zaki mutu sai kin haifeshi Ibtisam da tasha Mari ga ciwon kai na yunwa dake damunta, shiru tayi tana ganin jiri jiri Driver ne ya dawo tare da masu aikin hotel din da suka tayashi kwaso kaya ciki harda wayan ibtisam da suka bashi ya watsa mata wayar Hanya suka kama inda NAJEEB yama Dad d'inshi message akan su kamo hanyar kano urgent plz shida Mum, yana tura mishi message din ya kashe wayar gaba d'aya domin a halin da yake baya jin zai iya d'aukar wayar kowa yanzu Driver hanya ya Kama, inda yake ta sharara gudu, ibtisam bata komai sai kuka, ita burinta Wannan cikin ya zube shine burinta Sun isa kano inda suka tarar su Dad na nan cikin tashin hankali, domin tunda Dad yaga message din NAJEEB gabanshi ya fad'i Wanda hakan yasa suka biya jirgi wannan shine yasa suka rigasu zuwa gidan Dad cikin damuwa yace NAJEEB maiya f.... Ganin ibtisam na kuka fuska a kumbure Dad yace Mamana maiya sameki??.. Ibtisam batai magana ba sai kuka granny tace ke maiya faru ne haka?? Najeeb yace Dad ciki gareta and kuma ba nawa bane Gaba d'aya salati suka saki cikin tashin hankali Granny tace Kai Mai ya faru ne Wai?? Mum ta kalli Granny ta fad'a mata abunda yace Granny tace na uban Waye inba naka ba? Shege a Kai ma yarinya budurwa amma kace tana da ciki ba naka ba?? Najeeb wani irin kallo yake watsa ma Granny domin yana jinta sai dai ba komai yake ganewa ba, and bazai iya maida Mata ba Dad yace Toh NAJEEB inba naka bane na Waye?? Yace Dad na saurayinta KABIR Ibtisam da sauri ta kalli NAJEEB cikin mamaki tare da nanata Kalman daya fad'a Abba shuru yayi amma ranshi gaba d'aya a bace yake da ibtisam kenan irin abunda ta aikata kenan, duk irin tarbiyan daya bata shine ta bama kabir kanta Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, lallai ibtisam ta cuceshi, yanzu abunda ta aikata kenan?? Dad yace mamana Kinji abunda mijinki ya fad'a cikin harshen turanci yake maganan domin kowa yaji, ciki Granny ce kawai bata ji. Ibtisam cikin kuka tace Wlh Dad nashi ne b..... Abba cikin zafin rai ya tashi yakai Mata Mari tare da fad'in k'arya za'a miki da kike fad'in cewa nashi ne? K'arya zai miki? Mutuniyar banza irin abun kunyar da zaki d'auko mun kenan?? Abba sarkewa yayi wanda ya fara tari da sauri ummi taje ta Kawo mishi Ruwa yasha yana sauke numfashi sama sama. Kowa dake d'akin sannu yake mishi, inda Dad yake fad'in mai yasa Zaka bugeta, komai fah a hankali ake tafiyar dashi Abba yace Wlh da akwai abunda yafi duka saina Mata, inda badan Kar in bata lahira na ba da wlh saina kasheta.. Granny tace wai miye kuke ta Yaren da bana ganewa?? Gashi naga harda duka, ku fad'amin maike faruwa inji Mum ta fad'ama Granny abunda ya faru Salati Granny ta saki tare da fad'in shi kabirun yayi mata ciki?? Sai kuma ta saki kuka Ibtisam dake kuka domin gaba d'aya ita Abun ya d'aure mata kai, ita bata da laifi kuma ciki na NAJEEB ne bana kabir ba, ita tsakaninta da NAJEEB shine kiss kawai shima sau d'aya..... Dad ne ya Katseta tare da fad'in mamana Kinji abunda mijinki yace??..... Ibtisam cikin kuka tace Wlh Dad cikinshi ne, wlh nashi ne bana kabir b.... Najeeb ya Katseta tare da fad'in keep quiet duk abunda zaki fad'a bazan amshi wannan cikin ba, domin bani nayi ba and Wlh bazanyi accepting ba, you must punish for it I..... Dad yace NAJEEB ka mana shuru banso in k'ara jin maganan ka, har sai na baka izini Najeeb yace Dad akan wani dalili zanyi shuru? Kana ji tana k'okarin had'ani da d'anta na shege Wanda bani Nayi ba, dad shekaran jiya kawai wani abu ya taba shiga tsakani na da ita tunda mukai aure.... Ibtisam cikin kuka tace Wlh ba sau d'aya bane, yafi..... Najeeb yace yaushe na taba kulaki?? Oh is all my fault nine naja ma kaina da har na yarda nayi wani abu dake, dole Kimin sharri inda Nasan haka kike da ban had'a jikina da wannan k'azamin jikin naki ba, crap....... Dad yace kai NAJEEB kana da hankali kuwa?? A gaban mu kake irin wannan maganan??? Najeeb yace Toh dad in Banyi ba, kana ji tana k'okarin turamin d'anta na shege da tayi, wlh Dad duk inda zamu je I will not accept this Bastard unborn child din Abba wani irin tukukin ba'kin ciki ya tsaya mishi a wuya, domin komai najeeb ya fad'a ibtisam taja, lallai koshi bazai yarda da dan wani ba a gidansa Ummi kam hawaye take tare da takaicin abunda y'arta ta jawo musu Dad ya kalli ibtisam yace ibtisam ki fad'amin ya akai kika aikata hakan? Mai yasa kika aikata hakan??.. Ibtisam tace Allah shine shaida na wlh ban taba aikata zina ba tunda nake, Nayi kokari na kame kaina daka fad'awa dattin zina, Dad Wlh na kame kaina har zuwa gidan miji..... Najeeb yace wani mijin?? Ina fatan badai niba Dad yace NAJEEB Idan ka k'ara magana wlh saina saba maka Shuru yayi yana tsaki k'asa k'asa alaman nifa bazanyi shuru a cuceni ba Dad ya kalli ibtisam tare da fad'in ina ji ibtisam Tace Dad lokacin da kuka kaini America Bayan kun tafi NAJEEB yayi min wannan Abun...... Kuka yaci karfinta Sosai alaman tana jin nauyin abunda zata fad'a Dad yace ibtisam muna sauraranki Ibtisam kuka take Sosai, ta kasa magana. Abba yace bazaki magana ba? Saina ballaki Najeeb yace tana tunanin k'aryan da zata had'a ne Dad yace ibtisam ki fad'a mana abunda ya faru Ibtisam taci gaba da fad'in Bayan kun tafi wata rana ina kitchen ya shigo mukai cacan baki inda na gudu d'aki tun daka ranan ban k'ara ganinshi ba, saida akai wajan kwana biyu sai gashi shida wata mace inda na bu'kaci ya ...... Kuka ta kuma saki, lokaci d'aya ta basu labarin abunda ya faru.... Gaba d'aya salati suka saki Najeeb Kam tashi tsaye yayi yana fad'in Karya take mishi baiyi sex da itaba ranan Abba tashi yayi tsaye cikin zafin rai tare da fad'in najeeb da gaske kana shan alcohol?? Najeeb shuru yayi ba tare daya bama Dad amsa ba, Dad ya daka mishi tsawa tare da fad'in ina maka magana dagaske ne kana shan alcohol Najeeb Kai ya girgiza tare da fad'in no Dad Nasan wine ta gani ta d'auka alcohol ne.. Ran Dad ya baci Sosai akan cewa da ibtisam tayi NAJEEB yana shan alcohol, kenan sharri tayi mishi Ibtisam tace wlh Dad dagaske ne y..... Dad yace ya isa ibtisam, akan wani dalili zaki ce mijinki nashan alcohol?? ibtisam kuka take Sosai tare da d'auko wayarta ta nuna musu hotan giyan Dad kallon NAJEEB yayi tare da fad'in wannan miye Toh?? Najeeb yace ni ban San inda ta samo shiba, Dad so take ta kulla min sharri akan in amshi dan daba nawa ba, and wlh Dad bazanyi accepting yaron ba koda kuwa Mai zai faru Dad yace nima bazanyi Supporting ka amshi Yaron da ba naka ba, dan haka dole mahaifin Yaron ne zai amshe shi.... Abba ranshi ya baci akan abunda Dad yake fad'a kenan ya nuna NAJEEB ne Mai gaskiya ibtisam kuma Mai Karya, inbai manta ba sanda ta dawo daka America AI yaga ciwo a goshinta har ummi take fad'a mishi granny tace tayi mishi gardama ne yasa yayi mata da karfi, sannan yanzu bayanin da ibtisam ta bada ya k'ara tunawa da Abun... Granny ce ta Katse Ma Abba tunani tare da fad'in wai mai yake faruwa ne,?? Dad ne ya mata bayani tare da fad'in mama sai kusa ta, ta fad'i uban Yaron wanda yayi mata cikin?? Abba yace bai kamata ka kama maganan gefe d'aya ba, ya kamata Ayi bincike Kafin a yanke hukunci Dad yace babu wani bincike domin na yarda da abunda najeeb ya fad'a duba da sharri da ita ibtisam take k'okarin yi mishi, akan yana shan giya, yau inda ibtisam ba y'arka bace dasai Nayi karanta akan tayi mishi kazafi akan yana shan giya.... Granny tace kumin shuru cikin kuka tare da fad'in akan yaranku kuke son ku bata zumuncin ku, Bayan duka baku zurfafa bincike ba wlh ko kaffara bazanyi ba wannan cikin NAJEEB ne, domin na yarda da ibtisam Dad yace mama Nima na yarda da NAJEEB bai taba min k'arya ba tunda nake dashi.... Mum tace taya zaka fad'i haka, karka manta duka namu nesu NAJEEB da Ibtisam din S.... Dad ya dakatar da mum tare da fad'in enough, ya isa haka, idan ke baki yarda da d'anki ba Toni na yarda dashi dan haka dole ibtisam ta fad'i Wanda yayi mata ciki Abba wani irin hawaye ne ya zubar mishi a ido cikin kunci da ba'kin cikin abunda Dan uwanshi yake fad'a Wanda bai taba expecting ba, amma babu komai laifin y'arshi ce domin shima bawai ya gama yarda da maganan ibtisam din bane Najeeb kallon ibtisam yayi tare da fad'in zan fad'ama duniya abunda kika aikata I will make sure you regret abunda kika min cheater, lallai saina hukunta ki yanda bakya zato Ibtisam tace babu abunda zakamin domin duk inda zamu ciki naka ne, kuma kaine ubansa Najeeb yace OK zansa kiji kunya, sannan zansa kowa ya yarda ke mazinaciya ce domin kin aikata zina kin shigo gidana da cikin wani We will move to America tomorrow for DNA test Ibtisam tace babu inda zan bika domin bana kaunar koda da minti biyu ne In k'ara ganin fuskanka.. Najeeb dariya yayi tare da fad'in same with me, domin even me bazan zauna da mace fasi'ka ba, "AI dole kice ba zaki bini ba Domin gudun abun kunya ba Ibtisam murmushin takaici tayi tare da fad'in OK zanje but Ina son ni dakai muyi yarjejeni akan Idan muka je akai gwaji Indai cikin ya tabbata naka ne zan zubar dashi..... Najeeb yace ki zubar mana who care?? Nidai Nasan ba nawa bane and bazai taba zama nawa dinba har abada Ibtisam ta kalli iyayenta dake kallonsu ko wanne ranshi a jagule tace Abba ka yarda dani wlh cikin nan nashi ne wlh Abba Nayi k'okarin ri'ke mutunci na n..... Abba yace ya isa haka, koma dai mai nene idan akaje akayi gwajin komai zai bayyana.... Najeeb kallon abba yayi tare da fad'in duka su bashi password d'insu domin tare zasu tafi duka ciki harda Granny Abba yace a'a basai yaje ba, sannan ummi itama ba zata ba, kawai su suje Najeeb yace OK tare da kallon Dad yace Dad na tafi hotel sai goben Dad yace muje tare Muma hotel zamu tafi Fita sukayi Bayan sunyi musu sallama Koda suka isa hotel NAJEEB gaba d'aya kasa bacci yayi tare da kosawa subar k'asar domin suga karshen wannan Abun, ya tabbata cikin ba nashi bane. . Lokaci d'aya kuma yayi shuru yana nazari tare da tunanin abunda ibtisam din tace ranan da abun ya faru.... Lokaci d'aya ya girgiza Kai tare da fad'in no ba haka bane k'arya ta fad'a da Najwa nayi sex ranan gaba d'aya kawar da tunanin ma yayi tare da cire Abun a ranshi, sai dai wani abun mamaki ya kasa bacci sai juyi yake...... Ta gefen ibtisam kam tashi tayi ta shiga daki tana kuka, kiran zarah ne ya shigo cikin wayarta k'in d'auka tayi domin bazata iya magana ba. Itama wani abun takaicin kasa bacci tayi domin son kamshin turaren najeeb din taji tana sonyi, duk yanda tayi danta sama kanta tsanar son jin kamshin amma ta kasa, jin kanta na ciwo wanda ta tabbata yunwa ne yasa ta tashi dakyar Granny da itama ta kasa bacci sai juyi takeyi itama, itama Abun duk ya isheta Granny tace ina zaki??.. Ibtisam tace yunwa nakeji, zani kitchen Inci abinci Granny tace zoki zauna in dibo miki Kinji Ibtisam zama tayi akan gadon d'akin Granny tashi tayi ta fita Jim kad'an sai gata da abinci da Ruwa ta Kawo mata Ibtisam amsa tayi domin ganin dambu ne na cous cous, ci take Sosai kaman wacce bata taba ganin abinci ba. Granny kallonta take cikin tausayi domin ita in kowa bai yarda da ibtisam ba, ita ta yarda da ita domin tasan ko wacece ibtisam din, tasan halinta, zata iya cewa ko Ummi data haifi ibtisam bazata kaita sanin halin ibtisam din ba. Ta tabbata cikin na NAJEEB ne bana wani ba, in kowa zai karyata ita bazata karyata ba, koma dai miye y'ar nune zata nuna Idan aka haifi yaron koda ba'ayi gwaji ba Ibtisam ajiye plate tayi tare da gyasa alaman ta koshi, ganin kallon da Granny take mata yasa tace Granny Kema baki yarda dani bako?? Granny tace ko d'aya ibtisam ba haka bane, kawai Ina mamakin Abunne, ni nasan cikin NAJEEB ne, domin Nasan koke wacece, sai dai abunda yake bani mamaki da kika ce yana shan giya Wani hawaye Mai zafi ya fito Mata, tare da fad'in Granny Idan Nayi mishi sharri Riban Mai zanci??? Granny Wlh abunda na fad'a shine gaskiyan magana, amma koma dai miye za'ayi gwaji a gani Idan akayi DNA test za'a gane ko jinin Waye AI Granny tace taya za'a gane Bayan yaro bai fito duniya ba??? Ibtisam tace za'a gane, kawai jinina ake bukata, sai nashi su za suyi gwajin su gane jinin na Waye Granny tace ikon Allah kaga Abu iri iri dai a duniya Ta gefen Mum kuma koda suka k'arasa ta Fara fad'ama Dad abunda yayi bai dace ba, domin abunda yayi ya nuna yana Bayan NAJEEB ne, kuma hakan bai dace ba, domin Wlh ni nafi yarda da maganan ibtisam din Dad yace koma dai Mai zaki fad'a ni na yarda da NAJEEB, akan wani dalili zata kirashi da mashayin giya?? Wato ke baki ji komai ba akan an kira d'anki da mashayi ba koh??? Mum tace gaskiya kayi babban kuskure da ka yarda da NAJEEB, Bayan ko daka irin halin shi, ya kamata ka yarda cewa zai iya shan abunda yafi giya Indai akace yanayi, karka manta ko irin yanda najeeb yake...... Dakatar da Mum yayi tare da fad'in ya isa haka plz, I trust my son, so ban son wata magana plz koma dai miye gobe zamu tafi gaskiya zata fito and ina tunanin tunda basa son juna is better a raba auren Mum salati ta saka tare da fad'in Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, Mai kake fad'a haka?? Kana nufin akan d'anka har zaka iya yarda kayi fad'a da dan uwanka?? Ko kasan wannan abunda kakeyi zai iya Kawo rashin fahimta kaida k'anin ka? Yanzu kai saboda yaran da kuka haifa saiku yarda su raba muku zumunci K.... Dad ya Katseta da fad'in sai me?? Akan mai yasa bazai rabu da ita ba, Bayan tana binshi da sharri akan wani dalili zai zauna da ita?? Mum shuru tayi, lokaci d'aya tace ina guje maka abunda zaisa kazo nan gaba kana dana sani Yace babu dana sanin da zanyi domin Nasan NAJEEB komai yayi zai fad'a Dan haka kibar wannan maganan ki barni in kwanta In huta Mum shuru tayi tana mamakin yanda mijin Nata yadau zafi, ita bata ga abun d'aukan zafi ba, ita a yanda take kallon NAJEEB komai akace zaiyi zata yarda, domin su da kansu suka lalata rayuwar d'ansu da kansu, yaro sun D'aukeshi sun kaishi waje karatu ba tare da mai kwaba mishi ba, ai dole suga ba dai dai ba Washe gari wajan karfe 9 tayi masu NAJEEB a gidansu ibtisam, koda suka zo ,Ummi ta Kawo musu abinci Mum ce kadai taci amma shi Dad yaci abinci Najeeb kam baici komai ba haka kawai yaji baya son cin abincin domin gaba d'aya baya cikin nutsuwa, Ummi kiran ibtisam tayi wacce ta fito cikin jallabiya tare da yafa k'aramin gyalen jallabiya din wanda yayi mata kyau Sosai Najeeb tunda ta fito ya kura mata ido Lokaci d'aya ya kauda kanshi tare da jan gajeran tsaki Ibtisam kam wani irin dad'i taji, domin tana shigowa kamshin turaren shi taji wanda ya sata nishad'i Gaida su Mum tayi cikin girmamawa Dad ya amsa babu yabo babu fallasa Mum tace ibtisam sannu ya jikin naki?? Ibtisam tace Alhmdlh Najeeb yace Dad mu kama hanya 10 jirgin zai tashi Gaba d'aya tashi sukayi, suka fita cikin masu tafiyan harda Granny yau zata Ameka Koda suka k'arasa airport suka shiga jirgi granny dai ba wannan bane farkon shigarta jirgi ba, kar kuji batai kauyanci ba Hhhhh Bayan kowa Ya gama shiga jirgi ya d'aga zuwa America koda suka sauka Kai tsaye mota suka shiga inda NAJEEB yace shifa bai yarda aje Gida ba sai an fara zuwa anyi DNA test din hakan ko akayi Suna tafiya a mota domin zuwa asibti Granny tace oh ikon Allah kalli yanda suke yawo kaman tsirara Kai dole mutun ya lalace idan yazo wannan k'asar Wlh, jiba wannan Abun kunyar har Ina fisabilillahi Mum dariya tayi tare da fad'in Granny aisu ba musulmai bane, sannan Idan bakai wannan shigar ba su gani suke baka Waye ba Granny dake zaune sanye da riga da hijab tace kenan ni sai su koreni daka k'asar kenan Mum tace a'a sai dai ka zaman musu abun Kallo Granny tace Allah shiryesu Mum ta amsa da Ameen Ita kam ibtisam bama jinsu take ba, ita burinta aje Ayi gwanin ta samu ta zubar da cikin kowa ya huta hankali kwance Koda suka k'arasa asibitin ba tare da bata lokaci ba akama Dr bayani akan abunda suke bukata, nan aka d'iba jinin ibtisam aka d'iba na NAJEEB tare da fad'in sai nan da kwana biyu result zai fito Nan sukayi gida Kai tsaye, suna isa Dad yayi kitchen domin Ruwa yake bukatar sha Mum kam ciki suka shiga inda ibtisam tace d'aki d'aya zasu zauna da Granny hakan ko akayi Gaba d'aya ibtisam bata fita koda falo ne, abinci sai dai Granny ta Kawo mata daki,balle yanzu da komai taci sai tayi amai bata ma cika ciba sai taji kanta na Mata mugun ciwo shine zata ci Dan dole shima tana gama ci sai amai gaba d'aya ta kosa result ya fito a cire mata cikin ta huta da wannan wahalan Najeeb kam gaba d'aya baya zama a gidan tunda suka zo, domin aiki yayi mishi yawa sosai Ibtisam tana d'aki zaune bata son jin komai sai kamshin turaren najeeb, ganin ba samu zatayi ba, yasa tasa kuka Sosai kaman ranta zai fita Dan takaici gashi gobe ne result zai fito, gashi gaba d'aya taga lokaci baya gudu ibtisam na nan zaune taji kamshin turaren NAJEEB, da sauri ta d'aga Kai suka had'a ido, wani irin murmushi da bata san ya fito ba ta saki tare da sauke wani irin ajiyan zuciya Najeeb wani irin kallo ya mata tare da fad'in gobe result zai fito you better tell them the truth tun kafin lokaci ya k'ure kiji kunya Ibtisam tashi tayi tare da kallonshi tace najeeb nasan bazanji kunya ba, domin Nasan ban aikata abunda kake tunani ba am sure kaine zakai dana Sani Wani irin shu'umin murmushi ya saki tare da fad'in we shall see tomorrow Wani irin kallo ya watsa mata tare dayin gaba Zai fita har yayi nisa ya kusa fita, da sauri ta kira sunanshi da fad'in najeeb plz wait Tsayawa yayi cak ba tare daya waigo ba Nufanshi tayi tare da zuwa gabanshi tana fad'in dan Allah kaban..... Sai kuma tayi shuru alaman tana jin nauyin fad'an abunda take son cewa Gira ya d'aga mata tare da fad'in zaki fad'amin Waye kwarton naki ne??? Ibtisam baki ta cije alaman taji zafin abunda ya fad'a amma saita basar tare da fad'in turaren ka nake son ka bani plz wanda kake sawa.... Ido ya kura mata yana kallonta lokaci d'aya kuma ya saki murmushi tare da d'aure fuska yace shi d'an iskan da yayi miki cikin nashi baiyi miki bane??? Ibtisam tace plz ka bani ban son dogon magana plz Najeeb wani kallo ya k'ara watsa mata tare da fad'in kije uban cikin naki ya baki shi saurayin naki Cikin bacin rai tace OK zanje ya bani amma ina son ka sakeni sai in koma waj...... D'aga hannunshi yayi zai mareta alaman bacin rai ga idonshi da yayi ja, lokaci d'aya ya sauke hannun tare da cije baki ya fita fuuuu. YAWAN CLICK, YAWAN POSTING(function loadPageAds() { return afriPageAds({ 'pid': 8612, 'uid': 9740, 't': '300 by 250', 'url': 'https://2gnblog.blogspot.com/' }); }()); Bai dad'e da fita ba, sai gashi ya Kawo mata turare wajan Kala 8, tare da watsa mata akan gadon d'akin Har zai fita ibtisam tace babu shi a ciki wanda kake sawa shi nake so, dan Allah ka bani ka tausaya min ka bani sai kuma ta saki kuka......