
Dariya mukeyi Amman ƙasa_ƙasa gudun Umma ta san su muke yiwa dariyar,ƙwan_ƙwasa get ɗin ne aka soma yi, muka saurara muji nan ne ko kuwa, sai da muka tabbar da nan ɗin ne muka soma kallon_kallo, Umma ta ce, “a dubo mana kukayi Zaune”.
Tashi mukayi muka shiga cikin ɗaki muka ɗauko mayafi, muka fita da gudu Shuraim ya kama hannu na, muka fita, a lokacin duk ana ƙwan_ƙwasa ƙofar buɗe wa mukayi, “yam matane su ukku a tsaye, da murmushi a fuskar su, hannu na basu nace, “Assalamu Alaikum” muka gaisa dasu, haka su Amrah sukayi masu.
Dariya sukayi, ɗaya tace, haba “yan uwa sai kubar mu a waje, ba zakuyi muna karramawa ba irin ta baƙin ku ba? “.
Murmushi nayi nace, na ɗauka tambaya kukeyi ne shi yasa Amman kuyi hakuri ku shigo daga ciki”.
Tare muka shiga dasu har cikin falon suka gai sa da Umma, nace su zauna bayan sun zauna ne Amrah ta kawo masu ruwan sanyi suka sha.
Bayan sun shane ɗayar wadda tayi magana ɗazun tace, “Suna na Aysha Umar” da sauri muka kalli juna, duk suka bimu da ido suna kallon mu.
Tace, “sunan nawa babu daɗi ko? “.
Da sauri nace aa keko mai babba suna kiyi hakuri zamu kira ki da Humaira dafatan bamu ɓata maki suna ba”.
Dariya sukayi dukan su, tace, “ashe babba suna ne to na yarda”.
Ɗayar kuma tace, “ni kuma Hindu” ɗayar kuma tace, Halimatus Sadiya”.
Humaira ta ce, “mu ba baƙi bane a unguwar nan ba, kuma yan zun haka ana cikin hidimar bikin Hindu ne, to da an gama da sati ukku sai bikin Halima, ina fatan daku za’ayi komai dan muna yawan ganin ku kuna zaga unguwar nan bakwa shiga gidan kowa”.
Dariya mukayi nace insha Allah zamu halarta, ni ce Narjeesah wannan ƙanwata Amrah itace ke bina shekara biyu na bata, sai Auta Nusaiba gata nan “.
Suka ce wow, “wannan big boy din fa? .
Amrah ta ce, “yaron Anty Narjeesah ne”.
Humaira ta ce, “my boy yaushe zaka zo gidan mu ne? “.
Dariya yayi kawai bai ce dasu uffan ba gurin Umma ya komawar sa.
Fira mukayi sosai sai da la’asar muka rakasu kowace har ƙofar gidan su, gida muka dawo mukaci da har kar gaban mu kwata_kwata mun manta da maganar bikin da aka gayya ce mu, sai ranar kamu, su Humaira suka zo gidan mu ni kuma ina sama a kwance kaina ke ciwo Umma suka gaisa da ita, suke tambayar ta, “Umma kodai kece kika hanasu su zuwa bikin nan” .
Umma kuwa ta ce, “aa rufani ku sayani yaran nan, ku shiga ciki ita tana nan amman Amrah da Nusaiba sun fita da Shuraim na aike su”.
Da sallama suka shigo cikin ɗakin, zaune na tashi Hindu sai harata takeyi, dariya nayi na ce, “afuwa Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida”.
Dariya sukayi Hindu ta ce, “idan na kashe ɗan masu gida ai ke ce zaki fara bada shawarar a kaini kotu a ɗaureni ko kuma ki fara yaɗani a duniya”.
Dariya duk mukayi, na ce, “dan Allah kada kuce komai wallahi mantawa mukayi yau kuma kaina ke ciwo “
Hindu ta ce, “wallahi babu wani batun hakuri sai kin tashi mun tafi.
Dariya mukayi dole na tashi na ɗauki gyalena daman ban wani daɗe da fitowa wanka ba na saka kaya amman banyi kwalliya ba, ciwon kai kawai yafi damuwa na, fitowa mukayi Umma bata nan tana ɗakin ta, na shiga nace “Umma zan tafi bikin can idan sun dawo su sameni a can dan Allah “.
Ai kuwa Umma bata ce dani komai ba, har nagaji da tsayi, na juya zan wuce ke nan ta ce, “Adawo lafiya kuma a kula da kyau”.
Jin tayi shiru da sauri na jiyo ina kallon Umma wadda taci gaba da aikin gaban ta kamar ba itace tayi magana ba.
Cike da farin ciki na fito gurin su nace muje, tafiya mukeyi amman zuciya ta sai mai_maita addu’ar Umma takeyi farin ciki kawai nakeji wannan shine karo na farkon da Umma ta taɓa yi mani abunda nake so, kuma nake mafalki.
A gidan su Humaira muka sauka gaskiya Maman Humaira da yan uwan ta, basu da matsala gasu dai masu kuɗin gaske amman basu da wulakanta mutane, a ɗakin Humaira muka yada zango hum Humaira kam badai gayu ba, budurwa ce “yar gayun gaske nikam akan gadon ta na faɗa nayi kwance, yan mata kuwa gayu kawai suke ɗauka, Halima ce ta dube ni ta ce, “Narjeesah ki tashi ki gyara zamu gurin saloon ne fa kuma ke kin wani kwata, dolene fa ki ajiye ciwon kan ki a gefe sai angama biki ehe”.
Dariya mukayi nace, waye zai iya ajiye ciwo ke mu banda abinki? “
Tace, “to kisha magani kuwa” kallon ta nayi na ce, “ke kisha mani maganin mana idan kin sha mani zan warke”.
Dariya ta saka mani tace, “malama ki fito fili kawai kice bakya shan magani nafi gane hakan”.
Dariya mukayi dukan mu, duk kowa yana gama gyara wa, Angon ya kira waya yace, “a fito ga motoci nan.
Tashi mukayi zamu fita, Humaira ta janye ni ta maidani ɗakin ta, ta zaunar a kujerar madubi ta ɗauki kayan kwalliya ta soma yi mani dariya kawai na keyi nace, Humaira nifa bana kwalliya sam”.
Tace, “haba malama ai kuwa tunda kina tare dani dole sai kin iya dan ni jinki nakeyi kamar uwa ɗaya uba ɗaya muke, to waima ni kam haka kike zama ba bu kwalliya kamar ba mace ba? “
Dariyar Hindu muka jiyo a bayan mu tana faɗar da kyau my Humy wallahi yi mata raɗau da kwalliya “.
Jefe ta nati da marfin foda ai kuwa da gudu ta fita tana dariya.
Sai da Humaira tayi mani kwalliya mai kyau bamai yawa ba, mai tarkace, muka fito Halima ce ta dube ni ta ce, “wow ko kefa malama Narjeesh, wallahi kin fi kowa kyau a gurin nan harda Amaryar, jakar hannun Hindu na amsa na jefe ta dashi da gudu ta fita tayi waje”.
Maman Humaira ce ta ce, “Allah dai ya shirye ku, kuyi ku tafi dan Allah kun bar mutane nata jiran ku”.
Amrah da Nusaiba ne suka shigo da sallamar su, da sauri ƙanwar Humaira ta kama hannun su, suka shiga cikin gidan Humaira kuma ta ɗauki Shuraim suka fita muka bisu a baya, gidan su Hindu muka nufa inda motocin ƙawayen Amarya duk sun shege motoci mu kuwa, wata haddiyar motar ce, muka nufa, Halima ce ta shiga gidan gaba mu kuma muna gidan baya harda Amaryar”.
Tunda muka shiga cikin motar babu wanda ya ce uffan, Halima kuwa fira sukeyi da mutumen, har dasu dariya sukeyi, mu kuwa har muka ƙarasa ba muyi magana ba.
A bakin wani haɗaɗɗen guri suka ajiye mu, kawai muka shiga ciki gurin salon ne da gyaran jiki, wanke kai kawai da ƙafafun mu akayi muna muka fito suna ɗaukar mu sai holl muku nufa duk an ƙawata shi, ta ko ina yaji gyara sosai, shiga mukayi gurin na zauna a kujerar da aka tanadar wa manyan ƙawayen Amarya nida Humaira da Shuraim Halima kuma suke ƙara gyara wa Amarya, haka akayi komai da zamu koma Angon da kansa ya ɗauke mu muna tafe suna fafa tawa da Humaira, yana ce mata azzaluma ita kuwa tana ce masa zata saka a ƙara masa sati biyu, mukam dariya mukeyi.
Halima ta ce, “to kai idan ta saka aka ƙara sati biyu ka ce abokin ka ya ƙara wata biyu sai ayi bikin “.
Dariya mukeyi harda Angon da sauri Halima da Hindu suka ce “ƙarya kike yi ai kin mafi Angon zumuɗin bikin tunda yau saura kwana ishirin da biyu”.
Shiru tayi, nidai suna burge saboda na lura suna ƙaunar junan su, Halima ta ce, “nifa wallahi banƙi jinin a ɗaga wannan Auren ba”.
Humaira tace, “komai abun ki Aure kamar anyi sa an gama ne”.
Muna isa gidan aka fara kiran sallah da sauri muka fita daman ƙofar gidan su Humaira muka sauka muna shiga cikin gidan naja su Amrah muka tafi gida, tun da safe sai gasu Humaira mukaje gurin kitso da lalle akayo muna, tunda muka dawo gida, hima dai akeyi tare damu, aka ɗaura Auren aka kai Amarya ɗakin ta.