
Alhamdulillah anyi biki lafiya an gama lafiya, sai himar bikin Halima ta kunno kai bamu dai wani futa ba, rabon cimgam muka tafi, munsha yawo muka dawo munje gurin saloon mun dawo sai dai wannan bikin za’ayi dinier banyi niyar zuwa ba, amman ganin du sun ɓata ran su dole na yarda zanje harda ankon bikin akayi muna mu duka kuma bada ko naira namu ba.
Kallona Humaira tayi tace, “Nikam har yanzun banji kin sanar dani komai ba kina da Aure ko babu ina Baban Shuraim amman fa ban ce dole sai nasan komai a kan kiba, kada kiyi fushi idan har wannan abun sirrin kine dan Allah kada ki sanar dani kinji Narjeesh? “.
Dariya nayi ban ce da ita komai ba tace, “na fahim ta, amman nikam bari kiji, Narjesh kin ganni nan kwata_kwata bani da saurayin da nake saurare saboda na tsani yau dara, duk wanda yazo guri na sai na fara tambayar sa miye ya kawo sa guri ba da zarar ban gamsu da baya nin mutum ba nakan da katar dashi, shi yasa aka ce korar samari nakeyi “.
Dariya nayi nace “mutum sai Allah kinji Humaira Allah ya kawo maki miji na kwarai musha biki, ranar nice kan gaba “.
Firar mu mukeyi muna aikin gyara kayan miya tunda akayi abinci muka baiwa mutane tare da Hindu muke komai shirin zuwa gurin dinier mukayi sosai, nikam duk sai naji kamar kar naje, amman duk sun hana ni suna tsare dani, da nace zan je na dubo Shuraim sai Humaira ta ce, “Shuraim kam yana gurin mijin Hindu wato Aliyu”.
Cike da mamaki na ce, “kuma ya yarda yaje gurin sa? “.
Hindu ta ce, “to da miye nufin ki malama? Ai Shuraim yaron mune ba naki ba”.
Dariya kawai nayi na ce, “Allah yaron baida yarda ne kun dai san halin sa ni mamaki ne nakeyi”.
Dariya sukayi, motoci aka kawo muka tafi, tafe muke ni dai ba zan ce ina jin daɗin wannan dinier ba ko akasin hakan.
A gurin dinier ma kujera na samu na zauna nesa dasu saboda yanda naga wasu yam matan nayi abun baiyi mani ba, Humaira ce ta zo inda nake tace, “Narjeesh wallahi kin bani wahala ina ta neman ki kizo ku gaisa da Angon dan ya iso shida manyan abokan sa harda wani babban baƙon sa naji ana faɗa”.
Oh Humaira ke kinje kun gaisar ne nikam, tace, “ban jeba tare zamu je dake nima bada son raina nake son zuwa ba saboda ban wani saba da wannan angon ba, Aliyu munfi sabawa dashi, kuma shine ya aiko Hindu ta kira mu “.
Tashi nayi muka Jera muna tafiya sannu a hankali kamar wasu marasa lafiya Hindu ce ta taryemu tana dariya ta ce, “wai lafiyar ku kuwa twins sister na? Naga duk jikin ku yayi sanyi”.
Bamu bata amsa ba, taja hannun mu sai gurin mijin ta, yana ganin mu ya taso yazo ina muke ya ce, “haba dan Allah kuje ku gaisa da Angon da abokan sa mana, kuma munada babban baƙo amman yana can gurin saboda yan mata ya koma can”.
Ni kuwa nace, “hala ma mayen mata ne shi?”
Dariya sukayi ya ce, “kai wannan ai babu wata mace a gaban sa sai matar sa, muje kawai “.
Mere baki nayi hannu na Shuraim ya kama yana tsalle_tsalle gurin Angon da abokan sa mukaje muna ganin Angon muka gaisa, dashi ya amsa ba yabo ba fallasa abokan sane suka fara tsokanar mu, bamu biye masu ba, har mun juya zamu wuce Angon ya ce, “Humairah kuje ga babban aboki na can gurin ku gaisa dashi”.
Ba Humaira ba ko ni da naji yanda ya kira sunan nata sai da muka jiyo da sauri muka kalli junan mu, kai tsaye nace, “ai ba sai mun jeba saboda mutane sunyi yawa ni zan ma koma can baya na ɓuya Humaira kuje ki gaisa dashi”.
Kai tsaye ta ce ba zan je ba, Angon ne ya nuna rashin jin daɗin sa a fili yace, “ok nagode da karramawar da muka samu a gurin ku”.
Hannu na dana Humaira Hindu taja tace, to honey muje ka raka mu naji kace jami’an tsaro ne dashi”.
Harda Angon tare muka tafi muna tafe, Shuraim yana riƙe dani, ‘yan mata muka gani sai iyayi sukeyi, wasu har gurin sa suka nufa amman an hanasu su ƙarasa gurin, mu kuwa muna tafe nace, “Hindu Humaira banga fa Halima ba wai tana ina ne? “.
Humaira ta ce, “wallahi tun ɗazun nake neman ta, harda wayar ta na kira bata zuwa, duk shi yasa na shiga cikin wannan yanayin”.
Hindu ta ce, “to ina Halima zata tafi bayan itace ta, taramu a gurin nan “.
Angon ya ce, “wallahi na ɗauka tana can gurin da aka kira mani ku, to amman ina ta tafi ne? “.
Wayar Humaira ce tayi ƙara tana duba ta sauke ajiyar zuciya ta ce, video coll Halima Allah dai ya shirya muna ke, ɗaukar wayar tayi, kawai sai ga Halima muna gani ba’a cikin holl din ba.
Halima tayi dariya ta ce, Humaira ki saurare ni da kyau kiji, da hankali na nake komai, ina fatan kin san da sanin cewar Yazeed abokin Jafar wanda zan Aura ko? Wanda yake mutum makusan cin Jafar ko nace aminin sa, wanda yake zuwa guri na yace Jafar ne ya aiko sa guri na, har ka kace kin tsane sa, yana son ya ɓata Aure na da Jafar ne, to ki sani soyaya mukeyi dashi kuma shi nake so ba Jafar ba, yan zun haka ma nabishi mun tafi a ɗaura muna Aure dashi, shi kuma Jafar yayi hakuri Allah ya bashi wadda ta fini”.
Da sauri na anshi wayar nace, “Halima baki da hankali ne wai, taya zaki yanke wannan ɗanyen hukuncin kada ki biye ruɗin zuciyar ki mana? “
Halima ta ce, “ki baiwa Humaira shawara, nasan zata ɗauka, ki sani na baiwa Humaira miji ta Aura kece aminiyar ta dan haka kiyiwa Humaira adalci tayi Aure ga farin masoyi nan wanda take son na Aura wanda take fushi da nurul ƙalbina Yazeed a kan sa, lallai Humaira mutum ce kuma adilah”.
Hindu ta ansa tace, “Halima ki dawo hayyacin ki dan Allah “.
Halima ta ce, “Hindu nayi nisa bana jin kira, ku baiwa Jafar dasu Mama hakuri kuma kuyi recordin ɗin abun da nake faɗa yan zun “.
Jafar ne ya anshi wayar ya ce, “saboda miye zaku yau dare ni keda yazeed miye laina dan nace ina sonki kuma baku tashi yau dara ta ba sai ranar dinier? “.
Halima ta ce, “Jafar yan zun ni matar abokin ka ce, dan haka bara na bashi shine dai_dai da kai”.
Yazeed yace, “Kayi hakuri amini na haka Allah yaso Halima ba matar ka bace mata ta, ce”.
Halima ta ce, “nasan kuna recording ɗin komai Baba da Mama ku yafeni abunda nayi maku bana son Jafar a yanzun dan haka ku maida masa da kayan sa, na barku lafiya”.
Kashe wayar tayi, kowa ya shiga cikin damuwa Humaira kuka kawai takeyi, ta ce, “Hindu ban faɗa maki ba, ban yarda da alaƙar Halima da wannan wawan ba? “
Hindu ta ce, yan zun fa kawai musan abunyi kawai kowa ya rasa mafita, kawai wayar Jafar tayi ƙara yana dubawa, ya baiwa Aliyu sai Aliyu ya ce, “muje gurin Mutanen nasan shi yanada mafita”.
Haka mukaje gurin tun kafin mu ƙarasa naji zuciya ta kamar zata faso ƙirji na ta fito sai dukan ukku ukku takeyi da sauri da sauri rufe ido na nayi muka ci gaba da tafiya muna zuwa naja nayi tsaye batare da na kalli mutanen gurin ba, Aliyu ne ya bashi labarin akasin da aka samu da duk yanda akayi kallon mutanen kawai yake.
Dafe zuciyar sa yayi da sauri, ya tashi tsaye duk suka zuba masa ido, cike da mamakin sa, kallon inda ya kafe da ido sukayi ga mamakin su nice yake kallo gashi nima nayi tsaye na juya baya, ina dafe da ƙirji na.
Shuraim ne ya gudu yaje ya rungume sa, ya ce, “na kamaka wallayi”.
Cike da mamaki aka maida ido a kan Shuraim da wannan mutanen, kawai ya saka hannu wansa ya ɗauke sa ya rungume sa a ƙirjin sa, suna sauke ajiyar zuciya sun ɗauki wasu lokuta a haka kafi ya ƙara duba fuskar Shuraim ɗin ya yi masa murmushi.