NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Ni kuwa jin shirun ya yi yawa sai na maida ido na akan, su Humaira sai naga tana kallon wani gurin nima sai na ɗaga ido na abunda nagani ne ya fir gitani Shuraim ajikin wani mutum kuma sun kafe juna da idon sai murmushi sukeyi iri ɗaya.

Aliyu ne da Jafar suka ce, “man ya zamuyi da mutane zauna wa yayi da Shuraim a jikin sa, ya riƙe dashi, yana kallon sa, kawai naje kusa dashi nasa hannu na ɗauke Shuraim na juya zan wuce, naji an riƙe Shuraim a fusace na juya zanyi masifa kawai naga ashe…….

Comment And share

Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

???????? NARJEESAH ????????

Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN

ELEGANT ONLINE WRITERS

Bismillahir Rahmanin Rahim

           1⃣1⃣⏮1⃣5⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Kai sai naga Ashe Shuraim ne ya riƙe masa hannu cikin jin haushin sa kawai na doke hannun sa, ya saki mutumen, ya fashe da kuka, sukam kallon mu kawai sukeyi, da sauri naja hannun Humaira da Hindu muka bar gurin, muna fita na sauke ajiyar zuciya na maida hankali na a gurin Hindu nace, “Hindu ya kamata Humaira tayi kamar ita ce Halimar saboda kada mu kunya ta wannan bikin musam ma abokan Angon nan da yan uwan kamar Halima ko ya kuka gani? Tunda kaya iri ɗaya ne kuka saka kwalliya kaɗan ce ta ban banta, sai na baki wannan gyalen nawa yafi naki girma yanda babu wanda zaga fuskar ki bare yasan wace ce a gurin ki duba yanda ake ta cigiyar Amarya kuma dare kayi fa”.

Da sauri Hindu tayi na’am da shawara ta, mukayi wa Humaira kamar Amaryar mukaje muka zaunar da ita akan kujerar Amaryar, tafi kawai akeyi, Hindu ce taje ra sanar dasu abunda muka tsara suma daket Jafar ya yarda suka rakoshi ya zauna a gefen Humaira, kiɗa aka sanya aka fara yin dinier cake aka ce a zo a yanka, Humaira taƙi tashi sai da na roƙeta da ket ta tashi a hankali take tafiya gurin yanka cake ɗin sai da Aliyu da wannan baƙon nasu sukayi tsaye wa Jafar ya riƙe wukar muka, taku rawa Humaira itama ta riƙe wukar suka yanka, Dj yace, sai su ciyar da junan su, hakan duk ka ƙiya ni kaina banyi tunanin hakan ba, da ket muka samu ya saka wa Humaira abaki itama ta saka mashi, tafi akayi suka koma suka zauna haka dai akayi ta dinier har aka gama komai, motoci ne suka zo suka fara kwashe mutane Humaira na can tana kuka bayan ta gama gaisa wa da mutane da abokan Angon.

Mota zan shiga na juya banga Shuraim ba inada na barshi a kusa da Humaira da sauri kira Amrah da Nusaiba da suke jira na cikin kuka nace dasu banga Shuraim ba.
Hindu ta ce, “Narjeesah wane irin baki ga Shuraim ba, bayan a hannun ki na gansa”.

Nace wallahi a nan yake zaune kusa da Humaira, na barshi zan samar muna mota, cikin kuka nake magana.

Ai kuwa atake kowa ta shiga neman Shuraim babu shi babu labarin shi, kuka kawai mukeyi nida su Amrah harda Humaira gashi dare yayi har kusan ƙarfe ɗaya, Jafar ya kira duk motocin da suka fita sunce basu ga yaro ba, su kam”.

Neman duniya an yiwa Shuraim amman ba’a samesa ba, dole sukayi ta bani hakuri suka ce nemo mani shi, gida muka koma a ƙofar gidan mu suka sauke muka shiga gidan, Umma tana ta duba inda zata ga Shuraim amman bata gansa ba gashi duk idon mu yayi jawur dashi.

Da gudu na shige cikin ɗaki na, nayi kwance ina kuka, Umma kuwa cewa tayi, “kun baro sa a can ko? To kuwa kun kyauta, taya ma zakuje ku saki ƙaramin yaro a can cikin taron mutane kuma cikin dare gashi ba yarda yakeyi da mutane ba, wallahi badan kada ayi biyu ba, da sai ku. Koma cikin daren nan kun nemo sa, yo wannan ai sakarcin banza ne! “.

Faɗa kawai Umma keyi ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, ganin yanda Umma tayi fushi ne take ta faɗa kowa ya gudu cikin ɗakin sa, kuma kowa kuka yakeyi, alwala na ɗauro a ranar ban rintsa ba, kaina kuwa saboda ciwo kamar zai watse, da safe abun karin kumallo ne aka kawo mani bana iya saka komai a bakina Humaira ce ta shigo itama idon ya kumbura, ta gaida Umma, Umma ta amsa ta kafe ta, da ido har ta tashi ta shiga guri na, Umma ta dakatar da ita, ta dawo ta zauna abinci Umma ta zuba mata ta tsare ta, tace, “ki cinye sa ki bani kwanon nan shi nake jira”.

Humaira juya cokalin takeyi ta kasa saka loma ɗaya a bakin ta, Umma na ganin abunda takeyi tace da Nusaiba jeki ki ce ta fito ina kiran ta”

A tare muka fito da Nusaiba ina fito wa na kafe Humaira da ido, a kusa da Humaira na zauna cokali Umma ta bani tace, ” kwanon kawai nake buƙata”.

Duk kan mu juya cokalin kawai mukeyi, har abincin ya fuce, Maman su Humaira ce ta aiko kiran mu tare muka tashi su Amrah suka raka mu, Maman Humaira ce ta ce, “kuzo muje gidan su Halima ana can ana neman ku”.

Tare muka tafi gidan yan biki cike da gidan ɗakin Mommy muka shiga Maman Halima, ita ma tace kuzo muje inda ake neman ku”
Muna shiga cikin ɗakin mutane muka samu a gurin harda su Jafar mahaifin Halima ne ya buɗe taron da addu’a sannan yace, “naga saƙon Halima kuma muna godiya sosai da abunda ta aikata muna, zata kuwa gani ga kwaryar shanta”.

Sannan ya dubi mahaifin Jafar ya ce, “malam dan Allah kuyi hakuri laifin ɗan yau ne ba namu ba, mu bamu ƙi mu haɗa zuriya da ku ba, amman haka Allah ya so ga kayan ku da kuka kawo sai ayi lissafin abunda taci wanda babu shi anan ciki! “.

Mahaifin Jafar ne ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “tabbas bamu ji daɗin abunda ya faru ba, amman babu komai ƙuruciya ce kuma ni kam ba zani anji komai ba daga hannun ka tunda daga kan sadaki har komai, kai mahaifin Jafar ne, zaka iya nema masa mata aduk inda kake so kuma nasan zaka zaɓa masa ta kwarai dan haka wuƙa da nama duk suna hannun ka”.

Mahaifin Halima ya ce, “ina godiya da wannan karamcin amman ku baiwa Jafar hakuri kuma ku bashi damar fitar da wadda yake so ni nan zan masa waliccin Auren nata”.

Jafar yace, “bani da wani zaɓi duk zaɓin da kukayi mani yayi “

Mahaifin Halima ne ya kalli mahaifin Humaira ya ce, “to malama Abdullahi gani nazo da ƙoƙon bara na, ina son ka baiwa ɗana Jafar Auren “yarka, Humaira”.

Da sauri muka haɗa ido da Humaira wadda tuni ta soma zubar da hawaye, kuka ta fashe dashi ta kwanta a jiki na.

Baban Humaira ya ce, “da Humaira da Halima duk naka ne kamar yanda zakayi hukunci akan Halima haka zakayi sa akan Humaira dan haka wuƙa da nama suna hannun ka”.

Murmushi mahaifin Halima yayi ya ce, “Humaira zan tambaye ki ki sanar dani tsakanin ki da Allah, shin kina da wanda kike so ko babu, ina son ki sanar dani gaskiya bana son ki ɓoye mani komai “.

Kasa magana Humaira tayi sai kuka takeyi, kowa ya zuba mata ido, mahaifiyar Humaira ce tace, “Narjeesah ke nasan kin san sirrin zuciyar Humaira kada ki ɓoye muna komai shin Humaira nada wanda take so ko babu? “.

Shiru nima nayi har sai da mahaifin Halima ya ce, “ki bada amsa dan duk gurin nan mun yarda dake”.

Kallon Hindu nayi ta matso kusa dani ta kafeni da ido alamar nayi magana, da ket na buɗe baki kasan cewar murya ta bata fita naci kuka tun jiya har yau, nace, Humaira bata kula kowa ma, ita a tsarin rayuwar ta bata son samari barkatai”.

Shiru duk sukayi zuwa can Baban Halima ya ce, to Alhamdulillah, shin Humaira zaki iya yarda ki Auri Jafar a matsayin zaɓi na? “

Kallon Humaira akeyi har yanzun dai kukan takeyi, sai aka dawo da tambayar a kaina, Hindu ta gyada mani, kai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button