
Nace, “ku iyayen mune zaɓin da zakuyi muna shine mafi can_canta mubi dan haka mun yarda da zaɓin ku”.
Hamdala sukayi dukan su, anan aka maida sadakin Jafar akan Humaira suka ga addu’a akace yau za’a ɗaura Auren duk sai da muka zaro ido har Hindu, sai kuma aka koma zan cen neman Shuraim da aketi har gidan redio an bada ciya da gidan tv, da unguwar ni.
Baro ɗakin mukayi muka dawo gidan su Hindu Maman Hindu tayi ta bamu baki, kowa faɗar yakeyi duk sune silar ɓatan yaron nan, hankalin kowa a tashe yake, haka aka ɗaura Auren Humaira da Jafar, Humaira har yanzun kukan takeyi.
Nima kukan ɓatan Shuraim na keyi a ranar ne aka kai Humaira ɗakin ta, muna kaita na baro gidan muka dawo gida, yau ma da kukan na kwana, zazzaɓi mai zafi ne ya kamani, gashi idan ina ciwo komai bana iya ci, duk nabi na rame na susuce.
Har cikin sati biyu babu Shuraim babu labarin sa, nikuma har yanzun banyi lafiya ba kullum cikin ciwo, Humaira ce ta aiko kira kashe na tara, Umma ce yau ta ce, “ke ni gaji da wannan aiken ki tashi kije kiji kukan ta”.
Tashi nayi, na shirya cikin riga da siket na shadda lemon green na ɗora gyalen a kafaɗa ta yau ban yafa har a kaina ba, Amrah ma shadda ce marun Nusaiba ma shadda ce pink, fitowa mukayi zamu tafi Aliyu ne ya gan mu yazo gaida su Mommy daman ya saba yin hakan, tsayawa yayi yace, muje ya kai mu yasan dai gidan su Humaira zani yasan ba gidan sa zani ba”.
Kaina na dafe da yake yi mani ciwo sosai nace, “wallahi ko ita Humaira wannan shine aike na tara tun ranar da muka kai ta ban koma ba, sai yau gashi har yanzun bani da lafiya “.
Tausayi na bashi ya ce, “wallahi har yanzun bamu daina neman Shuraim ba, dan yaron nan idan muka daina neman sa ba muyi maku adalci ba, saboda ata dalilin mune aka ɗauke sa, to taya zamuje muyi farin ciki ku kuyi kuka kin kuwa ba zai yuyu ba, har gidan Humaira ya kai mu nace masa wani satin insha Allah zamu je gidan sa.
Muna shiga cikin gidan da farin cikin Humaira ta, tarye mu kallon ta kawai nake duk tabi ta rame ta sauya kamar ba Humaira ‘yar gayun nan ba, zama mukayi ta kawo muna abun sha su Amrah suka sha, kallon Humaira kawai nakeyi, tayi murmushi ta ce, “kada kice dani komai malama aike yafi nawa sai yau kika ga damar zuwa? “.
Murmushi nayi na ce, “Humaira kema kin san abun da yake damu na”.
Humaira ta ce, “nima shine damuwata wallahi kullum da shi nake kwana nake tashi, na rasa ma wace hanyar ce zamu bi mu nemo sa? “.
Amrah ce ta ce, “Anty zamu ɗan fita mu dawo “Humaira ta ce, babu inda zaku bari mu baku guri kunna masu kayan kallo tayi, ta basu remote tace, kuyi kallon ku, kichin ta shiga ta kawo masu kayan motsa baki muka basu guri sai dariya sukeyi wai mun gano manufar su.
Cikin wani ɗakin muka shiga, muka yada zango, bayan mun zauna ne nace , “Humaira ya gidan ya mai gidan da fatan dai kun sasanta kanku “
Humaira ta nisa tace, “wane sasanta kai kuma Narjeesah kin fa san ba son junan mu muke yi ba, zuciyar sa tana akan Halima kuma ni har yanzun ganin nakeyi dawowa zatayi ga masoyin ta to sakin jiki na miye? Inje in saki jiki a kaini a baro sai na faɗa son sa Halima na dawowa ya koma mata ni ya sako ni ko ya kike nufi? “.
Dariya nayi harda dafe ciki na ce, “haba da ranki ya daɗe har sai da kika sa nayi dariya wadda rabon da nayi ta tun ranar da mukayi abinci yan zuwa dinier, sai yau, to ke kice hauka ce kike zaune kikeyi a gidan mijin ki, haba Humaira kefa ce, kike son miji wanda zai baki kulawa, kuma mai hankali gashi Allah ya baki amman kike wasa da damar ki dan Allah kiso mijin ki, ki dawo da hankalin sa a gareki ki cire masa tsoron mara da yashe sa, wallahi Humaira kina da abunda ba kowa ce mace bace ta tara suba, koda a gurin tsatar ki da ilimin ki kawai aka tsaya uwa uba natsuwa, Humaira ki yiwa kanki faɗa mana”.
Shiru Humaira tayi Jafar dake tsaye a bakin ƙofar tun ɗazun, yayi murmushi ya ƙaraso da sallamar sa yana dariya ya ce, “madam yau ke ce a gidan namu to munyi farin cikin zuwan ki, duk da muna fushi dake, a ce sai yau kika dawo gidan nan “.
Dariya nayi na ce, “ranka ya daɗe ba wata lafiya ce dani ba wallahi ko yan zun haka kaina ciwo yakeyi “.
Ya ce, “wallahi kina da gaskiya ɓatan yaro ai babban abune wallahi tunda mutum bai san irin halin da yaron yake ciki ba”.
Ya dubi Humaira ya ce, “Madam baƙona ya iso yana ƙofar gidan nan yan zun ya kira ni, Allah yasa akwai abunda za’a tarye sa dashi dan wallahi nima bai sanar dani zuwan nasa ba, sai da yazo ƙofar gidan nan “.
Humaira ta ce, “ok babu damuwa bari mu haɗo masa abunda akwai idan baya cin sa, sai a sama masa wani abun da ban “.
Tashi tayi tace, “muje ki taya ni” kwanciya ta nayi na ce “wallahi ba zanyi ba, nima ta kaina nake da nakejin yana ƙara mani ciwo ga bugun zuciya ta ya ƙaru”.
Ido suka haɗa da Jafar da sauri tabar gurin shi kuma yace, naje na shigo da baƙo na”.
Da sauri na ce, badai a nan cikin ɗakin ba”.
Dariya ya yi ya fita ni kuma nayi kwanciya ta, abinci ta ajiye a cikin ɗakin na ɗaga ido na na ce, “ba dai nan zaku kawo wani can ba? “.
Dariya tayi, na ce, “nikam zan gudu kuwa dai_dai lokacin suka shigo cikin ɗakin, ƙirji na ne naji kamar zai fashe, ko kallon inda nake baiyi ba, na koma na kwanta na rufe ido na Aliyu naji yana faɗar badai ciwon kan bane, Narjeesah? “.
Kallon sa nayi kawai na tashi zan bar ɗakin na ɗauki gyalen nawa, na riƙe a hannu na bar masu ɗakin su Amrah na yiwa nace, ku tashi muje gida sunyi baƙo kuma ni bani son ganin sa, ban san dalilin hakan ba”.
Tashi sukayi Aliyu ya ce, “baƙon mu zai rage maku hanya” da sauri na juya na kallesa nace, bana so ya tafiyar sa”.
Dariya sukeyi, Amrah tace, “Yaya Aliyu mun yarda zamu je tare da baƙon mu dan har naji baƙon ya kwanta mani tunda har zai kai mu gida “.
Tsaki nayi na ce, “ai sai kuje tunda mayun mota kuka dawo”.
Dariya sukayi suka dawo suka zauna nayi_nayi dasu mu tafi amman suka ƙi tafiya har sai da Jafar yazo ya ce, “ku fito yana jiran ku, zai kai ku gida, amman fa tare yake da masu bashi kariya, dan kada kuje ku ji tsoro ” da dariya yake maganar ya kallon fuska ta Humaira ma dariyar takeyi Aliyu ya saka ni gaba yana dariya har muka fita ƙofar gidan da gaske kuwa mutanen yau sun fi wanda na gani ranar dinier din nan, muna zuwa suka buɗe muna mota ɗaya.
Tsaye nake su Amrah duk sun shiga sai da Aliyu da Jafar sukayi da gaske nazo shiga suka rufe ƙofar suka buɗe mani gidan gaba, kamar nayi kuka na shiga cikin motar kawai naji ƙamshin da bazan taɓa manta irin sa ba, a take hankali na yayi mugun tashi, muka ɗauki hanya muna tafiya wanda yake tuƙin motar ne ya dubi su Amrah ta madubi ya buɗe bakin sa ya ce, “mike damun wannan yarinyar da ai ban san lokacin da na wani irin juyowa gabaki ɗaya nace,…
Sauke ni a nan malam kaji ko? Shima da sauri ya ɗaga ido sa ya waro su waje ya kafe ni da ido ya ce, “what!! Wani wawan burki ya taka ji kake ƙiiiiiiii ya ce, “kina nufin cewar wannan yaron ɗan ciki nane!!?.
Cike da zafin zuciya na ce, “baka da ɗa kuma ka daina alakan ta ɗana da sunan ɗan kane, yaro na bai da uban kuma kai ba kowa bane a gurin sa!!! “
Tsawa ya daka mani ya ce, ” rufe mani baki anan malama! Kuma kada ki yarda ki sake dan gata yaro na da wani ban za can!! “.