
Cike da masifa da rashin tsoro nace, “an cevShuraim ba ɗan ka bane, Shuraim bai da uba!! “
Yace, “ƙarya kikeyi Shuraim ɗana ne baida wani uban bayan ni!! “.
Su Amrah duk sun shiga cikin ruɗani, da sauri ta buɗe motar ta kira yaron sa saboda yadawo a kujerar da ake ɗora yara ya baro gurin tuƙin, saboda masifa, bamu ma san wani ya shigo motar ba, jan motar yayi Amrah nayi masa kwatan ce, har ƙofar gidan ya yi parking ya fita ya rufo motar mu kuwa masifar mukeyi ba bu ji ba bu ga,
Da gudu Nusaiba taje ta kira Umma sai ga Umma ta fito nima fita nayi shima fitowa yayi nasha ɗamara da gyale na, nace wallahi baka da ɗa a tare dani, kuma sai nayi ƙarar ka kotu sai an bi mani haƙƙina! “.
Shi kuma ya ce, “idan kika sake alaƙan ta yaro na da wani ban za can sai kin bin ciko mani shi, munyi shari’a dashi koda duk dukiyar dana tara zata ƙare!! “.
Umma ce, ta daka muna tsawa tace, “ya Isah! haka dan Allah kuke shirin tara wa kan ku mutane! koda ya ke ai ma na fahim ci komai, wannan shine Baban Shuraim dan ga kamar su nan dash! Ku shigo daga ciki muyi magana “.
Da sauri nace Allah ya raba Shuraim yayi kaman ce ceniya da wannan mugun! “.
Shima ya ce, wallahi ɗa nawa ne, ehe! “.
Hannun mu Umma nawa dana shi wannan shine lokacin na farko a ta rihin rayuwa ta da Umma ta taɓa riƙa hannu na mukayi tafiya muna shiga a falon gidan muka zazzauna Umma ta ce, ” NARJEESAH!! yau ina son sanin sirrin da kike ɓoyewa yau nake son sanin taya kika sami cikin Shuraim har zuwa yau ɗin nan, yau nice da kai na na kira Sunan ki karon farko da nake son jin damuwar ki dan haka gareki”.
Cikin farin ciki da baƙin ciki na ce “Alhamdulillah Umma yau ne karon farko da zan fara faɗar abunda ya faru, sirrin da ban taɓa sanar wa kowa dashi ba, saboda a ayi sani da duk abunda ya sami ɗa uwar sace ta farkon da zata fara sani, to ni kuma tawa uwar tayi ban za dani tayi kamar babu ita a duniyar nan shine nima na ɗauki alkawarin sai uwata ce kawai zata san sirri na to yan zun tun da uwata ta damu da damuwa ta, zan sanar daku komai”.
“Umma a yau zan sanar dake gaskiya abunda ya faru a shekarar da nake zana hara bawar shiga j ss 3,………… “
Allah kajiƙan iyaye na kayi masu rahma ka saka su cikin aljannar ka ta firdausi dasu da duk kannin yan uwa musulmi baki ɗaya amin
Comment And share
Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????
???????? NARJEESAH ????????
Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN
ELEGANT ONLINE WRITERS
Bismillahir Rahmanin Rahim
1⃣6⃣⏮2⃣0⃣
➿➿➿➿
Amrah ta ce, “amman kafin ki fara Anty Narjeesah taya ya akayi kuka haɗu da wannan mutanen amman abun mamaki ke baki san shiba kuma kun haɗu dashi tun ranar da akayi dinier kuma a guri ɗaya kuke dashi amman duk baku nuna kun san junan ku ba, sai yau ko yau ɗin sai da yayi magana kika nuna kin san shi shima hakan ce a a gurin sa a gaskiya kun saka mu a cikin duhu miyasa hakan?
Murmushin takaici nayi nace, “ban san shi ba kuma ban taɓa ganin sa ba”
Amrah ta maida duban ta a gareshe ta ce, “bawan Allah kai kuma fa taya kake cewa Shuraim ɗan kane bayan ita bata san ka ba? “
Ya ce, nima ban taɓa ganin taba, amman kuma Shuraim ɗana ne wannan shine gaskiyar magana! “.
Su Umma duk sun shiga cikin duhu, tashi tsaye ya yi ya ce, “Umma ni zan tafi ina da uzuri ne, amman gaskiya zan sanar maki, ita ɗin mata tace, akwai Aure a tsakanin mu, kuma Shuraim ɗan mu, ɗan halak ne shi ba shegeba dan nine mahaifin sa, kiyi hakuri Umma na barku lafiya kuma a kila da igiyar Aure na duk da bata san ni nima nima ban san taba, amman muna da Aure nida ita”.
Kawai ya fita, da sauri na ce, “Allah ya raba ni da Auren mugu irin ka azzalumi! “.
Aliyu da Jafar da matan su su Humaira da Hindu suka shigo, suna kallon mu, Umma ta ce, gara da kuka shigo, ina fatan kun ga mutumen da ya fita? “.
Gyaɗa mata kai sukayi anan Amrah ta labar ta masu komai bata boye, masu ba, kowa tambayar yakeyi taya ya hakan ta faru kuna da Aure a tsakanin ku harda ɗa ɗaya amman baku san junan ku ba, sai a murya gashi kun haɗu ya kai sau nawa?.
Umma tace, “ke muke saurare”?
Kallon su nayi na ce, Zakuji labarina yanzun kuwa”.
Sunana Narjeesah Isah Musa, mahaifina malam Isah Musa mutume ne ɗan kasuwa Allah yayi sa da zafin nema, matan sa huɗu Maryam itace uwar gidan sa amman muna kiran ta da Inno sai Larai itace ta biyu muna kiran ta da Mama sai Atika ta ukku muna kiran da Yaya, sai Aysha wato Umma itace cikon ta huɗun”.
Zama akeyi na haɗin kai dan basa faɗa ko kaɗan idan ka cire Mama wadda take da zafin kishi da son abun ta da nuna nata_nata ne, ga shegiyar rowar tsiya, gashi itace da manyan “yaya a gidan, sam sauran halin su ya ban banta dana sauran mutanen gidan, haka yaran ta duk halin ta sukayo dan duk ta ɓata su.
Yaya ma cikin yaran ta Mama ta ɓata mutum biyu saboda suna zama a ɗakin ta ne, Yaya kullum cikin nasiha take da nuna masu halin da suka tsira bai da kyau, mata ne su gidan wasu zasu amman inaa.. Duk wanda yayi nisa baya jin kira”
Nice ta fari a gurin Umma dan haka ban samu kulawar ta ba ko kaɗan dan ni sai da na yi wayo nake yarda da cewar Umma ce ta haifeni amman sam ni bana yarda a tunani na Inno ce ta haifeni dan ma Inno tana yi mani yaƙi a gurin Umma tana amsar mani abu koda rabo ne na cikin gidan idan Umma tayi rabo, to nawa sai dai Yaya ta ɗaukar mani ko Inno amman ita bata cewa ga nawa, Umma bafulatana ce, kunya ne da ita ba ta wasa ba, kasan cewar bana samun kulawar ta ne Baban mu, ya maida ni ɗakin Inno.
A cikin gidan mu nice, wadda Allah ya ɗora soyayya ta a cikin zuciyar mahaifin mu, komai ya samu Narjeesah baya son gani na a ciki damuwa koda kuwa kaɗan ne, bawai yana fifita ni bane aa dai duk abunda ya samu nice zai kira na kaiwa duk wadda take aiki, gashi na taso da masifa ga faɗa sam bana yarda acuce ni, idan aka kaiwa Umma ƙarata, bata kula mutum sai dai mutum ya gaji da tsayin sa yayi gaba, sai da mutane suka fahimci cewar Inno ce, inna ta, kawai sai suka daina kaiwa kashe dina, idan Baban mu yana nan sai dai ya bada haƙuri ya ce, na daina ba kyau.
Baban mu ya Auradda da manyan mu, su Anty Basira su ukku har sun haifu daga mai biyu sai mai ukku, sai maganar Auradda su Anty Shamsiyya da Zuwairah da Hanan wanda suka bani shekaru biyar, wato shekarar su ashin ni kuwa sha huɗu ke gareni ke nan.
Wata ranar laraba ce, Baban mu zai tafi kasuwan cin sa, a ranar na tashi bani da lafiya, duk bana jin daɗi kuma ban san abunda yake damuna ba, yau rakiyar Baban mu naji ina son yi haka nabi sa harda su yaya Auwal wato babban Yayan mu na ɗakin Inno.
Tun da muka isa tasha Baban ne yaja hannu na gefe yake tambayar mike damu na nace, masa babu komai kawai dai ban san abunda yake yi mani ciwo ba, kuma ni jin nakeyi bani da lafiya.
Ya ce, “Allah sarki Narjeesha ki yi hakuri halin Umman ki nata ne, ba aro tayi ba, ki rage damuwa da abunda takeyi maki na rashin kulawa wata rana zata sauya, kuma ki sani sirrin ki naki ne kada ki yarda ki sanar da wani abunda yake damun ki ko ya sameki, ko waye kada yasani, indai ba wadda ta haifeki ba, taso jin damuwar ki, kada ki faɗa kiyi ƙoƙarin ganin mahaifin ki ta janyo ki a jikin ta, kuma ina son ko miye ta fara sanin sa kafin kowa ya sani, dan uwa itace Babbar masoyiyar mutum ta nan duniya, saboda haka kije kiyi ƙoƙarin ganin ta saurari kukan ki, ko ba a yan zan ba”.