
Ni kam saboda ƙuruciya ta, sam ban wani fahimci komai ba, daga cikin maganar sa, addu’a kawai nakeyi masa ta Allah ya kai shi lafiya ya dawo dashi lafiya, haka su Yaya Auwal addu’a ce, sukayi masa, muna tsaye har motar su ta tashi ta tafi, sannan muka dawo gida, zuwa marece, su Yaya Auwal suka dawo, cikin tashin hankalin ni kuwa dama ina kwance bani da lafiya jikina rawa, yakeyi har sai da Inno tayi marufa, Yaya ce ta kira ta ta fito kowa yana tambayar lafiya, kawu Bala ne ya shigo shima cikin tashin hankali, ya ce, “sai haƙuri Malam Isah sun sami hatsarin mota, motar da suke ciki babu wanda ya fita, sun ƙone ƙurumus! “.
Faduwa wasu daga cikin mu sukayi atake gidan ya kacame da kuka, ni kam fito wa nayi ana biyar layi ɗaya bayan ɗaya, na ce, sam wannan maganar ba gaskiya bane, ni ban yarda ba, ruɗewa nayi kamar wata mahaukaciya, somewa nayi, ban sake sanin kaina inda yake ba sai da safe.
Tunda na tabbatar da cewar gaskiya ne, Baban mu ya mutu shike nan nadawo kurma bana magana bana cin abinci kullum cikin kuka sai da aka haɗani da addu’a aka samu nadawo dai_dai tun daga wannan ranar ne Mama ta fara rigimar gado itada su kawu dasu goggo, amman saboda babu wanda ya goyi bayan hakan sai aka bar maganar.
Tunda muka koma makaranta daman burina bai wuce nayi karatu mai zurfi ba, boko da islamiyya har na ce sai nayi aiki saboda karatu, shi yasa bana fashin zuwa makaranta, gidan mu da unguwar mu sai suyi ta dariya wai sai sun ga yanda zan yi karatun mai zurfin tukun, ni kuwa sai nayi ta masifa, amman makarantar islamiyya idan ban haddace karatuna ba, malam Nura ne ke zuwa ya saka ni gaba, sai naje makarantar, idan ba haka ba bana zuwa.
A lokacin da nake shirin shiga jss 3 ne na haɗu da wannan iftala’in tare muka tafi makaranta nida su Hanan wanda suke ss2 a lokacin shikerata sha biyar ne, sai da muka gama jarabawar mu, muka fito misalin ƙarfe biyu da rabi na rana, bani mance wa munyi jarabawar Maths ne duk mun gala baita, ajin mu shine na ƙarshe da fitowa, na fito ina tafiya ni ɗaya a bakin titi duk nagaji yunwa nakeji kawai na zo zan raɓa wasu motoci da suke a gefen titin saboda idan nabi ta gaban motocin zan hau titin ne kuma mashin zai iya bigeni ko mota ko keke, gashi yau sam hankali na ba kwance yake ba.
Na wuce mota biyu lafiya lau nazo a mota ta, ukku, kawai aka kamani aka jefani cikin mota baƙa itace ta ukkun, rufewa kawai akayi a kaja motor da ƙarfin gaske, ihu na zun duma, kafin na rufe baki har an watsa mani wata, powder a take naji garin na juya mani, zuwa can sai bacci ya ɗauke ni.
Ban tashi falkawa ba sai a wani gurin, tare da wasu mutane manya_manya,
Wasu kuma malamai ne dan naga littafai ne a gaban su suna karatu, da sauri na tashi zaune ina dube_dube,
Nidai ganin nakeyi ba’a gidan mu nake ba, wasu matane suka zo inda nake, da sauri naja da baya sai ji nayi antaro ni ta baya, da sauri na juya na ɗaga kaina wata matar ce, zata kai sa’an Inno, da sauri na dun ƙule jiki na guri ɗaya, wannan matan ne suka riƙoni sai cikin wani ɗakin a gaban wasu limamai ina jin sun fara magana,
Sai naji sam wannan ba hausa irin tamu bace, dan hausar su bata fita kamar Umma na.
Mutumen yace, “yarinya kiyi hakuri ki anshi jarabawar ki, idan kina son ki tsira da mutumcin ki to ki yarda a ɗaura maki Aure a yanzun idan kuma bakya son wannan Auren anshrya maida ke karuwa, to ni kuma mutumen daya turo nu yace, kiyi hakuri ki anshi wannan Auren dan kuwa mukam mu sai da mukayi istahara akan Auren kuma munga babu wata illa idan kin yarda da ƙaddarar Allah to ki ashi Auren nan da hannu biyu “.
Kallon sa nayi na ce, “bawan Allah kadubi girma Allah ka tausaya mani ni marainiya ce kuna ƙaramar yarinya ce!”
Murmushi mutanen ya yi yace, “shekarun ki nawa ne yan zun? “.
Da sauri nace, “sha biyar”.
Ya ce, “shin kin mance, cewar NANA Aisha yardar Allah ta tabbata a gareta, shekara nawa akayi mata Aure? Shin ke nan ke a yanzun uwa ce ko? To kiyi hakuri ki ɗauki Auren nan kada ki bari ayi zina dake”.
Kalamai masu shiga jiki akayi mani, dole na yarda na amshi sadakin dubu sittin aka ɗaura Auren wanda nake jin kamar wuta aka ɗaura mani a jiki tashi sukayi bayan sun gama saka mani albarka da adduar kariyar Allah da wasu ruwan addu’a da suka bani, nasha ina kuka, suka fita, wasu matan ne suka kawo mani wani abun kamar zuma da kuka na nake sha saboda muguwar yunwar da nakeji ga tsoro ta ko ina, bacci ne ta ɗauke ni ban sake sanin inda kaina yake ba.
A cikin wani ɗaki mai duhun gaske na tsinci kaina, hannuwa na a ɗaure haka ido na da baki na, na rasa ya ya numfashi na zai iya fita a sauƙaƙe.
Jin motsi nayi a kusa dani, a take nayi yun ƙurin guduwa, kawai naji an janye mani ƙafa, na faɗi ƙasa Ashe akan katifa ne, ƙafa ta aka raba biyu, aka ɗaure a wani gurin da ban san miye ba, sai kawai naji saukar mutum a jiki na, Ashe ma ko kayan jiki na an cire, hannu na duk suna a ɗaure haka nayi ta dukan mutumen amman ina koda ba a ɗaure nake ba ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya ba, kawai ya afka mani.
Tabbas wannan itace baƙar rana a gareni yau nice akayi wa fyde tabbas babu wani bam banci wannan fyde ne! .
Sai da na kusa sumewa aka ƙyaleni, zuciya ta naji tana batun bugawa, naji duniyar ta isheni naji na tsani kaina da kowa ma na cikin duniyar nan!.
Bayan wani lokacin haka aka sake afka mani, haka dai nayi ta kukan zuci wanda yafi wuta zafi, da ƙuna, bayan kamar wani lokacin sai naji an fita, kuma an dawo, sautin murya naji, kamar haka:-
“Yarinya badan mace ɗaya bace, tsari na ba dana, ajiye ki koda a wani guri ne, kodan wannan abun da nayi maki, amman yanzun ga kuɗi nan, masu yawa ki nemi lafiyar ki, kuma kije ayi maki wankin mara, bana bu’katar ganin fuskar ki, kema ba zaki ga tawa fuskar ba, kisani nayi maki nisa, har abada, kuma bazan sake ki ba, kije kawai haka nan dan ni bana iya sakin mace, idan lokacin da mace takeyi, ya kai zaki iya neman wanda zai rabaki da Aure na, koda yake baki san sun nan mijin ba, zaki iya samun duk sunan da kika fi tsana a duniyar nan, kice shine mijin ki, sai a taimaka maki amman kafin ki nadawo zaki iya aikata hakan idan kuma Allah yasa nadawo cikin rayuwar ki, tofa babu wannan zan cen ya roshe,
Ga sabuwar waya nan nasan baki da ita dan na lura kuruciya na damun ki, kasan cewar ki mai tarbiya yasa har na kusan ceki, duk da banga fuskar ki ba, nasan baki son rasa wannan darajar taki, shi yasa kika tsaya baki damu da wata duniyar ba da ruɗin duniya, yanzun kije na baki wayar nan, da ƙuɗi gasu nan a cikin ƙaramin akwati sannan kuma harda wannan gidan duk sun zama mallakin ki da motoci guda biyu dake cikin gidan nan ke da duk wani abunda yake gidan nan.
Na baki dan kiyi jinyar jikin ki, duk da kin iya boye mani budurcin ki, ni mijin ki kawai nasan sirrin ki, duk da baya a gaba na.
Ni ma sakani akayi ina tare da security masu duba ko na cika aiki na ne?,
Babu wanda yasan da cewar wannan gidan nawa ne, amman ke haka kawai, naji na baki shi a kyauta.
Kuɗin nan kuma nasan zasuyi maki amfani, zan buɗ maki baki, kiyi magana nasan kina da buƙatar ki zageni, kuma idan kika sake kikayi mani mugun zagi him! “.
Allah Allah nakeyi ya buɗe mani baki, dan yanda zuciya, ta take ingiza ni jin nakeyi kamar na haɗe zuciya, na mutu.