
Hannun sa ya saka ya bud’e mani baki, ai kuwa abunda na fara faɗa shine, Allah ya isa na mugu azzalumi, kuma kamar yanda ka batawa marainiya budurcin ta, Allah yasa wannan abun ya hanaka jin daɗin rayuwa, Allah ya isa na, kuma wallahi na tsaneka na tsani duk wani abunda yake naka ne, ka ɗauki tsiyar ka, bana buƙatar komai naka, nagode wa Allah da yasa banga wannan mummunar fuskar taka ba, azzalumi kawai”.
Ya ce, “ya Isah haka! idan kika sake zagi na, sai na ƙara maki abunda nayi maki, koma fiye”.
Na ce, “azzalumi kawai, mai cutar karamar yarinya wadda take da buri masu yawan gaske inyi karatu inyi aiki inyi kuɗi masu yawa na ginawa Umma gida da Inno da Yaya banda Mama dan na rama abun da take yi mani na rowa da hassada”.
Naji yayi yace, “ko yanzun ma zaki iya cika burikan naki, duka tunda ba kashe ki nayi ba”.
Da ƙarfi nace, “Allah ya isa na!, ka ruguza mani komai amman sai na rama wallahi ko ba yau ba, na murguda masa baki duk da kuwa kasan cewar baki”.
Fita kawai naji anyi, ina ɗaga hannun na naji, a kwance harda ƙafa ta, hannu na saka na yaye abunda aka rufe mani fuskar ddashi, sai da na runtse idon, saboda haske.
Ina duba jikin na, na fashe da kuka na janyo dan kwalin da na gani gefe na rufe jikin na dashi.
Kuka kawai nakeyi da takaicin yanda naga, jikin na, Ashe bani da komai a jikin na, kuma glub kunne haske ta ko ina.
Allah ya isa kawai nake ja masa, na ɗauki alwashin sai na rama.
Tashi nayi daket da jan ƙafa ina cije baki, na shiga gurin da naga an rubuta toilet na duba banga bokitin wanka ba, sai bahon wanka, tunowa nayi da wani siries din film a take nakoyi komai nayo wanka na fito,
Sallah nayi ban ma san adadin sallar da banyi ba, nidai nayi ta kwana biyu, abinci naga an ajiye mani, naci, nadawo tunanin abunda zan sama a gida idan na koma gida, bacci ne ya ɗauke ni, ina tashi da zazzaɓi na tashi, naje nayo wanka haka dai na kasan ce har tsayin kwana biyu ni ɗaya ina jin na sami sauƙi na fito sanye da kayan jiki na, ƙasa na sauka na falon gidan na kalla har kichin naje bayan na fito ne, na kashe komai na gidan mai aiki da wuta, makullai kawai na ɗauka da nagani a cikin wani ɗan akwatin ƙarfe, na fito gidan na rufe a harabar gidan, motoci biyu na gani na buɗe get ɗin na rufe naje na binne akwatin na ɗora dutsi natashi na fara dube_dube gabas kudu yamma arewa ina tunanin ina ne hanyar gidan mu?.
Kawai na saka kai ina tafiya ina wai wayen gidan dana fito, a gurin bushiyar lemon tsami, na tsaya ina futawa na ƙara ɗaukar hanya ke nan, wata motar tazo taja wani wawan burki a gaba na, kafin na gudu han an turani cikin motar an shaƙa mani wani abun bacci ya kamani ban tahi falkawa ba, sai a cikin ɗakin Inno.
Ɗakin naji yana juya mani, na dafe kaina, da ƙarfin gaske, Inno da Yaya ne keta tofa mani addu’a, har nadawo cikin hayyacina, kuka na fashe dashi dan nasan, asiri na ya tonu, Kuka kawai nakeyi, tambayar duniya sunyi mani nace masu babu komai, kuma ni ban san komai ba.
Kyaleni sukayi, koda na fito tsakar gida cewa akeyi yawo na naje, nadawo, tun ina damuwa har na daina damuwa, ranar na tambayi Inno yaushe ne nadawo gida, shine take bani labarin anyi nema na ba dare ba rana duk ba a ganni ba, har kwana bakwai nikam tsoro ne ya ƙara kamani, kuma da aka tashi gani na a cikin layin mu ka tsince ni bana cikin hayyaci na har sai da na kwana ɗaya a gidan na falka.
Nan ma Inno tayi tambayar duniya amman nace mata nima ban sani ba, bayan wata biyu ciwo ya kamani ni har ma na manta da abunda ya faru dani saboda hauka irin tawa, na ɗauka cewar komai ya wuce ashe matsala babba na nan, ciwo nakeyi kamar zan mutu, Mama ta ce, ” da alama dafuwar ta nuna, ciki ya bayyana idan ba a yarda ba aje asibiti ayi awo ai kuwa cikin satin akaje asibiti rest din farko ciki wata biyu, aikuwa ƙarya tawa nayi, abu kamar wasa ƙaramar magana sai ta zama babba, duk inda akaje ciki wata biyu wasu harda sati ɗaya suke faɗa.
Tabbas na shiga cikin matsanan cin damuwa da tashin hankali, na rasa ya ya zanyi da rayuwa ta ne inji daɗi, kullum cikin kuka nake tun daga wannan ranar ne, Mama da iyalan ta da yaran Yaya su biyu suke zagi na aka bi duniya dani, kawu kuwa dasu goggo cewa sukayi babu wanda zai haifa masu shege a cikin dan gin su, itama Umma kawun ta da matar sa sun zo sunyi rashin mutuci, harda su cewa a zubar da cikin aikuwa su Mama dasu kawu suka dage sai an zubar dashi, ni kuwa tunowa da nayi cewar fa wannan cikin ba shege bane da uban sa duk da ban san waye uban nasa ba, to wallahi ba zan yarda ba.
Aka kaɗa aka raya naƙi yarda su yaya Halilu harda dukan tsiya sukayi mani amman naƙi yarda shine suka ce, zasu barni amman nasani duk ranar dana haihu to sai nabar masu gida Inno kuwa tace, babu inda zani ai gidan uba nane dan haka ciki itama bata yarda a zubar dashi ba, rigima sosai akayi a gurin.
Tun daga wannan ranar ne na daina shakkar a zageni mutum na zagi na sai na sakar masa magana, su yaya kawai nake tsoro, aiki kuwa ina shan sa hardai Mama wadda take bani aikin wahala kuma ina yin sa, gashi duk abunda ta dafa duk yan da nake son abun nan bata bani, kuma nikam bana ma biye wa abinta saboda bana son gori dan tace ita bazata iya bani abunta ba, saboda ita ba zata iya ciyar da shege ba, da uwar shege, a ranar dana haihu kuwa a ranar aka koremu, wai anyi rabon gado bamu da gado cikin gidan sai gona, wadda aka siyar aka bamu dubu ɗari biyu da saba’in”
Kallon su Umma nayi dasu Jafar nayi murmushi wanda yafi kuka ciwo na ce, “Umma kinji yanda akayi wallahi ni ban san fuskar sa ba, muryar sa kawai na sani koshi dan munyi musayar magana ne! “
Hawaye masu zafi nake sharewa.
Umma dai shiru tayi cike da mamaki tace, “ki sani baiwa ina shareki bane, wallahi ko bacci banayi saboda ke, kullum na kwanta da tunanen wane hali kike ciki nake kwana nake tashi, kuma ganin ki ɗakin Inno duk da kasan cewar tana sonki ina kula da yanayin da kike ciki, rashin kunyar miye zan nuna dan an taɓaki ai duk wanda ya nuna yafika son ɗanka to kai yake so, mahaifin ki yana kula da tarbiyyar ki, haka Inno to ni kuma saboda rashin godiyar Allah kulawar miye kike so nabaki eye! ? Itafa duniya kaƙi naka duniya taso shi kaso naka duniya taƙishi, dan haka ni ina godiya da kulawar da kike samu, a gurin wannan mutanen.
Kuma ko a gidan mu haka na taso Mama na ko kallon inda nake batayi saboda alkunya, amman mutane suna kula dani sosai dan haka ni ba ƙin ki nakeyi ba ina son ki, kuma daga yau ina son duk abunda yake damun ki, kizo ki sanar dani, saboda alfarmar da mahaifin ki yayi ta nema a kanki kuma nima yan zun na gane sakaci na ne da rashin kulawa dake yasaka wasu abubuwan suka faru dake da kuma ƙaddarar rayuwar ki”.
Duk shiru mukayi muna sauraren Umma har ta gama maganar tayi shiru sai hawaye nake sharewa.
Murmushi Amrah tayi tace, “Yaya Jafar Yaya Aliyu Anty Hindu Anty Humaira, zan ƙarasa maku labarin nan ta labarta masu komai har zuwa yau ɗin nan, cike suke da al’ajab.
Aliyu ya ce, “to ke nan Narjeesah matar Salman ce ko? kuma Maman Shuraim ko? “.
Ɗaure fuska nayi nace, “ni kotu zan kai shi ko kuma ya bani takarda ta, kuma duk da haka sai an bi mani haƙƙina! “.