NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Jafar ne ya ce, “Narjeesah Salman mutumen kwarai ne, amman duk da haka akwai gagarumar matsala! “.

Kowa faɗar, ” Matsala! Matsala!! Matsala!!! Kuma? in banda Aliyu, dan da alama yadan komai.

Jafar ne ya sharce zufar da ta zubo masa yayi yace, “eh matsala babba ma kuwa dan baku san waye Salman ba, amman yan zun zaku sani, keda kike cewar zakiyi ƙarar sa ki saurara da kyau kiji wane ne Salman da har kike takun saƙa dashi, ke da kanki zaki baiwa kanki amsa”.

Salman……..

Comment And share

UMMU Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????????????

???????? NARJEESAH ????????

Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN

ELEGANT ONLINE WRITERS

Alhamdulillah Am back

Bismillahir Rahmanin Rahim

           2⃣1⃣⏮2⃣5⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Salma Muhammad Yunus, ɗane a gurin Alhaji muhammad Yunus ɗan gidan Mai martaba, Yunus, mahaifin Salman bayan kasan cewar sa ɗan Sarki tofa shi jakadan nageria ne a ƙasar london, a can aka haifi Salman amman mahaifin sa yana nan nageria, kuma mahaifin Salman yake jira ya zo ya anshi sarautar sa dan shine ake so a masarautar shi kuma yace baya buƙatar sarauta sai dai a baiwa Salman shima Salman ya ce, baya so sam, to har yanzun rigimar da akeyi ke nan.

Salman ɗan gata ne gaba da baya, mahaifiyar sa, Hajiya Lamrat “yar gidan sarauta ce, ita kuma babbar masarauta a can london ɗin aka Auro ta, shi yasa Salman baya son zuwa nageria sai da Mai martaba ya nuna ɓacin ransa akan rashin zuwan Salman gurin sa, sannan iyayen suka shiryo suka zo, Salman yanada ƙanwa Salma da Autan su Muhseen, wannan zuwan nasu a nageria shine na farko a tarihin rayuwar su, Salman da ƙannen sa.

Tunda Salman yazo nageria sam baya da farin ciki shida ƙannen sa, suka takurawa iyayen su akan su zasu koma koda ba tare da iyayen su bane, amman Mai martaba, yace shi bai san zan cen ba, sai dai iyayen su koma, abakin aikin su abar masa yaran nan sai sun saba zama tare dasu, a take duk suka a za rigimar sam su basu yarda ba, an wani zo an takura masu, jin furucin su Salman ne ya ƙara har zuƙa mai martaba inda ran sa yayi munmunan ɓaci, a take ya baiwa mahaifin su umarnin bai son ya sake kwana ƙasar nan, yau_yau ɗin nan yake da wannan ɓukatar, iyayen su Salman badan sun soba, dole sukabi umarnin Mai martaba suka tafi a ranar.

Tunda iyayen su Salman suka bar su, shike nan suka rufe kan su a cikin ɗaki basu basu sha, kai sam basa ma fitowa, har sai da Mai martaba da kan sa yaje yana dukan ƙofar tasu akan su fito zaiyi magana dasu amman kamar bada su yake ba.

Fruit, ɗin dake cikin ɗakin shi sukeci, da swan saboda sam basu iya cin abincin yan nageria ba, dan haka su basu jin komai sai kewar iyayen su da mahaifar su, sai da Mai martaba ya saka aka ɓalle masa ƙofar ya shiga cikin ɗakin shida matan sa, da ƙannen mahaifin su, Salman, a zaune suka samesu kowa ne su ya yi uban tagumi, kowa da ƙana nan kaya harda Salma ita da take mace a cikin su, kuma a lokacin tana da shekara goma sha bakwai ne, shiyasa hankalin su yaƙara tashi, su Mai martaba a tsaye suke akan su, amman sunyi kamar basu san da zuwan su ba.

Mai martaba ganin yayi idan ya cika matsa masu tofa abin caɓe masa zaiyi, kawai sai ya zauna a kusa da Salman ya dafasa, a lokacin shi kuma Salman ya yi niyar tashi yabar gurin amman kuma ƙwar jinin Mai martaba sai ya hana shi aikata hakan amman bai kallesa ba, kallon su Salma da Muhseen yayi yaga duk sun juya masu baya kawai, ya yi dariya ya ce, “haba ku kuwa miye nayin fushi dan naso ganin ku a tare dani? Ashe laifine, dan na ce ina son na sabu da jikoki na? To kuyi hakuri dama sati ukku kawai nake son kuyi a nan sai ku koma ƙasar ku inda kuka saba, amman yan zun na janye wannan maganar idan naga duk kun saki jikin ku damu duka zan baku damar tafi, can ku futa inda ba’a takura maku kamar ni”.

Duk jikin su sanyi ya yi, ganin haka ne sai ya baiwa fulani damar taje gurin su Salma ta fito dasu shi zai fito da Salman, da ido yayi mata nuni a take ta fahimci maganar sa, kawai ta riƙa hannun Salma da Muhseen suka tashi suka bi bayan ta shi kuma Mai martaba ya riƙo Salman suka fito a falon sa ya zaunar dasu, ita kuwa fulani gyale ne ta yafawa Salma a jiki ganin yanda shigar ta, duk ta fito da tsiraicin ta, Salma duk taji wannan mayafin ya ƙara takura mata kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikin Salman, a take ya rungume ta ya doddoka bayan ta, alamar rarrashi, haka Muhseen shima lallashin ta yakeyi har yana share mata hawayen idon ta, duk sai suka ƙara shiga cikin damuwa.

Mai martaba tashi ya yi cikin fushi ya kira ɗansa, a waya yafara yi masa masifar yabar yara sun lalace, shi ba zai ɗauki wannan sakarcin ba, dole sai ya gyara masu tarbiya ko yana barin su, su koma gurin su, hakuri yake baiwa mahaifin nasa, Amman Mai martaba baima saurare sa ba ya kashe wayar, ya saka aka kawo masu abinci, aikuwa ko kallon abinci basuyi ba, sai kowa ya tafi ya basu guri bisa ga umarnin Mai martaba.

Mahaifin sune ya kira su video coll ai kuwa suk suka sakar masa kuka, Salman ya ce, “wallahi Dad yau gudowa zamuyi wannan wane irin mutane ne wanda basu san “yancin ɗan adam ba, gaskiya nikam na gaji Salma ku tashi ku shirya yau zamu bar wannan baƙar ƙasar”.

Tsawa Dad ɗin su ya sakar masu wanda har sai da suka zabura suka saki wayar wannan shine karon farko da hakan ta taɓa faruwa dasu, duk duka koma jikin Salman suka shige, suka bar wayar a gurin, mahaifin nasune yaci gaba da faɗar, “taya zaku zagi ƙasata ƙasar da aka haife ni, da ku a tunanin ku bana son ƙasata ne nake zaune a ƙasar wasu can, to ku sa ni nima zaman dole ne nakeyi anan ɗin kuma dolene ku zauna anan ku saki jikin ku da iyayena da yan uwana da dangi na, kuma ni kaina wannan lokacin na ajiye masu aikin su nima nawo gida, idan yaso sai kuci gaba da zagin ƙasar taku dan kuma kuna da alaƙa da ita tunda nida na haifeku, a nan aka haife ni, dan haka dolene ku saba kuma kubi umarnin mahaifina!! “.

Kawai ya kashe wayar, ganin wannan abun sukeyi kamar a film, a take Salma tace, “bros ba zamu zauna anan ba kuma gashi an sauyawa Dad tunanin sa ya daina son mu nikam zan koma gamany ne idan yaso duk sanda suka dawo da son mu su nemen! “.

Shima Muhseen wanda yake biwa Salma ɗan shekara goma sha huɗu, yace, “, zan koma school ɗina ne, ba zan je gurin su Dad ba dan haka tare zamu tafi “.

Murmushi Salman yayi yace, “da dare zamuyi wannan tafiyar “.

Aikuwa sai da dare ya tsala kowa yayi bacci, masu tsarin gidan ne kawai suke ido biyu, Salman Salma Muhseen duk suka ja jakar su, suka fito ko tsoro babu, kawai suka sa kai batare da sun kalli mutum ɗaya ba daga cikin masu gadin gidan har sun isa bakin ƙofar fita sun fara farin ciki harda tafawa, kawai Salman yayi turus haka su Salma da Muhseen suka zubawa ƙofar ido.

Ƙarasowa yayi inda suke ba tare da yace dasu uffan ba kawai yaja hannun su ya ƙarasa fita dasu a cikin wata mota aka ɓude masa ya saka su a ciki shima ya shiga daga ciki aka rufe, yaye mayafin fuskar sa yayi, atake suka haɗa baki gurin faɗar, “grandpa!! “.

Murmushi kawai yayi masu ya bada umarnin tafiya, aka ja motar, sai tafiya sukeyi, cikin wata unguwar da wasu mutane duk a waje suke kwana, saboda gida jen su duk sun rishe, wasu zane ne suka ɗaura suka killace, parking akayi a hankali ya sauka daga cikin motar ya fara jawo hannun Salma da take ita ce a kusa dashi, sai kuma yaja hannun Salman da Muhseen, duk suka fito suna dube_dube gashi dare ne unguwar sai ɗoyin kwata ke tashi, bayan motar aka buɗe aka riƙa sauke kwalayen taliya indomie shinkafa irin buhun nan masu ɗaukar kwano huɗu, ƙanan jarkar manja man gyaɗa magi gishi, sai amblant, layi Mai martaba yake bi yana ajiye masu kayan a gaban su tare da amblant ɗin, su Salman kuwa cike suke da mamaki, wata mata ce ana ajiye mata kayan zasu tashi da sauri ta riƙewa Mai martaba ƙafa, ta fashe da kuka, Mai ne ya ɗuƙa yace, “mike faruwa ne daga ganin wannan kukan kin daɗe kina yin sa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button