NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Tashi zaune tayi tace, “dan muna talakawa shine aka maida mu bayi babu mai kulawa da halin da muke ciki, maru nd gareni mata biyu dan rashin imani anzo an ɗauke mani su duka duk anyo masu ciki, ɗayar gurin haihuwa ta haɗu da lalurar yoyon fitsari kuma, mutanen ya ce, ba zai iya ɗaukar nera ya bamu ba mu nema mata magani ba, kuma bamuda wanda ya isa ya kamasa da laifin cikin da yayi mata kuma ya saka ɗan sa ya ɗauke ƙaramar itama yan zun haka tana ɗauke da cikin ɗan sa, munje police, an koro mu, to shine “yar tawa tace zata kashe kanta, nikuma na hane ta da aikata hakan shine suka gudu suka barni, wai basu kashe ni da baƙin cikin suba! “.

A take jikin kowa yayi sanyi a gurin, Salman ya ce, baku da human right ne a ƙasar nan? “.

Shiru Mai martaba ya yi kukan tsohowar na damun su, Salma tace, “yaran naki kin san inda suka tafi ne?”.

Kai ta gyaɗa masu ta ce, “ance mani an gansu, amman na kasa zuwa inda suke gudun kada su bar gurin “.

Salman ya ce, “zamu zo da safe amman kiyi shiru da bakin ki”.
Tashi sukayi suka ƙara sa gaba, haka sukayi ta cin karo da masu matsala, matsalar wani dattijo ta ƙara sanyaya masu gwiwa, saboda yaran sa ukku biyu maza ɗaya mace, ne gobe za’a yanke masu hukuncin kisa, saboda sun sace wa Mai gidan da suke yiwa aiki maƙudan kuɗade, a take hankali kowa ya tash.

Muhseen ne ya ce, kuma an tabbar da sune suka aikata hakan? “

Dattijon ya ce, “harda shedu suna su wanda suka ce, sun gane su da idon su suna aikata hakan, kunga kuwa ni babu abunda zan iya faɗa duk wanda mukaje gurin sa ya taimaka muna sai ya ce, shi sam baya iyawa, wani mane yace, zai taimaka muna amman sai mun bashi miliyan ɗaya, ni kuwa ko abincin da zamuci wahala yake yi muna nida mata ta da ƙana nan yara na, wani kuma ya ce,zai taimaka muna ashe ƙarya yakeyi, wannan mutanen ya turo shi, muna zuwa kotu, yace shi ba lauyan mu bane lauyan mutumen ne! “.

Tashi tsaye sukayi Salman ya ce, “zamu zo da safe insha Allah “.
Gida suka koma har ɗakin da suka baro Mai martaba ya raka su,suna shiga suka rufe ƙofar, suka kunna glub, duk suka zazzauna a ranar basuyi bacci ba, tun da asuba Salman da Muhseen suka nufi masallacin gidan kowa ya gan su a wannan nan lokacin sai yayi mamakin hakan amman su basa kula kowa har akayi sallah sai da safe suka fito bayan sunyi azkar”.

Darect gurin Mai martaba suka nufa a cikin falon gidan inda kowa yake kawo masa gaisuwa, kowa ka gani cike yake da mamakin ganin Salman da Muhseen, Mai martaba suka nufa suka rungume sa, suka sumbace shi, zasu juya ne ya janyo su jikin sa, shima yayi masu yanda sukayi masa, yace, “Allah ya yi maku albarka “.

Amin kowa ya ce cike da farin ciki, Salma ce ta fito itama da shagar ta ta ƙananan kaya amman wannan da ɗan damar su, ta zo ta rungumi Mai martaba ta sumbace shi, shima ya ce, “Allah ya yi maki albarka “.

Ta dawo gurin su Salman suka rungume juna, suka sum baci juna, ta koma jikin fulani ta sumbace tayi kwance a jikin ta, zama su Salman sukayi ƙasa a kusa da ƙafar Mai martaba, bayan sun zauna ne, ƙanen mahaifin su wata, shattima ya ce, “Alhamdulillah abu ya yi kyau sannu a hankali komai zai tafi dai_dai “.

Duk sukayi dariya, abinci aka kawo kowa da abunda ya ke ci, Salman da Muhseen Salma suka tsare kowa da ido cike da burgewa, sai da fulani ta ce, “ku ba zakuci komai bane? “.

Salma ta ce, “yau fa duk azumi mukeyi yau Thursday kasan cewar Dad da Mom sunayi shi yasa duk mun saba a kowa ne Monday da Thursday “.

Jin jina kai Mai martaba ya yi haka fulani da murmushi ɗauke a fuskar ta, wata budurwa wadda suke sa’a ɗaya da Salma ta ce, “shike nan ma kuwa daman naji labarin Uncle duk abunda ya keyi yana kaman ce ceniya da Mai martaba, gashi kuwa yau mun fara sani muma dan haka fulani ba zaku sake yin wannan azumin bada ni ba “.

Dariya akayi masu, Salman da Muhseen Salma ne suka tashi suka shiga ɗakin su, kowa ya fito a gyare Salman da Muhseen duk sun yo shigar su irin ta cikakken turawa, sunyi stoking, sai duk suka burge kowa Salma kuwa doguwar riga ta saka har ƙasa amman ta sako gashin kanta a ƙafaɗar ta, babu ɗan kwali sai fula facing cap, da haka a hannun ta, irin ta ma aikata, haka su Salman suke, kallon su kawai akeyi.

Mai martaba ne ya tashi ya ce, “kuzo muje daga ciki”.

Murmushi kowa keyi da mamakin taya akayi Mai martaba ya shawo kan, wannan yan rigimar nasa, koda yake Mai martaba Allah ya yi masa baiwa wadda ba kowa ne yasan da hakan ba.

Ɗakin Mai martaba suka shiga anan ne shima ya shirya ya kira waya, ya yi magana sannan suka fito yana gaba suna biye dashi, fadar suka nufa, sai gaisuwa ake kwasa, kowa ya kalli, su Salman sai ya sake kallon su, motoci aka fito dasu, aka jera shiga sukayi su Mai martaba da tawa gar sa, su Salman suka shiga wata motar ta daban, suka ɗauki hanya, motocin Mai martaba hanyar su, daban suka ɗauka, haka su Salman, wani ƙayataccen gida suka nufa, suna yin parking suka zauna direban ne ya fito shida wani bafade da suke tare suka shiga, basu wani daɗe ba, suka fito sukayi masu iso.

Wannan dattijon ne da wannan tsohowar da wasu mutane su ukku a zaune saman kujera, hannu suka baiwa Salman da Muhseen Salma kuwa hannu ta ɗaga masu ta ce, “Hi”.

Gurin zama aka basu suka tattauna tare da sake yiwa wannan dattijon tambayoyi yana amsa masu, haka wannan tsohowar, magana suka sakeyi da wannan mutanen, sukayi basu hannu sukayi masu sallama suka fita daga cikin gidan mota suka shiga suka nufi wani gurin basu daɗe ba, suka ɗauki hanya sai wata unguwar, a bakin wani gidan suka faka motar, bafaden ne ya fito yayi sallama aka amsa mashi mai gidan ne ya fito bayani yayi masa tare yake da baƙi mutumen ya ce, “nasan da zuwan su kace dasu si shigo”.

Tare suka fito suka shiga cikin gidan iso mai gidan ya yi masu har cikin ɗakin sa, wannan tsohowar ce, da wasu matasan mata zaune sai kuka suke wata mata tana gefen su, zama su Salman sukayi, suka fara yi masu tambayoyi suna amsawa, daga nan suka fito suka ɗauki hanya sai wata babbar kotu, suna isowa yayi dai_dai da mai shari’a yana yanke hukunci kamar haka:-ni alƙali Muktar na kotun mages tree na yanke wa wannan yaran Haruna Nuhu Musa Nuhu Saude Nuhu hukuncin.. Da sauri, Salman ya ce, “ya mai girma mai shari’a ayi hakuri da zuwan mu a makare suna na Salman Yunus muhammad, loya ne ni mai zaman kan sa, ina tare ne da loyan Human right daga hukumar human right ta duniya, mune wanda zamu Kate wannan mutanen da ake ƙara, takardu ya baiwa wani maga takardar kotu, a take ya ansa ya baiwa wasu suka duba aka baiwa alƙali ya duba, umarni ya basu da su ƙaraso ciki su zauna, zama sukayi si biyu, shi kuma Muhseen ya samu guri ya zauna.

Lauyoyin gurin duk haushin shigowar su Salman sukaji, mutumen da yake ƙarar su, jin yakeyi kamar ya tashi ya kashe su Salman, su kuwa bayin Allah kuka ne kawai sukeyi, mutane kuma masu kallo gyara zama sukayi dan kowa son yakeyi yau ayita ta ƙare, bayan Salman ya zauna shida Salma, alƙali ne ya baiwa Salman damar fara aikin sa, aikuwa Salman ya tashi tsaya, rigar lauyoyi ce ya saka, yaje gaban su Haruna ya kafe su da ido ya yi murmushi san nan ya ce, “Sunan ka muke son sani “.

Kallon Baban su da innar su sukayi ganin sukayi suna hawaye suna ɗaga masu kai, aikuwa ya ce, “Haruna Nuhu” kowa gurin cike yake da mamaki dan tun da aka fara shari’a dasu wannan zaman shine na biyar sai yau suka taɓa magana shi kanshi alƙalin sai da ya jin jina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button