NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Salman ya ce, “shakurun ka da aikin ka please”.

Amsa masa ya yi shekaru na ishirin da shida, ina yin wanko da guga ne a gidan Alhaji Ƙasimu, shekara ta ukku a gidan sa ina aiki”.

Murmushi Salman ya yi ya dawo gurin ɗaya ya tambayi sunan sa, sai ya ce, “Musa Nuhu shekara ta ishirin da ukku, ina aiki ne a gidan Alhaji Ƙasimu, nine wanda yake yi masa gyara da kula da fulawar sa, shekara ta biyu ina wannan aikin”.

Itama Saude ta amsa masa amman ita abinci ne kawai take dafa masu, shekara ta ishirin dai_dai”.

Salman ya duba alƙali da mutane ya ce, “ya mai girma mai shari’a ina son kotu ta bani dama nayi magana da Alhaji Ƙasim”

“Kotu ta baka dama” fitowa yayi yana tafe yana hura hanci ga uwar zufar dake zubar masa ta ko ina, yana tsayawa, Salman ya kafe sa da ido, ai kuwa duk ya daburce, murmushi Salman ya yi ya ce, “koto zata so sanin Sunan ka”

Kallon Salman ya yi, ya fara gyara babbar rigar sa, ya ce, “ba kotu ke ce ke son sanin sunana ba, kai ne kake son sanin suna na kaida ba ɗan nageria ba, su yan nageria ai sun san ko waye Alhaji Ƙasimu a ci dukiya! “.

Tun kafin Salman ya yi magana alƙali ya ce, “ina mai horon ka da ka guji kaucewa umarnin kotu nan kotu ce, ba gidan ka ba, dan haka dolene kayi biyayya ka yi duk abunda aka umurce ka idan ba haka ba akwai hukunci mai tsana nin da zai iya hawa kanka”.

Salman ya ce, “nagode ya mai girma mai shari’a” kallon sa ya mai da aka Alhaji Ƙasimu.
Shiru ya yi ya sharce zufa ya ce, Sunana Alhaji Ƙasimu aci dukiya shahararren mutum wanda ya tara dumbin duk… “.

Salman ya ce, “dakata malam iya Sunan ka kawai muke son ji, kuma munji shin da gaske ne kamar yanda suka faɗa shekarun da suka ɗauka a gidan ka, haka ne? “.

Cikin gadara ya ce, hakane kuma tun lokacin basu taɓa shiga can cikin gida na ba, saboda bana son sa ido, ehe!”.

Dariya mutane suka fara a ɓoye lauyoyin sane da sauri ɗaya ya tashi ya ce, ” ya mai girma mai shari’a taya lauyan wanda yake kare wanda ake ƙara yake daburta mai ƙara? “

Salman ya kafe sa da ido shima a take ya tsuke bakin sa, ya koma ya zauna yana goge zufa, alƙali ya ce, ai ba matsa masa akayi ba, kuma ba tukura masa akayi ba, tambaya ce yake amsawa dan haka ƙorafi bai ƙarbu ba, sai a ki yaye loya, Salman ya duba yace, ci gaba “

Murmushi Salman ya yi, ya ce, “nagode ya mai girma mai shari’a “.

Salman ya ce, “kace basa shiga cikin gidan ka, amman duk shekarun da sukayi a gidan ka antaɓa kamasu da wani laifin ne makaman cin sata? “.

A a yace, kuma ni har ma mantawa nakeyi dasu a gidan, sai da akayi mani wannan satar ne, nagane ashe su ɓarayi ne kuma ni ina da shedun da suka ga lokacin da suka fito da kuɗin suka gudu”.

Salman ya ce, “wato dai kai baka ga lokacin da suka fito da wannan maƙudan kuɗaden naka ba”.

Ya ce, “eh kai nifa nagaji da wannan tambayoyin naka ne shi yasa nake sanar da kai gaski, kuma lauyoyin dana ɗauka duk sun kasa bani taimako, to gaskiya tunda ba lahira muke ba, zan sanar dakai wanda suka gan su da idon su, Mai gadi na Lado sai yara na maza guda biyu Ashir da Yasir, sune suka sanar dani a lokacin da nake haukar neman kuɗin nawa”.

Kiran su aka ba Salman damar yi ya kuwa kira su, kallo ɗaya Salman ya yi masu, a take ya fahimci basu da gaskiya, Salman ya ce,”mai gadi kaine cikin ma’akatan gidan kaga lokacin da suka fita da kuɗin ko? “.

Tsuru_tsuru sukayi mai gadi sai soshe_soshe yakeyi, kowa ya kafesa da ido kawai ya fashe da kuka yace, “nidai ban ga lokacin da suka fita da kuɗin ba, kuma nima kashedi akayi mani akan nace sune, idan ban ce sune ba, kashe ni zasuyi, shine nazo nabada sheda suka bani kuɗi nera dubu hamsin ne suka bani, kuma wannan da muke tare sune suka fito da jakar kuɗin cikin dare kasan cewar ni ne mai gadin gidan dan haka ne, nima na gan su! “

Kuka yake, su kuwa tsuru_tsuru sukayi sai zarar ido sukayi, tambayar farko suka bada tabbacin sune suka saci kuɗin suka sayi mota suka ɓoye sauran kuɗin kuma sun kashe wasu, sun ɓoye wasu”.

Hamdala kowa yakeyi shi kuma Alhaji Ƙasimu aci dukiya mutuwar tsaye ya yi jin cewar yaran sane ɓarayin ba yaran wasu ba, dan haka mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege, sai yan zun yasan fassarar wannan karin maganar.

Salman ne ya kalli mai shari’a ya ce, ya Mai girma mai shari’a ina son kotu tayi dubo da aikin da wannan bayin Allah sukeyi a gidan wannan mutanen kamar yanda suka faɗa da yanda mai gidan ya faɗa da yanda shedu suka faɗa, duk da kasan cewar sheɗun sune suka aikata hakan, da wannan nake son kotu ta wanke bayin Allah nan nagode ya mai girma mai shari’a “.

Yana zama alƙali yayi rubuce_rubuce ya ce, ko akwai wani mai magana daga cikin lauyoyin ne? “
. shiru sukayi Salma ce ta tashi tsaye ta ce, “Suna na Salma Yunus muhammad nice lauyan da human right ta turo akan wannan ƙarar kasan cewar duk wani haƙƙi na ɗan adam muna da alƙa dashi, muna neman haƙƙin wannan bayin Allah da aka zalun ta, aka yi masu ƙazafi aka kai su gidan yari suka sha kunun gidan yari, da duka idan aka dubi yanda suka dawo ga tabon duka nan ta ko ina da wannan ne muke jan haƙƙin su a gurin mutanen da ya kawo su, wanda shine sanadiyar komai, nagode ya mai girma mai shari’a “

Zama Salma tayi kowa mamakin yakeyi yanda akayi su ba hausawa ba, amman suke jin hausa kamar mi sai dai hausar tasu bata hau bakin su ba, da kyau, dan suna yin magana zaka gane turawa ne, su.

A take alƙalu ya yanke hukunci ya ɗaure su, ya wanke bayin Allah nan ya nemeni haƙƙin su akan Alhaji Ƙasimu aci dukiya saboda shine ya ɗaure su, kuɗi akace ya basu kowa ɗubu ɗari da hamsin dubu ɗari huɗu da hamsin ke nan.

a take ya ce su bishi gida su ansa hannu da hannu.

Kotu ce ta tashi da sauri Salman yaje ya yanki wani sammacin aka baiwa yaron alƙali yaje ya kai, ya tafi, fito wa sukayi shida Salma suna riƙe da hannu juna, gurin Muhseen suka nufa da sauri ya rungume su yana yi masu barka da samun nasara akan wannan shari’ar, jikin motar su suka nufa anan ne lauyoyin suka zo suka basu hannu Salman ne kawai ya amsa Salma kuwa kai ta ɗage, fadawa ne suka zo kiran su, cike da mamaki kowa yake kallon yanda fadawa suke duƙawa suna gaishe su, tafiya sukayi gurin da mai martaba yake tare da tawa gar sa da wannan dattijon da iyalan sa, suna yi masa godiya duk wannan lauyoyin suna biye dasu, su Salman na zuwa aka basu guri kawai suka je suka rungume kakan nasu tare da sumbatar sa, nuna masu yayi masu godiya kawai Muhseen ya ce, “mu bama buƙatar godiyar ku kuje kuyi ta muna addu’a ita ce kawai muke buƙata”.

Hannu su Salman suka ɗaga masa, aikuwa sun sha addu’a haka suka tashi suka rafi, ɗan saƙon ne ya dawo tare da mutanen da akaje nema suna zuwa suka shiga chamber, anan ne aka sa santa suka ce sun yarda da cikin sune suka ɗauki nayin memawa ɗayar lafiyar ta, da kula da abunda ta haifa, itama ɗayar zasu kula da lafiyar ta da cikin ta har ta haihu tayi yaye dasa hannun kotu, kowa abun yayi masa, da daɗi, godiya da addu’a sun shata sosai.

Gida suka koma tun daga wannan ranar ne kullum cikin dare sai sunbi Mai martaba sun jiyo koken jama’a suna tsaya masu, cikin kwana ki ƙan ƙani sunan su ya baza gari kowa zuwa yakeyi da buƙatar taimakon su, suna taimawa, amman mai gaskiya kawai suke yiwa wannan idan kazo da rashin gaskiya yi sukeyi kamar basan da zuwan kaba, idan ka gaji dole ka tashi ka tafi, sai aka maida su garkuwar talakawa, Sunan su ya zaga ta ko ina, duk Nigeria an san dasu, anan ne mutane keyi ta kawo masu, gari mata da maza, yan mata kuwa kowa, Salman yake son Aure dan dai kawai babu damar ganin sane, samari da manyan mutane kuwa Salma suke son Aure amman sam basa kila kowa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button