NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Yaya tace, “Larai sai dai idan kece zakiyi wa Narjeesah rashin mutum ci tunda kin ga bata yi maki wani laifin ba, kika fara wannan maganar lallai ne Larai zuwa gaba kece zaki sauya zaman gidan nan! “

Haulatu ce “yar ɗakin Inno ta ce, “dan Allah dan Allah a daina maganar nan mu bama so wallahi ai ita ƙaddara tana akan kowa ko? “.

Da sauri Shamsiyya “yar ɗakin Mama tace, “ai dai ƙarya ce ake yiwa ƙaddara dan mutum inda baiyi niyar aikata hakan ba, da bai aikata ba, kuma mutum shine ya jawa kansa abun faɗa dan haka dole ne mu faɗa, cikin da ba’asan uban sa ba, gurin yawon lalata, aka janyo mugun abu mukam baza’a lalata muna gidan mu ba da mummunan iri ba, dolene asan abunyi, kuma in da Aure mutum yayi ai da yanzu mun fara shan jar miya, ni wallahi abun haushi ma, wai kamar Narjeesah “yar shekara goma biyar cikin ta sha shidda zata shiga, ace har ta iya lalata harda su guzurin ciki, muda muke yayun ta shekara biyar muka bata, amman bamuyi abunda tayi ba”.

Aunty Zuwaira yar ɗakin Yaya tace, “a gaskiya mukan an janyo muna rigima Narjeesah kin shafa muna kashin kaji, gashi har sai da Bilya yace, ya fasa Aure na, sai da nayi ta masa rantsuwa da alkawarin ban taɓa aikata irin haka ba, nasan dai yan zun ya haƙura kuma zai turo iyayen sa, su kawo lefe dan haka asan abunyi dan ni kam bazan “yarda da a hana ni Auren wanda na mutu a kan sa ba”.

Rigima ce dai suka saka wasu na goyon bayan Mama wasu kuma ni suke karewa, ajiye alalen nayi cikin jin ciwon abunda suke faɗa a kaina nace, “kowa sai faɗar albarka cin bakin sa yakeyi to wallahi nikam ku barni naji da abunda yake damuna, haba dan Allah shin dame zanji ne? Ko kuwa son kukeyi na haɗe zuciya ta na mutu haba! “

Daket na tashi tsaye nabar masu gurin suka bini da ido,Mama ce tace, “oho maki ai kodai miye ba mune muka janyo maki ba, baƙin halin kine ya janyo maki yau inda malam yana raye ai da kece zaki kashe, ya haɗiye zuciyar sa ya mutu, tunda ga saka makon da kikayi masa shi ya fifita ki akan kowa amman kinje kinyo cikin shege”.

Su Inno baro mata gurin sukayi, Yaya kuwa zagin Anty zuwarah take, tana faɗar albasa batayi halin ruwa ba, wallahi idan ta sake ai banta ni sai tayi mata abunda batayi tsammani ba, Ita kuwa sai cika take tana batsewa.

Umma ce na samu zaune inda nabar ta, tana zubar da hawaye ina ganin ta, tayi saurin gogewa, ta ɗauke idon ta, ni kuma sai nayi saurin shanye nawa kukan na zauna na fara karatun al, kur’ani mai girma dan na samu natsuwa, nida Umma na.

Haka muke rayuwa a gidan mu, idan na fito tsakiyar gidan sai an sakar mani magana, ko habaici, na sani sanadiyar ƙyalen su da nakeyi na wannan lalurar ne, dan haka bana yawan fita.

Wata rana daddare ina kwance can cikin barci na, naji kamar an tsun kuleni ai a zabure na tashi zaune, na yun ƙura in tashi tsaye kawai naji wani uban ciwo kamar zan mutu, addu’a na soma yi, Inno dake kwance a gadon ta na ƙarfe ta tashi zaune ta haska fitila tace, “ikon Allah Narjeesah abun ne ko? “

Da taimakon Inno da addu’a Allah ya sauke ni lafiya, duk wanda Allah ya baiwa ikon haihuwa lafiya farin ciki yakeyi da murna da godiya a gurin Allah maɗau kakin sarki, kuma duk wanda yaji wannan haihuwar farin ciki yakeyi da murna azo a ga jin jiri amman kash! wannan kam a guri na da “yan gidan mu abun baƙin ciki ne duk wanda yaji tofa sai ya zageni kuma a kira abunda na haifa da shege wanda sam ni ban ma san abunda na haifa ba mace ko na miji duk bani da masaniya akai.

Tun ƙarfe ukku da rabi na dare na haifu amman har garin Allah ya waye ban ɗauke abunda na haifa ba, haka zalika ban sa abunda na haifa a ido na ba, yana gurin Inno da Yaya sune suke kula dashi Umma da Mama basu zo sun duba lafiya ta ba da abunda na haifa ba, kan kace ƙwabo gidan mu mutane sai shigowa gulma sukeyi da tse gumi, Inno da Yaya mamakin ta yanda akayi mutane suka sani sukeyi.

Duk mutanen dake shigowa gidan basu sakani a idon su ba amman suna ganin abunda na haifa ni kuma ina kwance Inno ta shigo ta zauna a gefe na, tace, “Narjeesah tashi zaune zamuyi magana dake “.

A yanda naga yanayin Inno ba da wasa take maganar ba gashi ina jin ciwo kamar na mutu, a daddafe na tashi zaune na kafe ta da ido, Inno tace, “Narjeesah kin haifu Allah ya sauke ki lafiya baki dubi abunda kika haifa ba, baki ɗauka ba kuma baki tambayi abunda kika haifa ba, Narjeesah shin kina tunanin abunda kikayi kinyi wa ɗanki adalci ke nan? Shin Narjeesah kina nufin baki yarda da ƙaddarar data sameki bane ko miye? To bari kiji idan kuwa haka zaki tafiya da rayuwar ki zaki ɗauki alhakin wannan bawan Allah Narjeesah ki godewa Allah a duk hanlin da kika tsinci kanki a ciki! “

jikina ne yayi sanyi, ta bani yaron daket na anshe sa, ina kallon fuskar sa sai da gaba na ya faɗi da sauri nace, “Inno anya wannan yaron mutum ne kuwa?”

Inno tace, “Narjeesah ke ke nan keda sai yanzun kika ganshi da alokacin da yazo duniyar nan ne kika ɗauke sa kallo ɗaya, sai kinja, Innahu min Sulaimanu Wa Innahu Bismillahir Rahmanin Rahim saboda mugun kyaun da yazo dashi ka shi ƙaton gaske da nauyin sa, kamar balarabe duk ‘yan gulmar da suka zo da zarar sun kalli yaron sai kiji sunyi shiru sai dai suce Allah ya raya”.

Bata yaron nayi ta ce, “ba zan ansa ba, sai kin bashi mamma yasha ai iya hakuri yayi hakuri ban ma taɓa ganin jin jiri mai hakuri ba irin wannan dan ha oya maza bashi yasha”

Nidai cike nake da mamaki irin wannan rayuwar da na tsinci kaina nakeyi, ace wai ni Narjeesah ƙaramar yarinya dani nice na zama uwa wai haihuwa wai kuma shayarwa zanyi, kai wai dai ko mafalki ne nakeyi?.

Inno ce taga nayi zurfi cikin tunani kawai sai ta saka hannun ta ta fara ɗaga riga ta da sauri na dawo hayyaci na, na riƙe rigar nace, “Inno dan Allah ki bashi nonon Akuyar ki da tahaifu kwanan nan dan Allah kinji Inno? “.

Sakin baki da hanci Inno tayi tana kallo na, kawai ta kwalawa Yaya kira, ai kuwa da sauri Yaya ta shigo tana tambayar lafiya? Inno tace, ina fa lafiya wai Narjeesah ba zata shayar da yaron nan ba, sai dai abashi nonon akuya ta data haifu”

Salati Yaya ta saka tana kallona, shi kuwa yaron kamar yasan abunda akeyi ya fashe da kuka, jin yaron ya fara kuka ne yasaka Yaya tace, ” ko kibasa yasha ko kuma yan zun nan ki haɗu da fushi na! “

Nasan halin Yaya ba ƙaramin aikin ta bane taci ubana a yanzun aikuwa da kaina ba sakawa yaron nonon a bakin sa ai kuwa kamar jara yake ya fara ja wani uban ihu nayi na janye shi, ina faɗar wallahi da zafi ciwo wallahi “.

Zama naga Yaya tayi a kusa dani ta haɗe rai dole yasa na maida yaron yana sha ina yarfa hannu ba damar na janye sa, sai da Inno tace, “sauya masa ɗayan shima ya sha”.

Kuka na sanya yana sha hawaye na zubo mani wanda har sai suka tabbar da ya ƙoshi, yayi bacci sannan suka anshe shi, Yaya tace, Inno aje ayo mata wankan kodai naje nayo mata da kaina ne? “.

Ai sai na ƙara saka kuka, basu saurare niba, Inno ta saka mani hijab muka fito tsakar gida muka shiga bayi, ina ganin robar wanka da ruwan yanda turirin zafi ke fita kawai naji kukan ma ya tsaya kallon Inno nakeyi, ita kuwa Inno wankan tayo mani da kanta ta gasani nikam jin nakeyi tawa tazo ƙarshe, ruwan da suka rage ta sakani na zauna sai da muka daɗe a bayin muka fito da Mama mukaci karo, aikuwa cewa tayi, “uwar shege anfito ke nan”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button