NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Watan su Salman biyar basu koma london ba, iyayen su sunji kewar su, har gaji kawai suka shirya zowa Nigeria, barare da sun kira sun sanar da zuwan nasu ba.

Yau su Salman ne zaune a cikin “yan uwan su, dan yan zun sun saba da su, Salma kuma ta fara saka doguwar riga amman har yan zun bata wani saba, dan zafi takeji idan ta saka, sallamar su, Dad da Mom ɗin sune suka shigo cikin falon aikuwa kowa da farin ciki ya tashi suke tarbon su, su kuwa farin ciki sukeyi suna rungume jinin nasu, kallon su Salman sukayi da suketa harkar gaban su, Salman yana danne_dannen laptop Salma ma laptop ɗin ce a hannun tana aiki, shi kuwa Muhseen waya ce a hannun sa ya saka earpiece akunne sa, cike da mamaki kowa yake kallon su, fulani kuwa cewa tayi, “Salman Salma Muhseen bakuga iyayen ku bane? “.

A tare suka ɗaga kai suka dubi fulani, suka maida idon su akan aikin su, cikin sanyi jiki Mom ta ce, “my ɗear baku san da zuwan mu bane a nan way kuka share mu?.

Ɗaga idon sukayi suka ɗaga masu hannun “hi Mom hi Dad” suka tashi bar gurin iyayen bin su sukayi da ido suna shiga cikin ɗakin su, su Dad suka zauna daɓas cikin damuwa.

Fulani ta dubesu ta ce, da alama kunyi wa yaran ku, laifi amman zasu sauko ne, tunda gashi sun sauko yan zun sun saba da kowa”.

Uncle ɗin sune yake ƙara sheda masu aikin da sukeyi anan shine ya hana su koma gurin su ba, Mai martaba ba, Dad ya ce, eh duk abunda akeyi ina sane saboda ina magana da Mai martaba a kullum, kuma tun lokacin nake sheda masa yaran nan sam ko mun kirasu a waya ba wani magana mukeyi dadu ba daga gai suwa basa ƙara cewa damu komai! “.

Tausayin su sukaji ya kama su, a ce kai da ɗan ka, amman babu wata magana daga gaisuwa har tsayin wata biyar , lallashin su akayi sai da suka haƙura aka cika masu gaban su da kayan ciye_ciye.

Salman da Muhseen da Salma kuma suna shiga cikin ɗakin suka fara dariya harda tafawa ajiye kayan sukayi suka, zauna Salma ta ce, “kagafa Dad wai har ya manta irin tsawar da ya daka muna wai mun zagi ƙasar sa, ai ga munan mun zauna ƙasar tasu, kuma ba zamu koma ba”.

Dariya duk sukeyi, Muhseen ya ce, kuwa ma yan zun ma yawon zaga gari nake son yi, duk da ranar naji Dad da Mai martaba suna magana akan bikin ɗan gidan Mai girma governor ashe abokin Dad ne, shine naji yana faɗar ba zai samu damar zuwa ba, sai dai mu muje mu wakilce sa”.

Salman ya ce, “sai dai ku kuje ni kun san babu inda zani, saboda ni ban cika son yawan damuwa ba, ba kowa nake son hulɗa dashi ba, gaskiya kuma kun fi kowa sanin haka, kune ƙanne na wanda nasa daku, duk da a gida ma, ba wani cika shiga lamarku nayi ba, kasan cewar bana son haya niya kwata_kwata”.

Dariya duk suka sanya masa, sukaci gaba da aikin su, da sukeyi a computar su.

Tun lokacin da Mai martaba yaga gudan jinin sa ya dawo, shike nan farin cikin sa yakasa ɓoyuwa, sanar dashi damuwar su sukayi, murmushi ya yi yace, ai tunda kun dawo sai ku jawo abun ku a jikin ku, ku tashi ku shiga cikin ɗakin su”

cikin sanyin jiki suka shiga cikin ɗakin gurin Salman suka fara dosa domin shine babba sauran kuma biyayya sukeyi masa a tsakiyar su suka saka Salman, shi kuma yana ganin hakan ya shagwabe fusa ya kwanta, jikin Mom ya saki laptop ɗin sa ajiki sa, Mom tace, “son fushi dai fushi dai abu yakai some 6moth ya kama ta kuyi hakuri haka nan, duk irin son da muke yi maku, ku a tunanin ku, shike nan Mai martaba zai nemi alfarma muƙi yimasa ne? Haba son kudu ba fa, munyi kewar ku, sosai ko a waya baka sakar muna jiki duk kun bi kun hanamu kwanciyar hankali, iye? Nifa na haifeku ni mayi haƙuri nabi umarnin kakan ku amman ku sai kusa na kasa yi masa biyayya bayan tamkar mahaifi yake a guri na? “.

Dad ne ya ce, “ni kuma fa baiwa nayi maku tsawa bane dan kuji haushi bafa dan kawai kuyi saurin fahim tane nayi maku hakan amman shine kuka ɗauki fushi damu”.

Tsakanin ɗa da iyaye sai Allah atake suka shawo kan su, sukaci gaba da farin ciki tare dasu.

Bikin da su Dad sukace ba zasu zoba, sai gashi dasu za ayi Dad ɗin sune yaje dasu gidan governor, anan suka haɗa kan iyalen su, inda anan muka haɗu da Salman kasan cewar Khalid ɗan gidan governor abokin mune tare muka tashi dashi munyi karatu dashi tub daga secoundary har i zuwa university couse ɗaya mukeyi dashi har muka dawo gida nigeria, muka fara aikin likitanci, sai dai ba garin mu ɗaya ba, muma bikin sa ne muka zoyi, kasan cewar Salman sa’an mune, sam bamu wani sha wahalar zama abokai ba, kasan cewar mu bama da hatsaniya dan duk abunda abokan ango sukeyi, badamu ba, zuwa gurin Amarya da ƙawayen ta, sai da ma za’a gurin dinier ne, angon ya nuna fushin sa, akan dole nida Aliyu da Salman sai munje gurin dan yasan halin iri ɗaya ne, ganin yanda ya kafe dole muka shirya mukaje, koda mukaje gurin bamu shiga ba muna cikin motar, waya yayi ta kira saboda anfara shagali bai saka mu a idon saba.

Dole muka ɗauki wayar sa kasan cewar yayi kiran wayar mu har ransa ya fara ɓaci mu muna kallon sa, dole muka fito uban yan naci ya kira mu.

Bamu wani jima a gurin ba, saboda yanda “yamta ke ta zuwa gurin gurin amsar number waya dole muka dawo cikin motar, har aka tashi muka koma gida, tunda aka kai Amarya muka anshi number wayar Salman, muka baro kaduna muka dawo nan yola, tun daga wannan lokacin ne abota mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin mu, ko ince aminta har muka san junan mu da aikin juna da sirrin juna, kowa idan wani abun ya shige masa yakan kira ɗan uwan sane, kwata_kwata bama yin abu ko miye dan muna mu biyu sai mun saka Salman aciki shima haka, a dangin sa duk ansan mu haka ma dangin mu kowa yasan Salman.

Numfa sawa Jafar ya yi ya ce, “babbar damuwar da Salman ya fara fuskata a rayuwa wadda ta zame masa ƙalubalen rayuwa take ci masa tuwo a ƙwarya har yanzun wadda wannan ya shafeki Narjeesah shine zaki sani a yanzun kasan cewar, har yan zun baki san waye Salman ba shine…. “.

Comment and share

Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????

???????? NARJEESAH ????????

Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN

ELEGANT ONLINE WRITERS

Bismillahir Rahmanin Rahim

Ya Allah kajiƙan iyaye na kayi masu rahma ka sada su da rahmar ka dasu da duk kannin yan uwa musulmi baki ɗaya amin

           2⃣6⃣⏮3⃣0⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Narjeesah Salman sai da ya zamo fittacen lauyan da ƙasa take alfahiri dashi ya kasan ce mutum mai gaskiya wanda akeji dashi ta ko ina a faɗin ƙasar nan “.

Rayuwar Salman ta fara sauyawa ne saka makon haɗuwar sa da yar mataimakin shugaban ƙasa, Haulart, Haulart ta shiga rayuwar Salman ne da ƙarfin gaske, wanda muka rasa taya hakan ta faru kasan cewar bamu sani ba, dan bai sanar damu ba sai ranar ɗaurin Auren sa, wanda ta kasan ce iyayen Salman da “yan uwan sa sai ranar suma suka san da zan cen, dan haka Auren bai wani samu shagalin biki ko ɗaya ba, dan yace wa su Mai martaba kada ayi taron komai dan shima Auren zuwar masa yayi da rana tsaka.

Tunda aka ɗaura Auren Salman da Haulart suka bar ƙasar sai da suka shafe shekara biyu suka dawo garin Abuja suka sauka, Salman ya sauya, baya neman kowa nasa, daga shi sai matar sa kawai suke bidirin su.

Matsalar farko da ta fara fuskar tar Salman rashin haihuwa wanda alokacin kowa yasan Salman baya cikin hayyacin sa, dole Mai martaba da kanshi ya nemi Salman kuma yayi masa nasiha da ya dawo hayyacin sa, ya waiwayi iyayen sa, da suke fushi dashi, cikin ikon Allah kuwa Salman yayi abunda Mai martaba ya umurce sa, dashi kowa yaji daɗin sauyawar Salman, kuma fa duk wannan halin da Salman ya shiga, yana nan yana aikin sa akan gaskiya da sanya marasa gata a cikin lamarin sa, ƙungiyoyi ya kafa sosai na kula da gajiyayyu da marasa ƙarfi, da marayu, da malamai hidima sosai yakeyi masu, wannan shine ya ƙara wa Salman daraja a idon mutane,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button