
Ganin har shekara ukku Salman da matar ta basu haifu ba, suka fara shiga damuwa kasan cewar Salman shine ya shiga damuwar da yawa sai suka fara zuwa ganin likitoci amman abun mamaki duk ƙasar da sukaje result ɗin Salman yakan nuna cewar Salman kwata_kwata baya haihuwa matar sa ita kuma lafiyar ta, ƙalau, wannan abun ya ɗaga hankalin kowa ba kamar Salman wanda ya shedawa iyayen sa, zai rabu da matar sa, dan gudun kada ya cutar da ita, sunji tausayin Salman sosai kuma sunji daɗin Salman zai rabu da wannan “yar isakar matar wadda tunda sukayi Aure da Salman sau ɗaya suka taɓa ganin ta har su Mai martaba.
Tunda Salman ya shedawa Haulart hukunci da ya yanke tace, sai Salman yayi nadamar rayuwar sa, shida iyayen sa, duk sai sun zubar da hawayen su, ai kuwa tun daga wannan ranar Salman bai sake fita koda ƙofar gidan sune sai da jami’an tsaro wanda mahaifin matar sa, ya haɗasa dasu, ga baki ɗaya Salman ya manta kowa nasa, baya tuna koda sunan iyayen sa, haka iyayen suka tsani ace sun haifi ɗa mai suna Salman.
Abu kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba daga baya ma baya iya kallon ko wace mace, saboda duk maccen da zatayi wa Salman magana zai ganta a gaban sane kamar suffar alade, Haulart ce kawai yake ganin ta a matsayin mace kuma cikkakkiyar mace, wannan abun har iyayen sa, sun shiga daga cikin abun ƙin sa, akwai ranar da Salmah ta haɗu da Salman a wunin wani aikin da ya haɗasu a tare, kasan cewar sun san Salman yan zun baya ko tuna sunan su, ta matsa a kusa dashi ta ce, “bros nasan baka son ganin fuska ta, nima haka, amman kasani muna kewar ka muda iyayen mu, bro duk wanda ya aikata hakan a gare mu ba zamu taɓa yafe masa ba, na barka lafiya “.
Tunda Salma ta ambaci sunan sa, kansa yake a ƙasa bai ɗago ba, har tabar gurin, a ranar da ciwon kai ya kwana mai tsananin gaske, sai da ya kwana, biyar yana jinya sannan ya samu sauƙi, tun daga wannan ranar ne yake yi muna sallama a WhatsApp wanda rabon da yayi muna hakan har mun manta dukan mu, to anan ne yake sheda muna yana barar addu’ar mu, kuma muje ga iyayen sa, mu sheda masu halin da yake ciki da yanda yake jin kowa a garesa inba Haulart ba, to anan ne kowa yasan mike faruwa, shine muke bashi shawarar duk lokacin da muka gama magana dashi ya goge farar da yake yi damu, cikin ikon Allah kuma babu abunda ya sake faruwa muna yawan magana dashi kuma yakan turo muna da kuɗi muci gaba, da kulawa da har kokin sa, na yau da kullum, tare da sadaka da neman addu’a a bakin mutane da dama da malamai.
A wata ranar laraba ne yake sheda muna, yana cikin tsananin tashin hankalin, domin yana jin a jikin sa cewar akwai akwai macen da yakejin zata iya shiga rayuwar sa, kuma Haulart ta tada masa hankali akan cewar, ko wace mace ce sai ta ne mota, shi bai san a ina tasan da wannan zancen ba, dariya mukayi dan mun ɗauki abun kamar almara fa shirme, amman sai ya matsa muna akan muje mu sanar da Mai martaba dan abun bana wasa bane, jin hakane mukaje har gurin mai martaba muka bashi wannan labarin, a take mukaga hankalin sa yayi mugun tashi, a gaban mu ne ya saka aka kira masa malamin masarauta, ya labar ta masa kuma cikin ikon Allah ya ce, a bashi kwana biyu zai je ya dawo masu da amsa, mai matarba, ya hanamu komawa, dole muka zauna har zuwa kwana biyu.
Anan ne Malamin yasa aka kira mu, bayan mun zauna ne, yace, “tabbas wannan yarinyar itace haske a cikin rayuwar Salman kuma akwai rabo mai tarin yawa a tsanin su, kuma yan zun haka akwai rabon da yake a kusa_kusa dan haka duk yan da za’ayi a ɗaura Auren Salman da yarinyar nan saboda akwai igiyar Aure a tsanin su kuma igiya ko ɗaya ba zata tsinke ba, duk da kasan cewar su nesa da juna.
Yana gama bayanin ne duk mun kasa gane wannan bayanin kawai ya ce, kada ku sanar da kowa gaskiyar wannan lamarin har Salman ɗin a take ya sanar da mai matarba cewar, a riƙa bibiyar rayuwar Salman da matar sa daga ɓoye, haka kuwa akayi mai gadin gidan Salman shi aka baiwa wannan aikin har da wayar da zai riƙa kira yana sanar da abunda yake faruwa, da yake mutumen yana da hali mai kyau shine yayi ta sheda wa Mai martaba abunda ke faruwa.
Bayan wata biyu Mai martaba ya kira mu yake sheda muna cewar Salman zai zo gurin mu duk yanda akayi mu hanasa tafiya har sai idan shine ya kira mu ya bada umarnin barin sa ya tafi, ya tambaye mu cewar ko Salman yanada gurin sauka a garin mune, muka sheda masa cewar eh amman bamu san unguwar da zai sauka ba, dan yana da gidaje a garin mu harda motoci dan haka yanada masauki.
A gidan Salman kuwa wani irin ciwo ne ya taso masa, wanda yayi kamar zai mutu, sai shure_shure yakeyi ma aikatan gidan ne suka samesa a hakan da sauri suka kira wayar Haulart duk da kuwa irin tsoron ta da sukeyi, sukayi shahadar kiran ta, sai da taga damar ɗauka ta ɗauki wayar cikin masifa, take tambayar su miye?”.
Cikin tsananin tashin hankali direba ya ce, “ranki ya daɗe wallahi yallaɓai ne bai da lafiya sai shure_shure yakeyi! “
Kashe wayar tayi cikin minti talatin ta iso gidan ita da guard ɗinta, da sauri ta shigo cikin falon turus tayi ta kafesa da ido tana ya tsinar fuska, wani uban ashariya ne tayi, cike da masifa ta kira waya, ana ɗaukar wayar tace, “abunda aka faɗa ya tabbata, kuma ance ko na barsa ya aikata ko ni na mutu, gashi ina da tsananin kishi, amman tunda ni rashin aikata abun zai shafa, to nayi ƙoƙarin samo yarinyar da aka ce, har ankai photon ta, a gurin bokon kuma ya sheda muna cewar ita ce, kuma nasa an sato yarinyar har ankawo ta wata hotel, kuma yan zun zan saka akaisa a ƙofar hotel ɗin a jiye sa a hakan kamar yanda aka ɓukata, nikuma zan koma na cika ɗayan aikin “.
Magana akayi mata, daga can ɓangaren, kawai ta kashe wayar da gudun ta ta fita, tare da body guard dinta ta shigo su huɗu suka ɗauki Salman suka fita dashi, maigadin ne ya kira Mai martaba ya sheda masa, ai kuwa aka bisa daman shima nashi ma aikatan suna biye da duk wani motsin Salman da matar sa.
Ban san ya akayi ba, nu dai Kawai mun ya ankawo Salman tare da jami’an tsaron sa, airport mukaje muka ɗauko su, a hotel suka sauka, sai da ya kwana biyu ya fara magana, kuma tun daga lokacin bamu sake zuwa inda yake ba saboda umarnin Mai martaba, sai dai ya kiramu yace, Salman zai koma mu kaisu airport, tun daga lokacin Salman bai sake zuwa nan garin ba sai wannan karon .
Amman fa matar sa wani sabon salon ta ɗauka duk wata macen da ta samu labarin cewar Salman ya kalla sai taga bayan ta, da sai an nemeta an rasa, kai abun ma harda abokan Salman bata bari ba, amman ban san miye yasaka mu bata rabamu da Salman ba, har tsayin wannan lokacin duk da tasan da cewar muna tare dashi, saboda duk inda Salman ya saka ƙafa tanada masaniya, akai abu kamar aljana”.
kuma har yan zun sakamakon Salman baya haihuwa yake nunawa, amman kuma sai gashi Shuraim yazo a matsayin ɗan Salman, wanda kusan kullum matar Salman har a internet tana posting din Salman da result ɗin rashin haihuwar sa, anayi mata like, wannan abun ba ƙaramin ɓatawa Salman da “yan uwan sa yakeyi ba him! “
Nisawa jafar yayi ya ce, “NARJEESAH kinji tarihin Salman kuma har yan zun Salman tutar sa a gurin kowa tsaye take, koda kinyi ƙarar Salman ba zaki samu biyan buƙata ba, sai in da Matar sa zaki kai ƙarar sa”