NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Kowa shiru ya yi Amrah ce, ta ce, “Antyn Nargeesah dan Allah kada ki kai ƙarar Salman saboda idan har mutane suka kalli Shuraim duba na hankali zasu fuskaci cewar ɗan Salman ne, to masu kawo wa Salman hari kina ganin kamar yanda muka rasa sanin inda Shuraim yake ba zasu ji daɗin kashe muna yaro ba?, ki duba da kyau kada kiyi abunda zai janyo mu rasa ganin Shuraim

Kallon su nakeyi zuwa can nace, “wallahi nikam nadawo ai nahin Narjeesah ta marar ɗaukar reni masifaffiya, kuma ni ban wani ji tausayin wannan mugun ba, koda banyi ƙarar sa ba, sai na rama abunda yayi mani! “

Dariya sukayi Nusaiba ta ce, “da mun bani har mu, dan nikam ba zan iya mantawa da halin ki ba, Anty Narjeesh”.

Hindu ce ta ce, to yan zun a ina ne zamu nemo Shuraim? dan da alama Shuraim baya gurin Salman dan naga hankalin sa a tashe yake “.

Umma ta ce, “ku jira sa yazo muji ta bakin sa, idan Shuraim yana hannun sa, sai hankalin mu ya kwanta”.

Kowa ya yi na’am da maganar Umma.

Nace, dan Allah Jafar da Aliyu ku saka mugun nan ya bani takar data, dan nikam ba zan iya zama dashi ba”.

Kallona sukeyi suna dariya, Humaira ta ce, “ai lokacin da muka haɗu dashi munji yana faɗar akwai igiyar Auren sa a kanki kuma ba zai iya tsinke ta ba, kuma acikin labarin da kika bada ya ce, idan kika yarda ya dawo cikin rayuwar ki, kin makaro”.

Tsaki kawai nayi, na share su fira muka chanza saboda sun ga bana son maganar Salman, sai dare suka je gida bayan sun zaga iyayen su, da iyayen Halima.

Yau ma kasa bacci nayi, tun da safe Amrah da Nusaiba suka kawo mani abun kari amman na sheda masu sai zuwa anjima dole suka ɗauke, suka fita sai ƙarfe goma na fito tsakiyar falo na ƙara gaida Umma na zauna ina kallon labaran da Umma take kallo, Amrah da Nusaiba suka fito suka zauna muka fara labari Umma ganin mun cika ta da surutu ne ya saka tabar gurin ta koma warta cikin ɗaki.

Labari mukeyi na yaushe ne zamu je gurin Inno mu dubo ta ita da Yaya sai dai muna gudun haɗuwar mu da wannan mutumen wanda ya so sace, Shuraim yana jariri,.

Amrah tace, Aunty gashi kuma, Shuraim ɗin baya hannun mu, da munje kawai tun da mun gano mahaifin Shuraim ko”.

Nusaiba ta ce, “Allah yasa da Daddyn Shuraim zamu yaga ɓarawon yara ya kaisa kotu ayi muna maganin sa”.

Harara na ɓallawa Nusaiba na ce, “uban waye zai je da wannan mugun garin mu, kisa ya raina ni, wallahi ni, bazan yarda yama ga fuskar hakuri a gareni ba dan banda shi kuma bana jin tausayin sa, ko na ƙwayar zaira ai bani ce, na saka ya aurowa kansa annobar da tafi ƙarfin sa ba ehe! “.

Gimtse dariyar su, suke yi Amrah ta ce, “Anty nifa wallahi matar Salman nake son gani kin san ko dan saboda miye? “

Gir_giza mata kai mukayi ni harda su mere mata baki, tace, “saboda yan da result ɗin Salman na asibiti yake nuna cewar baya haihuwa kwata_kwata gashi kuma ansamu akasin hakan shin wai nikam anya ma kuwa ita mutum ce, kuwa, shin tanada tunani kodai kwanyar kifi ne da ita? Shin da tasa aka nemoki ta ƙarfin gaske ta haɗaki da mijin ta, idan har da gaske takeyi, tana kishin kamar yanda tace, to ai koda umarnin duniyar zai bata, ba zata ji wuyar yin saba, irin yanda ta baro gidan ta, garin su, ta ƙetaro cikin local, ta satoki bataji wahalar komai ba, kuma ta haɗaki da mijin ta abanza da yofi, duk dan cika umarnin bokan ta, gashi kuma ya shirga mata uwar ƙarya”.

Dariya Nusaiba keyi harda dafe ciki da kwan tawa, Nusaiba ta ce, “itafa mutuwa take tsoro ba wai kishin mijin ta bane ya sakata aikata hakan ita da bokan kida humai ne na bugawa a jarida, tunda sun bari har Salman ya kusan ci wata mace, ta daban bai karya tsafin nasa ba, da yace, zata mu ba”.

Nikam ban ce dasu uffan ba, har suka gama, zuwa nayi na ɗauko abin karin kumallo na na karya, na, mukaje kowa yayi wanka muka saka ankon Humaira, muka fito zamu gidan, su Hindu, gurin Umma muka nufa muka sanar da ita, ai kuwa Umma ta soma faɗa, mutum da Auren sa akan sa, yake wannan shigar mayafi a kafaɗa, kuma anbi jiki da turare, kuma bada izinin miji ba, za’a fita ko? “.

Duka Umma muka tsare da ido Umma ta ce, “ni ku tafiyar ku ku bani guri kukayi mani tsaye kamar wasu itace”.

Dariya mukayi muka fito nikam na ce muje dai nikam bazan wani takura kaina ba”.

Tafiya mukayi, mun fito daga cikin gidan ke nan, sai ga motoci har ukku ajere parking sukayi a gaban mu, sakin baki mukayi, ganin mutane sun fito harda mace, sai Salman, a take su Amrah suka saki murmushi ni kuma na ɗaure fuska na ɗauke kai na juya zan tafiya ta kawai naga mutum a gaba na, saura kaɗan nafaɗa a jikin sa, da sauri nayi baya, cike da masifa nace, Malam miye hakan? “

Kowa kallon mu yakeyi harda su Amrah, wannan budurwar ce, mai kama da Salman da namiji suka iso gurin kallo ɗaya nayi masu, na gane su waye, wato Salma da Muhseen ne, hannu ta bani tana dariya, tace, “madam kiyi hakuri mu ɗan gaisa mana, sai ki kaini masauki nasan zakiyi tarbon baƙi ko? “.

Kamar ba zanyi magana ba, kuma dai naga ai ba ita ce tayi mani laifin ba, nace, “da ace ke ɗaya kika zo da kin ga yanda ake tarbon baƙi dan kin zo gidan karamci amman sai kika zo da mugun mutum kin kuwa ansamu naƙasu anan gurin”.

Murmushi tayi ta ce, “to ai dai mu baƙin kine kuma ga Muhseen bro ɗina ne ku gaisa”.

Kallon shi nayi banyi magana ba, shiko dariya yake gimtsewa, Amrah ce ta ce, dasu “bisimillah ku zamu mu shiga daga ciki”.

Kallon su nayi na ce, “idan kika kaisu suka gaisa da Umma ki fito mu wuce, dan ni kam va zan shiga ba, tafiya ta kawai zanyi, kuma ki shaidawa mutum ya dawo mani da yaro na ehe! “.

Da sauri duk suka bini da ido Salman ya ce, wai kina nufin har yan zun Shuraim baya hannun ki, kuma kike zaune hankali kwance? “

Da sauri na dawo da ido na akan sa, nace, “kana nufin Shuraim baya hannun ka da gaske na rasa shi ke nan innalillahi wa inna lillahir rajiun, na shiga ukku ni Narjeesah waye wannan azzalumin da ya rabani da farin ciki na, Salma ce, ta dafa ni cikin kaɗuwa tace, “bani photon yaron na gani “.

Nusaiba ce, ta basu wayar da sauri Muhseen ya ansa ya Cuba photon Shuraim da sauri Salma ta ansa, shima Salman ansar wayar yayi ya juya cikin tsananin tashin hankalin, da sauri Salma ta ce, “kiyi hakuri yau muma zamu fara namu bin ciken yan zun kuwa zaki iya komawa cikin gidan ki zauna ga wannan wayar zan riƙa kiran ki muna magana “.

fasa fitar mukayi muka dawo cikin gidan muka zauna jagwab, kuka mukeyi har Umma ta fito ta same mu a hakan, zama tayi ta ce, “kuka ba shine mafita addu’a ita ce mafita a gare mu dukan mu”.

Su Salman kuwa wata unguwar suka nufa sunayin parking suka fito da gudu suka shiga cikin gidan, saman kujera suka zazzauna Salma kuwa kaiwa takeyi tana dawowa, tana cizon baki, ta duƙule hannun ta ɗaya tana ɗan dukan tafin hannun ta,

Muhseen ya ce, “sister babu wanda zai ɗauki yaron nan face, masu bibiyar bro, amman wallahi, duk wanda ya yi wannan aikin da wata manufar yayi ba wai dan ya san da sanin cewar wannan yaron yana da alaƙa dashi ba”.

Salma ta juyo ta fuskan cesu tace, “bros nikuma nawa hasa shen ba kowa bane ya ɗauki wannan yaron ba, face, ya fahimci yanda kayi saurin yarda da yaron har ya raɓeka, bayan kowa yasan cewar kai ba ma’abuci dariya bane ballema mutum yayi tunanin kana ƙaunar yara har haka ba, dan haka zamuyi bin ciken mu ta ƙar ƙashin ƙasa, dafatan zaka bamu haɗin kai kasan cewar ka babban lauya kuma wannan case ɗin kai ya shafa ba lallai bane ka iya aikin nan ba, dan haka ina son duk abunda kaga, mahaifiyar yaron nan tayi kayi mata uzuri kuma kasani ko ma miye da sa hannu na”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button