NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Kallon rashin fahimta sukeyi mata, amman sai ta sakar masu murmushi tace, “ku yarda dani bros”.

Gyada mata kai kawai sukeyi, amman duk basu fahimce taba, cikin wani ɗakin ta shiga ta kira waya ta ɗan daɗe tana magana, kafin ta fito ta zauna tana kallon su”.

Zaune muke bayan na gama yiwa Umma bayani, shiru tayi tace ke da Amrah ne zakuyi wannan tafiyar kuma duk zaku iya kuwa? “

Amrah tace, “addu’ar ki kawai muke buƙata “.

Addu’a Umma tayi mana, ita da Nusaiba suka rako mu, har ƙofar gida muka ɗauki hanya………

Comment and share

Ummu Ihsan ce*????????????????????????????????????????????????????????????

???????? NARJEESAH ????????

Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN

ELEGANT ONLINE WRITERS

Bismillahir Rahmanin Rahim

           3️⃣1️⃣⏭️3️⃣5️⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Tafe muke a hanya nida Amrah muna janye da trolley din mu guda biyu da muka ɗauko daga cikin kayan da suke ajiye a waydrop wanda duk Daddyn Shuraim ne ya ajiye su, to a cikin sune muka ɗauki biyu daga ciki.

Tafe muke hankali kwance illa jimamin barin gida da su Umma mukeyi, muna ƙarasa wa a bakin titi mota na jiran mu, muna zuwa aka buɗe muna muka shiga muka ɗauki hanya sai airport koda mukaje komai angama, muna shiga kawai mukeyi jirgin ya ɗaga sai Abuja, tunda muke a rayuwar mu wannan ne karon farko da muka shiga filin jirgi harma muka hau jirgin a gaskiya munji daɗin hakan.

Muna sauka muka fito wani mutum ne ya tarye mu, muka shiga cikin motar da yazo da ita, muka ɗauki hanya, a gaskiya Abuja babban gari ne, tafe muke muna kalle_kalle a wayan ce, saboda tsaro, badan tsoro ba.

Wata unguwa ce muka shiga gidan kam ɗan madai daici, dashi yayi kyau yana ajiye mu yayi gaba abun sa, mukam tare da kayan mu muka shiga cikin gidan, babu kowa a cikin falon gidan muna ta sallama sai daga baya wata, mata ta fito da fara’ar ta tana yi muna lale mar haban da zuwa, ajiyar zuciya muka sauke, nida Amrah.

Matar ta ce, “ku shigo daga ciki mana kuka wani tsaya nan kamar wasu baƙi”.

Dariya mukayi muka ƙarasa shiga cikin falon gidan akan kujera muka zauna muka gaisa da matar wadda a ƙalla zata kai sa’ar Inno, bayan mun gaisa ne aka ciki muna gaban mu da abinci dana sha, kai komai sai sam barka, ƙasa muka zauna mukaci muka ƙoshi, aka kwashe kayan matar tace, “to ku tashi na nuna maku ɗakin ku, kuyi wanka ku futa, ko? “

Murmushi mukayi mata, muka ɗauki kayan mu muka shiga cikin ɗakin da takaimu ta fito, a bakin gadon muka zauna muna sauke numfashi, Amrah ce, ta fara shiga wanka ta fito nima na shiga tare da ɗauro alwala muka sauya kayan jikin mu mukayi sallah muka zauna muna futawa, har mukayi sallar magrib da isha’i muka fito falon muka ƙara gaisawa da matar har take cewa”Amrah kodai anan zaki zauna dani kin ga ni ɗaya ce a gidan nan yara na duk sunyi Aure su ukku mata, Abida Asiya Lamra, sai maza ne kawai suka rage mani kuma duk suna gurin aikin su, kin ga na samu wata Autar mata ko? “.

Dariya mukeyi tun lokacin da ta fara maganar itama tana dariya Amrah tace, “eh fa zan kuwa zauna dake Ummi kin ga sai Anty Narjeesah da Auta Nusaiba su daina yi mani dariya suna cewa ni kam basu san a wane matsayin nake ba, niba ga yar fari ba, kuma niba Auta ba”.

Dariya muke yi harda tafawa na ce, “Amrah ai dai mun riga ki sanin matsayin mu, nifa wallahi yau naga, kin zama wata irin shagwaɓaɓɓiya da ke sai uwar shagwaɓa kikeyi, kai mun gode Allah da yasa ba kece Auta ba da mun shige su wallahi “.

Dariya mukeyi, fira sosai mukayi da Ummey kamar ba gobe, kwanan mu ukku a gidan mun saki jiki da Ummey sosai, yau ne mukayi shirin zaga gari ni da Amrah direba ne ya jamu sai wani haɗaɗɗen hotel muka isa, yanayin parking muka fito nida Amrah, munyi shiga ta alfarma, wani gurin futawa ne muka nufa muka nemi kujera muka zazzauna Amrah taje tayo muna order abin sha ni kuma ina zaune ina dan na wayar hannu na, Amrah ta dawo ta zauna, muka soma fira, muna ɗan kallon gurare kaɗan_kaɗan, har aka kawo muna abin sha, wasu matane su ukku suka zo a kusa da kujerar mu suka zauna, kowa ce daga cikin su, tayi shiga ta kece raini, ɗayar ma harda gilas a idon ta ga manyan wayoyi a hannun su, da sauri ma’aikata gurin suka soma kawo masu gaisuwa tare da abinci da lemo, suna ajiyewa suka bar gurin, sai a lokacin ne wasu daga cikin ma zauna gurin suka fara kai masu gaisuwa mukam ikon Allah muke kallo.

Bamu ƙarasa mamaki ba, naga ɗayar tayi nuni da gurin da muke zaune, ai kuwa da sauri wata yariya tayo gurin mu, muna ganin hakan muka ɗauke idon mu, daga gurin su, muka fara kallon wani gurin, budurwar ta ce, “am excuse me please ana son ganin ku a gurin can”.

Kallon juna mukayi nida Amrah na ce, “kije kice wa mai neman mu munje gurin koyon sallama “.

Zaro ido waje tayi tace, “pleace kuyi hakuri kuje basa son gar dama”.

Amrah tace, “iyayen kine a gurin halan da naga kina jin tsoron kai masu Saƙon da aka baki? “

Shiru tayi cikin sanyin jiki ta juya ta kasa sanar dasu Saƙon dana bata, amman ta makaro dan sunji abun da na faɗa da sauri suka juyo suna kallon mu, mu kuwa fira mukeyi nifa Amrah ƙasa_ƙasa, sake aiko wata sukayi tana zuwa ta ce, “ance kuyi wa kanku adalci kuzo da kanku tun kafin a ɗauko ku “.

Dariya mukayi nida Amrah harda tafawa muka share “yar aiken, ganin haka ne ta koma ta ɗurƙusa ƙasa, ta fara basu hakuri, a take wasu mutane na zaune a gefen mu, wanda suke kallon duk abunda yake faruwa suka fara zuwa gurin mu, suna bamu baki wai muyi hakuri muje gaisuwa ce kawai zamu kwasa a gurin su, nikam na ce, “abunda sukayi niyar bamu su riƙe abun su, kuma abincin da suke ciyar damu daga yau kada su ƙara bamu shi, su barmu da yunwa da dattin talauci ko kuwa Sis? “.

Amrah tace, “kwarai ma kuwa kai nifa har kunya kuke bani irin wannan rawar jikin kamar kun ga wasu doddani, yo in banda dodo miye ake gani aji irin wannan tsoron haka? “.

Na ce, “yar uwa gane mani hanya dan Allah “.

Cikin sanyin jiki kowa ya tafi ya bar mu, ganin hakan ne da jin abunda muka faɗa wanda muke ɗaga murya yanda zasu ji ne ya saka suka taso a fusace sukayo kan mu, suna zuwa sukayi muna tsaye a kai suka riƙe ƙugu.

Murmushi nayi, na ce, “yau wa kina jina kuwa idan har kin han go shi kiyi ƙokarin sanar dani inda yake zaune da inda yake har kokin sa a wannan garin sannan zan turo maki kuɗin da zaki riƙa baiwa masu bibiyar maki labarin halin da ake ciki, da yarinyar da suke yawon hotel da gidajen futu, da sauran su ke harma da iyayen yarinyar da kakanin ta, ƙannen ta, abokan ta, ina fatan kin fahimci baya nina, dai ko? Zan baki photon yarinyar nasan shi kin san sa baki da buƙatar photon sa, sai dai kuma zan baki saboda yaran da zasu taya ki aikin “.

Dariya Amrah tayi tace, “na fahimce ki, duk da nasan ba nice mace ta farkon da kika fara baiwa wannan aikin ba, amman kuma taya kike tunani zai bar wata shedar da zai bar maki, tunda yafi kowa sanin halin ki, akan sa? “

Dariya nayi na ce, “da ace yasan zan bishi a garin ko a ƙasar nan da tuni ya bar wannan ƙasar saboda tsabar sanin halin nawa, na naci da bin diddigi a kan lamur ran sa”.

Wata daga cikin matan ne, ta ce, “idan kun gama shirya cutar “yar mutane sai ku ajiye ku saurari masu garin da irin hukunci da zamuyi maku akan wannan rashin kunyar da kukayi muna”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button