NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Tashi tsaye mukayi na baiwa Amrah hannu na ce, “Allah ya baki sa’ar wannan aikin sai mun sake haɗuwa a nan gurin saboda naga akwai sirri gurin ranar Sunday da misalin ƙarfe biyar da rabi na yamma, dan Allah banda afrikan time”.

Sara mani Amrah tayi mukayi mubiha, ta juya ta fita nima na raɓa ta gefen su nayi tafiya ta, sakin baki da hanci sukayi suna kallon mu har Amrah ta fita ni kuma na ɗan tsaya amsa waya, sai da na baiwa Amrah kusan minti goma nima na ajiye wayar na fita a cikin mota muka haɗu da Amrah muna ta dariya, direba ya ɗauki hanya muka zaga garin muka koma gidan Ummey.

A can kuwa wannan matan cike suke da mamakin su waye mu a garin nan da mukayi masu wannan iskancin, ai kuwa suka gasa zama gurin kowa ce, a hasale taja motar ta, suka bar hotel ɗin.

Salman ne zaune shida Salma da Muhseen a gidan Umma Nusaiba ce, ta kawo masu abinci da ruwa, taje kiran Umma, kasa cin komai sukayi, har Umma ta fito ta zauna suka gaisa, cikin kulawa, Salma tace, “Umma dan Allah ko zamu iya ganin Maman Shuraim kuwa? “.

Shiru Umma tayi, Nusaiba ta ce, “ayyah ai Umma ba zata baki wannan amsar ba, nice kawai zaki samu amsa dan gane da Anty Narjeesah”.

Murmushi Salma tayi Muhseen ya ce,” saboda miye ba zamu sami amsa ba a gurin Umma akan maganar da ta shafi Anty Narjeesah? “

Dariya Nusaiba tayi tace, “kaima yau Anty kake cewa Anty Narjeesah? to ai kuwa zaka sha labarin Anty Narjeesah ko Umma? “.

Tashi Umma tayi tabar gurin, Nusaiba tasa dariya ta ce, “Umma ki zauna mana muyi labarin harda ke”.

Umma ta ce, “Auta kema kinyi koyi da halin Amrah ko? Allah idan kika dameni sai na fasa maki baki”Umma na gama maganar tayi tafiyar ta.

Dariya sukeyi banda Salman da yayi murmushi yana kallon Nusaiba.

Nusaiba ta nisa, ta ce, “am yauwa Anty Narjeesah da Amrah basa nan yau kwanan su biyu da tafiya”.

Da sauri Salman ya ce, “what…! Kina nufin cewar da Auren nawa ta je wani gurin kuma harda su kwana ba tare da neman izini na ba? “.

Sakin baki duk sukayi suna kallon Salman cike da mamaki, shi kuwa masifa yaci gaba dayi, Nusaiba ta ce, “ikon Allah to yan zun dan mutum yayi tafiya kawai sai a kama masifa, kamar yana gurin ashe dai nikam zan ga irin hakan da ido na biyu, to kai inda a gaban Umma ne hakan zakayi ta masifa mai laifin daban wanda akeyi wa masifar daban? Nikam gaskiya ba zan iya zuwa gidan ka ba”.

Dariyar ƙurciyar Nusaiba sukeyi harda Salman ɗin Nusaiba ta bala’in bashi dariya amman kuma haushin Narjeesah yake ji taya zatayi masa wasa da Aure bayan ta zauna har a gano inda Shuraim yake, ya ɗauke su ya tafi dasu gidan Mai martaba, amman wallahi idan ta dawo sai ta raina kanta.

Muhseen ya ce, “harda wannan Yayar taki a kayi tafiyar kuma yaushe ne zasu dawo? “

Nusaiba ta ce, “nima ban sani ba amman idan sun dawo zan sanar daku, dan inda suka tafi babu service “.

Dafe kai Salman ya yi yace, “ok yan zun ko kin san garin da suka tafi da gidan? “.

Nusaiba ta ce, “nifa daman ban fiye zuwa wani gurin ba, ina zama ne tare da Umma na, shi yasa ake cewa na cika shagwaba, dan bana son nayi nesa da Umma na, a toh”.

Dariya sukayi Salma kuwa ta ce, “Amman zaki zo bikin Aure na, dan har anfara shagalin biki, maganar ganin Shuraim da Maman sane da ɓatan Shuraim ne ya saka na dai na zama, yau saura kwana biyu ɗaurin Auren kin ga kuwa, ya kamata a ce matar Yaya Salman tana kusa, yanda zata ga kowa kuma tasan kowa kuma kowa yasan ta, amman tunda bata nan ita da Amrah ke kizo ayi dake sai ki wakilce ta”.

Shiru Nusaiba tayi, Muhseen ya ce, “bafa sace ki zamuyi ba, kin ga da Antyn mu tana nan ai nasan da zaki zo ko? “.

Dariya sukayi Salma kuwa ta ce, “ki kirawo muna Umma mana”.

Nusaiba tare da Umma suka fito Umma ta zauna, Salman ya ce, “Umma dan Allah ana bikin Salma ne shine nake son ki bar Auta taje dasu Humaira wannan bikin dan Allah “.

Murmushi Umma tayi tace, “babu damuwa ai Nusaiba ƙanwar kuce, zata je, amman ta cika laƙuwa da yawa, sai kunji ta bakin ta, ta yarda da kanta, dan gudun kada sai an shirya tafiya ta ce, ita ta fasa zuwa”.

Dariya sukayi Nusaiba ta ce, “Umma zanje ai”.

Sunyi farin ciki suka tashi sukayi masu sallama suka tafi suna fita Nusaiba ta ce, “Umma ba zani ba wayau ne nayi masu, gudun su dameni da magiya”.

Dariya Umma tayi tace, “ai kuwa dai sai kinje kije kiyi shiri dan ina ga gobe ne tafiyar “.

Zum ɓuro baki Nusaiba tayi tana shura ƙafa, Umma kuma ta share ta.

A ranar su Salman suka dawo fada inda fadar take cike da mutane ‘yan biki direct cikin gidan suka shiga sharp_sharp suka shirya aka soma hidimar dasu harda iyayen su duk suna a gurin da sauran yan uwa na gurin mahaifiyar su na can ƙasar London wato dan gin Mom ke nan.

Amrah ce ta gama shirin ta na zuwa royal hotel da shigar ta ta kece raini, tana fito wa, na soma yi mata iya shege, “wow kaga Hajiya Amrah ikon Allah Hajiya Amrah babbar mace, kai Allah dai yaja da kwana, matar babban mutum”.

Na ƙarasa maganar ina dariya, kwaɓe fuska Amrah tayi ta zauna tace, “Anty Narjeesh wallahi zaki daina ko na fasa zuwa ma “.

Ummey ce ta fito tana dariya ta zo ta dafa kafaɗar Amrah tace, “ke kyaleta kinji Amrah na, indai dan wannan abun ne da takeyi maki sha kurumin ki, ai Daddy Shuraim ne zai shigar maki wannan rigimar “.

Ai kuwa a take na haɗe rai na ɓata fuska, suna kallon fuska ta suka soma dariya Amrah harda dafe ciki, ta ce, “yauwa Ummy kin kuwa bani satar amsa, Anty Narjeesh ta Yaya Salman “.

Da gudu nayo kanta, ai kuwa ta fita gidan da gudu sai gurin mota, ina dariya suka fita ni kuma na shiga gurin wankan ina fitowa nayi kwalliya na saka shadda ta ash color na fito, turare na feshe jikina dashi na fito da mayafi na, a hannu, makulin mota Ummey ta bani ta ce, “ke kiyi amfani da wannan kuma ga Ashiru nan yana jiran ki tun ɗazun”.

Ansa nayi ina godiya na fito da sauri Ashiru ya tar yeni da fari ar sa, muka gaisa muka shiga ya jamu sai royal hotel, inda mukayi parking anan ne naga motocin wannan matan da masu basu kariya wato masu tsaron su, murmushi nayi, na Ashiru ne ya buɗe mani motar na sauko na fara taku, duk inda nabi na wuce, idon mutane, akaina jin nakeyi kamar na ɗora hannu na akai na fasa ihu Amman na dake na shiga gurin waya na kira Amrah ta ɗaga, ta ce, na ƙaraso.

Gurin Amrah na nufa, su kuwa da ido suka bini duk da kuwa ko wace, idon ta na a wayar ta amman hankalin su yana a kai na, murmushi nayi kujera Amrah ta ja mani na zauna da bisimillah, lemo ta bani na ansa na ce, “na gode” na ajiye na kalle ta a goggo hannun ta, ta kalla nayi murmushi na ce, “kinyi ta jira na kuma kinyi ta kiran waya ta, am sorry wani abun ne ya taso mani shi yasa ban samu lokacin ɗauka ba, ko na kira ki, to ya labari ina fatan kin nemo mani tarihin ko wace yarinyar ce? “.

Murmushi Amrah tayi, ta bani wani envelope na ansa da sauri zan buɗe Amrah tace, “kiyi a sannu mana, kibi komai a hankali zaki fi fahim ta “.

Kallon Amrah nayi, nayi mata murmushi nace, “da ace kin san yan da zuciya ta takeyi a halin yan zun da baki ɓata bakin ki ba, akai”.

Buɗewa nayi ina duba bayanin komai sai da na kai ƙarshe nace, da sauri “ƙarfe nawa ne yan zun pleace “.

Ta ce, “shidda da kwata”

Cikin zafin nama na tashi harda gudu nake haɗawa nafi ta sai gurin Ashiru da sauri na ce, kayi sauri muje, da sauri na sanar dashi titin da zai kaini ai kuwa da mugun gudu yaja motar muka fita, tafe muke da gudu ina duba a gogon hannu na, wani irin burki ne Ashiru ya taka, da sauri ya fito ya buɗe motar nima na fito ina duba agogon hannu na, a take na soma masifa, “haba wannan wane irin hauka ne kasan kuwa irin barnar da kayi mani yan zun, kasan mota nan bata da lafiya kabari na fito da ita, da ba sai na shiga wata, motar ba, gashi yan zun ka sakani cikin damuwa ba zan same suba, oh sheet! “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button