NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Na dafe goshi sai go and come nakeyi, wayar Amrah na kira, tana ɗaga wayar nace, sun bar ƙasar sai nan da sati biyu kuma zan sake ganin sa, dan haka zan koma gida ne, sai na sake shiri, zasu haɗu dani ne, kiyi mani bucking ɗin jirgi zan bar garin nan da daren nan kawai! “.

Kashe wayar nayi na dawo nayi jin gene jikin motar, ina dafe da goshi na, naji an doka mani uban horn, kallon gurin nayi bayan motar mune na ɗauke ido na, naci gaba da cizon yatsa.

Fitowa sukayi suka nufo ni, dafani ɗayar tayi na ɗaga ido cike da mamaki ina kallon su ɗaya bayan ɗaya, murmushi suka sakar mani, ɗayar kuma ta kawo ruwan swan ta bani, masu sanyi kamar ba zan ansa ba, amman kuma sai naga sun kafeni da ido na ansa na buɗe robar nasha, ina ajiyewa na fara sauke ajiyar zuciya.

Murmushi suka sakar mani a tare, sai ɗayar ta bani hannu tace, “Sarah ko kuma kice, Mrs Naseer”.

Ɗayar ma ta ce, “Nafisah ko kuma kice Mrs Nazeer”.

Ɗayar ta ce, “Zeenat ko kuma Mrs Yaseer”.

Ta ƙarshen ta ce, “Mrs brr or haulman nice duk faɗin ƙasar nan mai wannan Sunan, couse suna ne dana mijina, am naga kamar mijin kine yayi maki halin nasu na maza rashin gaskiya, amman nikam miyasa kikayi masa wannan saken da yawa har haka? “.

Kallon ta, nayi da kyau ban ce dasu uffan ba.

Dai_dai isowar Amrah, daket nace dace, “Nice meet your’s sorry fa kunga ina cikin damuwa amman idan na rage damuwar sai mu haɗu daku yan zun zan koma gidan miji na ne “.

Murmushi suka yi, Mrs barr, tace, “idan ba zaki damu ba zan so muje dake gida na, duk da ni bana barin ko wace, karya tazo mani gida ke harda, wannan da kike ganin mu a tare dasu kasan cewar tare mukayi karatu dasu, kuma mazajen da suke Aure fitattu ne, a ƙasar nan shi yasa ƙawan cemu yakai har wannan lokacin gashi duk halin mu ɗaya illah wannan da kikaji ta sanar dake sunan ta Mrs Yaseer amman duk da hakan bata shiga hurumin da banata ba, so ke naji ina son kije gida na ki futa kafin na baki wata mafitar wadda zakiyi mani godiya ina fatan zaki karɓi wannan buƙatar tawa”.

Ban ce da ita uffan ba, har sai da suka haɗa baki gurin roƙo na, nace dasu, haba, taya zan biki gidan ki, wata kila ma mijin ki yana, gida, idan dai har dan shi kika hana kowa zuwa gidan ki to ya zakiyi da ni nida baki san inda na fito ba? “.

Kallon_kallo suka shiga yi, sai sukayi dariya, Nafeesa tace, “a yanda kika mutu da kishin mijin ki, har kika biyo bayan sa, kika kashe kuɗi gurin neman labarin sa, to duk wani namijin baya a gaban ki, kin ga kuwa koni ce zan iya yarda kibi ni har gida na, bani da shakku a kan ki”.

Dariya nayi na ce, “ok to ku dai yi mani wannan hakurin idan nadawo zuwa jibi zan sauka a gidan naki, koshi dan naji zaki bani mafita ne kawai, kin san akan mijina babu abunda ba zan iya ba”.

Cikin farin ciki muka rabu dasu tare da musayar number, motar Amrah nabi, muka tafi airport koda mukaje muka shiga daga ciki, muka bi ta wata ƙofar Ashiru muka gani, ya ɗauke mu a mota sai gida.

A can gidan Umma kuwa sai da Umma tayi da gaske san nan Nusaiba ta yarda tabi Jafar da Aliyu Humaira da Hindu suka nufi gurin bikin Salma suna tafe, suna yiwa Auta tsiya su Jafar na tare mata, ita kuwa ta kyalesu ta turo baki gaba, ita ala dole fushi takeyi dasu.

Zaune nake ina, yiwa Ummey yan kan farce, Amrah nayin game a waya ta, kira ya shigo da sauri Amrah tace, “Anty Narjeesh Mrs Nazeer na kiran ki “.

Dariya nayi na ce, “kyale ta soma kira” kiran ne ya ƙara shigowa sai da ya kusa tsinke wa na ɗauki wayar na kara a kunne na, ta ce, “sai Mrs Nazeer uwar gida kuma Amarya daga ke ba ƙari”.

Cike da wani irin farin ciki ta ce, “ramki ya daɗe ya kike ina fatan dai komai ya zama dai_dai, ina nufin kin rage jin haushin kowa “.

Dariya nayi na ce, “da sauƙi dai kam amman har yan zun ina jin haushin wasu”.

Ta ce, “to share kawai madam gobe ne zaki zo ko? To ki zo da yam ma, saboda Mrs barr taje unguwa amman zata dawo gobe kasan cewar a hotel ta sauka kuma jirgi zata, biyo ko kuma kizo gida na kawai idan ta iso sai na saka direba ya kai ki ko ya kika gani ne? “.

Murmushi nayi, na ce, “kodai na bari a ƙara kwana biyu saboda bani son na takura wa kowa gashi ita bata nan ke kuma na zo na ɗaura maki nauyi”.

Dariya tayi tace, “ina ma zaki zo tun yau ai da naji daɗi, wallahi”.

Dariya kawai nayi zuwa can na ce, “sai goben dai Mrs Nazeer idan na sauka a airport kizo ki ɗauke ni, amman fa tare da wannan yarinyar zan zo sai ki ware muna ɗakin da zamu sauka gudun haɗuwar ta, da mijin ki, kin san mace, komai ƙuruciyar ta namiji na iya ƙyasawa da ita, dan kin gan mi nan akwai zafin kishi “.

Ajiyar zuciya ta sauke tace, “to sai kin zo babu damuwa ni nasan gurin da zan ajiye ta, kuma zanyi wa Mrs barr magana nasan ba zaki samu wata matsalar ba indai akan wannan ne”.

Sallama mukayi naci gaba da aiki na, haka kuwa tun da safe ita ce, ta tayar dani daga bacci, dole tasa na tashi muka fara shiri tare da parking ɗin kayan da zamuyi amfani dasu, zuwa tara da rabi Ashiru ya zo mukayi sallama da Ummey muka nufi airport, zuwa ƙarfe sha ɗaya na kira Mrs Nazeer ai kuwa da farin ciki ta zo ta ɗauke mu sai katafaren gidan ta, duk ma’akatan gidan nata maza ne sai “yam mata, masu ƙananun shekaru daga sha biyu sha ukku suke nan,

Wani haɗɗen falo, kafin kace wani abu har an cika muna gaban mu da abinci irin da ban_daban, sai da muka futa sannan muka ci abinci da abun sha, wata yarinya ce, ta kira tazo, ta durƙusa ƙasa idon ta a ƙasa tace, “gani ya shugaba ta”.

Dariya naso nayi amman na dake, Mrs Nazeer ta ce, “jeki ki kai wannan baƙuwar can kusa da part ɗin ku kuma duk abunda take buƙata ki tabbar mata da kin yi mata shi, kada ki yarda ta nemi abu ta rasa”.

Da sauri ta gyaɗa kai, tashi Amrah tayi taja trolley ɗin mu tabi bayan wannan yarinyar, mu kuma muka saka fira inda take tambaya ta, labari na da suna na, nayi dariya na ce, “to yan zun ya ke nan Mrs barr ta ce, kada na yarda ku rigata jin wannan “.

Dariya ta saka ta ce, “kai wato dai wannan Haulman ɗin ta riga mu a komai kuma tafi mu sa’a to mun yarda maji daga baya, amman kin san wani abu kuwa”.

Gir_Giza mata kai nayi, ta ce, “kin ƙara burgeni fa, wallahi, saboda tun yanzun kin fara riƙon sirrin mu, tun da gashi Haulman bata kusa kin faɗi sharaɗin ta, ɗaya daman haka muke so, shiya sa, har yan zun muke tare da Mrs Yaseer saboda tasan komai namu sirrin mu babu wanda bata sani ba, amman har ila yau bata taɓa fitar da sirrin mu ɗaya ba, a gurin kowa, dan haka kici gaba da hakan “.

Dariya nayi muka ci gaba da fira, har sai da Mrs barr ta kira ta ce, mu ƙaraso gidan ta, ta dawo tun ɗazun tana fatan dai Mrs Nazeer bata san komai a kai na ba”

Dariya mukayi haka muka bi ta gurin ɗakin da aka kai Amrah gurin akwai nisa da inda muke, kanar ba gida ɗaya ba, muka kira ta muka fita da direba ta haɗamu tare da sha tara ta arziki, na ce ba zan amsa ba, Amrah ta matsawa ita ce ta amsa, mukayi sallama, direba ya ɗauki hanya sai gidan Mrs barr, him to ai sai naga gidan Mrs Nazeer ba wani gidan bane tun lokacin da muka iso bakin get ɗin gidan nake ji wani irin bugun zuciya sai da na rufe ido da addu’a ɗauke a baki na muka lula cikin gidan, get ukku a na huɗun ne muka tsaya, da sauri wasu ma’aikatan gidan suka zo suka buɗe muna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button