NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Kallon Amrah nayi naga duk a tsorace take sai da na dafata nayi mata murmushin ƙarfin hali sannan ta, fita nima fita nayi baki na ɗauke da addu’a kayan mu aka amsa aka shiga dasu, muka ma muna biye da masu yi muna iso har cikin gidan, faɗar haɗuwar falon ɓata lokaci ne .

Muna isa tsakiyar falon kamar ance mu kalli gurin tv turus mukayi muka zaro ido waje cikin rawar murya na ce……….

Comment and share

Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????

???????? NARJEESAH ????????

Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN

ELEGANT ONLINE WRITERS

Bismillahir Rahmanin Rahim

         3️⃣6️⃣⏯️4️⃣0️⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Cikin rawar murya na ce, “Amrah kin ga wani irin surprise kuwa, wannan tar ba haka, kai am very happy fa, har naji na rage yawan damuwa ta”.

Ba komai bane a burin photon mune nida Amrah a lokacin da muka haɗu a royal hotel haɗuwa ta biyu muna murmushi a jikin photon an rubuta, your welcome pretty and friend da zaiba, kula ga flowers masu masifar kyau a gurin.

Kallon gurin kawai mukeyi, mun shagala da kallo, takun takalmi ne, na jiyo a bayan mu, ana sauko wa daga step juyowa mukayi, da murmushi ɗauke a fuskar mu, itama da murmushi ta ke tafe, tayi shiga ta kece raini.

Ta ce, “ku ƙasa ku zauna mana kamar wasu baƙi?”

Bayan mun zauna ne a saman manyan kujerun gurin da suka kusa make falon duk kuwa da irin girman sa, bayan mun gaisa ne kukun tane ya fara kai komo a gurin, abinci dana sha kamar hauka, har sai da nace, ya isa hakan, muka ɗan taɓa kaɗan, bayan mun ƙarasa ne tace, “please muje daga ciki na kaiki ki futa dan ina son yin magana ne da ƙawata, so sirri ne zamuyi” .

Tashi Amrah tayi dan taga irin kallon da takeyi mata, tare suka bar gurin, ta ɗan jima kafin ta dawo a kisa dani ta zauna tace, “yauwa sunan ki da labarin ki sister nake son ji domin nasan irin taimakon da ya kama ta na baki “.

Kallon ta nayi murmushi na sakar mata sai kuma na ɗaure fuska na ce da ita, “Mrs barr zaki ji suna na da labari na, domin nasamu mafita da sauri dan jina nakeyi kamar saman ƙaya nake, mafitar da zaki bani kuwa ita ce ta sakani naji ƙwarin gwiwar zuwa gurin ki, dan ina son yau idan nasamu mafita nayi amfani da damata gudun a bari ya huce”.

Ajiyar zuciya ta sauke tace “to kafin nan naji sunan naki dana mijin ki da fari”.

Dariya nayi nace, “NARSAL, shine suna na dana mijina, bana saken furta wa kowa Sunan mijina saboda, ina jin kishin wani ya mai_maita Sunan da bakin sa “.

Dariya tayi tace, “amman Sunan yayi daɗi kjn kuma burge ni da kishin da kike yi da badan nasan yanda nake jin kishin mijina ba, da nace, kin fini haukar kishi amman nj nasan kishi gaskiya ne, to yan zun dai muje ga labarin Auren ku”.

Kallon ta nayi na sauke ajiyar zuciya na ce, “Munyi Auren soyayya ne nida shi kulawa muke baiwa jjnan mu, har mukayi shekara da Aure, to a watanni baya da suka wuce, yace, dani haihuwa yake so shi, nikuma ban shirya hakan ba gaskiya ina yar yarinya dani yasa na tsofe da wuri, shine yace zai nemi Aure ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba, aikuwa duk budurwar da ya nema, da Aure har gidan su nake zuwa da wuƙa da guba, nace, su shirya kwasar gawar yar su, idan suka yarda aka ɗaura Auren ta da mijina dan mijina nawa ne ni ɗaya, aikuwa sai a fasa, abun yana yi masa, ciwo duk yan da, ya ɓoye mani zan cen Auren sa, sai na gano sa, to shine ya sauya yake biyar matan titi, ni kuma babu ruwa na da karuwar waje dan matsayin kishiya na ɗauke ta, nasha korar masa matan bari ki shine yan zun, ya gudo wannan garin, kuma gashi har naga nasara, amman ta kubce mani” na ƙarasa zan cen da dafe goshi na.

Ta ce, “tab ai kuwa kin kawo kukan ki inda za’a share maki, ki kwantar da hankalin ki, zan kaiki inda ko sunan mace, yaji ko muryar ta, indai ba ke bace, zai iya ɗaukar ta matsayin mugun abu ke koda uwar sa ce, magana kuma sai kin basa, umarni, yan kin shigo cikin tafiyar mu, amman yan zun zan saka a kaiki gidan Mrs Yaseer da Mrs Naseer, Mrs Yaseer nake son ki jawo muna hankalin ta, a matsayin ki na baƙuwar mu nasan kina da dabarar yin hakan “.

Kallon ta nayi nace, “zan yi wannan ƙokarin amman ke baki bani labarin nasarorin da kika samu ba, ballema naji daɗin yin amfani da wannan nasarorin naki gurin shawo kan Mrs Yaseer ko ya kika gani? “.

Itama ni take kallo, tana saurare na har sai da na dasa aya.

Nisawa tayi tace, “ba zan ji shakkun sanar dake ba, NARSAL amman a takaice ne zan sanar dake “.

Gyaɗa mata kai nayi, a take ta soma bani labarin ta, har ƙarshe, ai kuwa tsalle na doka na ce, “dole ne nayi aiki da wannan damar yan zun ma kuwa, amman yau zaki kaini gurin ko? “.

Dariya takeyi har da tafawa ta ce, “kai NARSAL kin ƙara burgeni tashi dai kije ki gani wan nan Mrs Yaseer ɗin ko zata bamu haɗin kai, amman kiyi amfani wayon ki”.

Tashi nayi, muka fito a jikin motar muka sami Amrah shiga kawai mukayi, direba yaja mu sai gidan Mrs Yaseer ai kuwa da farin ciki ta tarbemu, ta shigar damu cikin falon ta, turus mukayi, ganin mijin ta, zaune yana aiki da laptop ɗin sa, ɗago idon sa yayi muka gaisa dashi a daddare, tashi yayi ya bamu guri muka zazzauna.

Kayan motsa baki ta saka aka kawo muna, mukayi godiya kallon Miss Yaseer nayi naga ni take kallo, nayi murmushi na ce, “to ke ba sai ki sanar damu Mai gidan yana nan ba, kin fa mun zo mun takura masa fa? “

Dariya tayi ta ce, “to dan Mai gidan yana nan sai akace ko wane baƙin ne bana son su gan shi? “.

Cike da mamaki muke kallon ta Amrah cike da dariya tace, “to ke ba kya gudun nayi maki snatched ne madam, kowa ce, na ɓoye mijin ta ke kina nunawa? “

Dariya tayi tace, “ai kuwa tunda mijina ba mugun abu bane sai na nunawa kowa shi Aure fa mukeyi ba zina ba, ballema naji kunyar nuna shi, a gaban idon kowa “.

Dariya mukayi, ta ce, “nasan kin zone kiji ta baki na, kija ra’ayi na, na yarda muje gurin da zamu halaka baƙi ɗaya”.

Da mamaki muke kallon ta, gashi ta ɗaure fuska ba alamar wasa, a tattare da ita, taci gaba da faɗar, “kada kuyi mamakin taya akayi nasan hakan, to a zahirin gaskiya tun farkon ganin ku da nayi da kuma yanda nake a natse ina iya gano cewar ke da wannan yarinyar Yaya da ƙanwa ne, kuma tun daga lokacin da na fahimci hakan sai na ƙara zurfafa tunana, a kanki da abunda kika zo nema,

Tabbas abunda kika zo nema yana nan a kusa dake ki natsu da kyau kada kuyi garaje, kibi komai a sannu zaki fahimci gaskiyar abunda kike son sani, yan zun ki tashi ku tafi kada ku daɗe anan dan kuna cikin tarko ne amman kisan abunda kika faɗa a kai na Allah ya bada sa’a”.

Kallon ta nayi nace, “to kin san da hakan miye yasaka kike biye dasu, kuma kin san cewar hakan yanada illah babba, sannan a iya sani na, biyayya da ƙasda kai a gurin miji da nuna masa kulawa, tsabta tattalin iya girki iya ado kwalliya nuna masa yafi kowa a gurin ki, girma mawa, farin cikin sa shine naki baƙin cikin sa kin fisa shiga damuwa, samun sa shine naki rashin sa, tare kuke da muwa kina kwantarwa mijin ki hankali tare da addu’a sune suke saka, miji yaso mace, har yaji baya iya haɗata da kowa ce mace, to sakacin na miye? “.

Dariya tayi ta ce, “shi yasa nace dake keda yar uwar ki, kallon farko na fuskaci akwai abun da kuke nema, ku tashi kuje “.

Tashi tsaye mukayi, Amrah ta ce, “naga alamar sun tsoratar dake da yawa, kuma na fahimci cewar ke mace, ce mai sanin ya kamata Allah ya ƙara danƙon soyayya keda Yaya na “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button