
Da Amin muka amsa muka fito da mijin ta muka haɗu ya ce, “har kun fito Mrs Salman? To Allah ya bada sa’a”.
Ganin irin yanda muka zaro ido waje nida Amrah kawai yayi murmushi ya raɓamu ya wuce war sa, ssi da ya shige ciki sannan muka dawo da idon mu a kan ta murmushi kawai tayi muna, tayi gaba abinta, tayiwa direban ta, maganar inda zai kai mu, tunda wancan direban yayi tafiyar sa.
Jikin mu a sanyaye muka shiga motar ita kuma ta komawar ta cikin gidan ta, muka ɗauki hanyar gidan Mrs Naseer, itama da farin ciki ta tarye mu, amman har yan zun nida Amrah bamu ce da junan mu uffan ba, ganin yanda muka shigo cikin yanayin damuwa ne, ya saka Mrs Naseer tace, “I hope everything is fine, kodai Mrs Yaseer tayi maku wani zan cen ne akan mu? “
Gir giza mata kai nayi, na sauke ajiyar zuciya nace, “Mrs Yaseer tayi nisa bata jin kira mijin ta ya kafe ta, ya hure mata kunne bata jin zata iya aikata irin hakan, ke a gaban idon mu ma cewa yayi baya hana ta kwashe_kwashen abokai ba? Shifa baya son ganin ta da ƙawa ko ɗaya fa, dan haka mu tashi mubar masa, gidan sa, haka kawai daga ganin mutum baƙuwar fuska sai ya yarda dashi? “.
Zaro ido waje tayi ta ce, “a gaskiya bai kyauta ba, amman ni banga wani laifin sa ba, ke nima fa nayiwa kaina karatun ta natsu, ba zan koma aikata irin aika_aikar da mukayi ba, abaya ba, dan haka kema ki janye kanki daga aikata irin wannan mugun nufi da kika tsirowa kanki”
Kallon ta nayi nace, “ke koda ni ɗaya ce a wannan tafiyar tunda nayi niyar cika burina sai ya cika, ba zan janye akan baka na ba, kuma ki rubuta ki ajiye ni NARSAL sai na baku mamaki “.
Na kalli Amrah na ce, “ke tashi muje “.
Da ido ta bimu sake da baki, Amrah tace, “idan ke gwiwar ki ta kwance, to mu yan zun muka ɗaura ɗamarar tun karar filin daga, dan nima sai na shiga a cikin wannan tafiyar mun bar ki lafiya “.
Fita mukayi sai kiran mu take tana mu tsaya, amman muka shareta muka nufi direban ta, nayi masa bayanin inda zai kai mu, aikuwa muna shiga yaja mu sai gidan Haulman direba ko parking bai gama gyarawa ba, na fito nayi cikin gidan da sauri, ai kuwa a tsakiyar falon muka sameta ta da sauri taja hannu na ta zaunar dani, taje ta ɗauko ruwan Ever ta bani nasha, ta zauna tayi murmushi tace “ita fa Mrs Naseer da wasa take yi maki, dan ta gwada ki ne taga ni, kodai Mrs Yaseer ta sauya maki tunani ne”.
Kallon mamaki nakeyi mata, ta ce, “kwarai kuwa, ni nasan halin kowa daga cikin su, dan haka ki kwantar da hankalin ki, ke gama labari mai daɗin ji, yau da dare zamu tafi gurin nan ina fatan yan zun hankalin zai kwanta”.
Murmushi dayi wanda har haƙora na suka bayyana, na ce, “haba yan zun naji zance nikam”.
Dariya tayi tace, to jeki na nuna maki ɗakin da zaki zauna kafin na zo da dare misalin ƙarfe sha biyu na dare, sai ki shirya da kyau “.
Dariya nayi nace “Aa yau zan kwanta ne tare da wannan yarinyar saboda tsaro kin san yan zun akwai waya hannun ta, kada muyi sakaci”.
Ta ce, “yauwa shiyasa kike ƙara shiga raina dan akwai ki da saurin fahim ta “.
Ɗakin da Amrah take ciki anan na shiga kwance na sameta, nima na zauna a kusa da ita, ita kuma ta ce, “idan kuna ɓukatar wani abun kuje kichin da kanku kuma idan kuna son miƙe ƙafa ku shiga duk inda kuke so, ni zan shiga daga ciki zanyi bacci na tun yanzun “.
Dariya mukayi ta juya ta fita, ni kuma wanka na shiga na sauya kayan jiki na, haka ma Amrah, zaga gidan muke son yi, ai kuwa muka fito nida Amrah mun sha yawo kafin mu dawo cikin ɗakin, waya na ɗauka na shiga cikin bayi, na kira mukayi magana na fito, nida Amrah mukayi sallar magriba muka zauna akayi isha’i mukayi, muka kwanta can misalin ƙarfe goma da rabi, muka tashi nida Amrah muka fito ta bayan wani corridor da muka gani da addu’a ɗauke a bakin mu, muka fita, ta jikin flowers muke bi cikin sanɗa cikin ikon Allah sai gamu a jikin ƙofar mai gadin gidan wanda Miss Yaseer ta bani a rubuce, a test message ɗin da tayo mani,
Ƙwan ƙwasa ƙofar ɗakin mukayi aka ɓude da sauri muka shiga cikin ɗakin aka rufe ana rufewa ta jikin window na hango security suna dube_dube, ajiyar zuciya muka sauke a tare glub ne aka kunna ɗakin yayi haske ta ko ina, mutum ne muka gani zaune akan sallaya ya bamu baya, kuma sallah ce yakeyi, kallon sa mukeyi amman gaban mu faɗuwa yakeyi, nikam harda dafe zuciya ta ina karanto duk addu’ar da tazo baki na, sallame sallar yayi, addu,oi yakeyi sai da ya jima kafin ya tashi tsaye ya ɗauki sallayar ya fara lunkewa, juyowar da zaiyi kawai muka saki baki da hanci muka zaro ido waje muna nuna mutumen da hannu,
Shima mu yake kallo ya zaro ido yana, kallon mu cike da mamaki kawai ya dafe kai yayi luuuu…. Ya tafii… Zai faɗi ƙasa kawai, aka taro sa kafin mu ƙarasa kaiwa gurin har numfashin sa ya ɗauke ɗab.
Cike da tsoro da kukan daya kubce muna, nida Amrah mukayi kansa, shi kuwa wanda ya taro sa, shine yayi dubarar ɗauko buta, ya ɗebi ruwa a hannun sa ya shiga yayyafa masa, ai kuwa cikin ikon Allah sai gashi ya fara buɗe idon sa ya sauka akan wanda ya yayyafa masa ruwan ya kafe sa da ido yace, “Da gaske Salman abunda nake gani da ido na Narjeesah ce, da Amrah a gaba na ko kuwa mafalkin da na saba yin sane? “.
Jikin sa muka faɗa cikin kuka na ce, “da gaske ne Baban mu nice Narjeesahr ka, tare da Amrah a gaban ka, ba mafalki bane, daman sai da na faɗa masu cewar baka mutu ba, amman suka ƙaryata ni”.
Shafa kaina ya keyi, nida Amrah, Amrah ta ce, “Baba mi yasa ka ƙi dawowa a cikin mu gashi gidan mu duk ya watse, akan yarka abar kaunar ka da jarabawa ta faɗa mata, amman idon wasu ya rufe Baban mu, Anty Narjeesh tasha wahala sosai nasan da kana a kusa ne da wanda ya isa ya aikata muna irin wula’kancin da akayi muna Baba! “.
Share muna hawaye yakeyi ya ce, “yan zun ba lokacin labari bane, saboda ƙurewar lokaci nima yan zun ne ganin ku nadawo cikin hayyacina da kyau na gane waye ni kuma na gane garin dana fito da iyalai na”.
Da sauri na tashi zaune kallon Salman nayi sai yan zun ne, na ma gane shi ashe shine ya riƙe Baba ya hana sa faɗuwa ƙasa, ai kuwa muka haɗa ido na banka masa harara, shi kuma yayi murmushi, yayi ƙasa da muryar sa, yace, “wato kin kawo kanki gida na bama kijira har a kawo mani ke, kin ga yaro ɗan shala son kowa ƙin wanda ya rasa, kin biyosa har gidan sa”.
Kallon kama raina mani da wayau na bisa dashi, nayi ƙasa da muryar ta nace, “malam kama shirya bani takarda ta, dan ina gama haɗa aikin da nazo yi a gidan ka, zan koma ƙauyen mu”.
Harara ya watsa mani nima ramawa nake yi Amrah ce, tayi gyaran murya tana dariya ƙasa_ƙasa, kallon ta mukayi a tare sai muka ga ita da Baban duka idon su na akan mu, waskewa nayi, nace, Baba wane gurin ne aka ɓuye Shuraim? “.
Da sauri ya ce, “shin Amrah wane Shuraim Narjeesah na take faɗa ne? “.
Salman da sauri ya ce, “Abba ɗan mune nida ita, wanda muka haifa, shine aka kawo a gidan nan “
Sakin baki mukayi nida Amrah muna kallon sa cike da mamaki cikin jin haushin sa, nace, “ai daman kasan inda aka kawo sa, kayi kunnen uwar shegu dashi, ka barni ina ta wahalar da kaina har da kuka, kullum cikin kuka”.
Na ƙarasa maganar ina murguda masa baki.
Cike da masifa ya taso mani, nima nataso masa, Amrah tace, “dan Allah ku bar wannan rigimar haka nan mu fuskan ci ƙalubalen dake gaban mu, kuma a gaban Baba kuke wannan rigimar taku da bata ƙarewa”.