NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Sannan ta ce, “Baban mu yaron da aka rufe a gidan nan wanda Miss Yaseer ta baka kulawa da cin sa, da suturar sa, shine muka zo nema a gidan nan, kuma yaron su Yaya Salman ne da Anty Narjeesh wanda yake tsakanin su”.

Cikin sauri Baban yace, “ku tashi da sauri muje ku gani kafin a riga mu ɗaukar sa”.

Da sauri Salman ya ce, “ba zasu riga mu garesa ba, dan na zuba mata maganin bacci, kuma tayi baccin, sai dai masu yi mata aikin, masu tsaron gidan nan, amman nasan yanda zanyi dasu”.

Tashi mukayi muka buɗe ƙofar cikin sanɗa muke tafiya muna kusa da shiga cikin ɗakin ne aka taƙa muna bindigogi ai da sauri nadawo bayan Salman na rungume sa, na rufe ido gam, saboda nafi kusa dashi Amrah kuma ta shige jikin Baba, wani daga cikin wanda suka taƙa muna bindigogin ya ce, “ku juya ko kuma mu kashe ku mu kashe banza”.

Ai kuwa da sauri Salman ya juyo ni nadawo gaban sa ya riƙe ni, ya kalle su, ɗaya bayan ɗaya, ya ce, “to ku aikata mana kuga abunda zai faru, kuma kubar gidan nan tunda ba gidan uban ku bane, jahilci banza da yofi! “

Ai da sauri suka juya suka bar gurin cikin tsananin tashin hankali, sakin sa nayi ina sauke ajiyar zuciya haka Amrah cikin ɗakin muka shiga kwance yake cikin duhu sai da muka kunna fitilar waya muka hango shi kwan ce cikin sanyi sai rawar sanyi ya keyi, ai da gudu muka isa, gurin sa har muna rige_rige hawaye keta ambaliya a idon kowa rungume sa muka, cikin kuka da tausayin yaro na na ce, “Shuraim tashi ka gani ga Mommyn ka a tare da kai, da Anty Amrah da Daddyn ka da kakan ka, kaji yaro na!? “

Buɗe idon sa yayi, ai kuwa ya fashe da kuka ya shige cikin jiki na ya rike ni da ɗan ƙarfin sa, ya na kuka kamar ran sa zai fita, nima ƙara shigar dashi nayi jiki na, sai kuka mukeyi sai jiki na ke rawa, amsar sa Amrah tayi ta rungume sa, itama kukan takeyi haka, Salman ansar sa yayi, idon sa yayi ja saboda tsananin ɓacin rai, jijiyar kansa duk sun tashi sunyi ruɗu_ruɗe, haka Baban ya anshe sa ya rum gume sa a jikin sa.

Mun kusa awa ɗaya a gurin, Salman ya buɗe bakin sa da ket ya ce, tashi muje na raka ku ɗakin da zaku zauna ba tare da kowa ya san mike faruwa ba, kai kuma Baba ka koma bakin aikin ka insha Allah ba zasu fahimci komai ba”.

Ɗaukar Shuraim ɗin yayi ya janyo hannu na, ya ce, “muje Amrah “.

Muka fito waje ta wata ƙofar yabi damu, ai kuwa sai cikin gidan har ƙofar ɗakin da muke da kayan mu a cikin sa, yazo zai wuce da sauri na ce, “wannan shine ɗakin da kayan mu suke ciki”.

Kallon Amrah yayi ya nuna mata ta buɗe, ai kuwa ta buɗe muka shiga daga ciki a, tsakiyar gadon ya kwantar da Shuraim nima ya janyo hannu na, ya ce, ki kwanta, anan sai ki san dabar da zakiyi kafin ta shigo cikin ɗakin ki fito falon ki zauna, Amrah ke kuma ki kula da motsin Shuraim kin dai san wane mataki, ake cikin sa yan zun gashi yan zun ƙarfe biyu ta kusa na dare, kar ku ɓata lokaci please”.

Gyaɗa masa kai mukayi, ya juya ya fita, muka rufe ɗakin muka kwanta, muka sanya Shuraim a tsakiyar mu, muna shafa sa har yayi bacci.

Waya na ɗauko nayi ta kiran layin Mrs barr amman ba’a ɗauka ba, Mrs Nazeer na kira, tayi saurin ɗauka, na ce, “kin kira layin Mrs barr kuwa?, nifa nayi ta kiran ta, har yan zun babu reply, to kodai kunyi tafiyar ku ne kun bar ni”.

A cikin damuwa nake maganar gashi murya ta muryar kuka ce, dan har ta soma shaƙewa.

Da sauri ta ce, “nima fa tun ɗazun nake kiran ta, babu, reply anya dai ko mijin ta ya dawo ne, ta manta da maganar cika alkawarin bokan, ai kuwa kada tasa mu tafka asara, ki kira muna Mrs Naseer mu gani ko suna tare? “

Kashe wayar mukayi, na shiga kiran wayar Mrs Naseer itama sai da nayi mata kira ukku ta ɗaga, na ce, “haba taya zakuyi tafiyar ku, kubar mu, nida Mrs Nazeer, sai kiran wayar Mrs barr mukeyi taƙi ɗagawa kema sai da nayi kira ukku zaki ɗauka, da kun san ba zakuyi dani ba, da baku sa na kwaɗai tuba, da wannan aikin haba dan Allah! “.

Cikin tashin hankali tace, kika ce bata ɗaga wayar ki keda Mrs Nazeer anya kuwa tana lafiya dan ban taɓa ganin ta kasa cika wannan alkawarin ba, bayan daga wannan ta gama wahala nifa inada shakku a kai, indai ba ta ɗauki wayar ku ba, to batada lafiya, nima bacci ne ya sace ni dan ina zaune ina jiran ta kira ni, amman shuru kake ji kamar anshuka dusa, gaskiya da alamar tambaya “!?.

Kashe wayar mukayi muka ci gaba da kira ba amsa har Asubahi Amrah kuwa murmushi takeyi, tana ƙara gyara wa Shuraim kwanciyar sa, alwala muka ɗauro muka fara nafila, har aka kira assalatu, mukayi raka atainin fijri, mukayi sallar Asubahi, mukayi lazumi da azkar, sannan na fito cikin falon gidan nayi zaune na buga uban tagumi, sai kusan ƙarfe takwas ta fito a har gitse bata ma lura dani ba zata raɓani ta wuce nayi saurin shan gaban ta.

Na ce, “madam miye ya same ki ne mukayi ta kiran ki duk hankalin mu a tashe? “

Dafe kai tayi ta zauna daɓas a ƙasa tace, “nashiga ukku ni Haulart na rasa wannan damar ban san miye ya same ni ba, nayi wannan kuskuren nayi bacci mai mugun nauyin gaske, kira mani su a wayar ki suzo yau a gidan nan mu san abunyi, tun kafin guguwar nan ta taso ta dun ƙule guri ɗaya ta haifar da illar da aka ce, zata shafemu dukan mu! “.

Gir giza mata kai nayi, na ce, “duk suna a hanyar zuwa gidan nan saboda kowa da far gaba ya kwana saboda kiran da mukayi ta maki harda Mrs Yaseer a ciki “.

Shiru mukayi dukan mu ƙofar aka buɗe Miss Nazeer Mrs Naseer Mrs Yaseer a tare suka shigo a har gitse dukan su, indon su na akan Haulart saboda yan da duk ta birkice.

Mrs Nazeer ce ta ce, “Bafa zama zamuyi ba, kawai shawara ce, zamuyi mu samu mafita “

Mrs Naseer ta ce, “mafita kam babu ta, ta tashi kawai ta shirya mu ɗauki saƙon mu doshi cikin dajin nan wannan shine mafitar kawai “.

Ai kuwa duk sunyi na’am da wannan shawarar da sauri ta shiga cikin ɗakin ta har tan tun tuɓe da capet, ko wanka batayi ba, ta chanza kayan jikon ta, ta fito ko mayafi babu.

Kallon su nakeyi cike da mamaki Mrs Yaseer ta ce, “kinyi brush kuwa?.

Cike da masifa Haulart ta ce, “ke brush ya dama ni damuwa ta, ta fiye mani komai malama, kallona sukayi suka ce, muje, kada ki sa mu ƙara ɓata lokaci “.

Waya tace tayi ringing na ɗauka, nayi shiri na ajiye wayar na kalle su da kyau na ce……..

“Comment and share*

Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????

???????? NARJEESAH ????????

Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN

ELEGANT ONLINE WRITERS

Bismillahir Rahmanin Rahim

           4⃣1⃣⏭4⃣5⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ kafin na furta wata kalmar, Mrs Yaseer ta dakatar dani gurin faɗar, “kamar motar mijin ki nagani a waje shida yaran sa, kodai ido nane yake yi mani gizo? “

Cikin da mamaki Haulman ta ce, “barrister ka? ki kagani kuwa? “.

Da sauri Mrs Nazeer ta ce, “kina nufin cewar baki san ya dawo ba ko miye? “

Cikin fushi ta ce, “taya zan san ya dawo ne, bayan nayi nauyin bacci amman wallahi sai ya haɗu da fushi na, bari nadawo gurin da zani zai gane kuren sa wallahi, ke kuma NARSAL tashi muje dallah! “

Dariya nakeyi harda dafe ciki na gir giza kai na, nace to ina ajiyar taki ne ko duk fushin yasa kin manta ne”.

Tsaki kawai tayi tace, “nama manta ne” da sauri ta nufi hanyar kichin, ni kam da ido nabi bayan ta dashi, tayi kusan mintina goma sai gata ta dawo a har gitse cikin tsananin tashin hankali, ta ɗora Hannuwan akai duka biyun ta kwatsa uban ihu tana faɗar, “na shiga ukku na lalace sun sace, mani shi sun gudu dukan su, ban same su ba! “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button