NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Tafaɗi ƙasa tana shure_shure ƙafafuwan ta, a ƙasa, kowa cike da tashin hankali suke faɗar su waye ne wai!?.

Ƙofar da ta fito take nuna masu, duk suka saka salati suna faɗar, “mun shiga ukku dai zaki faɗa” duk sukayi zaune daɓas a gurin da suke, ai kuwa wata irin uwar dariya ce, na kece da ita har ina tafa hannu, na tashi tsaye ina kallon su ina ci gaba da dariyar, ai kuwa suka tsare ni da ido cike da mamaki in banda Miss Yaseer.

Takowa nayi har inda suke ina fara zagayen su duk su ukkun, ina tafa hannu, sakin baki da hanci sukayi suna kallona harda murza ido.

Sai da na gama zagayawa na tsaya a tsakiyar su, nace, “to yau dai anyi walkiya an haska kowa, yau ne zaku girbi abunda kuka shuka, Miss Nazeer Mrs Naseer Haulman, ina son ku bani aron ɗan sauran hankalin ku da ya rage a nan, tun kafin ya ƙarasa ɓacewa”.

Kallon su na sakeyi ɗaya bayan ɗaya, na sauke mayafin nawa na ɗaure a ƙuna, na ci gaba da faɗar, “Amrah…! “Da ƙarfi yanda zata jini, na ce, “ki shigo daga ciki mana”.

Ai kuwa duk suka maida idon su gun da Amrah ta fito ai duk sai suka tashi a tsaye suna sauke ajiyar zuciya, harda su faɗar wai har hankalin mu ya kwanta a gaskiya ki daina yi muna irin wannan wasar yan zun ba lokacin wasa bane, da sauri Mrs Naseer tayi niyar tun karar gurin su Amrah wadda take ɗauke da Shuraim a hannun ta,

Da sauri na dakatar da ita gurin faɗar, “dakata saurin miye kikeyi ne, ai bari kiji ƙarshen zan cen wanda kike ɗaukar sa da wasa, wannan yaron da kuke gani da kun san waye shi da hankalin ku yafi hakan tashi ba kamar Haulman “

Sake ɗaure fuska nayi ganin irin kallon da suke bina dashi naci gaba da faɗar “yan zun lokaci yayi da wannan guguwar da kuke tsoro zata haɗu guri ɗaya” Shuraim na kalla ina murmushi na ce, my lovely Son Come with me, “

Ai kuwa da gudu ya sauka jikin Amrah yayi kaina da gudun gaske ya ce, “Mommy I miss you “.

Da sauri na ɗaga shi sama ina juyi dashi muna dariya ina faɗar ɗan farin fitilar gida, ɗan farin mai maye gurbin soyayya ko wace, iri ce, ina son ka ɗana ɗan albarka “.

Dariya mukeyi, cikin giɗima da fir gita suka haɗa baki gurin faɗar, “ɗan kiii…..! Kuma!? Ta ya ya hakan ta faru ne!?…. Kodai kinyi hauka ne!? “.

Kallon ban za nayi masu nace, “eh amman ba irin taku haukar ba, yan zun ɗan wannan abun har ya isa ya firgita ku hakan kuma harda zufa, ina ga nace, daku Shuraim ɗan manyan mutane ne, ɗan masu mulki masu, gari ba irin muƙamin iyayen wasu ba, wanda suke ƙare rayuwar su a gidan yari ba? “

Sannan na ce, Shuraim ina Daddyn ka su gan shi, ko da yake nasan yana kusa bisimillah “.

Ƙofar falon suka maida idon su dan ganin mai shigowa, kawai suka ga Salman ya shigo, suka ƙara kafe ƙofar da ido ko zasu ga wani ya sake shigowa amman sai sukaga babu kowa a bayan sa, sai suka maida idon su a kaina suna yi mani kallon raini.

Dariya nayi nace, “Shuraim Daddy…! ” na nuna masa, ai kuwa da gudu yayo kan Salman, shi kuwa ya durƙusa ƙasa, ya tara masa hannu ya ɗauke sa, ya shigar dashi cikin jikin sa, yana juyi dashi, suna dariya.

Ai sai Haulman ta daka masa uwar tsawa kamar wani bawan ta, ta ce, “wannan wane irin salon wulaƙanci ne, malam ku ajiye wannan diramar haka, kuma wallahi sai ka gamu da matsanan cin fushi na! “.

Dariya ya yi, ya tako yazo inda nake, ya haɗani da Shuraim ya rungume mu, ya sakar muna pick ni a goshi Shuraim a kumatu, wani irin uban ihu Haulman ta saka, tayo kan mu amman kafin ta ƙaraso, taji muryar Salma na faɗar kada ki kus kura ki kai gurin da suke wallahi idan kuma ba haka nan ba, jikin ki ne zai gaya maki! “

Da sauri suka maida idon su akan Salma, sai suka ga Muhseen a tsaye yana murmushi shida Salma, Muhseen ya ce, “bisimillah ku shigo daga ciki “.

Ai kuwa Mai martaba ne ya fara shigowa shida fulani da Mom da Dad, sai Naseer da Nazeer da Yaseer, da Jafar Aliyu Humaira Hindu Auta Nusaiba sai Baban mu, hannu duk suka ɗora akai cikin fir gici, suka faɗi zaune sai jikin su ke rawa.

Salma ce tayi gyaran murya tace, “Narjeesh kici gaba please “.

Ni kuwa muna can muna halin da muka saba, mintsil sa nakeyi, harda cizo idan na faki idon mutane, shi kuwa magana yakeyi ƙasa_ƙasa, “yarinya komai abun ki tunda kika kawo kanki gida na ba zaki koma zuwa wani gurin ba, ehe! Kima zauna a kusa da mijin ki uban “ya”yan ki, wata kila naɗan sama maki guri a zuciya ta”.

Tsaki na doka masa wanda ya fito fili, Amrah tace, “Auta jeki gurin su, kiyi masu magana suna can suna aikata halin su”.

Ai kuwa da gudu tayo kan mu ta rungume ni ta baya, tana faɗar, “Anty Narjeesh nayi kewar ki keda my Shuraim”.

Sai alokacin ne ya sakeni na jiyo na run gume Nusaiba muna dariya Shuraim da sauri ya ce, “Anty nima ban ganki ba, ki ɗauke ni ki goya ni kuma ki rama mani dukan da wan can tayi mani taci zali na, harda baki na ta doke har da jini da hannu na, kuma bata bani abinci bata, goya ni inyi ta kuka kuma bana buga boll bana, yin komai…! “

Hannun sa yana kan Haulman yana nuna ta da yatsan sa, da sauri Nusaiba ta ɗauke sa ta fashe da kuka tayi gurin Amrah dashi, itama Amrah kukan takeyi shi kuwa Baban ganin Nusaiba bata gane sa bane ya saka shi kamo hannun ta ya zaunar a kusa dashi, ya anshi Shuraim yana goge masu hawaye yana lallashin su.

Kallona, na maida akan, su Haulman naci gaba da faɗar, “Haulman kike koma waye, nasan yan zun kin fahimci wani abun, amman bari kiji yanda abun yake, na shigo cikin kune da tsabar wayau na da ɗaukar fansa, da ceto yaro na, Haulman tun kafin nazo garin nan nasan ki da ƙawayen ki da halin ku baki ɗaya, sai dai sam ban riga da nasan halin Miss Yaseer ba, sai da naji daga gareku, him! Haulman kama Dila sai an shirya tunda shi sarkin dabara ne, shi yasa sai da na shiryo na shigo cikin ku,

Tun ranar da kika sanar dani cewar Sunan ki Haulman ne, na fahimci Sunan ki ne dana Salman, ma’ana Haulart Salman, shine kika haɗa farkon sunan ki da ƙarshen sunan Salman, wato Haul Man, ni kuwa shi yasa na , buɗe sunan naku wato Haulart Salman, nayi dariya nima shine na sanar dake, NARSAL wato, Narjeesah Salman, kin ga na ɓatar dake, tun daga nan nabaki labarin dana ƙir ƙira, da kaifin basira ta, dan na daki cikin ki, naji sirrin ki, kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu, nasan komai naki kuma na sami yarina ƙarin farin ciki harda mahaifina na”.

Na nuna Baban mu, da hannu na, da sauri Nusaiba ta kafe sa da ido ya sakar mata murmushi ya rungume ta, haka gurin kowa yake mamakin taya hakan ta faru.

Kallon Yaseer nayi nace, Yaseer a jiya dana tafi gidan ku, kai da matar ka, ban san tan da akayi kuka gane wace, ce niba, kuma narasa taya akayi har kuka san shiri na wallahi badan matar ka, tayo mani test ba, akan kada na yarda da nadamar Miss Naseer ba, da kun saka asiri na ya tuno, amman Allah ya kyauta, Haulart ni ban taɓa kawo wa kaina cewar zaki iya sace, Shuraim ba, saboda nasan baki san niba, baki san wace ce niba haka Shuraim duk da kuwa kammanin Salman da ya ɗauko, na manta cewar kina bibiyar duk wani motsin Salman, kuma na manta cewar zaki iya aikata komai akan Salman, sai da aka lurad dani hakan na fahim ta, koshi kuwa sai da su Jafar suka tuna sar dani cewar har na manta yanda akayi kika sato ni kika haɗa da mijin ki har zan kasa fahim tar, aikin ki? “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button