
Maganar ta daki zuciya ta tayi tsaye Inno kuwa tace, “mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege bai sani ba ko ya haifa” muka raɓata muka wuce, ashe taji haushin amsar da Inno ta bata, aikuwa Mama ta saka masifa tana faɗar ni wallahi babu abunda zaku iya yi mani duk taron ku mutanen gidan nan kuma ni ban haifi shege ba dan yara na duk sun girma ballema kice mani ina da yara a goye, ita dai ce da ta haifi shegen akafaɗa kuma na faɗa wata ta haifi shege”.
Duk abunda takeyi babu wanda ya kulata, saboda magagganu take saki wanda babu wanda yasan manufar ta, shi yasa kowa ya fita iskan ta.
Da yamma zuwa ƙarfe biyar bayan anyo wankan marece ni kuwa ina gyara wa, Su Yayan mune duk suka shigo cikin ɗakin Inno su takwas duk maza mata ukku masu Aure da sauran wanda basu da Auren da ƙanen mahaifin mu da matan sa harda yaran sa duka, duk sukayi tsaye suka zuba mani ido.
Ni kuwa na saka kayan da Yaya ta fito mani dasu harda hijab na ɗauko mai zan shafa ke nan, sai na saki man domin na shiga tashin tsananin tashi hankalin wanda ba’a sa masa rana, gashi mutanen duk fuskar su a haɗe take, Goggon muce ta shigo cikin ɗakin a har gitse ganin yaron a hannun Inno kawai cikin fushi tace…..
Comment And share
Yin comment din kune zai bani amsar karɓuwar littafin
Ummu Ihsan ce ????????????????????????????
???????? NARJEESAH ????????
RUBUTAWA, DAGA ALƘALAMIN:-
NANA KHADEEJATU UMMU IHSAN
YA ALLAH KAJIƘAN IYAYE NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SADA SU DA RAHMAR KA ALLAH KA SANYA SU DAGA CIKIN DAUSAYIN ALJANNA ALLAH DASU DA DUK KANNIN YAN UWA MUSULMI BAKI ƊAYA AMIN YA ALLAH
_BISMILLAHIR RAHMANIN
*3&4*
➿➿➿➿➿➿➿➿
Tace, “wannan wace irin masifa ce? A gidan ɗan uwana akan “yar da yafi ƙauna a rayuwar sa, wannan shine ake kira da baya ta haihu ke nan! An maida gidan Yaya na gidan tara shegu, Narjeesah sai da kika ɓata sunan gidan nan, to wallahi ba zamu ɗauka ba, yan zun nan zamu ɗauki mata ki akan abun da kika aikata, kuma duk wanda yake da niyar aikata makaman cin irin abunda kika aikata, idan yaga hukunci da ya hau kanki sai ya gyara idan yaso yin hakan! “
Kawu Bala yace cikin masifa, “ai dama na daɗe da yanke hukunci shiru kawai nayi tagama haife abunda ke cikin ta, to bari kuji hukunci da na yake ku a gurin ku ya yi kuwa ko kuna da ja acikin sa? Yau ɗin nan za’a raba maku gado kowa ya kama kansa wanda suke da yawa kuma suke da abun siyen gidan nan ko kuma sukaci gidan nan su zasu zaune shi, saura kuma kowa ya kama gaban sa! “
Ai kuwa da sauri Mama tace, “nida yara na mun yarda ku tambayi sauran yaran da kanku kada kubi ta iyayen su dan zasu hana su ƙwatar “yan cin su”.
Zuciya ta nake jin kamar zata fito daga cikin ƙirjina, sai dafewa nayi ina karanta duk abunda yazo baki na.
Su Yaya Auwal suka ce duk abunda kuka yanke bamuda ja, da a bata muna sunan gida, gara kowa ya kama kansa”
Su Basira murna kamar su zuba ruwa ƙasa su sha, Inno dai kallon kowa takeyi yaran ɗakin ta sam sun nuna basu son ayi hakan, Amman ɗakin Yaya idan ka cire Yayar da yaron ta Mudarsir sune kawai basu yarda ba, sauran kuwa duk sun yarda mu kuwa muda ba’a bakin komai muke ba ba a bi ta kan muba kawai suka fita aka kira dillalai akayiwa gidan kuɗi akaje aka duba gonar Baban mu, suka je gurin malamai akayi rabon, muda muke zaune a gidan su goggo da Mama da sauran su Anty Asma dasu duk suna kasa sun tsare sunƙi fito cikin ɗakin, har su kawun suka shigo gidan.
Kiran Umma na akayi da ƙanne na a take kawu ya fara magana wadda ban san ranar da zan iya man tawa da ita ba, yace, “to an raba maku gado daman nasan shi su Narjeesah suke jira ita da Umman ta, dan hakane suka tsiri ɓatawa gidan nan suna, to Allah ya fiku, ga abunda kuka samu dubu ɗari biyu da saba’in ku dukan ku, yan zun sai kuzo ku bar gidan nan ku kwashe kayan ku, yau_yau ɗin nan nake buƙatar kubar gidan nan! “
Inno tace, “wannan wane irin rabon gado ne haka da rana tsaka, kuma kuce ga abunda suka samu bayan baku sanar da abunda kowa ya samu ba? Wallahi wannan ba adalci a cikin sa, indai ba zalunci kuka tsaro ba”.
Cike da masifa akayo kan Inno wadda su Yaya jafar suka dakatar tare da faɗa, “sufa bazasu ɗauka ba kuma gaskiya Inno ta faɗa”
Rigima ce aka sanya kowa ya faɗi albarkacin bakin sa, Yaya tace, “kowa a sanar dashi abunda ya samu dan gaskiya nima ban yarda ba”.
nan dai aka ce, Mama mai “ya”ya maza su shidda mata ukku sune sukaci rabin gidan duk girman sa, Inno da take da “ya”ya maza biyar mata hudu, taci kusan rabin gidan kaɗan aka rage ɗaki ɗaya da zaure, sai aka baiwa yaron Yaya ɗaya wannan ɗakin da Zauren, sai aka koma gona, inda muda sauran su Yaya aka rabawa gonar.
Umman muce ta shigo cikin ɗakin ba tare da tayi magana ba, kawai ta bashi hannun ta, a take duk suka zuba mata ido shi uban gayyar kuɗin ne ya watsa mata, wanda duk muka zaro ido waje muna kallon wannan wulakancin.
Umma tace, “nagode sosai fa” Sannan ta dubi tace “Inno mun gama shirya wa ga su Amrah can suna fitar da kayan mu ina ga ma sun kusa kwashe wa dan basu ɗaya bane harda yaran, unguwa zamu tafi duk wanda muka yiwa laifi to yayi hakuri”.
Babu wanda yayi magana daga cikin su, Umma ta dubeni tace, “Ke! kuma ki tashi ki baiwa masu gida gidan su ki fito ga mota can tana jiran mu”.
Kafeni da ido Umma tayi wanda a tarihin rayuwa ta shine na farko haka zalika a tarihin rayuwa ta wannan shine maganar da Umma ta taɓa yi mani a cikin mutane jikina sai rawa yakeyi, ashe bani ɗaya ba, duk wanda yake gurin yasan Umma yau anyi mugun cika ta, dan ita sam bakajin bakin ta koda kuwa kashe ni za ayi a gidan mu kuma bata taɓa yi mani magana ba, koda a cikin ɗakin mune ballema acikin mutane.
Tsaye tayi, har sai da ƙanwata Amrah tazo a gaban Inno ta tace, “Inno bani ɗan albarka na nan gurin abun sona farin cikin rayuwar mu wannan yaron da kike gani ya shige a cikin zuciya ta, yaron nan daga gani mujaheed ne dan zaiyi taimakon addinin Allah da taimakon mutane, shi daga ganin sa ba zaiyi aiki da jahilci ba kuma, bazaiyi aiki irin na jallai ba”.
Dariya Inno da Yaya sukayi dan kowa yasan Amrah ta sakar wasu kawu Bala magane, Inno tace, “amman kuwa kin zaba masa sunan da ya dace dashi dan Allah ki riƙa kawo mani shi ina son shi wallahi har cikin raina, Allah sarki Allah ya rasa rayuwar musullunci” amin aka faɗa.
Yaya tace, “kice dai a riƙa kawo muna shi duk da muma cikin satin nan zamu bar gidan nan amman ni kun san gidan da nake dashi wanda na bada haya a can zan koma, dan Allah ku riƙa kawo muna shi Allah ya rayasa Allah yayiwa rayuwar sa albarka Allah yasa ya zamo farin ciki a garemu baki ɗaya amin “.
Amrah ta ansa ta goya shi,Nusaiba na shigowa ta raɓa kowa tazo ta kwashe kayana da suke ɗakin Inno ta rufe jakar ta riƙa hannu na tabi ta gaban Umma dani muka fita, Inno ta share hawayen idon ta, tazo ta anshi kuɗin wanda kowa ya kasa ɗauka ya bata, ita ta ɗauka ta baiwa Umma, Umma ta ce, “to mu yafi juna Allah yasada mu da alkawarin sa”
Fita Umma tayi ta duba ɗakin taga babu komai tayi murmushi ta juya zata fita Inno da yaran ta, da Yaya da yaron ta suka rako Umma har gurin mota, Inno ta dam ƙawa Umma kuɗin wanda ta ɗaure da leda, Umma ta amsa, ta shiga cikin motar, mu kuwa a lokacin muna ciki, ga mutane ƙofar gidan kamar rana duk kuwa da cewar magriba ce, sai da motar ta tashi muka ɓacewa ganin su .