NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Cikin da razana take kallona, nayi dariya na ce, “kwarai kuwa ban san kammanin ki ba, amman nasan labarin ki, sai da Salma ta turo mani photon ki dana kwayen ki iri daban_daban da bayanin garin ku da shige da ficen ku, da gurin da kuke zuwa, da yanda al’adar ku take, dan haka ne, aka shirya mani wannan tafiyar wadda ban san wanda ya biya kuɗin jirgi da direban da suke zirga_zirga damu, ke harma da gidan da muke zaune, nidai nasan Salma ce ta tsara, amman ita da waye shine ban sani ba, Salma ya abun yake, a ina kika sami wannan shawarar?

Dariya Salma tayi tace, “am dafatan duk kuna biye damu, to a zahirin gaskiya kowa yasan bana shiri da matar Yaya Salman ballema nasamu photon ta, dan bana jin zan iya ajiye photon ta, a waya ta, haka zalika ni ko kallon ta bana son yi ballema naji labarin ta, to abunda yasaka na ce, ita ce zata iya aikata hakan saboda, nasan yanda take bibiyar rayuwar bro, kuma nasan yanda bata son ya raɓi kowa ne, ɗan adam nasan zatayi tunanin yana da alaƙa dashi duk da, kuwa a lokacin shi kan sa bro da Anty Narjeesh basu san, alakar dake tsakanin su ba, har sai kusan ɓatan Shuraim da kusan wata ɗaya koma fiye, tun lokacin da bro ya sanar dani komai, kuma ya tabbar mani da cewar ya ɗauki Shuraim a ranar kuma a ranar aka nemesa aka rasa, to kawai na fahimci cewar aikin Haulart ne, shi yasa na nemi shawarar wanda zan Aura a lokacin, shine ya taimaka mani, haka, Muhseen shima ya bada tashi gudumawar, a gurin wanda zan Aura ne nasami photon su da bayan su cikin sauƙi ba tare da nasha wata wahalar ba, amman kuma ma sauki da direbobin da ke zirga_zirga da ku da gidan da kuke zaune ba aiki na bane, aikin Muhseen ne, Muhseen kai muke saurare”.

Gyaran murya Muhseen yayi yace, “a lokacin da na fahimci miye Sister Salma take shirya wa ita da Narjeesh, shine na, sanar da direba na ya ɗauko su a hanya ya kaisu airport, kuma a hannun Salma na anshi photon su Anty Narjeesh naje, gurin abokin karatuna a airport domin ina son yayi masu komai a cikin sauri kuma Alhamdulillah nasami yanda nake so, haka na kira abokina kuma amini na, Al’amin akan buƙatar su Anty Narjeesh su zauna a gurin Ummeyn su, kuma yayiwa abokan mu bayani sune zasu riƙa kaisu duk gurin da na kira na faɗa ina bukatar aikaisu, ai kuwa haka, suke bin umarnin na, sun bamu haɗin kai ɗari bisa ɗari, harda su sauya suna akan sunayen “yan kauye wannan ke nan”.

Salma taci gaba da faɗar, “tun daga lokacin muka fahimci su Anty Narjeesh sun sami nasarar shiga a gurin su Haulart muke neman yanda zamuyi, su sami ɗaukar Shuraim, gashi mun sami labarin tafiyar dare ne, duk hankalin mu a tashe yake, mun rasa mafita, gashi duk mun haɗu a guri ɗaya nida Muhseen da Yaya Jafar da Yaya Aliyu da ita Anty Narjeesh da Amrah da muke waya, dasu, suna sanar damu halin da ake ciki, na tabbar da cewar Shuraim yana gidan kamar yanda Miss Yaseer ta sanar da ita, gaskiyar lamarin, ai kuwa kamar daga sama, Bro ya fisge wayar ya kashe idon sa yayi mugun ja saboda ɓacin rai, duk sai da muka tashi tsaye, muna zarar ido, cikin ɓacin rai yace, “haba taya zaku riƙa ɓoye mani halin da ake ciki bayan mata ta da ɗana da “yar uwar ta suna cikin hatsari, kuma kun san irin matsanan ciyar damuwar da nake ciki,? A gaskiya kun ɓata mani rai ku tashi muje gurin su Mai martaba dan duk abunda ake faɗa tun daga farko har ƙarshe munji komai! “.

Haka muka doshi ɗakin Mai martaba duk da kuwa yawan mutanen biki da suka cika ko ina na cikin gidan, a can ne, Mai martaba yayi muna faɗa sosai shida Dad shine muka shirya zuwa Abuja kuma Alhamdulillah mun iso da wuri, bamu san lokacin da Bro ya baro mu ba, amman ya kiramu yace, na kira Anty Narjeesh akan cewar duk abunda sukeyi su isa ɗakin Mai gadi, a cikin daren, to kunji abunda ya faru”.

Murmushi nayi nace, “Allah sarki sannun ku da ƙoƙari” anan ne Daddyn Shuraim ya ce, “a lokacin dana zo gidan, sai na shigo cikin sanɗa batare da kowa ya ganni ba in, banda yara na, masu, kare lafiya ta, shine na shiga cikin gidan na zubawa Haulart maganin bacci a cikin ruwan lemon da ta a jiye ta shiga toilet, ina kallon ta ta jikin labule har ta shanye duka anan ne bacci ya ɗauke ta, ni kuma na baro ɗakin naje ɗakin mai gadi dan jiran zuwan su, ai kuwa suna zuwa na ɓude masu ƙofar na ɓuya, kasan cewar yasan da zuwan nasu tun kafin nazo, to anan ne, suka gane cewar mahaifin su ne, kuma shima ya ƙarasa dawowa cikin hayyacin sa”

A Nan ne yaci gaba da basu labarin har zuwa yan zun da komai yake faruwa a gaban kow.

Cikin sauri Miss Naseer ta nufi gurin Miss Yaseer da niyar dukan ta, cikin tsawa mijin ta ya ce, “haba dai tun kafin kiji naki saka makon, to tun da kin so jin naki tarihin bari kiji”.

Turus tayi tana kallon mijin nata, kamar wata hauka sabon kamu,

Ya ce, “to duk abunda kika ji Salma ta faɗa nine wanda take magana a kai kuma nine na basu information a kan ku, kuma nine na basu tarihin ku, da halayyar ku, kuma Yaseer da Nazeer dani kai na duk kowa ya bada gudu muwar sa, a cikin wannan aikin, kuma Salma da kike gani ita ce nayi niyar Aure ita ce muka haɗu da ita a shari’ar da sukayi ta farko wadda na bata, rigata, ta rufe jikin ta, saboda kallo ɗaya nayi mata, a lokacin suna baƙin zuwa wannan ƙasar, kuma ni ban san ya ya, akayi ba kika shigo rayuwa ta, har na Aure ki, dan haka yan zun ina yi maki albishir da cewar, an ɗaura Aure na nida Salma yan zun haka, ita a matsayin mata ta, take”.

Wani irin uban ihu tayi ta zube a ƙasa sai ihu take zubawa tana ba zai yuyu ba.

Kukan mutum ukku da ihun su kawai kake jin yana tashi a gidan dan duk sun cika wa mutane kunne, ihu Nazeer ya ce, “Shin yan zun guguwar ta zo ne ko da sauran ta? “.

Da sauri Miss Nazeer ta ce, “aa kada ka ce komai a gurin nan na roƙeka da ka tausaya mani! ” sai gir giza kai takeyi.

Wata uwar tsawa ya daka mata ya ce, “yan da kika rabi da iyaye na, mata ta da yarana da kowa sukaji baƙin ciki kema sai kinji fiye da hakan shegiya muna fuka azzaluma! “.

Mai martaba ne yayi gyaran murya ya buɗe taron da addu’a, bayan ya ƙarasa ne, ya ce, “tabbas Allah shine mai iko akan komai, gashi Allah ya baku aron dama kunyi watsi da ita, to bari kuji Salman da wannan yarinyar Narjeesah ni ne, na saka aka ɗaura masu, Aure tun lokacin da tsafi gaskiyar mai yin sa, ya saka, aka sato yar mutane da niyar cin zalin ta, na riga su, a gurin domin nine na saka aka bar hotel ɗin da aka yada su, kuma wannan yaron da ake rigima a kan sa, ɗan halak ne gaba da baya” anan ne Mai martaba ya basu labrin komai har zuwa yau ɗin nan.

Ham dala kowa keyi duk da ni da su Yaya Jafar dasu Amrah dasu Humaira da su Salma mun san da wannan zan cen wanda basu sani bane kawai suke cike farin ciki, saɓanin mutum ukku, wato Haulart da wanda a tare suka wani ƙurma uban ihu suka bushe da dari suka fara yaga kayan jikin su, sukayi waje da gudu suna ihu, duk abunda suka gani sai sun daka, cige gashin kan su sukeyi, wata irin uwar guguwa ce ta taso, ta tur nuƙesu tayi sama dasu.

Mutane kuwa kowa yayi ta kan sa da gudu.

Nan nauyar ajiyar zuciya kowa ya sauke, Mai martaba ne ya ce, “to kun dai ga ƙarshen masu shirka, duk wanda yace, tukunyar wani ba zata tafasa ba, to shi tasa tukunyar ko zafi ba zatayi ba, dan haka muji tsoron Allah a duk inda muke, ku kuma Allah ya saka maku da alkhari, gabaki ɗayan ku, Salman kuna sakaci da addu’a duk da nasan ka da ƙoƙari, kuma ita ƙaddarar mutum duk inda yake sai abun nan ya shafesa, sai dai saboda addu,oi abun ya zowa mutum da sauƙi, Allah ya ƙara bamu kariyar sa baki ɗaya “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button