NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Amin, duk aka amsa Mai martaba ya sake cewar, ku tashi kowa yaje ya shirya yau zamu bar garin nan, kema Salma bikin da ya rage sai kuje ku ƙarasa, Narjeesah da mahaifin su, a maida su gidan su, dan hankalin Umman su ya kwanta”.

Kowa ya amsa da “Insha Allah”.

Dad ne yakewa Shuraim wasa, yana faɗar, “abokina zaka bimu ko? “.

Ai kuwa da sauri ya tashi ya gudo ya haye jikin Amrah ya ce, “gurin Umma zani, ita ne mai yi mani wasa, tana siya mani kayan wasa kuma tana sakani nayi bacci na mai daɗi… “

Ai kuwa dariya aka saka masa, tashi mukayi, cikin farin ciki nida Nusaiba mukayi waje, Amrah tana riƙe da hannun Shuraim sukaje suka janyo trolley ɗin mu, suka fito shima Baban mu, ya ɗauko kayan sa, duk kowa yayo waje, motoci aka shiga, nida, Humaira Hindu Amrah Nusaiba Shuraim mota ɗaya Yaya Jafar Aliyu Baban mu mota ɗaya, Salman Salma Muhseen Dad Mom motar su ɗaya, Mai martaba mota ɗaya Naseer Yaseer Nazeer Miss Yaseer motar su, ɗaya.

Haka muka ɗauki hanya sai gidan su Ummey muka ɗauko kayan mu, mukayi mata, sallama muka rabu cikin jimamin juna, tana tsokanar Shuraim, haka muka nufi airport, jirgi muka hau dukan mu, yan yola, cikin ikon Allah muka sauka lafiya, yaron Yaya Jafar ne yazo da motoci muka shiga sai ƙofar gidan mu, ai kuwa Shuraim da Nusaiba da gudu sukayi cikin gidan, mu kuwa dariya mukeyi masu, muka mara masu baya.

Umma ce zaune tana famar kiran wayar mu amman shuru, duk hankalin ta, ya tashi kamar daga sama taji muryar Shuraim yana kiran Umma….. Umma…., ai kuwa da sauri ta buɗe idon ta ganin Shuraim ya shigo da gudun sa, ƙofar falon ma da ƙarfin sa, ya turo yayo kan Umma cike da farin ciki ta cafe sa, ta rungume tana dariya Nusaiba ba ce, ta shigo itama ta rungume Umma tana dariya, ahaka muka same su.

Hindu ta ce, “kai Umma sune kawai kike yiwa oyo amman banda mu”.

Sai a lokacin ne Umma ta ɗago idon ta, ta kallemu taga kowa ya zauna yana murmshi, ta ce, “to bayan kun nemo muna wannan mai saka mutane kuka ya hana su cin abinci? “.

Dariya mukayi Humaira ta ce, “ai dole ne muyi kuka Umma, kema fa kawai kinyi dauriya ne, amman fa abun babu dama”.

Dariya Umma tayi tace, “Humaira ungo wannan na ce gidan ku”.

Dariya muka shiga yi, a dai dai lokacin da su Yaya Jafar da Yaya Aliyu da Baban mu suka shigo bakin su ɗauke da sallama, amsawa Umma tayi ai tana ɗaga ido, kawai sukayi ido biyu da Baban mu, cikin wata irin zabura Umma ta tashi tsaye, ta zaro ido tana murza idon ta ta gani ko mafalki ta keyi ne, da sauri muka ƙarasa inda take muka riƙe ta, sai jikin ta, ke rawa bakin ta sai mur_mar yakeyi ta kasa furta kalma ɗaya.

Nusaiba ta ce, “Umma a zahiri ne ba a mafalki bane , Baban mune da kan sa, wanda kowa aka sanar dashi mutuwar sa, ashe yana a raye wasu ne dai suka mutu”.

Zaunar da Umma mukeyi Amrah tace, “a gidan Daddyn Shuraim muka samesa a lokacin baya cikin hayyacin sa, sai da idon sa ya sauka akan Anty Narjeesh san nan yadawo daga cikin hayyacin sa”.

Kuka Umma ta fashe dashi, shima Baban kukan yakeyi ganin hakan ne ya saka Yaya Aliyu ya ce, “dan Allah ku dai na kukan nan haka, kada ku saka kowa ya kama kukan, tun da Allah yasa Baban yana a raye kuma an samesa ai sai godiyar Allah “.

Share hawayen su, sukayi, kowa yayi shiru sai Shuraim ne ke wasa a jikin Umma yana jan jelar gashin Umma, yana dariya.

Tashi Umma tayi tace ku tashi Amrah keda Nusaiba ku kawo abinci muje na nuna maku, komai”.

Abincin aka kawo bayan anci ansha ne, Amrah ta labar tawa Baban komai wan da yayi kuka sosai, shi kuma ya ce, sai sun koma gida zai basu labarin abunda ya sani game da hatsarin, kowa yayi na’am da hakan.

An ajiye maganar tafiya gobe laraba da safe, ai kuwa su Yaya jafar sukace duk tare za’ayi wannan tafiyar dasu, dan haka sukayi sallama suka tafi tare da matan su, mu kuwa cikin farin ciki muka kwana ga Shuraim a jikina.

Yau tun da mukayi sallar Asubahi, bamu kwanta ba, muka shiga haɗa kayan tafiya, Umma kuwa suna kichin ita da Auta da Shuraim.

Bayan mun gama shirin mu, mun ci abinci su Humaira suka zo daga baya su Hindu suka zo, muka shiga fitar da kayan mu, motar Yaya Jafar muka shiga muka ɗauki hanya…..

Comment and share

Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????

???????? NARJEESAH ????????

Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN

ELEGANT ONLINE WRITERS

Bismillahir Rahmanin Rahim

Hahhhh???????? Narjeesah team kun fa sakani dariya, a page biyu, 36/40 41/45, haba dai har kun manta cewar mutuniyar taku, irin gidan da ta fito gidan mata huɗu gidan makirci? Tafa san ta kan kishi da iya zaman da mutane, kuma, cikin Shuraim shine ya saka ta, ta dawo wata irin shiru_shiru da ita, amman kowa yasan Narjeesah bata dama, haka Amrah, dan haka nasan yan zun kun gane dalilin da yasa, sukayi, acting ta maida Sunan ta NARSAL

Ina godiya sosai da Comment ɗin ku da sharhin ku, kuma ina ƙara godiya da addu’ar ku, sosai

           4️⃣6️⃣⏯️5️⃣0️⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Tafe muke a cikin motar Yaya Aliyu Hindu na gefen sa, nida Amrah da Shuraim muna a baya, kowa ka kalli fuskar sa, a cikin farin ciki yake.

Yaya Jafar kuma shine ke driving Humaira tana gefen sa, Baban mu da Umma da Nusaiba suna baya, kowa yana cike da farin ciki idan ka kalli fuskar sa, amman Baban mu ba zaka gane wane yanayin yake a ciki ba.

Shuraim sai surutu yakeyi, yana faɗar, “yeeee! Mun hau mota zamuje yawo, Uncle ka siya mani giwa da zaki inyi wasa dasu, mu shiga ta cikin wannan jejin muyi ta faɗa, da… Da… Dami ma ake ce masa Anty? “

Dariya mukeyi, Yaya Aliyu ya ce, “nikam ba zan iya siya maka giwa da zaki ba, amman inda kace, na siya maka doki ka hau zan iya kayi ta su guda” da dariya ya ƙarasa zancen.

Haɗe rai Shuraim yayi Hindu ta, juyo tana dariya tana kallon Shuraim ta ce, “kada kayi fushi nawan bari na anshi wayar sa na kira maka Daddyn ka, nasan shi zai siya maka su, ko? “.

Kwallar idon sa ya goge ya gyaɗa mata kai, Yaya Aliyu ya ce, “kai my boy badai kuka kake yi ba, to yi hakuri da wasa nakeyi maka, zan siya maka duk abunda kake so, kaji yaro na? “.

Maƙe kafaɗar sa yayi, mukam dariya mukeyi masu, Hindu ce, ta ɗauki wayar Yaya Aliyu ta kira number Daddyn Shuraim, ai kuwa ringing biyu, ya ɗaga suka gai sa, take sanar dashi Shuraim ke magana, ya ce, da ita “bashi wayar ki saka mashi Hans free”.

Hans free ta saka mashi, ta bashi wayar, shi kuwa ya amsa, yayi kwanciyar sa, a jiki na, ya fara faɗar, “Daddy ina kwana? ” dariya ya yi yace, “lafiya lau my lovely son, ka tashi lafiya ya Umma na, dafatan ta tashi lafiya da Baban mu da su Amrah da waye ma? “.

Dariya Shuraim yayi yace, “lafiya lau Daddy baka ce, da Mommy na ba, kuma muna cikin mota zamuje wani gurin, kana zuwa muzo mu tafi da kai ko? “.

Shima dariyar yayi, ya ce, “Shuraim ai Mommyn ka bata son tafiya fani, kaga bata sanar dani ba, ko? Amman zan zo yaro na dami kake son na zo maka dashi ne? “

Cikin sauri Shuraim ya ce, “Daddy zaki da giwa, da doki mai tashi sama”

Ai kuwa kowa ya saka masa dariya shi kuwa Salman ɗin ya ce, “to kai kuwa yaro na a ina ne, zaka ɗaure giwa da zakin ka kuwa san Mommyn ka tsoron su takeji ko? Kuma gashi har doki mai tashi sama, ina fatan dai zaka hau dokin”.

Cike da jin haushin su, na ce, “ai da yake shi mutum baya tsoron zakin dolene a cikawa mutane baki, kuma kada a sake sakoni a cikin shirmen ku ehe! “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button