
Dariya yakeyi ta cikin wayar, haka su Amrah, Shuraim ne ya ce, “Daddy ka kawo mani mage ƙarama mai kyau “.
Da sauri na ɓalla masa harara, na ce, ki nemi gidan uban da zai kai maka ita, ku ajiye, kai wallahi kun fa fara cika ni, zan baku mamaki, idan baku fita hanya taba”.
Yaya Aliyu ne, ya ce, “to ke Narjeesh wannan faɗan kuwa, kamar yana a gaban ki, firar suce sukeyi a tsanin ɗa da mahaifin sa, sai kuma kiji haushin su? “
Ni kuwa na ce, “to baka jin sune suke sako suna na a cikin zan cen su? To kayi masu magana mana su dai sakani a harkar su, ehe! “
Dariya sukayi shi kam firar shirmen su sukeyi kuma duk abunda nake faɗa, a kunnen sa, ne yaƙi magana sai ma cewa yayi, “Shuraim ka kirani da wayar Mommy ka yan zun sai muyi firar mu ko? Ka baiwa Uncle wayar sa kaji yaron kirki? “.
Dariya yayi ya baiwa Hindu wayar ta kashe suna dariya, kallona ya keyi yana son na bashi wayar amman na ɗaure fuska, kuka ya saka, na kallesa, na daka masa tsawa, “rufe mani baki daga nan ko yan zun nayi maganin wannan rashin kunyar, anƙi a baka wayar, tunda da kuɗin ku na siya, ko kuma ta mutum ce, na ɗauka dole sakani abunda banyi niyar aikata wa ba, kuma ba zaka kira shi da wannan wayar ba, sai dai ku zauna kurame ni babu ruwa na, a ciki” ina zare masa ido.
Ai kuwa cikin jikin Amrah ya faɗa ya saki kuka yana kiran “Dadd… Daddy”, share sa nayi kamar bana a kusa.
Amrah ce ta shiga lallashin sa, da taga yaƙi yin shirun ne, ta rasa ya zatayi, zuwa can tayi kamar zatayi kuka, ta ce, “Anty Narjeesh dan Allah ki aro muna wayar taki, mu kira masa Daddyn nasa, tunda ba kece zakiyi maganar ba, kinji Anty Narjeesh wallahi har jikin sa ya fara zafi”.
Shareta nayi, itama tayi shiru Hindu ta ce, “shima dai Salman yaso ya haɗa wannan rigimar ne, yasani sarai, Narjeesh ba zata bada wayar ta ba, amman ya saka Shuraim a ciki dan ya fahimci rigimar sa, ke kuma dan Allah ki basu aron wayar tunda ba cinye wa za suyi ba”.
Kamar nayi kuka na zaro wayar a jaka ta na bashi, ai sai kukan ya dawo dariya idon sa da hawaye amman dariya yakeyi.
Suma ajiyar zuciya suka sauke suna dariyar, Hindu ce ta anshi wayar ta saka number ta kira, ta saka murya ta bashi da farin ciki ya amsa, ya fara magana amman bayaji saboda munzo gurin da service yake rawa, dole ya haƙura, zuwa can yayi bacci, sai a lokacin ne Yaya Aliyu ya ce, “Narjeesah wai miye ya saka kika saka yaron nan kuka kuma ba zaki lallaba sa ba, kodai irin yanda Umma takeyi maki zaki yi masa ne? “.
Na ce, “to ya zanyi masa, ai dai kasan ni bana son lambar wayar wani ta shiga cikin waya ta, sabo bana buƙatar ya takura ni, tunda ba shine ya siya mani wayar ba”.
Ya ce, “amman kin san zai iya siya maki wadda tafi wannan ko? “
Na ce, “aa ni ban sani ba dan ban buƙata ba, kuma ban roƙa ba”.
Hindu ta ce, “hahh wata rana zaki buƙata Miss Salman Allah dai ya ƙara danƙon soyayya dan wannan zazzafar soyayyar tana tafiyar dani ne fa”.
Tsaki kawai na sakar masu ban sake bin ta kan su ba, tafiya kawai mukeyi , amman mun tsaya a hanya munyi sallah munci abinci mun riƙo wani, na guzuri sai gab da magriba muka iso garin namu, ham dala muka shiga yi mun shigo garin dutse, a wani hotel muka sauka, muka kwana, tun da safe muka ɗauki hanyar shiga garin gumel, mun iso cikin garin gumel lafiya muka ɗauki hanyar shiga ƙauyen mu.
Tafe muke wasu zafafan hawaye ne, suka shiga zubo mani, ina tuna irin fitowar da mukayi a lokacin, kallon Amrah nayi naga tana wani makirin murmushi, ta ce, “Alhamdulillah Allah mun bar garin nan da far gaba da tashin hankali da tunanin makomar gurin da zamu sake sabuwar rayuwa, sai gashi yanzun zamu shiga garin nan da ƙarfin mu, kuma cike da farin ciki, da tarin nasa rori”.
Kwatan ce hanyar da zasu bi Amrah takeyi, har muka iso ƙofar gidan mu, mukayi parking, duk muka furta “Alhamdulillah”,
Bamu fito ba muna daga cikin motar, kusan mintina biyar, idon mutane, yana akan mu, Yaya Auwal ne ya fito daga cikin gidan yana kallon motocin, a kuwa nida Amrah da gudu muka buɗe ƙofar motar muka fita da gudu muka faɗa jikin sa, muna hawaye, cike da mamaki da farin ciki ya ce, “Alhamdulillah Alhamdulillah Amrah Narjeesah kune nake gani da ido na? Ina Umma ina Auta Nusaiba ina yaron nan Shuraim? “.
Yaya Aliyu ya ce, “to taya zasu iya amsa maka duk wannan tambayar lokaci ɗaya, ka bari ku shiga daga ciki ku zauna mana “.
Dariya Yaya Shuraim ne ya ƙaso gurin yana faɗar “Mommy waye ya dakeku kuke kuka, na kira Daddy na, nasar dashi yazo da Bindigar sa ya rama maku? “. kamar zaiyi kukan shima
Da sauri Yaya Auwal ya janye mu daga jikin sa, ya matsa, ya ɗauki Shuraim yana dariya yayi cikin gidan dashi, mutane kuwa tuni labarin zuwan mu ya riski kowa.
Inno ce ta fito tana gyara ɗaurin zanen ta, ta ce, “dama nadan duk daren daɗewa zaku dawo, toni yan ban zanga kuzo na rungume ku mana”.
Ai da gudu mukayi kanta har da Auta da ƙaraso gurin mu, rungume ta mukayi, kuka ta fashe dashi taja hannun mu kukayi cikin gidan, kallon gidan mukayi duk an sauya masa tsari icce dalbejiyar mu yana nan, amman ɗakin Umma babu shi kwata_kwata wasu ɗakuna ne akayi daga baya, a tsakiyar gidan cikin inuwar icce inno ta saka akayi muna shimfiɗa muka zazzauna, Shuraim ne suke fira shida Yaya Auwal yana bashi labarin Daddy sa, suna dariya Inno kallon mu takeyi ta kalli Shuraim.
Ta ce, “wai nikam Amrah yaron nan ne yayi wannan wayon haka? “
Dariya mukayi Yaya Aliyu ne ya ce, zan je nadawo Shuraim kayi mani rakiya mani”
Da sauri ya tashi yana murna, Inno ta ce, “kuce ɗan naku swai_swai ne jirgin yawo to ayo muna tsara dai”.
Dariya mukeyi Shuraim ya ce, “zanyo maki tsaraba mai yauwa ko Uncle? “
Dariya yayi masa ya shafa kansa, Inno ta ce, to da kuɗin waye zakayi mani wannan tsabar mai yauwa, dan nasan kai dai ba kuɗi ne da kai ba, baka da ko naira”. Tana yi masa dariya
Fuska ya ɗaure ya ce, “Uncle Daddy na yanada kuɗi masu yawa ko? Kuma shine zai bani kuɗi nayo maki tsarabaaa”.
Dariya akeyi masa antaru a gurin harda maƙota da yan gidan wanda bamu sani ba, baƙin fuska, Humaira da Yaya Jafar suka shigo da sallama da sauri Shuraim ya nufesu yana yi masu oyo kuma sai dawo “mun riga ku, wallahi”
Ɗaukar sa Yaya Jafar yayi ya shillashi sama, suna dariya.
Humaira a kusa da Inno ta zauna tana gaisawa da ita, ta ce, “wash Allah na gaji, Inno a bani filo na kwata naɗan futa”.
Cike da mamaki Inno ta kalle ta ta ce, “da alama jiki na ne yake wahalar mani da ‘yata “.
Dariya muka shiga yiwa Humaira Inno tayi mata tonon silili, rufe ido tayi, kawai aka kawo mata fillon ta ce, “to malama Narjeesh matar shugaba Salman “.
Duka na kai mata, Inno ta tare, tare da faɗar “kada ki kusa dukan ta a gaban idona, Allah zan saɓa maki”.
Baki na turo na tashi daga gurin nace, “ai inda Yaya tana nan da sai ta shigar mani, nima”.
Dariya suka saka mani, ina hara rar su, harda kyabci nakeyi masu.
Su Yaya Aliyu kam tafiya sukayi, sai ga Yaya ta shigo tana faɗar “Inno da gaske dai sune suka zo”
Da gudu mukayi kanta mu ukku run gume ta, muna dariya, itama kukan ta saka tana faɗar, “miyasa kuka daɗe baku wai waye muba, ne duk kun tafi kun bar mu da tunanin rasa sanin inda kuka shiga, munyi nema munyi cigiya gashi Allah ya dawo muna daku cikin ƙoshin lafiya, ina Umman Nusaiba, ina fatan tana lafiya naga anfito da yaro ƙarami baƙi nakuwa san cewar shine yaron da kuka tafi dashi yana jin jiri”