
Dariya muka shiga yi, hannun mu taja muka ƙarasa muka zauna sai tambayar mu take “kuna lafiya ya bayan rabuwa, Narjeesah duk kun sauya muna kamar ba ku ba”
Humaira ta ce, “Yaya ai ita Narjeesah Daddy Shuraim ne yayi mata wannan gatan bakiga irin yanda suke zuba soyayya ba, ke da zamu zo harda kukan rabuwa sukayi harda cewa tayi wai ita ba zata zo ba, sai dai mu muje ita ba iya barin mijin ta, ya zauna shi ɗaya”.
Ido na zaro waje na ce, “ke Humaira Allah Yaya kada ku yarda da uwar sharrin nan, Allah ƙarya takeyi maku! “
Hindu ta ce, “Inno da gaske ne bata son mu faɗa ne kawai amman ko yan zun hankalin ta yana gurin gurin sa da kuka suka rabu dashi “.
Tagumi na zuba ina kallon su, Anty Basira ce da Shamsiyya da Hanan Haule, Hannatu Yaya Halilu Yaya Hamza, Yaya Mudarsir Anty Asma duk sune suka shigo cikin gidan kamar wanda aka koro su, zuwa can kafin su zauna sai ga goggo da Kawu Bala har yan cin tun tube da babbar rigar sa, kamar zai kife, Mama ce, ta fito tana ɗir gisa ƙafa duk tayi baƙi ta fita hayyacin ta.
Su Humaira duk sai suka maida hankalin su akan wannan mutanen dake ta shigo wa, mu kuwa kallon kowa mukeyi ɗaya bayan ɗaya.
Kawu Bala ne ya ce, “kamar dai naji ance, wai su Nusaiba ne suka dawo kodai mutane basa gani da kyau ne kuma basu dai ji abunda ake faɗa da kyau ba, har kasuwa akaje aka sheda mani, ɗan achaɓa ne ya kawo ni gidan nan”.
Duk a daburce yake magana, Hanan ce tayi dariya ta ce, “wallahi sune suka dawo Narjeesh Amrah Nusaiba kun dawo kamar wasu “ya’yan turawa” tana dariya tayo kan mu ta zauna a kusa damu tana cike da farin ciki ta ce, “ina Umma da Shuraim? “.
Humaira ta ce, “ko bamu tambaya ba nasan wannan ita ce Hanan”.
Dariya mukayi tashi Hanan tayi, ta ƙarasa gurin su, aikuwa sai fira kamar sun daɗe da sanin juna.
Kallon Inno nayi batare da na kula da kowa ba a gurin na ce, “Inno tare muke da Umma da kuma wani babban al’amarin daya shafe mu baki ɗaya”.
Cike da mamaki kowa yake kallon mu, suna mamakin wane babban al’amari ne da yashafi kowa a zuri,ar mu?
Kawu Bala ne ya ce, “badai wani cikin ki sake yowa ba, ko wannan ce ma tsaurin idon tayo shi, to ba a gidan ba, dan kun san baku da gado a cikin sa”.
Da sauri Hindu ta ce, “gado kam ai ya tashi tunda mamalkin gidan da ransa bai mutu ba, nifa wallahi ba zan iya jurar abunda su Narjeesah suka jura ba, ehe! “.
Humaira ta cafe tace, “waifa gado ina ma wani gadon yake ne, malamai bari kuji, ita fa Narjeesar nan da kuke gani zaune a gaban ku, ku kiyaye sakin duk maganar da tazo a bakin ku, saboda idan masu tsaron lafiyar ta, sukaji zasu iya datse wa mutum halshe dan haka mutum ya kiyaye, kawu Bala kaida goggo da Mama kubi a sannu dai ehe! “
Kowa kallon su Hindu yakeyi cike da mamaki, goggo ta ce, “to da alama dai ankai maku ƙarar mune dan naji kuna furta Sunan mu kamar a bakin ku aka zana shi ki? “.
Amrah tayi dariya ta ce, “wato dai mu bamu da aiki sai tara “yaya kun maida mu fasiƙai, to Alhamdulillah duk cikin mu babu wanda ya taɓa zubar da cikin shege kuma, yan zun da mutum yasan wace ce Anty Narjeesh da ɗan mu Shuraim da zufa tayi ta zubo masa! “
Ni kuwa nayi saurin faɗar ku ce, dasu da sun san abunda muka zo masu dashi da wasu sun kusa sumewa, marasa gaskiya kuwa za suyi ta kan su, Inno da Yaya duk abunda kuka gani kada ku firgita kuyi aiki da hankalin ku, komai a zahirin gaskiya yake tafiya kuma, mutuwa bata ɗauka sai lokaci yayi, haka zalika ko wane bawa da irin tasa ƙaddarar wasu suyi imani da ita ƙaddarar wasu kuwa suyi biyu babu, Nusaiba jeki kice da Umma kowa ya hallara a gidan nan! “
Ai kuwa da gudu Nusaiba ta tashi ta fita, kowa yana jiran dawowar ta, Inno ta kasa haƙuri ta ce, “kodai masu neman Auren kune? “
kawu ya ce, “ashe dai kun ƙaro fitsara eh lallai kam na fahimci komai “.
Goggo ta ce, “wato rashin kunya kuka dawo kuyi muna ku nuna muna baku shiryu ba kuma duniya bata hora kuba ko su kuwa wan can fitararrin daga ina kuka samosu ko suma abokan fitsarar taku ne? “
Sai a lokacin Mama tace, “sune ma dan wannan rawar kan nasu yayi yawa, ai kuwa abunda kika aikata zasuji babu wani rufin asiri”.
Yaya tace, “ai dai masu goyon shegun suna da yawa, dan haka baki da bakin yiwa Narjeesah gori dan kema kin goya shegu, ga kuma wani cikin nan wanda bamu san uban saba, a gurin yarki, kin ga kuwa dama can mun sanar dake mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege bai sani ba ko ya haifa, ashe kuwa ya baki ya boka, kin haifa shegen ke nan”.
Tsit kaji bakin Mama tayi ƙasa da kanta.
Dariya Amrah da Humaira da Hindu sukeyi harda tafawa.
Sallamar Umma ce ta katse masu tattaunawa suka maida idon su, akan Umma cike da mamaki suke kallon yanda Umma ta sauya ta zama wata Hajiyar da ita, sakin baki sukayi wasu ma murza ido sukeyi.
Inno ta ce, “Allahu akbar kabira, Umman yara kece kika dawo haka ikon Allah to lale maraba da zuwa, sannu da zuwa sannu da zuwa ” cike da farin ciki suka rungume juna.
Ita kuwa Yaya hannun Umma ta riƙe tana kallon ta, tana godiya a gurin Allah subhanahu wata’ala.
Umma tayi murmushi tace tare muke da baƙi fa, dan Allah ku zazzauna hannun Inno da Yaya ta kama suka nufi gurin su Humaira suka zauna,
Nusaiba ce tare da Baban mu suna riƙe da hannun juna suka shigo Yaya Jafar Yaya Aliyu suna biye dashi.
Hailala da salati gurin ya ɗauka sai murza ido sukeyi ai kuwa da gudu Yaya Auwal ya matsa yana taɓa jikin Baba sai da ya tabbar shine ba mafalki bane yakeyi ai kuwa ya rungume shi, ai sai ga Hanan itama ta faɗa jikin sa, sai kuka yadawo sabo.
Kawu Bala ne ya ce, “wannan ai ba gaskiya bane waye ya taɓa mutuwa kuma ya dawo sai dai ko fatalwa ne eh lallai kuwa ni ban yarda da wannan lamarin ba! “
Goggo ta kasa tsayuwa ta zube a gurin bata numfashi haka Mama faɗuwa gurin tayi, su Yaya Halilu kuwa suman zaune sukayi hada su Anty Asma.
Hamdala Inno tayi tace, “ikon Allah tabbas wannan Malam Isah Musa, dan naji a jiki na, mai gidan mu ne ya dawo ran sa, Allah mun gode maka”.
Yaya tace, “hakane Inno wannan uban “yayan mune Allah ya dawo muna shi, yara kun tashi daga marayu kun dawo masu uba, mu kuma mun dawo matan Aure Allah da ikon sa yake”.
Tashi nayi natako nazo nace, “muje ka zauna Baban mu ka futa sai ka bamu labarin abunda ya faru a shekarun baya”
Hannu na ya riƙe muka je muka zauna muka saka shi a tsakiyar mu, duk kowa yayi shiru muna jiran muji daga garesa, harda maƙota masu kallon Ikon Allah, duk suna a gurin.
Wayar Yaya Jafar ce tayi ƙara, da sauri ya kalli Baban ya ce, “sun neman izinin shigowa”
Murmushi Baban yayi ya maida idon sa akan Yaya Mudarsir ya ce, “kaje ku shigo da baƙi”.
Tashi yayi ya fita, sai gashi sun shigo tare zaro ido waje nayi, na buɗe baki zanyi masifa, da sauri Humaira tayi wa Inno da Yaya raɗa a kunne da sauri suka ce, “A hir ɗinki Narjeesah Allah kikayi wata magana a gurin zamu swaɓa maki “.
Zuɓurar baki nakeyi gaba, ina ɗaure fuska, Shuraim kuwa ƙafata, yazo ya haye Salman a kusa da Yaya Jafar ya zauna, Muhseen kuwa a kusa da inda muke zaune ya zauna ya ce, “Anty Narjeesh bakiyi maraba da zuwan mu ba ne? “.
Gir giza masa kai nayi nace, “kai nayi maraba da zuwan ka amman banda wan can mutumen ka duba yanda yake harara ta”