
Ɗaga ido sukayi shida Amrah ai kuwa harar ta, suka kamasa yana yi dariya sukeyi ƙasa_ƙasa.
Gyaran murya Baban yayi yace, “To Alhamdulillah Allah shine mai tsara yanda yaso a duk lokacin da yaso, to gashi Allah yayi dawo wata a cikin iyalai na, kuma gashi nasami sauye_sauye da dama kuma abubuwa duk sun birkice, motar da muke ciki ce, tayi hatsari ba tare da mun san miye musabba bin ba, amman kuma ni a cikin jeji aka jefa ni, motar ta kama da wuta, kaina ya bugu da icce nikam ban sake sanin inda kaina yake ba, na dai falka ne na sami kaina a asibiti kuma na manta kaina da Sunana kawai dai na rasa Yaya zanyi na tuna inda na fito, koda aka sallame ni daga asibiti wannan yaron ne na gani a kaina, kuma shine ya ɗauke ni ya kaini gidan sa, naci gaba da jinya ta har nasami sauƙi amman kuma, hal zuwa lokacin bana iya tuna waye ni, ganin haka ne ya mai dani asibiti aka ce, idan naga abunda nafi ƙauna zan iya tunawa, gidan su muka dawo ya bani aiki wanda na nema duk da kuwa cewar gidan sa cike yake da ma’aikatan kaki da marasa kaki ya bani gadin get ɗin ƙuryar gidan sa, kasan cewar get huɗu a gidan nasa”.
Kallon Salman sukeyi wanda idon sa yake a watar sa kamar baya gurin.
Baban ya ce, “sai shekaran jiya ne Allah ya kawo mani Narjeesah da Amrah, muka haɗa ido dasu ne, a lokacin ne, nafaɗi ƙasa, kaina na juya mani, a take na some a gurin, ina farkawa na fahimci cewar nawo cikin hayyaci na”.
to kunji abunda ya faru.
Zufa su kawu suke gogewa, kallon Baban Inno tayi tace, “Alhamdulillah barka da dawowa Malam, sai kuma abunda ya faru bayan baka nan” a take Inno ta labarta masa komai.
Ai kuwa kallon kowa yakeyi a gurin yana gir giza kai, ya ce, “wato koda mutuwar ce, haka zakuyi wa iyali na, wula’kanci, Narjeesah! Narjeesah!! Narjeesah!!! Kuna nufin ita ƙaddara bata isa ta faɗa a kan ta bane ko miye kuke nufi? Ai ada na ɗauka, koda a ce da gaske cikin jikin Narjeesah da gan ganci ta same sa irin yanda kukafi kowa sanin ina son ta, to kuma zaku sota kuma zaku janyo ta a jikin ku, a hankali kuna nuna mata, laifin ta,
To yan dai bari kuji waye wannan Shuraim ɗin yaron Narjeesah wanda kuka tsana kuka kureta ida da ‘yan uwan ta, harda mahaifiyar ta, suka rasa matsu gunni, kuka basu wasu ‘yan kuɗi, wai gadon da suka samu ke nan, to kun ga wannan yaron Shuraim? “
Ya janyo hannun Shuraim ya zaunar dashi a jikin sa ya ce, masu “yaron nan ɗan halak ne kuma wannan yaron da kuke gani Narjeesah ta hanyar sunna suka sami cikin sa, kuma, shi jika ne, a gurin sarakai kafin nan Aliyu ku sanar dasu waye mahaifin Shuraim”
Gyara zaman Yaya Aliyu yayi yace, “Shuraim” labarin komai ya basu har sace sa zuwa yan zun, san nan ya sake kallon su, ya ce, “kun ga wannan”
Ya nuna Shuraim yace, “ga Salman nan shine uban Shuraim halak malak”.
Dukan su mamaki sukeyi wai a ce Shuraim ɗan gata gaba da baya, sukayi muna wannan walaƙancin haka?.
Salman kuwa haushin su yakeji, Inno ce da YAya da su Yaya Auwal Hanan da wasu daga cikin yan uwa na kawai yaji baya jin haushin su, tashi kawai yayi ya bar gurin yayi waje kamar wani kubu buwa.
Da sauri su Yaya Aliyu da Jafar suka mara masa, baya.
Inno ce ta ce, “Malam Shamsiyya da Atika ciki biyu sunayin kuma suna haifewa, ita Shamsiyya wannan cikin na jikin ta shine na ukku, duk da anso zubar dashi amman abun ya faskara”.
Cike da mamaki Baban ya ce, cikin fushi, wato……..
Comment And share
Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????
???????? NARJEESAH ????????
Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN
ELEGANT ONLINE WRITERS
Bismillahir Rahmanin Rahim
5⃣1⃣⏭5⃣5⃣
➿➿➿➿➿➿➿➿➿ “wato sune “ya’yanso ko? Basa laifi, ai ni a ganina duk yara na ɗaya suke a gurin ku kamar yanda nake ji a zuciya ta, Bala kai da ƙanwata da ke Larai kun cutar dani kun raba mani kan “ya”yana manya basa tausayin naƙasa dasu, ni kuma ba haka nabar ku ba, amman babu komai kunyi son ranku, duniya ce, gashi nan tun yanzun kun fara gani!”.
Kawu Bala yace, “kayi hakuri ɗan uwana sharrin sheɗan ne hakan ba zata sake faruwa ba “
Goggo ta ce, “haba ɗan uwana ai wallahi mu bamu da niyar watsaye maka zaman lafiyar da ka ɗora iyalan ka, shi yasa ma bamu siyar da gidan ba”.
Tsaki Muhseen Humaira da Hindu sukayi, ni kuma na ce, “andai ji kunya wallahi, a ce ya’yan ɗan uwan ka, kayi mugun tsana to taya ma zan yarda in saki jiki daku, kudai kawai a daiyi zumunci”.
Baban murmushi yayi, ya ce, “ba kuda bakin kariyar kan ku amman ina mai jin takaicin abunda kuka aikata mani, domin ni kuka to zarta ba wani ba, ke kuma Larai kin girbi abunda kika shuka ko? Nafi kowa sanin irin yanda kike ƙin Narjeesah amman na ɗauka ko da bayan rai nane zaki iya renin duk nin abunda na bari a baya na, amman ba bu komai a ga su Shamsiyya nan sun bar maki darasi, Narjeesah ƙarama ce, akan su Shamsiyya amman babu tausayi babu tausayawa keda yan uwa na da sauran yara na aka kora mani iyali, saboda idon ku ya rufe akan dukiya, to gani nadawo kowa ya dawo mani da abunda yake hannun sa indai nawa ne! “
Shiru duk sukayi sai zarar ido sukeyi da soshe_soshe.
Muhseen ne ya ce, Anty Narjeesh nifa haushin mutanen nan nake ji wallahi, musam man yan zun dana ƙa jin haushin su”
Dariya mukayi na ce, “duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a gare su, sai wani kame_kame sukeyi”
Fira akeyi tsakanin Inno da Yaya da Umma na yaushe gamo har suke sanar da ita cewar ai su yayan mu sunyi Aure, wannan sabon ɗakin da muke gani na sune, da matan su, Yaya Auwal ne da Yaya Anas ne basu yi Auren ba, saboda sun ce, sai Mun dawo ko suna dawowa cikin natsuwar su, haushin kansu sukeji, saboda kasa iya tsare muna wannan fitinar data faru da rashin adalci, sun je neman mu gidan da muka zauna ko suna da labarin garin da muka nufa? Maƙota sukace basu da labari, shine bayan kwana biyu suna neman mu basu same mu bane shine suka tuna da ƙawar Umma baba Luba, to sunyi nasarar zuwa gurin ta, sun gano gidan ta, amman kuma itama ta ce, dasu neman ku takeyi ta nemi yafiyar ku, domin saboda ita kuka zo garin amman hassada ta saka ta koreku, gashi ita bata da labarin, wasu ‘yan uwan ku, bayan kawu, haka suka dawo jiki babu lakka, to shima dai kawun Umma yana cikin tashin hankalin rasa, rike ammar da aka bashi saboda tsabar son zuciya , kun fa ji abunda ya faru “.
Amrah ta ce, yauwa Inno ina mutumen da ya tashi sace muna Shuraim ya turo muna yan daba, wanda shine silar barin mu garin nan? “
Ai kuwa da sauri Mariya ta ce, “number shi tana nan na amsa, mayar sa ta kusan bakwai neman ku, shi da yan daban sa, ala dole sai anfito masa da ɗan sa, bari na ɗauko maku number “
Tashi tayi ta shiga cikin ɗakin Inno mu kuwa murmushi muke sakar wa juna, Muhseen ya ce, “kamar ya ke nan?”
Nusaiba ta ce, “bari na baka labarin abunda ya faru” ai kuwa harda zufar sa cike da masifa ya anshi number wayar ya tashi ya fita waje Yaya Auwal ya mara masa baya.
A can ƙofar gida suka sami su Daddyn Shuraim tare da Shuraim ɗin yana maƙale da hannun sa, sai rigima ya keyi, duƙawa Salman yayi ya ɗauke sa, ya ce, “my friend miye ne mi kake so ne wai, wannan rigimar ta miye? “.
Dariya Shuraim ya yi ya ce, “Daddy ka bani sharabar da nace, maka ance na kawo idan kazo, kuma na ce shan bata”.