NARJEESAHNOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

NARJEESAH COMPLETE HAUSA NOVELS

Dariya suka saka masa, “a’a Shuraim yau kuma maganar ma irin ta shagwaba ce akeyi, to Allah ya taimaka man bashi tsarabar sa da sukayi rigima shida Inno ya kai mata”

Salman ya ce, “Aliyu yaron nan harda su cika baki yayi wa matan nasa ke nan? Eh lallai nabaka goyon baya, ka kai masu kada matan su kira ka miji marar cefane “.

Dariya aka saka Jafar ne ya buɗe motar yana dariya ya fara ɗauko masa ledodin masu zane kuma cike suke baya iya ɗaukar su, gashi leda ukku ce, riƙo masa sukayi har cikin Zauren gidan namu, suka rage yawan kayan suka bashi da ket yake tafiya su kuwa dariya sukeyi masa, da sallama ya shigo cikin gidan sai uban nishi yakeyi, duk muka amsa muka bishi da ido.

Dariya mukeyi ganin yanda yake ta uwar zufa, ya raɓa ta gefen mu yayi gurin Inno yana cewar, ” wai…! Wai..! Na gaji Inno ga sharabar ki na kawo maki, kuma bari na kawo maki sauran, Anty Nusy muje ki tayani ɗauko mata shauyan”.

Kowa sakin baki yayi yana kallon sa musam man yan da ya riƙe kun kumin sa, yana sauke numfashi, tashi Nusaiba tayi tana yi masa dariya ta ce, “wallahi Shuraim ka cika ran ganci yaro daga ɗaukar wannan yan kayan sai uwar zufa kakeyi da sauke numfashi a cikin wahala? “.

Baki ya turo mata yayi gaba abin sa ya ce, “ban ma so kada kizo nama fata dake”.

Auta ta ce, “Ai kuwa yaro sai nabika dan kaji daɗin kai ƙarata a gurin Daddyn ka ko? “

bin bayan sa tayi a cikin Zauren ne ta gan su ta anshi kayan tare da neman ta kira masu ni, a tare suka dawo ɗauke da kayan a gaban Inno suka ajiye, Inno ta ce, “Shuraim wannan aikin ai yayi yawa ko? Nifa da wasa nake yi “

Humaira ta ce, “Inno ko yan zun idan kina buƙatar wani abun kiyi bayani dan yaron namu akwai lafiyar kyauta”.

Dariya akeyi a gurin Yaya tace, “a a iyayen sa dai suke wannan aikin “

Hindu da Humaira da Amrah harda Auta shiga chapta da su Inno, zuwa can Auta tace, “Anty Narjeesh Daddyn Shuraim yana neman ki a waje”.

Ɗaure fuska nayi, kawai na share ta, kowa ya maida hankalin sa a kaina, Inno da Yaya cikin hasala su kace, “anya Narjeesah ba kiji mijin ki na kiran ki bane ko ya ya? “

Umma tac, “humm…!

Hindu da Humaira suka ce, “Inno sai kunyi da gaske fa, dan har yan zun haushin sa, takeji bayan kuma ta riga da tasan ƙaddarar suce a hakan bayan ma ta gode Allah da Mai martaba da yasa da Auren su wannan abun ya faru “

Ɗaure fuska Inno tayi, tace, kina tashi ko sai nasamu wani abun na jefeki dashi, ja’irar yarinya kawai “

Cin no baki nayi gaba, na tashi na ɗaure fuska na fita, waje. Baban mu ne yayi dariya ya ce, “Narjeesah manya in banda harkar ƙuruciya ina ke ina Salman keda Allah yayi maki babbar kyauta, ai kuwa kada kiyi wa kanki mugun abu, koda ace Salman a iya taimako na ya tsaya ai zaki so ki faran tawa wanda ya ceci rayuwar mahaifin ki a lokacin da kika kusa rasa shi, koda kuwa wannan farin cikin naki shine ya rage maki”

Amrah tace, Baba tanafa son shi, haushin da take ji idan Haulart tana yabon shi da mugun abunda takeyi masa, har jikin ta ke rawa sai nayi da gaske gudun kada ta bari kishi ya saka ta, ɓata muna aiki, kai Baba a ranar da muka shiga cikin gidan kasa bacci tayi, sai yawo takeyi a tsakiyar ɗakin da aka ware muna, sai faɗar take, wallahi ita sai ta ramawa Daddyn Shuraim wannan cin kashin kajin da akeyi masa”

Kun san Allah ce mata nayi, “Anty Narjeesh miye naki a ciki kedai mu ɗauki Shuraim shida yake namu kawai “.

Anty Humaira kin san yan da ta taso mani kamar ta dakeni ta ce, “ke mahaukaciyar ina ce halan, uban ya’yan nawa zaki ce na barshi a cikin wannan halin tare da wannan mummunar mata? To wallahi ni bazan iya barin shi tare da wata ba, sai dai ke ki ɗauki Shuraim ɗin ku tafi ni kubar ni na kwaci “yan cina ehe! “.

A da ido kawai nake bin ta, na zama wata wawuya dani, amman idan suka haɗu sai haushin wannan lokacin ya taso mata, sai ta murje idon ta kamar ba ita ba”.

Dariya suka saka, “Yaya ta ce, ai kuwa zamu riƙa takura mata da lurad da ita kada taje tayi saki na dafe “

Amrah tace, “shima fa halin su ɗaya wallahi idan suna a kusa da juna faɗa kawai ke shiga tsakanin su, amman idan bata a kusa himm..! “

Nusaiba ta ce, nice zan baki wannan labarin domin yayi maya ta kai goma neman ta, har sai da ya riƙa zuwa shida Salma da Muhseen, sune suka tambayi inda taje, mukace, bamu sani, ba cike da masifa ya ce, “da Auren nawa zata tafi wani gurin ba tare da izini ba? “

Nan dai sukayi ta bada labarin irin halin, su Inno da Yaya sukayi wani shiri akan mu.

Ni kuwa ina kaiwa zaure na haɗu da shi, shima cikin fushi ya janyo ni, jikin sa, ya riƙe ina ta son na kwace jiki na na kasa, yace, “uban waye ne uban sa a garin nan da zai ce zai rabani da ɗana! ? “

Na ce, to malam sake ni mana, nama ɗauka gamo ne nayi, ashe akan wan can shegen mutanen ne”

Ƙin sakin nawa ya yi, “na ce nifa ban ma taɓa ganin saba sai yaran sa, Amrah da Nusaiba ne suka taɓa ganin sa, sai Mariya, ko farmakin da suka kawo muna a cikin dare bamu gan su ba, dan maƙota sune suka ce ce mu”.

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, “to kuwa zai gamu da gamon sa, tun da ya firgita mani rayuwar iyalina, sai na ɗauki fansa, muje cikin mota muyi magana saura kiyi mani musu, ni kuwa na baki mamaki dan wallahi har cikin gidan zan shiga na ɗauko ki a jikina “.

Kallon sa nayi nace, “ai dama nasan zaka iya aikata hakan muje ni kada ka kunya tani dan ni nasan darajar mutane “.

Sakina yayi ya riƙe hannu na, muka jera muka fita, kallon mu mutane kawai suke, abokan Baban mu ne suka aika kiran sa, ya fito yayi ta gaisawa da mutane, tafiya mukayi, har jikin motar daya zo da ita muka shiga nida shi su Jafar kuwa a can cikin majalisar samari muka hango su.

Shiru mukayi nida shi babu wanda ya ce, uffan har tsayin wani lokacin motocin su na can gefe sun faka.

Wata mota ce gob3 ta iso ƙofar gidan mu a tsiyace, duk taci uban ta, ta bubbuge ta tsofe, sai mashin kusan bakwai, duk mutanen dake bisa moshin ɗin da na cikin motar ɗauke suke da makamai, sauka sukayi, suka fara ihu, na cikin motar ne suka fito suna busa taba, sigari.

Zaro ido waje nayi ina kallon ikon Allah, shi kuwa murmushi yakeyi wayar sa kawai yake shafawa, cike da tsoro na ce, “Daddyn Shuraim wannan mutanen fa irin sune suka tashi kashe mu, harda su Umma “.

Kallo na ya yi yace “to ke kuma keda kika je kikayo rigima kika ɗauko Shuraim yau kece da tsoro? Ki fita kawai ki zama jaruma dan sun sami labarin zuwan ki, kin ga yan zun ma sun zo ɗaukar Shuraim ne”.

Dariya nayi nace, “to su ɗauke sa mana, ai yanzun bani ce kawai abun zai shafa ba, dan gasu Yaya Jafar da Yaya Aliyu da Muhseen can idon su saboda harara kamar su fito waje, kai ni kallo ne kawai nawa”.

Shima kallon su Yaya Aliyu yakeyi, ai kuwa bai san lokacin da ya kama dariyar su, ba.

Ƙofar gidan mu suka suka yada zango, Yaya Auwal ne dasu Humaira Hindu da Amrah da Nusaiba su Mariya suka fito suna ƙare masu kallo, wani mummunan mutum ne ya tsaya a gaban su, ya ce, “ina take ina yaro na da aka gudu dashi? Dan yau ba babu wani tausayi ko ɗauke ƙafa, sai naje da yaro na, kuma sai nayi gun duwa_gun duwa da naman duk wanda ya hana mu ɗaukar ɗana! “

Cikin irin maganar yan tasha, da shaye_shaye yake maganar, dariya Yaya Auwal yayi ya dube shi ya ce, “daga cikin wannan wace, ce, uwar yaron naka duba da kyau dan duk suna da yaro a wannan lokacin? “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button