
Kallon kun raina mani hankali yakeyi masu, sai kuma ya tsare Humaira da ido ya ce, “ke kin ɗauka zan manta kine, to kin gama guje_gujen naki kin dawo ina yaro na yake ne? dan yau ko ki bani na tafi dashi ko nayi filla_filla da naman ki”
Mutane cike da mamaki suke kallon wannan mahaukacin mutumen kace, yaro naka ne amman kuma baka san uwar yaron ba, wata dariya ce, naji Salman nayi, harda dafe ciki da sauri nake bin sa da ido, cike da mamaki nake kallon sa dan yau shine farkon ganin sa yana yin irin wannan dariyar.
Buɗe motar yayi ya fito nima fitowa nayi su Yaya Jafar dasu Muhseen dasu Baban da yan gidan cikin gidan mu da maƙota duka gurin muka dosa, Humaira kuwa cike da haushi ta ce, “amman dai kai kam anyi jahilin mutum, a ce kai saboda tsabar jahilci da ƙarya da rashin hankalin wato kama rasa sanin wace haukar zakayi sai ta satar yara ai kuwa da kasan ko suwaye a gaban ka da kasan irin masifar da kajefa kanka, da kayi kuka da dana sani na shekara ukku zuwa huɗu dan ba ƙaramin bala’i ka jefa kan kaba, amman na lura da kai da wanda ka kwaso suka biyo ka daƙiƙaine wawaye, kida humai kun zo ku saci, yaro, yaron ma wanda baku san ɗan waye ba, to ina taya ku farin cikin zaman gidan yari tare da horo mai tsanani, dan naga ku mahaukata ne, baku ma gane ko miye nake nufi ba, Muhseen bashi yaron shi! “
Mutumen ya ce, “amman wallahi kin sa’a kina da kyau kuma har yanzun ina son ki, kuma naji kin ce a bani yaro na, amman da kin gane waye kikeyi wa maga haka, kai bani ɗana” yana mai kallon Muhseen kamar yanda Humaira tayi.
Dariya Muhseen ya yi ya ce, “Salman kazo yana neman ka”.
Aikuwa shima mutumen ya bushe da ƙatuwar dariya ya ce, “kunji sunan yaro na, wai Salman amman kin kyauta kin saka mashi suna mai daɗi”.
Wasu mutane ne wanda ban san lokacin da suka zoba, suka biyo bayan Salman yana ɗauke da Shuraim a kafaɗar sa, suna zuwa Salman yayi murmushi ya ce, “Shuraim duba ka gani su waye wannan mutanen? “
Ai kuwa Shuraim yana haɗa ido da wannan mutanen ya kwasa wani uban ihu wanda sai kowa ya rufe kunnen sa, da sauri Hindu ta janyo hannu na na ƙaraso a kusa da Salman na anshi Shuraim ɗin ina jijjiga shi dan yayi shuru, yana yayi shirun na sauke shi na riƙo hannun sa na ƙasa gurin na ce, “lallai yan zun nasan kowa ya fahim ci waye kai a wan can lokacin da naso su fahimci halin da nake ciki akan cewar ban san kaba, bani da wata alaƙa dakai duka basu yarda dani ba, sai gashi sabo da satar yara ta zama sana ar ka, ka saka aje har gida a kashe mu A ɗauko maka yaron, Allah ne ya kare mu, ya nuna maka shine ya haliccemu, mu dakai ya kuɓutar damu, a hannun ka, muka bar garin mu mahaifar mu saboda kai, shine yan zun dan ɓatan basira kazo ƙarasa nufin ka, kuma baka ma san uwar da ta haifi yaron ba, mutane yan zun kowa ya shaida him lallai duniya! “
Zan ƙara magana Mariya ta ce, “to andai ji kunya duk wanda ya baka shawarar nan kwanyar kifi ne dashi, kaga wannan ba ita ce kake nema ba wannan ce kake nema, ga kuma yaron nan “
Ta nuna Humaira dani da Shuraim, sannan tace dashi, “kazo kana wani zaƙewa da hura hanci kai ala dole aji tsoron ka, to ga uban yaron nan a gaban ka shine Salman ɗin da kaji a na faɗa, wawa kawai “.
Salman kallon wannan mutanen yayi wanda suke bayan sa, “da sauri suka kewaye su, suka fito da bindigogin su, suka ɗora a kan yaran sa, dashi kansa aka nuna masu aid card, tare da faɗar kidnappers, your under arrest “
Dur ƙusawa ƙasa sukayi suka ɗora Hannuwan a ƙeyar su, sai kuka wasu sukeyi, dariya aka sanya masu, Salman ya ce, “mu haɗu daku a kotu, nine mijin Narjeesah kuma nine mahaifin Shuraim Salman Muhammad Yunus ke nan, jika a gurin Mai martaba Sarki Yunus, kuma ni loya ne mai zaman kan sa, wanda ƙasa take alfahiri dani, mahaifina kuma Muhammad Yunus ambassador ne, ina fatan ka fahimci ɗan waye kake son yin kidnapped ɗin sa, ku tafi dashi “.
Magana mutumen yaso yi gurin bada hakuri amman babu wanda ya kula sa, hannu na Salman ya kama muka nufi cikin gidan haka su Humaira su Yaya Jafar suka tasa su a gaba sai cikin gida.
Kowa dole ya watse mutane cike suke da mamakin a ina na haɗu da Salman gashi, koda ganin Shuraim an san ɗan sane, a cikin gidan kuwa muna shiga na nufi cikin ɗakin Inno nayi kwanciya ta, tsakiyar gidan sai firar haukar wannan mutanen sukeyi su Salman kuwa suka bar garin suka bar mu, tunda na samu labarin basa nan na fito akaci gaba da fira dani.
Kwanan mu biyar muka shirya muka nufi gidan Kawun Umma, zo kuga yanda ake yin ina nakan a za daku, jin sukeyi kamar su goye Umma sai hakuri suke bata, har dare muka kai, sannan muka dawo gida.
Yau tun da safe aka fara kawo mani tantabu masu romuwar magani, ai kuwa nace, Inno a gaskiya daga ganin wannan abun zaiyi ɗaci, nikam ba zan ci ba, haka kawai naje na ɓata baki na”.
Inno ta ce, “ci kuwa kamar anyi an gama ne, da alama kin soma man tawa da halina, ko? “
Jan kwanon nayi a gaba na, na soma ci ina zubda hawaye, su kuwa dariya sukayi Hindu ta ce, “kada ki ci ƙashi malama kuma kisha romuwar da yawa kinji matar Salman ” ta kashe mani ido ɗaya.
Harara na zabga mata, sai da na ƙoshi na fara yun ƙurin amai sannan aka ajiye sai zuwa anjima, tsimi Yaya ta kawo ta tsare ni babu musu nasha dan nasan halin Yaya.
Haka sukeyi mani kullum wata rana harda su Humaira a gurin ci, ko sha.
Kwanan mu goma sha biyu a gidan mu, Mariya tayi muna zanen lalle ja, da baƙi, Hanan tayi muna kitso, gyaran jiki kam kullum sai anyi maganin mata sun ishe ni, da kayan fruit da su Yaya Auwal suke kawo wa ni abun harma tsoro nake ji gashi a jiki na tabbas naji chanji sosai.
Turare humra kayan ƙamshi kuwa kawo wa akeyi yan uwa da abokan arziki, yau muna zaune a ɗakin Inno harda su Baba da su Yaya Auwal ana fira nake cewa, “Yaya Auwal dan Allah su Inno su tashi garin nan su koma gidan mu da yake a garin Yola inda muka fito wallahi babban gida ne kuma akwai ɗakuna da yawa, ko Amrah? “
Cike da farin ciki Amrah tace, “wallahi Yaya gidan zai ishi kowa dan kowa zai samu nasa ɗakin “.
Hindu da Humaira da Auta suka ce “Allah da yafi kam dan zamu fi jin ɗadin ganin ku a tare da mu, dan kada abari zumunci mu ya lalace “.
Shiru duk sukayi Umma ta ce, “Inno to ku yarda mana tunda gashi wannan gidan yan zun yayi kaɗan saboda yara sun fara zama a cikin gidan su”.
Yaya tace, “a gaskiya hakan ba zaiyuyu ba saboda gidan Shuraim ne da Nargeesah taya zamu yarda muje gidan yara mu zauna haba dai ku duba ku gani “.
Da sauri nace, “Allah Baba ku yarda na mallaka maka gidan Yaya Auwal kuma na mallaka maka mota ɗaya a cikin motocin nawa, dan Allah kuyi hakuri ku yarda”.
Cike da mamaki suke kallo na, Amrah kuwa da Humaira da Mariya da Hanan rungume ni sukayi, suna dariya Anty Asma tace, dan Allah Baba ku anshi wannan kyautar da tayi maku Allah nikam naji daɗi sosai “.
Yaya Auwal kuwa cike da mamaki yake kallon kowa a gurin wai kyautar mota kodai mafalki ne yakeyi?.
Baban mu ya ce, zamu ansa mana Narjeesah amman sai kin anshi tayin mu bada tursa sawa ba, tukun”.
Da sauri nace, “Allah zan yarda da duk abunda kuka umarce ni, tunda har kune iyaye na kuma Inno da Yaya basu gujeni ba, har bayan rashin gatan da nayi da ƙaddarar da ta afka mani, lallai ni kam mai biyayya ce a gare ku”.