
Jikin kowa sai da yayi sanyi amman Inno ta daure tace, “Narjeesah kiyi wa kiyiwa Shuraim gatan komawa gidan Salman ku riƙe yaron ku da kyau yanda zaiyi farin ciki mai ɗaurewa”.
Da sauri na ɗago ido ina kallon Inno da duk wanda yake cikin ɗakin naga duk idon su yana a kaina, duƙar da kaina nayi ƙasa da ket na buɗe baki na ce, “indai wannan shine burin ku na amin ta, wallahi Allah yasa hakan shine mafi alkhari! “
Amin duk suka amsa cike da farin ciki Yaya tace, “to yau she ne kike son mu koma gidan Narjeesah? “
Da sauri na ce “Yaya duk ranar da kuka shirya, zamu iya tafiya “.
Cikin sanyin murya Mama tace, “nikam nasan bani da masauki a gidan saboda abun da na aikata maku, sai nace Allah ya kaiku lafiya Allah ya sanya alkhari “.
Nidai ban ce komai ba Umma ta ce, “Larai ai duk abunda ya faru yari ga da ya wuce, miye amfanin dawo da abunda ya wuce baya, kin fi kowa sanin yanda muke da yanda malam ya koyar damu yafiya da maida komai ba komai ba, dan haka abar komai dan Allah a fuskanci gaba, kawai, anriga da an zama ɗaya, babu yanda za’ayi “.
Kuka Mama ta fashe da shi ita da yaran ta, Anty Basira ce ta ce, “Umma mun gode da haƙurin ku haƙiƙa ke mace, ce, abun koyi a cikin duniyar nan muna godiya da halaccin ki a gare mu “.
Inno ce tayi murna da wannan sabuwar rayuwar ta ce, “to Narjeesah muna godiya sosai zamu tashi wannan gidan mu barwa sauran yaran mu da sukayi Aure, ke kuma da mun koma zaki bi mijin ki, ku ɗauki ɗanku ku tafi dashi Allah yayi maki albarka ya huci zuciyar ki, ya ƙara maku haƙuri ya baku zuri’a ta gari mai albarka, mun gode sosai Narjeesah yar Albarka keda sauran yan uwan ki da abokan ku duk Allah ya albarkace ku da iyalin ku baki ɗaya “.
Duk muka amsa da, “Amin ” Baban mu kuwa farin ciki kawai yakeyi, su kawu da goggo kuwa, hawaye suke sharewa.
Haka akaci gaba da fira, kullum cikin farin ciki muke shirye_shiryen tafiya akeyi mutane sai zuwa taya murna sukeyi Shuraim kuwa tun da safe idan yaci abinci akayi masa wanka bana sake saka shi a idona sai dare idan yayi bacci.
Yau tun da safe Humaira take sanar damu su Salman suna a hanya, tun a lokacin nake jin wani irin, ganin idan fa yazo zan bar su Umma dasu Amrah da gani sai Shuraim, kawai naji kuka ya zo mani.
Sun fahimci abunda nakeyi wa kuka dan haka suka shiga bani baki.
Ƙarfe goma na safiya suka iso nasan kuwa a garin mu suka kwana, tare da motocin ɗaukar kaya suka zo, ai kuwa aka shiga fitar da kayan mota ake saka su, gidan gaba ki ɗaya muka fito motoci muka shiga, aka rufe gidan muka ɗauki hanya……..
Comment and share
Ummu Ihsan ce????????????????????????????????????????????????????????????
???????? NARJEESAH ????????
Rubutawa
NANA KHADEEJATU
UMMU IHSAN
ELEGANT ONLINE WRITERS
Bismillahir Rahmanin Rahim
????
5⃣6⃣⏭️6️⃣0️⃣
➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Alhamdulillah mun iso lafiya cikin amin in Allah, tun lokacin da muka ɗauki hanyar unguwar mu, su Mariya aka fara buɗe ido, suna kallon yanayin unguwar, bamu tsaya ko ina ba, sai bakin kofar gidan mu, su Yaya Aliyu basu ma shiga cikin gidan ba, sukayi tafiyar su, mu kuwa fitowa mukayi, muka dum fari bakin get ɗin mu, na fara ƙoƙarin buɗe get ɗin, duk da ido suke bin mu cike da mamakin ganin irin wannan haɗaɗɗen gidan.
Kasa hakuri Yaya tayi tace, “anya kuwa Narjeesah gidan ne kuwa? “
Murmushi na sakar mata, ban bata amsa ba, har na buɗe gidan Shuraim da gudu ya riga kowa shiga, su Yaya Auwal suka ɗauki kayan suka mara masa baya, Umma kuwa ita ta yiwa su Inno jagora suka shiga cikin gidan kwasar kaya muka tsaya yi, na baiwa Auta makullin ƙofar falon, ai kuwa da sauri ta shiga ciki dan ta buɗe masu ƙofar, muka ɗauki kayan muka mara masu baya, a bakin kofar falon na ajiye masu na dawo na rufe get ɗin, na juya na shiga cikin falon.
Koda na shiga duk sun baje a tsakiyar falon wasu a kujeru wasu a ƙasa, nida Amrah Nusaiba da Humaira da Hindu muka haye sama, ɗakin Umma muka shiga muka kwashe mata kayan ta, muka dawo dasu cikin ɗakina, muka shirya mata komai nawa kayan kuwa a akwati suka zuba su, da kayan Shuraim.
Bayan mun ƙarasa ne, muka fito muka shirya wa Inno nata, ɗakin inda muka kwashe kayan Umma, a ɗakin kusa da Inno muka shirya wa Yaya nata, haka Mama ma mukayi mata, muka sauko Amrah ce ta sanar dasu, suje ta nunawa kowa nasa ɗakin, haka kuwa akayi Mariya a ɗakin su Amrah aka kai nata kayan, su Zuwaira Shamsiyya nasu ɗakin daban.
Su Yaya Auwal kuwa a ɗakin ƙasa suka zaɓa sai farin ciki suke yi Baban mu ma ɗakin sa yana sama yana daga gefen nasu Inno.
Kai Alhamdulillah gidan kam sai sam barka kowa ka gani a cikin farin ciki yake, kamar wanda akayi wa albishir da kujerar makka.
Bayan komai ya dai_dai tane, su Humaira suka tafi, gidan iyayen su, mu kuwa duk yam matan a kicin muka haɗu domin shirya abinci, saboda basu san takan komai ba hakan ya saka muka dage gurin koyar dasu, bayan mun kam mala ne, Zuwaira Basira da Shamsiyya suka ni a gaba suna ƙara neman yafiya a gare ni, nikam na ce dasu, “na riga da na yafewa kowa dan Allah abar tuna baya”.
Godiya sukayi mani, haka muka yini cikin farin ciki muka tashi cikin farin ciki, su Mommyn su Humaira da Hindu da Haleema, duk sun zo tare da yaran su, sosai suka nuna farin cikin su da jin daɗin su, akan dawowar familyn mu guri ɗaya.
Bayan kwana biyu, muna zaune anata fira, nace, Yaya Auwal gafa motoci nan guda biyu a harabar gidan nan muje ka zaɓi wadda kake so, ɗayar kuma su Yaya sai ku san yanda zakuyi da ita, dan nikam na mallaka maku ita halak malak amman Yaya Auwal shi ɗaya yake da wadda ya zaɓa”
Cike da farin ciki muka doshi harabar gidan ai kuwa Anty Asma da Anty Basira suka zaɓar masa, shi kuwa kukan farin ciki yakeyi musam man lokacin da na bashi makullin motar su kuma na basu makullin ɗayar.
Yau ne a tarihin rayuwa ta naji Mama ta kama hannu na, ta rungume ni, tana zubar da hawaye tana faɗar, “haƙiƙa ɗan hakin da ka raina shine yake tsone maka ido, haƙiƙa ko wane ɗan adam Allah ya rubuta masa arzikin sa, a haƙiƙa zafin nema baya kawo samu, tabbas hassada gamai rabo taki ce, na yarda da wannan Narjeesah tun daga lokacin da Allah ya nuna mani, cewar bani da dubara kuma babu wanda yake tserewa ƙaddarar sa, kuma yan zun na ƙara yadda da cewar, mutum yana tare da arzikin sa, Narjeesah gashi Allah ya nuna mani da ido na, cewar ke ɗin dai da nake fatan naga kin dauwa ma a cikin baƙin ciki, sai gashi Allah ya nuna mani, ke baiwar sace, shine mai tsara komai akan bayin sa, gashi dai a ƙarƙashin ki yau muka dawo, ina riƙon Allah da ya yafe mani,
kuma kema ki yafe ni, kada kiga laifin yan uwan ki na rashin sonki nace na ɓata ki a gurin su, ada ina dariyar kinyo cikin shege duk da na fahimci kin ɓiye wa kowa gaskiya ne, kuma ni kaina na fahimci cewar cikin jikin ki, ba shege bane, tun lokacin da na fara shegan ta cikin na fahimci hakan amman a lokacin bana sonki da farin ciki shiyasa nayi ta, zagin ki ina saka kowa ya kyace, ki, Narjeesah tabbas duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba, to shi tashi tukunyar ko zafi ba zatayi ba, kuma tabbas na yarda da cewar mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege dan bai sani ba ko ya haifa, sai gashi ina zagin ki ashe nima a cikin ɗaki na, akwai shegu har huɗu, dan Allah kiya feni wallahi haƙin kine yake bibiyar rayuwar mu…